Showing 27001 words to 30000 words out of 105161 words

Chapter 10 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13436

dasu kuma,Na sani ai ki
kirasu kawai kuyi hira ungo karbi cewar Alim,shi Alim so yake yaji shirmen gidan su Amana ya
sha dariya ko zai samu saukin zuciyarsa.
Amana kuwa karba tayi amma sai ta kasa amfani da wayar,karba yayi ta karanta masa
number Baba yasa tare da dialing,bugu daya Baba ya dauki wayar tare da cewa Alo...Alo ..da
sauri Alim ya mikawa Amana wayar ta kara a kunne tare da cewa Hello Baba Amana ce.

Hhhhh Baba ya kyalkyale da dariya tare da cewa 'yata Amanatullah wannan lambar fa ta
waye? Kallon Alim tayi ya yayi mata nuni kawai tace ta saurayinta ce ,Baba number Saurayina
ce,wata kara Baba ya saki Amanata yanzu a lagos kinyi farin jini kin samu masoyi,Ashe zanga
aurenki a duniya,Amanata duk bakin jininki a lagos kika samu miji,murmushi Amana tayi tace
Baba sai ma ka ganshi kamar bature,me kudin gaske,yeeeeeeee ahayye yan gidan su Amana
suka dauki shewa da guda tuni yan gidan kaf suka yanyame Baba,Umman Amana ce ta fashe
da kuka tace Allahu Akabar kabira,yanzu Yar nan duk bakin jininki kinyi saurayi,Ki gaishe mana
dashi idan zaki zo ki taho da shi mu ganshi,Goggo ma ta fisge wayar tare da cewa ice ko yana
bada kudi me kyauta ne?Amana tace dubu Dari Dari yake rabawa sai yan gida suka dau tafi da
ihu,Haladu ne ya matso ya wafce wayar Amana dan ubanki wayar tarho zai siyo min ki fada
masa, wlh kika zo babu wayar sai Na karyaki,kaji Haladu kaifa jarabane karma ka dameni cewar
Amana,Badariya daga gefe tace kai Amana shegiyar gari ce,yanzu tana can tana Shanawa.
Jamila tace Amana ki kula mazan lagos HIV ce garesu karki bari ya sa miki ita,gwara ta kama
Baba,Baba dake gefe samu yayi ya kwadawa Jamila mari tare da fisge wayar ,nan take matan
gidan suka fara fada ana zage zagen juna,kafin kace me gidan ya hargitse ana ta cakaki,gajiya
Amana tayi ta kashe wayar cike da bacin rai, Ga kunya ta lullubeta domin Alim yasa wayar a hands free.
Kallonsa Amana tayi taga shi sai dariya da murmushi yakeyi abinsa.tare da fadin why zaki
kashewa Baba waya ana hira yaci gaba da murmushinsa.

Kwanaki kadan akayiwa su Amana hutun makaranta Alim yace su shirya zasu je kano wajen
danginsa for 1wk zai kai musu Aabid,su. Dameshi da son ganin Aabid,murna wajen Amana ba
a magana zata ga danginta,yauce ranar tafiya Alim yace kuma a motocinsa zai tafi bazai bi
flight ba,Amana ce me driving Alim da Aabid, escort suna sauran motocin, Fitowa sukayi Amana cikin shigarta ta yau da kullum,Alim ne ya Ce ina kayan Dana siya miki
aka kai dinki gaba daya Riga da skert ne kala 10 harda dogayen riguna readymade wajen
5,takalma da bags,gyale komai dai me tsada akwati guda Alim yayi mata duk wani kayan

tsaraba kuma an jibge a mota basu da matsala
In dai baki canja kaya ba wlh baza ki je ba,ko kunya bakyaji yanda kika zo lagos ki koma
haka,

Akwatinta dake mota ta zuge ta dauko wani lace me tsadar gaske milk and brown,cikin gidan
ta koma ta shirya sosai ta fito a yan mata,ba karamin kyau tayi ba kamar a saceta,takalmi gyale
da jaka duk brown,bata iya daura dankwali ba acuci maza kawai tayi ta yafa siririn gyalen a
kanta ta fito cike da takun gadara,wai ai Alim ya kusa suma yanda yaga Amana yar india,ta
hadu sosai,shi kuwa wani milk wandon jean ne pencil a jikinsa sai wata T-shirt pupple, takalmi
ma milk color yasha kyau,Amana fa an waye sosai key ta karba ta shige mazaunin driver Alim
Na gaba ya daura kafa daya kan daya can saman gaban mortar, Aabid a bayan mota,Amana a
nutse ta fara sarrafa kan mota sannan suka dauke hanya,tafiya Amana take shararawa ta
gaske tun Alim yana tunanin zaiji tace ta gaji amma sai yaji shuru kida kawai takesha tana
murza kan mota,Aabid yayi bacci wurin kai Uku,Alim ma sai bacci yakeyi,
Sai da sukayi Rabin tafiya har dare ya kusa yi sannan Amana ta kalli Alim tace Master yunwa
mukeji ga my Boy ma sai bacci yakeyi aci abinci ayi sallah, ok kawai Alim yace tare da
gwadawa Amana garin da zata tsaya restaurant din,

Abinci da sallah sukayi Amana da escort suka take kan mota har dare yayi har wurin 2am
Na dare suka zo Kaduna Alim yace suyi bacci a kd gobe su karasa kano saboda kafafunsa har
sun kumbura,Amana tace a'a wlh baza mu tsayaba sai munkai kano,ke engine ce wai bakya
gajiya ko namiji ba kowa ne zai iya abinda kike ba, Ae naji amma ba wani kwana a kd sai munje kano.haka suka dinga sharara gudu 4:50am
suka isa kano,wajen ciromawa suka tsaya sukayi sallar asuba Amana harda yin brush a gefen
titi,haka tacewa sauran ma duk saida kowa yayi brush har Aabid,Alim ma,sannan suka tsaya
zasu dan huta,kafin wani lokaci Masu shayi sun fara yi,Amana har teburin me shayi taje ta
zauna aka yi mata hadin kauri da indomie da kwai a wajen taci ta koshi ta shanye tea dinta
Allah yasa ma mutane basu fara fitowa ba,haka tayiwa Alim da Aabid take away har mota,su
kuma sauran escort sukaje duk suka sha suka ci abinda suke so Alim ya biya kudin,shi kam
Alim sabo da yunwa shima cinye nasa yayi,Aabid ma Amana tayi feeding dinsa,Amana harda
wanke fuska da sabulu tayi fresh,ta shafa powder da lipglow,Alim ya kalleta tare da tabe baki
tare da cewa bafa saurayi zakiyi ba,dama bakin jini gareki,kar muje gidanku wlh kice ni
saurayinki ne ba ruwana,
Amana murmushi tayi tace za a gani ai.ni nace kace Na fadawa Baba hakan.

Ci gaba sukayi da ta tafiya a nutse har kano cikin Tudun yola GRA,wani tsantsararren gida
suka nufa nan take aka wangale musu gate suka kutsa ciki,matan gidan da sauran wasu
mutanen yan uwan Abban Alim,duk suna waje sunzo tarbar Alim da Aabid,abinda ya basu
mamaki mace ce driver dinsu,
Basu ce komai ba Amana ta fara budewa ta fito tare da gantsarewa tayi mika tana Hamma
da salati,duk an zuba mata ido ganin ta fito ba dankwali gyalen na ta ma a hannunta yake,
Zagawa tayi ta dauko Aabid Alim kuwa daya daga cikin guards shi yazo ya bude masa kofa

sannan ya fito a gajiye,danginsa yan mata da samari kowa rungumeshi yakeyi ana masa sannu
da zuwa,haka manyan iyaye ma,sannan suka koma kan Aabid,gaba daya securities din Alim
sun kwashi gaisu wajen dangin Alim sannan aka basu part guda masaukinsu da masu basu
abinci etc,Amana kuwa duk cikin manya samari da yan mata ba Wanda ta kalla da idon
rahma,babu Wanda ta gaisar kawai gefe taja ta tsaya tana binsu da kallo,har suka gama
rungume rungumensu,
Daya kanin Abban Alim ne yace Alim wannan fa?

Sai lokacin Alim ya yafito Amana da hannu ta karaso wajen,tunawa tayi yace in sun hadu da
manya ta dinga gaisar dasu da wannan dalilin tace barkanku da gida tayi shuru Abinta,Alim
yace Kawu wannan me kula da Aabid ce,madalla cewar Kawu,kakar Alim ce ta jawo Amana zo
muje wannan ta wajena ce da kyar Amana ta danyi murmushin yake,ita gidansu can wudil take
so ta tafi,
Alim ta kalla kurrr tace Daddy gidanmu zanje ni dai,nan take Alim ya watsa mata hararar
data firgitata, a hankali yace haka ake gaishe da manya gidanku,zan fasa barinki kije gida wlh in
kikara irin wannan,kuma kibi kaka kuje can ki zama me tarbiya kina koyawa Aabid why ke baza
kiyi ba. Haj Sameera kanwar Abban Alim itama tazo daga Nassarawa G.R.A gidan mijinta sabo da
tarbar Alim,tare da iyalanta yan mata su 4,sai Alhaji Ishaq shima kanin Abban Alim shi tare suke
zama da Babarsu wato kakar Alim da yaransa Maza samari manya su 4 mata 2 yara sune suka
taru a gidan. Shuru Amana tayi tabi Kaka suka tafi sashenta Aabid sai kuka yakeyi shi Anty Amana zai bi.

Kaka sai tsokanar Amana takeyi tun Amana bata saki jiki ba har ta saba da kaka, ita kaka
dai haka kawai taji tana son Amana,wanka Amana tayi taci abinci ta haura gadon kaka sai
bacci,Alhaji Ishaq sai fada yakewa Alim ya wahalar masa da jika tun daga Lagos har kano a
mota, ka tabbata sai dai securities su koma da motocin kai da Aabid kubi flight. Kowanne cikin Wanda sukazo baccin gajiya suke ta kwasa tun safe har 5 sannan suka tashi
sukayi wanka da Sallah,Banda Amana domin hutun sallah takeyi,kuma Ita kadaice batayi bacci
ba har sukazo kano,Aabid tuni yar Haj Sameera Ikram tayi masa wanka ta shiryashi,Alim ma ya
gwangwaje cikin shiga ta alfarma.sunyi sallar isha an hallara ana jiran kaka da Amana amma
shuru Alim sai baza ido yakeyi ina sa ran ganin Amana.




AsmaBaffa
[6/27, 9:25 PM] +234 808 968 1079: ✳CIRANIN AMANA✳



60-65

By
AsmaBaffa






Amana ta fito daga wanka a toilet din Kaka ta gama shafe shafenta sannan ta dauko Riga
da wando zata sa abinda harda pcap,Kakace ta karbe kayan tare da cewa haba jikata gidan
nan maza ne da yawa samari,bai dace kiyi wannan shigar ba kinji,
Babu kyau,kuma daga yau jikata idan kinga manya ki gaishesu sosai ba irin gaisuwar da
kikayi dazu ba kinji,ki rusuna ki gaishesu a ladabce,nan Kaka ta zage ta dinga koyawa Amana
abubuwa sosai,
Kuma Amana ta gamsu ta yarda maganar Kaka gaskiyace,ita kuwa Kaka ta tabbatar Amana
tana bukatar tarbiya,da alama bata samu kulawar iyaye ba,a hankali Amana tace to Na gode
kaka kuma zanyi yanda kikace,ki zama mace ta gaske me aji kinji? nan ma jiki a mace Amana
tace to kaka domin tunda take arayuwarta babu Wanda ya taba cewa ta gyara halinta sai
kaka,nan taji ta kara kaunar tsohuwar,
To dauko atamfa kisa a kayanki muje cin abinci,ba musu Amana ta dauko wata Riga da skert
Na atamfa me kyau da tsada red ta saka ta shafa powder harda jambaki red,ba karamin kyau
tayiba kamar yar India ga diri da shape ga fadin hips da tudu sosai,komai cib,
Kaka tace masha'allah,to saura daurin Dan kwali,kaka ban iyaba cewar Amana tare da dakko
red gyale ta yana Dan siriri,tasa flat shoe red,suka fito tare da kaka gwanin sha'awa.

Palo suka fito karo Na farko kenan da Amana taji kunyar mutane,kowa ya zubo mata
ido,Baren ma Alim da yake kallonta kamar me,karasowa tayi a nutse ta tsuguna har kasa gaban
Abba Ishaq da matarsa da Haj Sameera tare da cewa Ina yini Abba,kuna lfy?fuska sake ya
amsa mata,haka tayiwa su Sameera ma,mazan samari da suke ta faman binta da kallo tace
sannunku Ina yini,suma sun amsa da fara'a,ganin yan matan tayi ai sa'anninta ne koma ta
girmesu,ga wani kallo da suke mata Na banza kawai sai ta sharesu ta mike tsaye,daya daga
ciki wato Ikram tace mu baza ki gaishe mu ba?

Amana ce ta juyo a fusace tace hey mind ur tongue bana daukan nonsense,ta juya wajen
Alim abinta sauran kuwa da mamaki suka bude baki lallai yarinyar nan masifaffiyace daga
magana,su kuwa mazan birgesu Amana tayi ma,

Huzaifa dan gidan Abba Ishaq dake wajen yace bakuwace fa maybe ma ta girmeku Ku Baku
kulata ba, tazo gidanku sai ita zata gaisheku,Kaka da Abba Ishaq sukace kyaleshu shashashai.
Amana kusa da Alim ta koma ta zauna a hankali tace ina Aabid,A hankali shima yace Aabid
yayi fushi da ke,ni baza ki gaisheni ba?

Dariya tayi tace Daddy Kakace ta koya min fa,Kallonta Alim yayi yana jin wani farin ciki da ya
rasa Na mene,ga kamshinta da kyan da tayi yana wani fusgarshi,
Alim da Amana hirarsu kawai sukeyi a palon an zuba musu ido kowa da abinda yake sakawa
a ransa,

Abinci aka shirya kowa ya hau dining banda Amana da Kaka su basa zama a kujera,suna ci
suna hirarsu,Huzaifa ma wajen Amana ya koma ya like musu,sai hira suke sha,Dan danan
Amana ta saba da mazan gidan gaba daya banda matan,

Suna gama cin abincin Alim ya cillawa Amana Key din mota muje ki kaini gidan su khaleed
Frnd dina ne.cafe key din Amana tayi tace wlh ni bacci nake ji ka nemi wani driver din, tun daga
Lagos ko bacci banyi ba har kano kuma kace mu kara fita,

Palon gaba daya aka cika da mamaki mace ta tuko mota tun daga lagos har kano ansha
mamaki tare da jinjina mata,Haj Sameera tace ke yan mata ya sunanki ma, sunana Amana,
great name,Huzaifa yace lallai sunanki Na daban ne Baby Allah sa ki zama me Amana

Kaka tace ke kyaleshi muje kiyi baccinki,shi kanshi Alim fasa zuwa yayi yaje ya kwanta shi da
Aabid,cikin dare Aabid ya dinga tsala ihu shi A kaishi wajen Antynsa,
Daukoshi Alim yayi har part din Kaka ya buga mata kofa ta fito,yace Aabid ke Neman waccen
yarinyar,sai kaje ka kai mata tana waccen dakin,nan Kaka ta koma dakinta Alim ya shiga dakin
Amana,

Da sauri ya runtse idonsa ganinta sanye da short wando da kadan ya rufe duwawunta,sai
wata half vest a jikinta ta tale kafafu tana ta bacci,
da sauri Alim ya daura Aabid a bed din ya fice da sauri tare da rufo dakin.
Da kyar Alim ya iya runtsawa a ranar,washe gari da safe Amana ta hada kayanta Dana kaka
ta fito can bayan gidan jikin wani panfo daga ita sai wata doguwar Riga me hannun vest,wankin
kayanta dana Kaka take faman yi,

Mutanen gidan sai dadi sukeji tana girmamasu tsohuwa,Aabid yana kusa da ita,Alim yana
sama yana kare mata kallo ta window,

Kwanansu Amana uku a kano,Alim yace tashirya zasuje ya kaita gidansu,Ta gama shirinta Na
tafiya Garinsu wudil sai murna takeyi,
Motocin Alim gaba daya da escort suka jera zuwa gidan su Amana cikin yan tafiyar harda
Huzaifa.

Amana tana ta driving dinta sanye take cikin wani rantsatsen lace Golden Colo tayi matukar
kyau,Alim yasha arniyar shadda light blue fitted,Aabid kam English wear ne,Huzaifa ma ya
chakare,jerawa sukayi har garin su Amana tun a hanya Alim ya fara sa ido yana dariya kasa
kasa,zasu sha kallo yau. Ana zuwa wata majalisa Amana ta tsaya da motar tare da sauke glass kasa tace hi guys

Baaabaa Baabaa kuna sha'aninku,kallonta sukayi sosai da kyar suka iya ganewa Amana
ce,Alim Huzaifa sai kallon ikon Allah sukeyi,ganin gungun samari sun yanyame motar ana ta
kawowa Amana gaisuwa,haka Amana ta dinga tsayawa majalisa majalisa suna gaisawa,tace
sai Na nutsu Baabaa akwai labari fa.
Har kofar gidansu ta tsaya sauran motocinma suka tsaya,Ko wa kallon irin rubewar da gidan
yayi sukeyi,su Baban Amana suna waje sun zata shugaban kasane yazo wucewa,shi kanshi
Baba kasa gane Amana Yayi su Alim gaba daya fitowa sukayi daga motar,mutane sun
yanyamesu ana kallon turawa sunzo,wasu suce turawane zasuyi Titin kwalta,wasu suce ai
makaranta zasu Gina,wasu sunce ruwan tuka tuka za ayi ko pampo,

Amana tace Allah taimaki Baba, Baba Amana ce fa,ai Baba kamar ya suma, Da karfi yace
Amana yaushe kika zama haka ko takarar Gomnan Lagos kika fito kika ci bamu sani ba,ai Alim
da Huzaifa Dariya suka kamayi,can sai ga Haladu da gudu yana haki yana zuwa ya dakumi
Amana yace arniyar kasa wlh itace Dan ubanki ina wayata?
Matan gari sai leke sukeyi ta Katanga suna gulma gidan Baki sunyi kudi,Amana ta dawo da
arziki harda sojoji masu take musu baya,Amana kafin ta shiga cikin gidan yan gidan kaf maza
da mata yara da manya sun fito gaba daya kamar yaki,
Hamza babban yaya yazo wajen Amana yace shegiyar ban biyar Amana ta bashi hannu suka
tafa tace How far man,Hamza a Abuja yake Cirani kawai sai ya juya harshe suka fara broken
English pigeon shi da Amana,
Huzaifa da Alim dariya kamar su mutu,duk shuru shurun Alim kasa dannewa yayi.

Badariya yar kwalisa ita ta matso tace Banza yar kauye to ki shiga cikin gidan mana,kinzo da
mutane kin barsu a waje,wajen Aabid Badariya taje tace kaga Bature amma wannan baya jin
hausa,Fatar Aabid ta latsa da Sauri ta kalli Alim tace laushi wlh,dariya Alim yayi tare da cewa
Badariya ko?tace laaaa dama kuna jin Hausa?a ina kasanni? Huzaifa ta kalla tace kuzo Na
Baku wajen zama Ku kyale shashasha Amana,dariya Huzaifa yayi yace antynki cefa ko? Ae
yayata ce amma Allah Amana bata da mutunci kaf garin nan an sani,yanzu ta balla mutum,
Amma fa tafi kowa hankali a gidan har Baba dasu Umma cewar Badariya, dauko mana
tabarma mu zauna a waje kinga muna da yawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login