Showing 81001 words to 84000 words out of 105161 words

Chapter 28 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13587

yasa hakuri ya rike
spoon din gam, da kyar ta zaro cokalin itama tai ta ci da yawa ya kwace cokalin tare da tattaro
indomie gabansa,yana ta ci,Amana tace Mama kinga zai cinye du,Mama tace wai kai wanne irin
mugu ne?bata spoon dinta taci,Amana ta warce itama ta sharba,Alim yace Mama kalli kazantar
da takeyi wlh zata lalata abincin,Mama tace to kema baki dai dai ba bashi cokali yaci,Alim ya
kwace yaci da yawa Mama tace kaima kayi zari ka bar mata plate din sai an kawo wata Alim
yace haba Mama ko romon ni fa ban sha ba,Wata a cikin dangi tace to kai kaci girma mana
akan Indomie kamar mayunta ku bari a kawo wata mana wlh Mama ke kike kulasu,ji nake jiya
suka gama iskancin ture ture da yakushe yakushe,
Amana tace Allah ni bana kulashi shine yake takalata,cokalin ya dan buga mata a
goshi,Mama tace ah...kema da halinki duk halinku daya,ni ban san Alim da haka ba sai yanzu,

Asiya ce ta kawo musu lafiyyar Indomie tare da mikawa Alim cokalinsa daban,
Nan kowa ya fara ci sai gwaren cokali sukeyi a plate,ka daina cimin gabana,cikin rada Alim
yace tab wannan maganar tafi karfina kin jin nace ina nema zan....Amana tayi shuru har ya
fassara mata magana. Suna ci gaba da ci Sai ta ebo yasa cokali ya kwace,Amana ganin
mutane yasa ta kyaleshi,da yaga taki kulashi kuma so yake ya sata bakin ciki sai,ji tayi kawai ya
turo plate din jikinta Indomie ta zubo mata a gefenn cinya ta bata mata kaya Amana kwalla tab a
idonta tace Mama kin ganshi ko wlh kar na rama aga banyi dai dai ba,na gaji da halinsa sai
yana dukana yanzu ma kina kallon can ya mareni kaji Amana da karya, wata dattijuwa tace abin
naku iskanci ne kawai ,Mama tace kai ku rabu dani na gaji da halinku,Amana tace Mama shine
fa yake ta min abu,jiya ma haka ya dinga dukana,har marina yayi a wajen dinner da zamu
dawo,Wata a cikin yan biki tace wai ba mata da miji bane? akace mata da miji ne,matar tace
iya shegen banza da ya kuke zama a gidan auren? Wannan ai sai kusa mutum hawan jini,

Mama tace Alim ka kiyayeni na fada maka,Kanwar Abban su Alim ce tazo tace Mama
yaranan ina kallon gangancin da sukeyi da Mota a titi zasu je dinner suna ta fada ta windon
Mota,mutane suka saki Salati,kunya Amana taji ta mike ta bar palon,Alim ma haka,mutanen
wajen suka ce wannan matar tasa yar nema ce naga a tsaye take itama,amma Alim da miskili
ne ta koya masa sun zama daya,wasu sukace wannan Yara da kuruciya suke abin dariya,fadan
nasu duk ba fada bane.

Amana suna waje a zaune da mata da Maza kawaye da angwaye ana ta hira,Alim shi da
wani frnd dinsa suka zo wajen kusa da Amana Alim ya zauna cikin hira Alim yace ai shi yasa
akace mata duk sunfi yawa a wuta,Amana tana ji tasan da ita yake zaraf cikin dagewa da
masifa tace ai wlh wannan karan sai dai ayi kunnen doki Maza rabi mata rabi,Mazan gasu nan
duk azzalumai,

Alim a fusace yace kinji nayi magana dake zancen mu mukeyi zaki sa min baki,Amana ta
shareshi,Alim ya kara cewa ai idan mace ta isheka to ka karo aure,Amana tace wace zata

zauna da kai da baka san komai yanda duniya take ciki ba,duk mutane wajen shuru sukayi ana
jin fadan su Alim,Alim yace dadin abin dai Aljannarku na kasan kafafunmu,Amana tace idan
mun zo shiga ku take,ke da ke nake wai? Alim ya mike tare da Barin wajen yana masifa

9pm aka fara shirye shiryen tafiya dinner,Hamza ma duk sunzo kuma sun karbi motar hannun
Amana suna kai kawaye,Amana data shirya ta fito cikin shiga ta gaske,ba kowa a tsakar gida
duk an gama tafiya sai kakar su Alim kawai ta fito zasu tafi da Alim tana ta tsokanar Amana,Alim
ya fito fes cikin rantsatsiyar shiga,kaka taja Amana wai dole su tafi tare,Amana taki yarda Amma
kaka ta matsa mata,dole ta bude gidan baya a motar Alim ta shi ga ba walwala,Alim ma fuska
ba rahma,ya zauna gefen kaka,Asiya ta fito ta shige gaban Mota,
Bai ce komai ba driver yaja Mota kamar abin arziki sun danyi nisa da tafiya, Alim da Amana
sunsa Kaka a gefe karshen mota Amana a tsakiya Alim a gefenta

Alim ya leko da kansa ya kurawa Amana ido,dagowa tayi suka hada ido aí kuwa ya mata
gwalo itama ta rama,
Bayan minti daya yace Anjima idan mun dawo zamuyi magana ta fahimta yayi zancen ne ba
wasa da gaske,Amana tabe baki tayi tana so tace bata da lokacinsa Amma kuma Kaka na
wajen da Asiya,kawai sai tace ba time,
Pls kinji?tayi banza dashi kamar bata ji ba,yace am talking to u fa,tayi banza dashi,
Nan ya zuro hannu tare da latsa cikinta ina abina?

Amana ta kwadawa Alim duka a hannun,Kaka tace yau naga fitsararre,Dariya Alim yayi ya
Mika hannu again Kaka ta bige hannun,Amana ya kara rukowa hannu pls ki bani time,Amana ta
rike hannun Alim ta garza masa cizo sai suka fara kokawa da hannaye, Kaka na kallonsu suna
ta yakushe ya kushe,Alim ya kara tafkawa Amana mintsini,tana haki da Hawaye tare da cewa
ka mintsinen?

gyara zama tayi suka fara kokawa sosai,garin fada suka tugewa Kaka dankwali Kaka tana
mene haka ku bari lfy?saboda taga Amana harda kuka,Alim kuwa yi yakeyi Amma dariya ta cika
masa ciki yanda Amana ta zage,Kaka ta daura dankwalinta,Amana tace Kaka kiyi hakuri kinga
dai laifinsa ne ko,Kaka kuwa manne kanta tayi a jikin kujera tana gefe suna ta faman yi,Amana
tace kai kai kai kai dannamin kashin wuya uhmm....zaka gani Amana ta Yakushi Alim ta cijeshi
yayi kara da karfi,Kaka ta matsa sosai gefe suna ta yi,ganin haka kaka ta rabasu a tsakiya ta
zauna a tsakiyarsu wai ta shiga tsakani, sai gashi sun tsallake kaka Alim ta gaban kaka ya zuro
hannunsa sai ya taba cikin Amana,Ita kuma taki yarda shine suke ta faman kokawa,

Amana ta rike hannun Alim kamar kunama sai fasa masa cizo takeyi yana ta kwalla kara,Kaka
tace yawwa jikata yi maganinsa,
Alim ya karbe hannunsa da kyar yasa dayan ya cirewa Amana gogoron da tasha wahalar
sakawa ya ja gashinta da karfi,tayi kara Kaka ta sa hannu biyu tare da Dukan Alim ka haba ka
bar yarinya ta sake,Driver da Asiya dariya kawai sukeyi saboda kowa ya kalli abin yasan ba
fada sukeyi ba, Amana tace nafi karfinka ko banza na cijeka da yawa kaifa me ka iya yimin ta karasa tana

hakki kamar tayi tsere.
Alim ganin Kaka ce shi yasa baya Jin kunyarsa

Alim yace sai na ballaki kika kara yi min magana,Amana tace na gaba yayi gaba na baya sai
labari,gobe i yanzu na tafi gida ina zaka ganni kuma kafin na tafi sai na tabbatar dana yi
maganinka.

Ina ma da ne yaro da kagane shayi ruwane,Alim yace kanki ake ji,
Har aka je cece kuce akeyi,amma Kaka tasan da wata a kasa idan sun koma gida zata
hadasu taji me laifi acikinsu,

Amana da Alim ba wanda ya kula wani har akayi party suka dawo gida,Kaka tace kuzo muje
dakina zanji dalilin wannan shirmen da kukeyi a matsayin fada.

Suna dakin Kaka zaune a kasa Kaka tana saman Bed tace ke fada min jikata mene matsalar
ke da mijinki? Amana tace ki tambayeshi,Alim yace ke dai ki fada,k a fada dai kai da akayiwa
laifi,Alim yace in zakiyi bayani kiyi,bazanyi ba nan suka fara cacar baki,ita Amana mamakin Alim
takeyi har yaushe yake da baki haka yanzu,
Alim ne ya gyara zama tun farkon haduwarsu da Amana da halin Mum da abinda Sulemanu
yayi musu da sanadin rabuwarsu duk Alim ya kwashe ya fadawa Kaka yace Amma kaka sirri pls
kinji iya mu dake,Kaka tace kaine da laifi baka kyauta ba,kasan da halin Mum Dinka dana
Saude amma ka zargi matarka ba tunani ba komai,kayi kuruciya Alim ga matarka ta gari,kuma
yanzu gashi kasan kayi laifi ba bincike ba komai maimakon ka fara bata hakuri da lallashi sai ka
dinga fada da tsokana da yakushi,

Ke kuma jikata nasan yayi laifi bai kyauta ba kiyi hakuri ki dauka kaddarace,nan Kaka tayi
musu nasiha sosai tayi musu fada sannan tace kar na kara ji da gani ya wuce daga yau,Amana
a ranta tace tab yaci banza ma kenan wlh Bai isa ba,a fili Amana tace ya wuce Kaka insha'allah
bazai kara faduwa ba,
Alim wani sanyi yaji da dadi a ransa marar misaltuwa,Amana ma taji dadi da sanyi sosai
zuciyarta wasai saboda Alim baya zarginta yayi tunani ya San ta gari ce ita,

Alim ne ya kalleta tare da cewa Kaka kice ta biyani cikina,Kunne kaka ta toshe tace kai ban
son shashanci,to wlh ta fadi inda ta kaimin ciki cewar Alim,Amana tace ciki ya zube ka auri wata
ta haifarma ta Mike tare da ficewa,Kaka tace sai kayi aiki da lallashi fa,
Kaka yarinyar nan taurin kai gareta,nasan baza ta taba kulani ba shi yasa kika ga ina
tsokanarta da fada,nasan tana da saurin zuciya shi yasa nake mata abinda zatayi magana in ba
haka ba nine zan Sha wahala,
Koma me ta maka kai ka jawo ba tunani ba komai ka yanke hukunci cikin fushi,Kaka kishine wlh
da shedan amma nasan Amana ba yar iska bace a virgin na samu abata cikin kwali a like,kaka
tace tashi ka tafi marar kunya,

Fita Alim yayi tare da tunanin ta yanda zai bullowa Amana ta hakura,washe gari da rana Mum
Alim ta sauka tana gadara da takama,

Amana ce ta shigo palon Mama tana neman Aabid,
Mum Alim ta gani zaune tana latsa waya,har gabanta Amana taje tare da tsugunawa har
kasa ta gaisheta cikin ladabi,lfy kawai tace ta dauke kanta cike da mamaki dama jarabar
yarinyar nan tana makale da Alim lallai aiki Bai kare ba,dole ta aikata lahira kowa ya huta.

Amana dama tasan abinda Mum zata mata kenan kawai sai ta Mike,Alim ta gani a bayanta
ya harde hannaye yana ta murmushin Jin dadi an girmama uwarsa.

Ta gefen sa Amana zata wuce ya rukota tare da hadata da jikinta,wani so da shauki hade da
shock sukaji gaba dayansu,Amana Hawaye ya cika idonta Alim ya kai bakinsa a kunnenta tare
da cewa am so sorry ki yafe min kinji,missed u kwace jikinta tayi tare da ficewa daga dakin,Mum
ta kalleshi tace kayi asarar halinka jibi yanda take tureka kana manne mata,Alim ficewarsa yayi
baice komai ba,

Amana kuwa room ta koma tana share hawaye sosai ga wani sabon son Alim da yake
azalzalarta,
Alim ma kasa Zama yayi ya rasa inda zaisa kansa matarsa yake so,kuma taki hakura
A ranar duk yanda Alim yaso suyi magana da Amana abin yaci tura,sam Amana taki ma
yasan inda take,
Last party ma da zata je babu yanda baiyi ba ta kulashi ko ta saurareshi suyi magana ta kirki
amma taki yarda
Duk hanyar dayabi ta tosheta, kukane kawai Alim baiyi ba,
Haka aka gama biki sannan suka dawo garinsu har Amare washe gari aka daura Aure tare da
kai Amare abinsu shar komai yayi a gidansu.

Amana ta dawo gida washe gari da safe wanka tayi ta shirya tare da komawa baccin
gajiya,Alim yazo gidan gaba daya sai da yabi dangin Amana da iyayenta wai su bata hakuri ta
saurareshi,su kuwa kaf Alim nasu ne musamman yanda yake kyautata musu ba musu suka
kwantar masa da hankali harsu Umma.
Gaba daya manya da yara tare da iyaye suka dungumo dakin Amana tana bacci suka
tasheta,Amana gabanta ya fadi da ta gansu gaba daya,nan fa suka zauna zasu fara magana.




AsmaBaffa

Happy sallah to u all
✳CIRANIN AMANA ✳



175-180



Official


By
AsmaBaffa





Maza da mata iyaye harda yara ne suka sa Amana a tsakiya suka fara caccake ta, me
fada nayi me masifa nayi me nasiha nayi da masu lallashinta yan yara kenan,
Amana tana jinsu a ranta tace lallai Alim ya gama siye dangina da kudi amma ai nafi sonsa
daku ina son abina kuma nafi Ku farin cikin dawowar mijina wajena,a fili kuwa sai Amana ta
fashe musu da kuka, Gwaggo ta hangame baki tace yau naji shashashar yarinya ana nema miki
gata kina shirme, Umma ta hayayyako yo dan ubanta ma laifinsane ki duba sharrin da aka kulla
miki har yau gaskiyar abin Bai fito ba amma ya dawo wajenki a haka zai mai dake amma kin
tsaya shirme,

Hamza yace akwai me kaunarta irin wannan bawan Allah idan wani ne a take a wajen zai
sakeki,yana da kudi ga mata nan ke kadai ce mace,
Kb ya fara ai ni wlh tana kin komawa wata rangadediya zan Nemo masa ya aura,Amana ce ta
dago tare da gallawa Kb harara,Isa yace ga kannenta da yawa ai ya halarta ya rabu da ya mu
bashi kanwa, Amana ta sigar wasa ta daki Isa a kirji,Haladu yace munafunfun ana so ana kaiwa
kasuwa wai ke jan aji ko?
Wayar Hamza ce ta dau ruri Badriyya ce ta kira tana fada masa yanda Alim ke kiranta a
waya ita da Sakeena akan su tayashi lallashin Amana.
Umma ce tace duk kuyi shuru zan yanke hukunci yanzu Amana dolene ki koma wajen mijinki
jibi nace ya dawo jibi ya tafi dake kuma Umarni ne na baki a matsayina na mahaifiyarki,yanzu
ma yana palo ki tashi ki shirya kije ko yanzu na turoshi nan,
Amana kamar zatayi kuka tace haba Umma wai mene haka.
Gwaggo tace kai kuzo mu fita karki koma idan kinga dama,mazan ma sai da suka tsaya tare
da yiwa Amana nasiha sosai sannan suka fita,

Suna fita Amana ta Mike tsaye tare da daka tsalle ta fada kan Bed ta jawo pilo ta kanka me
tana ta dariyar Jin dadi tare da furta Alhmdllh,ta kara mikewa tsaye ta daka tsalle tare da furta
jibi sai lagos ko da kafar katako ne Allah kaimu,towel ta daura ta fada toilet,

Umma kuwa ganin Amana shuru taki fitowa taje wajen Alim kawai sai ta sa Kb ya rakoshi har
dakin Amana,daga bakin kofa Kb ya juya,Alim daya shiga ciki karar ruwa yaji a toilet yasan itace
take wanka,jikin kofar toilet din ya karasa tare da cewa na shigo? Amana tana jin muryarsa tace
ya salam kai Umma,ji tayi ya kara magana nazo muyi wankan?Amana tayi banza dashi da
wasa ya murda handle Amana cikin fada tayi magana basai ka shigo ba pls.
Murmushi Alim yayi tare da komawa kan bed ya kwanta yana shakar kamshin Amana.

Tana sani taki fitowa daga wankan ya dade yana jiranta har bacci ya daukeshi sosai sannan
ta fito, saida ta leka fuskar sa taga bacci yakeyi sosai,ta fara kare masa kallo sanye yake cikin
farar shadda dinkin Maza fitted domin Maza ma yanzu dai dai su suke dinki sai ya dan damesu,
Harda sa hula domin shi ba sosai yake sa hula ba Amma yau harda hula dai dai shi ya wani
coko ta gaban goshi sawar yan gayu na zamani duk gashinsa me uban yawa gasu nan
waje,yayi kyau sosai komai fari dama shi akwai sa farin kaya,

Murmushi tayi a fili tace dan duniya kenan harda bacci a hankali ta cire masa hular tare da
ajiyeta gefe,kafarsa ta kalla duk rabi a kasa karfinta tasa a hankali gudun kar ya tashi ta gyara
masa kwanciyar saida ta hau dashi bed din sosai,Amana da karfinta to, Amma duk da haka
tasha wahala dama tasan Alim din nata idan ya fara bacci to sai ka saceshi bai farka ba,
A nutse ta shirya tsab cikin riga da skert na material black tayi kyau matuka nan ta fara Barin
turaruka a jikinta harga Allah a zuciyarta dan Alim tayi kwalliyar Amma a fili wai sai tace badan
shi nayi ba dama nayi niyyar kwalliyata,idan zuciyarta ta tabbatar mata dan Alim tayi sai ta
karyata,tunani Amana tayi ta shiga kitchen ta dafa masa abinci amma kuma idan ta shiga
kitchen kwalliyarta zata baci duk da cewar da Gas suke amfani amma ai aiki zaisa kwalliyar ta
lalace tun Alim bai gani ba,

Fasa shiga kitchen tayi tace idan ya tashi na hada masa,wata zuciyar tace idan yaki tashi
da wuri fa har sai kwalliyar ta baje,tace kai bari na tasheshi na masa wayo ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login