Showing 84001 words to 87000 words out of 105161 words
Chapter 29 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf
gani sai ya koma
baccinsa,
Toilet ta shiga tare da ebo ruwa a hannunta ta yarfa masa a fuska zumbur ya bude ido tare
da mikewa ya zauna,
Kallon Amana yayi gaba daya kwalliyar Amana ta tafi da hankalin sa sai kallonta yakeyi bai
ce komai ba,
Amana ta kara tamke fuska irin ba wasa ta kara gyarawa tayi tsaiwar daukan hoto ta gama
Zuko da matso kyau tare da kallon saitin Alim,tunowa tayi baiga bayanta ba sai ta juya tare da
kallon mudubi tana neman wani abu a kan Mirror dan Alim ya ga bayan,Alim kuwa ai tuni ta
gama kashe masa jiki da kwalliyarta sha'awarta ce ta taso masa,
Sai da ta tabbatar ya kalli bayan ma sannan ta juyo tare da tamke fuska ta furta malam
lafiya ka sani a gaba,nayi maka kara,na maka tauna,nayi maka hadiya ina jira naji me kazo yi a
gidanmu harda shigo min daki ka kama bacci?
Shuru Alim yayi baice komai ba,Amana ta kara magana jibeka simi simi kamar mutumin
kwarai,Alim dai baice komai ba,Amana tayi mamaki shi da yake tsokanarta ma,
Alim a hankali ya furta am so sorry abinda na miki kiyi hakuri kinji,Amana wani tausayinsa taji
kamar tace ta hakura amma sai ta daure tace ka daina bani hakuri haka ya isheni me zaka ce
Dani yanzu na yarda,kai harni zaka Zarga,da masifa Alim yace taya bazan zargekiba ko kece
kika shigo kika sameni wata tayi min haka exactly abinda na gani ya zakiyi? Dole ki shiga
kokonto,ni waye da bazanyi laifi ba?Sufi neni?dan Adam ajizine Kuma na fada miki na baki
hakuri uncountable ya kikeso nayi kashe kaina zanyi?na biki na biki ok to zo ki cinyeni ko ki
yankani,ko sati biyu bamuyi ba da rabuwa sai da na nemeki,ranar da Baba ya rasu zuwana
nawa?ance miki da bana sonki zanzo inda gidanku yake ne?abinda yasa ban ce a kira min ke
ba nasan kina cikin wani Hali kuma banson ganin damuwarki tunda Baba ya rasu,ki tambaya
zuwana nawa gidanku bakya garin nan,kafin ma ki tafi Adamawa, ni fa ko a waya kin nemeni?
Ko text kin taba yi min na tunanin wanke kanki ko kimin bayani ko kiji halin da nake ciki,ko
namiji shine marar aji?shi ba mutun bane? Gidanku nazo ki fada min abinda kika ga dama
kuma dole ki koma gidana yarinya amma kisan me zaki fada min banson raini ya karashe
fadan da kinyi kyau dai badon halinki ba,
Amana dake tsaye sannan ta fara nata itama ka dakeni ka hanani kuka,daga yin abu Baka
tsaya ka saurareni ba kayi tafiyarka,harda zazzagina kuji sharrin Amana,
Alim yace kiji tsoron Allah yaushe na zageki?Amana ta gwada muryar Alim tace haka fa
kace ke din banza ni nafi karfinki talaka,wawiya,doluwa,bahuwa,kuchaka kuma saina ballaki
idan na kara ganinki sai na karya miki wuya,
Salati Alim ya saki sannan yace kiji tsoron Allah,Amana ta kara hade rai tana Hawaye Alim
yace to mene na Kukan kuma?,Amana tace ai kaci mutuncina da yawa dole idan na tuna nayi
kuka,Alim dai sharrin Amana ya isheshi yace to yi hakuri kinji.
Ni Bazan hakura ba yanzu cewar Amana,Alim yace to sai yaushe? yayi maganar cikin sigar
lallashi,Amana tace sai an gano wanda ya kulla min sharri,tsaki Alim yaja ke ban son shirme fa
dole ki hakura kinji na fada miki, Bazan hakura ba to dolene,mikewa Alim yayi tare da furta bari
na mike kika tsawona,tunkarota yayi sosai da gudu ta fice tare da cewa ka jira na sanmaka
abinci amma ban hakura ba
Kwanciya Alim yayi bacci ya kara dauke shi,ya dinga yi har Amana ta gama hada masa jullop
din taliya tasha hadi sosai,tana zuwa ta ciji yatsansa ya tashi firgit tare da rike wajen,
Kallonta yayi kana yace bashi kike ci,
Toilet din ya shiga tare da dauro Alwala sannan ya zauna yace to zuba min abincin tace ka
zuba da kanka mana ai ban hakura ba bare na fara yima hidima,kyaleta yayi ya zuba abinsa
tare da hada tea yaci yasha,
Amana ta kalleshi tace kwadayi anzo ana cinye mana shinkafarmu da taliya bai san sanda
dariya ta kamashi ba sosai,Alim yace yimin kudi na biya mana,banza ta masa tana danna
wayarta yace me kikeyi a waya Ba tare da ta dago ba tace Charting,idan da namiji ne wanda ba
muharraminki bane bada yawu na ba, tashi ka tafi gidanku gaskiya ka takura min, basai kin
koreni ba ya furta tare da mikewa tsaye
Kudi ya zaro Bundle biyu na yan dari biyar biyar yace dauki daya kallon kudin tayi dama bata
da ko sisi sun kare a biki,hannu tasa ta kwace duka bundle biyun duka nake so kuma ka biyani
kudin da ci da kaina da nayi yunda da aurena a kanka ka barni nasha wahala kasan hakkinka
ne ka biyani duk kudin dana kashe,kudin sabulu da omo,kamo hannunta Alim yayi suka zauna
gefen bed sannan yana murmushi yace sai ki fada min dalilin kenan na fushinki tuntuni na
biyaki ashe da dalili to fada min komai na biya,Amana sai yanzu tayi dariya sannan tace dan
kadan ne ma fa,banda wannan kudin da ka bani saboda wannan kyauta ka min,Alim yace ina
Jinki,Amana ta gyara zama tace kudin Kukan dana sha da wahalar da ka bani na bacin rai,Alim
yace daya,tace kudin ci da kai,kudin rainon ciki kafin ya zube,kudin kayan kwalliya dana siya
nayi amfani dasu baka nan,kudin zirga zirga ta zuwa unguwa kasan dole zan kashe kudin Mota,
sauran na yafe maka basai ka biya ba,
Dariya Alim yayi cikin jin dadi yace to ki jira zaki ga Alert ya mike zai tafi,Amana tace na manta
kudin mintsini da Yakushi,sai kudin gyaran jiki kafin na bika mu koma lagos.
jagira (eye liner) baka da ja sun kare ka siyo,ko kuma kaga fuska ba kwalliya, jambakina sun
zama tsohon yayi a siyo wasu, sannan sai ka sake min lefe zan koma kuma duk ka bayar dinki
a dinka da kana nan kaya ka bani 2wks sannan kazo mu tafi,Alim yace an gama indai zaki
koma ai shike nan,Amana tace kuma ka Aiko min da Mota ko na dinga hawa mashin dan acaba
kasan kauye har yau ana hawa machine cinyata ta gogi ta dan achaba ba ruwana ni,
To karki hau dan Allah Huzaifa zai kawo miki Mota,Amana tace kuma aikin hajji da za aje
bana sai ka biya min na sauke farali,Alim yace wannan me sauki ne, yawwa nima nasan me
kudine mijina Amma kazo sai cutata kakeyi kana jin dadinka kai kadai cewar Amana
dariya Alim yayi sosai yace to zamuje,
Amana tace na karasa yafe maka sauran laifinka to,dariya Alim yayi sosai sannan ya jawo
Amana jikinsa tare da rungumeta kam kam,
Baby so kike ki karar min da kudi ko?,Amana cikin shagwaba tace me teku tasan anyi dan an
ebeta da cokali? Murmushi yayi tare da yi mata rada Baby danyi min kiss kinji,Amana tace naki
din Ai dane muka dafawa jaka shayi ,Alim yana sheka dariya yace ina kika samo karin magana
haka ni ban taba ji ba,
Amana tace ae mana kalli dai jaka wato donkey Amma a dafa mata shayi ai an bata dadi
kuma gatan yayi yawa shine nima nace ai dane muka dafawa jaka shayi,
Murmushi Alim yayi tare da furta i love Amanata tare da kankameta i missed u,a hankali Alim
ya hade bakinsu waje daya yana faman tsotsa kudin dake hannun Amana ta watsar daga
hannunta tare da kara kankame mijinta,sosai suka shiga mirzar juna kamar zasu cinye kansu,
kan bed suka fada Alim ya shiga zare mata kayan jikinta one by one,da kyar Amana tace ka
bari na koma lagos dan Allah,Alim yace ina so ni dai ki kyaleni,zan fasa yin hakurin to naki yafe
ma cewar Amana,Alim yace bakya tausayina dama na sani,to ka bari mana na kara warkewa
har yaushe nayi Barin cikin ma da za ka kara min wani,ka bari idan na koma lagos sai kayi,na
hakura to ai tunda bakya so nasan ko bari naji dadi Baza kiyi ba Allah kaimu ki koma zaki fada,
Gyara kayansa yayi itama ya mayar mata da zip dinta sannan ya mike tace to karka manta da
motar kuma kudin gyaran jiki kwandalata Baza tayi ciwon kai ba don bani nace ka koreni daga
gidanka ba sannan lefe Sabo in ba haka ba bazan ma kwalliya da masu kyau ba ehe,
Alim yayi murmushi tare da cewa Amma a Adamawa kika koyo rashin Imani ko?haushi ka
bani da har ka iya zargina shi yasa Sabo da na huce zan ci ma kudi nima,zance kayi aka baka
ni?a sadaka ka aureni tsabar gata ranar da aka daura aure ranar na bika muka tafi ba wani
tarzoma,
Alim yace to naji fadi kudin gyaran jikin Amana tace salon na fadi kadan saboda da zan iya
tausaya maka,kawai ka bayar da abinda kaga dama,au na tuna ribbom dina ma suna bukatar
canji,
Check Alim ya zaro tare da rubuta mata check na million biyar ya Mika mata karba Amana
tayi ta duba,sannan tace laaaa ashe da gaske kake zaka bani,ungo abinka ni wasa nake maka
to,
Alim yace bazai karba ba,Hh dama tsokanarka nakeyi ai sai dai nace Allah kara budi ubangiji
ya biya ma bukatunka nan gaba ka bani 20million kace Amanata gashi a siyawa Yara a
Icecream, murmushi sukayi gaba dayansu,har Mota ta rakashi ya tafi cike da jin dadin samun
nasara.
Tun daga ranar Amana gyaran jiki takeyi kawai da sauran shirye shirye sai zumudi da
jindadi takeyi,bangaren ogan ma haka yana can sai da ya canja komai na gidansa,kayan sawa
kuwa na Amana da Rabin nasa duk ya bayar dasu ya canja mata sababbi kamar sabuwar
Amarya,Yanda Mum taga Alim ya wani rude gaba daya kullum cikin farin ciki yake har yayi kiba
ya kara fresh ta zata sabon aure zaiyi har murna takeyi ta zata Zainab din da ta bashi ya aura
ita zai kawo,Abba da sauran yan uwansa duk sun san Amana ce zata dawo,
Asiya ma Abba ya tsai da ranar bikinsu ita da Ahmad yayan Huzaifa,murna wajensu ba a
magana,Mum kuwa bata murna dan kawai Abba yafi karfinta ne,
Bangaren Amare su Badriyya ana can ana cin soyayya da angwayensu,
Sati biyu kenan yaune Alim yawa Amana waya ta shirya gobe zasu tafi,
Amana sai murna akeyi a boye, Umma tace Allah yasa dai uwar miji ta barki lafiya,kar kiji
komai Umma kawai addua ce taku,
Musamman Amana ta figi mota taje lalle tare da tsantsaro saloon,dama tuni Huzaifa ya kawo
mata motar hawa a cikin nasa ya bata daya Sabo da Alim ne ya bashi Umarni ya kai mata.
Amana ta kashe kudi sosai haka su gwaggo dasu Umma duk sunyi mata nasu suma,
Washe gari da sassafe sai ga Alim Sabo da tsabar zumudi,Amana lokacin ma ko bacci bata
tashi ba,bayan sun gaisa da mutan gida,Umma tace shiga tana ciki,harda ledar take away a
hannunsa,yana shigewa Umma tace gwaggo yau naga rashin kunya zumudin yayi yawa kamar
wata Amarya.
Gwaggo tace kema kya fada wannan uban sammako haka ko kasar waje zaije ai sai
haka,kamar zai tashi sama kai irin Sulemanu harka suna da yawa a kasar nan cewar Inna dayar
kishiyar, Amana tana cikin bacci tajita a sama an daga tare da direta a kasa,da kyar ta bude ido
tana kallon yanda yayi mugun kyau,
Kije pls kiyi wanka ba kallona zakiyi ba sauri zamuyi muje gida,flight zan canja mana Baza
mubi na 5pm ba yayi dare da yawa,
to naji ka zauna banfa ci komai ba ma,to nidin naci ne? kiyi sauri dan Allah mu tafi gida, janta
yayi har toilet ya Suri brush tare da zaunarta a wata kujera tana layin bacci idonta a rufe yace
bude bakin mana ai kuwa ta bude yayi ta yi mata brush a hankali ya gama,
Ki bude idonki mana haka sai wani bacci kike,a hankali Amana tace zaka bata kayanka da
ruwa fa,kamota yayi suka fito taki bude idonta wai bacci takeyi ita,fresh milk ya dura mata a
bakin tare da bata chips da egg,ina ka samo abinci?da abina nazo nasan zaki bata min
lokacine,haka ya dinga tura mata tana cinyewa shima yaci,suna gamawa yace wanka je ki
shirya ko na miki,kuma ki bude idon haka mana kiyi sauri,
Wanka ta shiga tayi sannan ta fito tana goge jikinta,ta fara sha mai duk jikinta,tazo kafafu
Alim ya fisge man kamar wani engine ya karasa shafa mata,kayan ta dauko ya kwace ya dauko
pant yace to dafani kisa, Amana ta dafa shi ya sa mata da towel dinta a daure,
Cire towel din asa bra,haba a'a ni dai ka sa min akan towel din sai na zame towel din haka
akeyi,kamota yayi yanda tace haka ya sa mata ita kuma ta zame towel din ta gyara sosai ta
kara daura abinta,
Rigar tasa fitted Gown readymade Brown color,tasha kyau ta shirya ta dauko hand bag da
katuwar akwatinta na abubuwan da take bukata duk shirye ciki,wanda zata bayar ta bayar
dasu,sai wata katuwar Ghana must go na tarkacen kayan gyaran jiki da wasu abun,
Wannan kayanfa?Amana tace nidai kawai a samun a mota dasu zan tafi kuma dole ka
dauka,
Alim yace Bazan iya daukan Ghana must go ba wlh tayi local bari muje cikin kano sai a
canja wata kalar,Amana tace yanda kaga yafima saukin dauka nidai ga mijina bazan dauki kaya
ba,Dariya Alim yayi sarkin son girma,
Yaran gidan ne suka sa kayan a Booth Amana ko kuka da canja fuska babu tayi musu
sallama tare da cewa sai munyi waya,duk abunda ya faru a dinga fada min ta waya,
Na tafi a mana addua,
Har mota suka rakata sannan ta Mika musu hannu daya bayan daya suna gaisuwar sallama.
Alim kuwa kudi ya basu masu yawa suna ta godiya driver yaja mota Amana da mijinta suna
bayan mota,
Suna zuwa kano ya canja wata tsantsareriyar jaka ya cire Ghana must go ya jefar suka je
gidan Badriyya da Sakeena suka musu sallama har gidan Abban Huzaifa sunje sannan suka
wuce airport sai gasu a jirgi sai lagos......
AsmaBaffa
Love u all
✳CIRANIN AMANA✳
180-185
Official
By
AsmaBaffa
Kuji dadinku readers ina godiya.
Tun a jirgi Alim ya fara mutsu mutsu yana takurawa Amana,ta kasa kafarsa yasa yana
faman gogata a kan ta Amana,
Amana ce ta juyo tare da kafeshi da ido tana aika masa da wani kallo mai tokare zuciya,
Shima ogan nata ba a barshi a baya ba wajen aika nasa,
Kwanto da Amana yayi a jikinsa sannan ya fara magana ko dai baki hakura ba baby?
a hankali ta furta me ka gani? Naga sai wani shareni kikeyi,to bakuwa ce ni yaushe na saba
da kai da har zan saki jiki,ban ganeba duk zaman da mukayi zakice wani bamu saba ba,
to wai ni shike nan baza ka barni na huta ba,da ban sanki da mita da korafi ba amma yanzu
ko rainani kikayi ban sani ba,y a za ayi na rainaka ya Alim,gashi nan kinyi ma yanzu wai Alim
ma ba ko Dear,honey etc kawai Alim.
To kayi hakuri na daina,suna haka jirginsu ya sauka suna fitowa taga motocin Alim masu
matukar kyau da bata san dasu ba,suka shiga sai gidan Alim,masu kwasar gaisuwa saiyi sukeyi
har suka shige part dinsu,
Duk inda suka shiga sai Alim yasa key ya garkame ko ina,
Har bedroom dinsa ya kai Amana
Mamakin Amana yanda komai na gidan aka canja Sabo kamar ma ba gidan ba ya kara
haduwa sosai.
To kije kiyi wanka mana mu kwanta ni na gaji bacci nakeji, kallonsa Amana tayi da mamaki
yanzu fa 2pm tayi ma kawai sai mu kwanta ko abinci banyi mana ba,nayi order za a dinga
kawowa kullum har na tsawon 1wk Baza kiyi girki ba hutawa kawai zamuyi,baccinmu zamu
dinga yi kawai, Baki bude Amana take kallonsa,Allah ni ba haka nasanka ba ka canja sosai sai kace Ayu,
Murmushi Alim ya saki me rikita tunanin mace daga bisani yace Amarya ce fa dole nayi doki
dama ai bana gajiya dake kece dai kika fara koyar rowa.
Janta yayi har toilet tare da turata ciki kiyi wanka,dayan bed room din ya shige wanka shima
yayi