Showing 72001 words to 75000 words out of 105161 words

Chapter 25 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13426

ya dane tare da lekowa a hankali,sai
yaga mata biyu saboda duhu gashi baya so Amana ta farka tayi ihu ya kasa shafa jikinta,haka
ya shiga gidan ta saman Katanga sadab sadab ya shige cikin Net din Umman Amana ya zata
Amana ce, kawai ya ya kara shigewa jikin Umma sosai ya fara shafa jikinta,Umma cikin bacci
taji ana shafata ta manta Sulemanu Harka ya rasu cikin magagin bacci tace

uhhmmm......Sulemanu....Sulemanu a'a....a'a mene haka Sulemanu,kaji jarabar taka ko,Da
gudu Deeni kwaro ya fito fit kamar walkiyya Umma ta dawo hayyacinta ta jawo rigarsa baya ai
kuwa Deeni kwaro ya cire rigar cikin zafin Nama ya barwa Umma a hannunta ya tsallake ta
Katanga ya fece,
Umma ta fara kuka da kurruwa Sulemanu ya jawo mana yayiwa matan wasu wlh dole ayiwa
nasa wani tsohon zan samu na aura kafin wani ya min Illa ohhh yau na gane da saurana Ashe
saurayi haka na bi na ai sai aure,
Tashin Amana tayi tace tashi dan Ubanki mushe kina can wani zaimin fyade,bazan iya zaman
nan ba wani satin zamu koma gidan Babanki gwara gidan Mirgayi wlh ina gama takaba zan
samu sakarkarin dattijo na aura domin ubanku ya jawo mana sai mun tsare mutuncinmu.

Amana sabo da murna harda tsalle da kyar ta iya bacci sabo da murna zata koma wajen yan
uwanta,murnar Amana dayace tasan dole bikin Huzaifa da Badriyya Alim zai zo ko don Huzaifa
to dole ta ganshi ko taji sanyi.
Malam Nuhu kuwa dadi yaji zasu bar masa gidansa wani satin.

Alim duk abin duniya ya masa Zafi shirye shiryen bikin Huzaifa sukeyi kuma shine kan gaba
shi ya tsaida dashi zuwa Adamawa neman Amana.
Washe gari Amana ta tashi fes cikin tsananin murna,karin Jin dadi n Amana Umma tace ta
daina talla kudin da suke dashi ya ishesu har su koma gidan Baba Mirgayi.
Yau Amana ta fita siyo kayan miya a hanya garin tsallaka kwalabati kafarta ta goce ta fada
katon Kwalabati marar ruwa cikinta ya bugu sosai nan take cikin ya juya sai jini ya yanke mata
sosai yake ambaliyar fita daga kasanta,Amana ihu takeyi tana wayyo Allah dana dana zai mutu
na shiga uku dana wayyoooo dana kar ka tafi me kama da ubansa,kai nake sa rai zan haifa na
dinga ganinka kamar babanka 'yata ko dana me kama da Alim dina,
Gudan jinin Alim,zarota mutane sukayi da kyar ta kara dafe cikin taci gaba wayyo dan Halak
dan Alim,wlh Alim ne yayi cikinka mijina Alim a gidan aurenmu,Ka tallafamin kaine shedata da
zan wanke kaina wajen babanka,
Deeni kwaro ne ya taho da gudun tsiya masoyiyarsa ta samu matsala yace mahaukata kun
tsaya my love tana gabanku shinfide cikin wani Hali kun kasa kaita asibiti sai kallonta kukeyi
kuna kallon daga inda jinin ke fitowa kuna Jin dadi kuna kissima surart a zuciyoyinku,to gurin
yafi karfinku,daga wanda yayi mata cikin sai nine kadai zan San wajen nan,
Amana dai ta fara fita daga hayyacinta sai nishi takeyi tana Dan Alim...shedata...dan Alim
Habawa ai tuni Deeni kwaro ya Sureta tare da tare napep sai asibiti.




AsmaBaffa

Tnx alot readers.

CIRANIN AMANA


160-165



Official




By
AsmaBaffa






Dukkan yan AsmaBaffa fans club godiya gareku da jinjina.love u all






Da sauri Deeni ya shiga da Amana cikin wani private hospital nan danan akayi emergency
da ita likitoci suka rufa a kanta,komawa Deeni yayi tare da sanarwa Umman Amana da Malam
Nuhu,a sukwane suka rufta asibitin,Umma sai kuka takeyi tana ohhh na jawo miki,na jawo miki
masifa Amana Ashe kaddarace ta kawoni na daukoki nan Adamawa, Deeni ne ya biya kudin asibiti da komai da aka bukata domin Deeni kwaro akwai neman kudi
baya talauci..

Duk iya kokarin da likitoci sukayi dan ganin Cikin Bai fita ba amma abu yaci tura domin tun
kafin ma a kara so asibiti ciki ya zube,dan haka suka mata wankin ciki,sai allurai da magunguna
na Karin jini da sauran abubuwa,Deeni Kwaro kuwa maltina carton 3 ya kai da madara peak ta
ruwa kwali biyu,sai kuma kullum da kalar naman da yake kaiwa asibiti wajen Amana. Amana kuwa bata magana sai yanda akace da ita,da ance yi zata yi bari zata bari,kai ko
gabas kace kalla zatayi,arewa,kudu,
Sai hawayen da basa tsaya a idonta,tasan yanzu ita da Alim sai a darul salam dama da cikin
ta dogara idan ta haifa dole zaiyi ko kama da Alim sai ya San da gaske shine Ubansa to gashi
ya zube.

Umma kuwa ko a asibitin gasa Amana takeyi sosai tana gyara ta cike da tausayi,
Satinsu guda aka sallamesu,Deeni kam yayi Namijin kokari,sai yanzu ya gane lallai son
Amana yakeyi,kuma yaji labarin tana da aure,hakan yasa ya tattara soyayyarsa da kwadayinsa
ya kara gaba dan karma ya dinga ganin Amana yana Jin wani abu ya koma daga gida sai wajen
aiki,sanadin hakan Deeni kwaro ya daina halayen banza ya samu shiriya Sanadiyyar Amana
me Kunu,Amana ma batasan yana yi ba,sunje dai har gidan su Deeni sunyi Godiya sosai,sai
lokacin Maman Deeni ta basu labarin Deeni da komai har shiryuwarsa sanadin Amana,ai nan
take ya birge Amana ta dinga yi masa fatan alkhairi,Amana ta bashi Address dinsu na gidan
Baba.Deeni dai ya karba kawai amma bazai je ba tunda Amana Nada aure, kuma ga kunyar
shiga net din Umman Amana da yaya satin Amana biyu cif da yin Bari yanzu kam Umma
gyarata tayi sosai a saboda Shan madarar rakumi da sauran Abubuwa yasa Amana ta maida
jikinta tayi sumul sumul tayi kyau na ban mamaki sabo da kayan da Umma ke bata tana ci da
Sha na gyara,

Itama Amana saboda kullum cikin sa rai take zata hadu da Alim dinta yasa take yarda da
gyaran sosai,kai ba kace Amana ta taba aure a duniya ba yanda ta kara komawa kuma gashi
kullum dai sai tayi kukan rashin Alim amma a hakan ba laifi ramarta kadan ce ta rashin mijin ta.
Saura kwana Uku su koma gidan Baba Sulemanu Umma ta samu Amana tace na dauki
Number Hamza dake littafi jiya na ari wayar Malam na kira shi mun gaisa sosai duk sunce a
gaisheki,bikin Sakina da Badriyya Saura kwana 5 biyar a fara kinga zamuje a dai dai,Badriyya
tace na fada miki ta kai miki dinkunanki cikin Kano za a yo miki,wai ya cikinki na basu Labari ya
zube da abinda ya faru,sunyi jaje sosai,
Murmushi Amana tayi tace Umma bari naje gidan su Nusaiba ayi min dilka da halawa,Malam
Nuhu shi ya bawa Amana kudin,Amana kuwa gaba daya kwana Ukun nan a gidan gyaran jiki
take yini,ko ina ta gifta kamshi take bari me dadin gaske,skin dinta tayi smooth sai sheki da
kyalli takeyi,duk wannan Alim takewa tanaji wai ko zai ganta ya ganta bata lalace ba ya ganta
har yanzu fa za a je da ita,yaga bata ci baya ba,kuma duk sabo da tsaro bata San ya ta Allah
zata kasance ba ko Alim zai yi tunani ya daina zarginta ya maida ta wajensa kunga kenan a
shirye take,dama kuma kun San Amana bata son raini akwai son har kar wanka da gyara hade
da tsabta.

Umma tace kinga gobe zamu tafi ko zakiyo lallen bikin?Amana tace a'a Umma salon ya goge
ma da wuri kenan ai sai naje can zanje har cikin Kano city ayi min na kece raini,
Duk sabo da Alim Amana ake wannan cakarewa.

Ta wani bangaren Amana tana Jin haushin Alim sosai yanda ya manta da ita duk zaman da
sukayi,ya kasa tunani akan abinda ya gani,ya zargeta,har ya yarda zata iya cin Amanarsa,
Uhmmmmm Amana ta furta a fili tace Namiji kenan me manta alkhairi,ka shekara kana aikin
me kyau rana daya ta baci ba mutunci...wai ni Alim zai yarda Ina bin maza,wai Alim ya gujeni ya
manta Dani,lallai a duniya anything is possible shuru tayi tana ta tunani,
Maybe idan Alim ya ganta ma ko kallonta bazai yi ba ya manta da rayuwarta,wani Hawayene ya
zubo mata masu Zafi,ganin Umma na kallonta yasa tayi sauri ta fada daki ta kwanta tana ta
shesheka har bacci ya kwasheta.

Alim kam bangarensa sai duai domin yafi Amana shiga kunci yaje Har Adamawa ya gama
bulayi baiga Amana ba ya dawo ya dage da addua sosai na tabbata da Alim Bai rungumi addua
ba shima da tuni ya haukace ya zare.amma a haka idan ka ganshi sai ka dauka bashi da
matsala haka Addua take da yawan karatun Qurani yan uwa mu dage da Addua karatun Qurani
shine magani.Alim gaba daya sun rankaya sun taho Kano bikin Huzaifa aboki kuma dan uwa.

Baban su Huzaifa part guda ya warewa Amare da kawayensu haka angwaye da abokai
nasu daban duk cikin gidansa sabo da Amare Sakina da Badriyya ba a cikin Kano suke ba su
kuma angwaye a cikin birni suke saboda dinner kala uku da angwaye suka shirya yasa Abba
yace Amare da kawayensu su taho gidansa angwaye ma haka har mijin Sakina sabo da shima
sanadin zuwa zance suke haduwa da Huzaifa har zumunci ya kullu tsakaninsu tare suke shirye
shiryen komai,Alim kuma shi ya shirya musu party har kala biyu,Abban mijin Sakina ma ya
shirya musu daya.don haka duk shagalin biki gidan su Huzaifa za ayi shi,daurin aure ne kawai
za aje gidan Amare a dauro,su kuma iyaye mata suna can zasu Kula da jamaarsu ta gari.
Alim sabo da zaman mutuncin da sukayi da Amana da kuma sonta da yakeyi yasa kaf mazan
da matan gidan da yara yayi musu dunkuna na alfarma manyan mazan kala Uku uku yaran kala
biyu biyu,har iyaye har Umman Amana ya bayar da nata a Dinka a ajiye mata,Amana kuwa ya
Dinka mata har kala Goma da takalma da jakankuna da mayafai tsakaninsa da Badriyya sukayi
sirri yace tace wai Huzaifa ne ya Dinka mata itama kar ta fada shine,Badriyya tace to bakina
kanin kafata,a halin yanzu Huzaifa yasan Alim da Amana basa tare amma duk ya tambayi dalili
ba wanda ya fada masa har Badriyya kawai sai ya kyaleta.
Kayan abincin biki kaf Alim ne ya saukewa su Hamza shi da kudin kayan dakin Amare,amma
Sam Angwaye sukace kar a kawo Amare da cokali sunyi komai nasu.
Alim ya karbi kudin ya siyawa Hamza da Kabiru kb fili kato guda biyi a Na'ibawa Kano,sun
Hamza harda kukan dadi za a koma City,
Yacewa su Haladu ma za a basu nasu suyi aure shi kuma Huzaifa yace zaiyi tallafin Gina
gidajen nasu,Ishaq Saurayin Sakina yace shi kuma zai zuba musu furniture,wannan murna
kawai sukeyi suna cewa duk A sanadin Amana suka hadu da wannan alkhairi,Ciranin Amana
ciranin alkhairi,ta yo musu hanyar arziki gaba daya gidan,domin ta hanyar su Alim kadai Alkhairi
ke fado musu,

Allah sarki Amana ana nan ana Jin dadi ta sanadinta ita kuma tana can ma ba ita ke Jin dadin
ba haka ikon Allah yake.
Saura kwana biyu a fara biki misalin karfe biyar Amana da Umma suka kwado Sallama cikin
gidan Baba Sulemanu,
Kaf gidan suna nan ana ta shirye shirye,nan kowa ya tashi da ihu ana rige rigen rungume
Amana,Mazan kuma suka tafa tas tas da Amana suna ta kashewa ana dariya,da karfi Amana
tace surprise no going back sai ihu yeeeeeee,Amana ta rike kugu tare da juyawa ta furta look at
me ? Ya kuka ce heeeeeee wlh a basu wuta,Amana tace ai da girma ya fadi gwara na kwana da
yunwa,nan suka hargitse da murna yara da manya Amana ta dawo gaba daya,kowa sai cewa
yake I missed u Sis,yaran gida suka hada baki we missed u Anty Amana,murmushi Amana tayi
tana daukansu daya bayan daya tana ajiyewa,

Nan fa aka fara labarin bayan rabuwa daga nan suka bawa Amana labarin komai na yadda
suka shirya biki,suka bata labarin yadda Angwaye da iyayensu suka taimakesu sosai da kawo
agaji,a karshe suka fara bata labarin kaf alkhairan da Alim ke musu,suna fada mata Amana
kuma bata San sanda Ruwan Hawaye ke bulbula a idonta ba, Yana yin wannan taimakon a danginta amma Bai taba tambayarta ba lallai badan ita yakeyi
ba don taimakon Allah yakeyi,ba komai hakan ma an gode masa cewar Amana.
Lallashinta akayi sosai harda su Gwaggo,Umma kuwa tuni ta sa kayanta a dakinta ta yi sallah
ta huta ta fito wajen kishiyoyinta sukayi hira sannan ta basu hakurin abinda tayi,sannan tayi
musu godiyar Kula da yaranta da sukayi,
Gwaggo tace ba komai ai daki har yau nakine tunda yakice ta siya,mukan munji dadinmu
arziki sai bunkasa yakeyi ta hanyar mijin Amana nan suka bawa Umma ma labarin,umman
Amana ta saki baki tare da cewa ohhh....rashin rabo ya sa na tabi ina ta Shan
wahala,iyyyeeeee kuce sai cin jar miya da zaki,Inna tace ah mu sai Sam barka Allah ya kai
gaban Annabi,wannan yaro Allah masa Albarka,Hajiyayye kuwa daya matar ta shanye hannu
tare da bugar cinya tace ai dadi ya barki baki ga yanda muka canja ba harda dunkuna naki yana
wajena kala Uku Alim Bai manta dake ba harda ke,
Umma ta rike haba tace oh kinjiiii na gudu na bar ladana,to ai ta faru ta kare yanzu mun dawo
kenan,gwaggo tace af wa yagaya miki barni gabas take gane min hanya yar uwa cewar
Hajiyayye.

Amana kuwa Badriyya ta jawo akwati guda na kayan Alim da ya dinkawa Amana,Badriyya
kuma ta cika alkawari tace Huzaifa ne yayi mata Amana tayi mamaki tayi godiya sosai.
Tace dan Allah ki fada masa idan kunyi waya to kawai Badriyya tace,

Badriyya a cikin wayoyinta biyu ta bawa Amana daya tasa sim dinta da memory wayace me
kyau,sosai yanzu gidan Sulemanu suka kara nutsuwa suke zumunci,suka samu zaman lafiya
ba a ware kowa.
Dama sai ba wani wasu zasu gyaru,ranar da wani ke kukan babu wani shi kuma ranar yake
samun nasa kudin.
Sai yaba kyan da Amana tayi akeyi,kowa kallonta yakeyi har yan uwanta mamaki
sukeyi,Amana ta kara gogewa ta Zama mace sosai,
Wannan bacin ran da ta shiga yasa ta Zama miskila,bata magana irin da,ba fada ba
masifa,amma duk da haka me Hali baya fasawa watarana sai an dan gwadashi,

Alim kam rashin Amana da halin da yake ciki yasa ya tashi daga miskili, shuru shuru,
mararar magana, ya dawo kasurgumin masifaffe number daya,abu kadan zaka masa ya zage
yaci mutuncinta,ko maganar arzikice sai ta koma fada a wajensa,kullum cikin hade rai da bakin
ciki yake, Ko Aabid yanzu tsoronsa yakeyi da yayi abu zai ci Ubansa,Duk yan gidansu basa ma ganin
fara'arsa,bare Mum da yake gani ita ce ta jawo komai.
Mum kuwa bata zo Kano biki ba sabo da bata son dangin miji,tace ranar yini zata zo a flight
ta koma da yamma.

Ana gobe Amare zasu dawo Kano a fara biki angwaye tuni ma sun fara zuwa domin wasu
duk daga kasar waje suka sauka,sai na wasu state duk sunzo,Alim yana cikinsu sun cika a Palo
yana kwance a 3seater baya magana duk hirar da sukeyi,bacci kuwa ya daukeshi Bai Dade da
bacci ba ya fara mafarkin Amana,Yana ta dariya a mafarki yana washsh....Amana zaki
kasheni,sai yayi dariya yace my wife I love u,do u know what? Can yayi shuru sai sukaji yace I
missed u,
Mika ya karayi ya ci gaba da mafarkinsa yana ta furta I love u.......I missed u......sai hawaye
zirrrr zirrrr ta idonsa suna ta gangarowa yana I missed u kuka na kara yawa,sai yi yake ta
yi,yayan Huzaifa Ahmad ne ya danawa Alim duka tashi banza na mamajo,zumbur Alim ya tashi
yana taba fuska alamar Bai San ma yayi mafarkin ba,sai da ya nutsu ya tuno mafarkin Amana
ya kara yi dama kullum aikinsa kenan,da masifa yace mene haka zaka tashe ni,Ahmad yace to
dan iska kaje can wajen Amana ka sauke gajiyarka da kwadayinka zaka zo nan kana mana
kukan banza da wofi,mayen mata kawai manniru,kwana dayan ma baza ka hakura ba,me yasa
Baka taho da ita ba kasan Baka iya Zama saida ita,Alim ya cika tam amma ganin mutane sai ya
share zance sai tsaki da yaja kawai yana turo bakin shagwaba kamar mace,Ahmad yace
Allah....sannu Ayu....mu zaka kawowa iskancin shagwabarka nan to bada mu ba kaje can
gaban Amanan ka mata, Huzaifa yace pls Babban yaya a kyaleshi haka.

Gobe dai za a fara party daya dan haka Amare da kawaye yan makaranta hadaddu Sabo da
Badriyya duk kawayenta yan cikin birni ne bata kula na kauye,Sakina kuwa nata duk yan
makarantar boarding schl dinsu ne,sai da suka zabo gogaggun yan wanka da masu kyau
hadaddu su suka gayyata dinner saboda kar a lalata musu party,tuni Ishaq ya turo abokansa
aka ebi Amare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login