Showing 57001 words to 60000 words out of 105161 words

Chapter 20 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13419

ke ga yar iska
ko kinzo sai kuka kike ma mutane kina firgita min Huzaifa kina cika masa kunne shashasha ta ja
tsaki,kb dake cin indomie yace ki taya jaje saurayinta ne ya fasa aurenta Mohd abokin Isa,
Fuskar tausayi Badriyya tayi tace eyya sorry kinji Sis rashin masoyi ba dadi kamar nice ace
Huzaifa ya daina kulani ai daji zan shige kawai.

Sakina tace ni dai Allah a San yanda za a dawo min dashi ehe
Harara Amana ta watso mata,Badriyya kitchen ta shiga tace Amana ki dafa da Ya Huzaifa
fa,ae ai dama dashi nakeyi kira min Haladu pls na aikeshi,Amana yayanki ne fa Haladu amma
zaki aikeshi,ina ruwanki to kawai ki kira min shi.

Yara yan makaranta sun taso suna ta surutu Amana da masifa ta fito kai kuyi min shuru
mijina Bacci yake kwakwaran Motsi Amana ta hana yaran nan suyi har ta gama girkinta ta fesa
wanka ta dan dasa kwalliya cikin doguwar rigar materal fitted gaunt tasha kyau hips komai ya
fito das das ta Jere abinci a gefen bed sannan ta tashi Alim ya shiga toilet din dake cikin room
din domin yin Alwala

Saude kuwa tana kauyensu bayan ta samu nasarar guduwa daga gidan Alim ko me take
aikatawa oho ta ya Saude ta gudu sai mun koma wajen me gadi za muji labari
Amma dai Saude ta murmure ta dawo fes da ita tana harkokinta can kauyensu dake Gombe
state.
Alim kamar gidansu yana shigewa toilet saida yayi wanka da soap din Amana,yayi Alwala

da sallar Azahar,Amana kuwa period takeyi ma
Zaune yake kan katuwar sallaya abinci Jere a gabansa ga Amana tasha wanka tana aika
masa da wasu sinadaran kallo masu rikitarwa.
Wasu flasks masu kyau ya bude wow....ya furta miyar danyar kubewa ce tasha kifi da tuwon
danyar shinkafa,wani flask ya bude farfesun kaji sai kamshi ke tashi sai wani glass Bowl
kankanace a yanke da fork spoon ciki
Ga wani zobe yasha kayan hadi a glass juck har ya fara kankara,sai ruwan roba,yanda aka
kawowa Alim haka aka bawa Huzaifa ma,
Alim ya manta ma tare suke da Huzaifa ma

Amana zagewa tayi ta cire masa rigarsa ta shadda daga shi sai dogon wandonsa wai kar
mistakenly miya ta bata masa riga hehehe love

Alim kamar gidan ubansa ya wani kwanta a kafadar Amana tana ta ciyar dashi saida ya koshi
sosai sannan a karshe ta bashi kankana yasha,
Brush ta kawo masa sabo ya tsaftace sannan ya dinga kora zobon,
Amana kuwa abincin itama taci ta kwashe komai ta gyara room din tare da kara wanke toilet
din ko Ina kamshi yakeyi,
Alim saman bed yajata suka shige sai wasanni sukeyi a ciki.
Huzaifa yaga Alim shuru yaki fitowa sai mamakin rashin kunyarsa yakeyi a gidan surukai,
Badriyya tace ai mu nan gidan ba ruwan wani da wani,lallai rayuwarku tana birgeni a gidan nan
kowa harkarsa yakeyi cewar Huzaifa.

Har magriba Baba Basu dawo ba,Huzaifa har ya fito jikin mota suka hadu dasu Baba sun
dawo an kwaso Baba kamar kayan wanki yana ta numfarfashi,har dakin Baba yaje suka gaisa
harda yar hira sama sama sannan ya masa ya jiki,Baba yana nishi yace ina wannan dan
marasa mutuncin dan uwanka mijin Amanata Huzaifa ya sosa kai Baba yana dakin Amana yanzu ma jiransa nakeyi ya fito mu tafi kar dare
yayi,
Sanda Baba ya jawo a kusa dashi ya rafkawa Huzaifa a kansa nan take wajen ya
kumbura,dan ubanka fitar minshi daga gidanaa na tsaneshi,Huzaifa dafe da kansa yace Baba
lafiya kara daga sandar yayi da niyyar kwala masa Badriyya ta fado dakin ta tare tace ni ka
dakeni Baba akan ka daki wannan me sukayi maka?
Huzaifa ne ya janye Badriyya yana bawa Baba hakuri suka fita,
Amana ne suka fito tare da Alim kamar zasu hadiye juna,sallama yayiwa mutan gidan kaf tare
da yi musu kyautar ruwan kudi,Huzaifa kuwa Badriyya ya kashe da kudi sai Haladu da Sakina.

Huzaifa yacewa Alim malam dan Allah ka shiga wajen Baba ka fito mu tafi dare nayi mana,
Murmushi Alim yayi, Amana tace karka damar min miji dariya sukayi gaba daya.
Suna shiga Baba ya dinga zagin Alim da Bala'i. Yace kuma dole ka sakar min yata gadon
tsiya, Amana ce take kuka haba Baba wannan butulcine,Baba yace Butulcin Ubanki akan sun
bamu yan kudi da yi mana wannan gidan.gidan banza gidan wofi nan fa Ba irin cin mutuncin da

Baba baiwa Alim ba,Alim sai hakuri yake bashi tunda shi Bai San dalilin zagin da Baba ke masa
ba.
A hankali yace Baba kayi hakuri amma bazan iya sakin matata ba,
Baba sai da yaja nishi sosai sabo da azaba ciwo yace da yake uwarka ce ta haifa min ita ko
kai nafika iya shege na fika tantiranci,ka tambaya kaji gogaggen dan duniya ne ni nafi karfin
uwarka ma.
Amana cikin kuka tace Baba wai Mene haka dan Allah,Jan hannun Alim tayi muje kawai na
bika mu koma Lagos.
Baba yace kije gidan uwarwa kai na fiku tasha wlh,kaje ka kawo min takardar yata kuma saki
uku tafi ka bani waje ke kuma na fada miki idan kika kuskura kika bar garin nan namu to ban
yafe miki ba,

Amana tace Baba iya garin nan ko ka yarda na fita na zagashi yace ae iya garin nan zaki
zauna,ko gidana zaki bari to ki zauna iya garin nan kiyi ta yawon duniyarki amma a anan garin.

Shi Baba ganinsa ya kafawa Amana tarko,Alim yace Baba na tafi Allah kara lfy ya zaro damin
kudi ya ajiye masa,Baba ba kunya ya karbe tare da Jan tsaki
Amana suna fitowa waje tacewa Alim sallami Huzaifa ya tafi gida ni kuma ka jirani muje wani
gida a garin nan tunda Baba Bai hanani fita a nan ba.

Haka kuwa Huzaifa ya tafi Amana ta dauko kaya a hand Bag Babba tace muje,Alim yace nifa
tsoro nakeji kar Baba yayi mana wani Abin,
Dariya Amana tayi tace rana zafi inuwa kuna both Mum naka da Babana ai kawai muyi me
dalili mu rufta kawai Baaaba komai ta fanjama fanjama.
Dariya Alim yayi tare da lakace mata hanci,taja Hannun Handsome Alim suka Sha kwana ta
wani lungu.





AsmaBaffa

Tnx all
CIRANIN AMANA




140-145

Official



By
AsmaBaffa







QUEEN MERMU AGAIN,THS PAGE IS FOR UUUUUU





Corner su Amana sukesha kawai ba ji ba gani har Alim ya gaji yace gaskiya honey a
tsaya am so tired daga cewa ba nisa nan nan sai Shan corner mukeyi da layika,
Kafeshi tayi da Ido duk ya jigata saboda Sam Bai Saba da wahala ba,gashin kansa ya
hargitse harda bige kafarsa domin wajen ma ya dan yi jini kadan,
Lazy kawai kamar ba Namiji ba,yanci zamu karba wajen iyayenmu Amana ta furta tana kada
masa idanuwa,murmushi Alim yayi kinga karfa wani yazo wucewa ya kallar min farin da kike
min da ido am gealous,
Kuma taya zamu karbi yanci a haka wai ma ina zamu،hope dai baza mu Dade ba kinsan Aabid
dina yana can Mum zata kara lalata minshi da wasu halaye kina gani yaron yanzu kullum
boyeshi takeyi a room dinta ko ganinsa bamayi a gidan makaranta ma ba kullum take bari yana
zuwa ba,yaron kafin na zo nan na ganshi duk ya rame,idan yace Momy ko Daddy Mum makeshi
takeyi,wlh na rasa yanda zanyi da Abin ga Aabid saurin girma gareshi...

Nasan komai fa ba sai ka fada min ba Allah zai kawo mafita kaji sai hakuri,kwalla Alim ya
share da sauri kar Amana ta gani,ita kuwa Amana ta gani amma sai tayi kamar bata gani
ba,Naushinsa tayi kadan a kirji ba shiri ya saki kara ouchhhh.....be a man,u have to be strong fa
muje ta kama hannunsa oya muje kawai, Sun kara tafiya me Nisan gaske kamar zasu bar garin sannan suka isa wani dandasheshen
wani gida dan karami harda gate yasha tiles da flowers.
Gidan ta kwankwasa wata dattijuwar mata ta bude tare da fitowa nan take matar ta washe
baki tare da cewa barka da zuwa Hajiya,
Amana tace yawwa suka gaisa,matar Sa'adatu tace Hajiya lafiyar gidan kikazo dubawa
domin nasan mun biya kudin hayarmu
Amana tace Sa'adatu wannan miji nane shine me gidan nan mun dawo zamu zauna a

saman benen tunda dama iya kasan na Baku haya nace Ku dinga hawa kuna gyara min sama
kar a bar mana gida da dirty,
Murmushi Sa'adatu tayi tace hakane komai yana nan tsab a part dinku wato upstairs,bari na
kira mijina,
Malam Salisu ne ya fito suka gaisa cikin mutunci sannan Amana ta masa bayani ta kama
Alim suka haura sama part dinsu,domin gidan part biyu ne,kasa 3 bed room ko wanne da
toilet,sai Palo kitchen da toilet,saman ma haka take komai da komai. Sa'adatu da Malam Salisu
sai yaransu 3 babbar macece yar 20yrs Iklima,kamal da Yahaya suna part din kasa.
Alim shi kam mamaki yakeyi Amana yaushe take da gida bari su huta zai tambayeta,
Suna shiga abin mamaki latest dubai furniture ne a saman yasha Alatu,sosai an kawata part din
da kaya na Alfarma amma komai a rufe da ledarsu.
Amma Sabo da Sa'adatu na gyara shi kullum ta kulle da key kal kal komai suke sai kamshi ko
ina ke yi kasancewar Sa'adatu me tsafta ce.suna shiga ya shige bedroom kalar bed din sun
birge Alim tafiya yayi da niyyar fadawa bed din domin ya gaji caraf Amana ta damkoshi tare da
jawoshi baya tare da kakkabe masa rigarsa wai zai bata jikinsa,
Ledar dake lullube da katifa ta kwaye nan ta leka kasan bed din fes dashi Sa'adatu na daga
katifa ta share da moping,sip ta bude ko ina bedsheet ne kalakala sun kai 5 masu kyau ko
wanne room da kalolinsu,duk ta da musu turaren ajiya a ciki sai kamshi sukeyi,share room din
tayi tare da moping cikin zafin nama dan babu abinda babu a part din na amfanin gida komai
Sabo kamar sabuwar Amarya nan ta shimfida bedsheet wani Mai kyau na gaske,room freshner
ta fesa da turaren wuta ta kunna, toilet ma ta kara wanketa fes fes, kafin kace me room din ya
dau kyau, palo ta fito Alim ta hango a tsaye yana ta layin gajiya sai rufe ido yakeyi gashi Amana
ta hanashi zama wai zai bata kayansa,

Ido suka hada ta kashe masa ido daya tare da jan hannunsa ta kaishi har kan bed din riga
ta cire masa da wando daga shi sai tight da singilet sannan tace oya slip kafin sallar isha bari na
kara sa aikin,sai binta yake da kallo wani farin ciki ya cika masa zuciya.
Ficewa tayi haka tabi ko ina a upstairs part dinsu ta cire ledar kayan ta gyara komai ta
share ta goge ta kunna kamshi sannan ta kunna Ac ta duka dakunan kasancewar da wuta tuni
gida ya dau kamshi,waje ta fita ta siyo taliya spagetti da kayan miya hade da danyen kifi harda
indomie da kayan shayi da wasu abubuwan na amfani da babu,direct kitchen ta shige kamar
kitchen din Amarya komai na harkar kitchen akwai kayan abinci ne kawai babu fridge ta kunna
ta zuba lemuka da ruwan robar da suka siyo sannan ta fara girki, ko gas babu sai kerozine da ta
siyo ta cika katona resho ta,ta kunna miyar jajjage tayi tasha kifi ta dafa taliya sai coffee da ta
hada ta cika musu flask ta shirya abincin a dining sannan ta gyara kitchen din kamar ba a ciki
tayi girki ba,toilet ta fada a dayan bed room din wanka tayi sosai,
Ba sallah takeyi ba tana fitowa gashinta ta busar da hand drier da ta taho da ita a jakarta
sannan ta shafa lotion dinta ta shirya cikin wata gaunt iya gwiwa me dogon hannu peach color
toilet ta koma ta wanke kayan data cire tare dana Alim data cire masa ta Shanya su.
Zama tayi ta rangada kwalliya sai kamshi takeyi sannan ta dauki jakarta ta koma dakin da
Alim ke ciki,tana shiga ta tadda shi ya tashi sai mika yakeyi da salati bakinsa dauke da addua

Sabulu da sabon soso ta kai masa toilet sannan ta dawo ta zauna kusa dashi ta zo zata
rungumeshi Alim ya buga tsalle ya ja baya,
Tana dariya tace lfy? Murmushi yayi yace rana ta dake ni dazu ga tafiya munyi da kafa nayi
dirty ai sai ki shafi dirty na,
Amana tana murmushi ta karaso kusa dashi suna facing juna tace see u kaji kamshin da
kakeyi kuwa zaka ce kayi dirty,babu me cewa kayi wani tafiyar kasa,come here joooo ta afka
tare da hugging Alim harda cusa kanta a kirjinsa tare da manna masa kiss normal babu wani
canji saima kamshi da yakeyi, Brush da toothpaste ta mikawa Alim to maza yi wanka ka fito tare da mika masa towel ya
shige ta rufo masa kofar.

Wasu sabuwar farar jallabiya da sabuwar singlet da boxers ta dakko cikin wanda ta siyowa
Alim da taje cikin Kano hospital kai Baba shine suka je ShopRite ita da Sakina sai ta ajiyesu da
nufin idan ta koma lagos zata bashi.

Yana fitowa ta mika masa mai me tsada da kamshi ya shafa sama sama,turarukanta ta
mika masa ya shafa sannan cike da mamaki tambayoyi cike a zuciyarsa yasa kayan da ta bashi
dai dai shi kamar an auna yayi kyau sumarsa sai sheki takeyi,comb dinta ya karba ya taje
kansa, Tunes ce ke kwakularsa Bai gama Shan mamaki ba saida Amana ta jawoshi Palo saman
dining food flask hadaddun gaske nan suka ci suka Sha suka godewa Allah,
Kwanikan ta kwashe suka koma Palo ya jawo Amana jikinsa suka kwanta a kan 3seater suka
mamuki juna domin a kan jikinsa ta kwanta,

Ga plasma TV Amma ba a hada kayan kallonba
Gashin Amana dake matukar fidda kamshi ya fara shafawa a hankali kana ya fara magana
kasa kasa Amana tashi zaune muyi magana,ba musu ta Mike tare da Zama suna gugan
juna,yace tambayarki zanyi duk wannan Abubuwan ina kika samosu wai I mean
gida,food,kayan jikina etc.
Murmushi tayi sannan ta Mike tace ina zuwa bedroom ta shiga handbag ta bude ta ebo wasu
takaddu guda uku ta fito dasu ta zauna kusa da Alim tace Babyna ba Abin mamaki bane,
Wannan gidan daka gani gidanka ne,sanda ina gidanka ina Kula da Aabid dina kana bani
kudi masu yawa haka duk wata a accnt dina kana biyana kudi kafin a daura mana aure

Numfashi ta ja tace to da kudin da kake bani na sai maka wannan gidan har kayan dake ciki
dalilina kuwa ko Mum tace ka sakeni nasan baza ka iya ba idan ma ka sakeni kaga sai na fada
ma na dawo gidan nan da Zama har Allah ya dai daita komai,Ko iyayena basu San da gidan
nan ba,Badriyya da Ya Hamza ne kadai suka sani domin su na turawa kudin nace su sai min
gida,to sai suka ga wani ya gida wannan wai baya son gidan garin ya masa kauye da yawa
shine suka fada min nace su siya min da shedu,
Takardar shedar gidan ta mika masa da sunan Alim da komai a jiki daya takardar ta kara

mika masa ga wannan shi kuma takardar kayan da aka zubane gashi,kayan sawa dana Baka
shekaran jiya munje kai Baba hospital Kano city na siya ma da niyyar na Baka idan na koma
lagos suna cikin akwati da yawa gobe zan dauko ma a gidanmu

Abinci kuma kana bacci na siyo kayan dafawa na yi mana duk cikin kudin da ka bani dazu a
gidanmu,
Mamakin Amana ya cika Alim gaskiya Amana macece ta gari duk da basu da kudi amma
gashi Abin duniya Bai dameta ba,da wasu ne ai iyayensu da yan uwansu zasu bawa komai har
cutar mijin zasu dingayi

Firgigit ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login