Showing 93001 words to 96000 words out of 105161 words

Chapter 32 - CIRANIN AMANA BOOK COMPLETE BY Asma Baffa .pdf

22 Mar 2025

13414

tare da furta ai ka cancanci na yafe maka,na yafe maka Deeni,Alim
yace wai ke meke damunki ne yanzu ni gaskiya Amanata ta farko nake so bata yanzu ba,gwara
Amana me Zafi da masifa ta,ke wannan Amanar ta yanzu ban gane miki ba,Dariya Amana
sukayi gaba daya harda su tsoho
Matar ce tace gani nima dan Allah a yafe min,ni kun Sanni farin sani Saude ce,duniya ta
dawo Dani haka,Amana tace na Dade da ganewa kece Saude,ko dan dukan da kikaci a
hannuna na yafe miki,Alim ne ya kwalawa Amana Biro a kanta na gaji da wannan abin naki
komai kice na yafe,
Amana tace idan bamu yafe ba mene ribar mu kawai ka kyalesu,Allah ma yana yafiya bare
wasu mu,duniyar nawa take kowa yaje da halinsa,Halinka jarinka babu abinda dan Adam zai
hanaka ko yi ma a rayuwa face da Sanin Allah,
Deeni kuwa shi ya taimaka min da tuni na mutu ya kaini asibiti ya biya kudin magani lokacin
da bani da kowa bani da ko sisi lokacin da cikina ya zube,
Ka kusa aure kuwa?Amana ta tambayi Deeni,Alim ina ruwanki dashi kuma,Amana cikin rada
suruntunta ya kaita tacewa Alim da fa sanda Ina Adamawa so na yakeyi sosai,sunansa Na me
Kunu,bai San ni matar Aure bace,amma da na fada masa ya hakura,har address dinmu na
bashi,niyya ta na bashi kanwata Salam tunda ta girma,
Kafin kace me Alim mood dinsa ya canja gaba daya ya bata rai sai muzurai yakeyi hannu
yasa ya gyarawa Amana hijab dinta sosai sannan yace to Alhmdllh duk mun yafe muku,ke
kuma Saude kin makara Baba da kika sa aka sassara ya rasu shariarku sai a lahira sai dai kiyi
tuba Allah ya yafe miki nasa laifin, Allah kiyaye gaba,kuje driver ya kaiku wajen shiga mota Ku
koma gida Allah kiyaye gaba,

Jansa gefe Amana tayi tace haba honey jirgi zaka biya musu,harara ya balla mata,pls kaji da
kudin nan fa mene amfaninsu,to bari ni na biya musu a nawa kudin,Alim yace gwara da kikace
ke ni dai bazan yi asarar kudina ba bare waccen munafukin yaron wlh karya kara zuwa
gidana,kuma baza a bashi kanwarki ba salon a dinga zumunci dashi yana kallonki yana jin
dadi,ko ya zauna da Salma ya dinga tunanin kamar kece.
Suyi sauri su bar min gida.

Amana kuwa Bedroom dinsu ta koma tare da jawo wardrobe wajen da Alim ke ajiyar kudi da
yawa ta ebo tare da dubawa a hand bag, Alim yana Palo a kwance ta wuce da sauri ya jawota
ina zakije ya kuma ganinki ya dinga sonki,yana sha'awar min ke, zuwa zanyi na
sallamesu,kudina kika ebo? Yeah cewar Amana kudinmu dai,zauna to naje ni na sallamesu idan
akan jirgine zan biya amma ki zauna baza ki kara lekawa Palo ba sai sun tafi,
Ai dai mayi Sallama ko da Deeni ne cewar Amana,Alim ne ya fita tare da banko kofa,yana
zuwa yasa driver ya kaisu airport sannan yace tace ku gai da gida,Deeni kuwa yasan Alim ne
ya hana ta fitowa sabo dashi,kawai sai yace ni dama Abuja zan wuce ba sai ka bani komai ba
na gode ina da returning ticket dina,Alim yace Good tare da tabe baki,haka suka tattara driver
ya kaisu suka ware,Deeni dama da kudinsa shi yana da sana'a.
Alim kuwa masu aiki ya kira yace su kara share masa Palo su goge shi tas su sa air freshener
da yawa da turaren wuta,wai dan karma Amana taji kamshin kalar turaren Deeni kwaro domin
Deeni kwaro dan gayune sosai kuma kyakyawane ba laifi,

Deeni kwaro kuwa Bai zarce ko ina ba sai kano har gidan su Amana,yaje cikin gidan ya
gaishe da Umman Amana yana ta zura Ido ko zaiga kanwar Amana ya so ta ya aureta,yana
zaune da Umma suna hira sai ga Salma ta shigo kuwa daga makaranta Salma yan Ss3,ai kuwa
Deeni yaga Salma kyakyawa itama yar caras da ita, Umma ya tambaya Umma wannan yarkice? Umma tace yar gidan Inna ce kishiyata, nan ya
shiga ina..Ina...da kyar yace Umma zata bani ita,Umma kuwa taga Deeni ya shiryu sosai gashi
dan garinsu tasan asalinsa tace me zai hana idan tana sonka,ka nemi soyayyarta.

Salma ce ta shigo dakin Umma tare da cewa Umma ina su Inna da sauran yara? Umma tace
sun tafi gaishe da yayan Babanki Alhaji Shehu,zasu biya gidan sauran yan Uwa ma sabo da
kulla Zumunci,
Shagwaba Salma ta fara wai Umma amma basu jirani ba nace zanje gidan Anty Maimuna
fa,Maimuna itama yayar su Amanace me aure da yaranta.
Deeni a ransa yace naga waje irin wannan shagwaba haka me birgewa,
Salma gaishe da Deeni tayi sannan ta fita tana fushi,
Mikewa Deeni yayi tare da yiwa Umma Sallama zai tafi Adamawa,har kudi ya bawa Umma,

Umma ta kwalawa Salma kira,Salma na zuwa Umma tace kinga wannan Saurayin daya fita?
Salma tace eh,to Sonki yakeyi kuma mutumin kirki ne,Antynki Amana ma ta sanshi sosai,maza
kije Ku gaisa ki rakashi zai tafi gida a garinmu Adamawa yake.

Salma murmushi kawai tayi tare da zurma hijab ta fita wajen Deeni,jikin kofa ta samu Deeni
yana jiranta,cike da kunya taje wajensa suka gaisa,Deeni da idonsa yake a tangare tuni ya
tsara Salma saiga Salma kamar ta Dade da saninsa Suna ta hira,duk yaron da ya shigo in dai
kanin Salma ne ko kanwa sai Deeni ya bashi Dari biyar sabuwa kar, Haka suka gama Hira ya tafi tare da karbar Number Salma.

Gwaggo dasu Inna kuwa kaf yan uwan Sulemanu sai da suka je suka basu hakuri suka ce
kuma za a ci gaba da zumunci,sosai sunji dadi,Alhaji Shehu yace zasu je har gidan su Amana
da Badriyya da sauran yaran Sulemanu inda zasu ga mazauninsu a kara karfafa Zumunci.

Amana tana zaune Alim ya shirya zai fita office,Amana tace dan Allah Baby kaje Dani kaji
gidan so boring idan baka nan,
Lallashinta ya fara tare da rungumeta yana goga fuskarsa a wuyanta tare da magana a
hankali,ba dadewa zanyi ba,kinga anjima su Asiya zasu zo da Autan Mum,idan mun tafi kinga
ba kowa gidan ko,kai ta girgiza shike nan to bari na jirasu,
Zagayowa yayi da ita gabansa tare da fara kissing dinta,ya naga kamar kina fushi,murmushi
tayi ba fushi nayi ba kawai dai banjin dadi ko period dina ne zaizo I think,har yau bamu samo
Aabid ba?na zata ma mun samu dana ga kina wani kiba da kyau,

To da alama bamu samu bafa dan Allah kayi sauri ka dawo a kara nemowa ko zamu dace
kafin period yazo kasan yanzu mahaifa ta bude,na matsu a samu Aabid dina,dariya Alim yayi
tare da cewa ai kece idan nace a kwana ana yi sai kice waye waye ai gashi nan anji samowa,
shagwaba ta fara masa da badan ya daure ba bazai iya fita ba, Yana fita ta zauna tare da kiran Badriyya suna ta Shan hira,bayan sun gama ta kira Sakeena
ma,ta koma su Hamza da su Anty Maimuna,Sadiya da sauran yan Uwa.

Tana gamawa ta fada kitchen tare da shirya lafiyayyen girkinta,ta kara gyara gidan ko ina
neat,Alim minti kadan zai kirata yaji wai ko period yazo sabo da sauri yakeyi kar yazo baiyi
komai ba,
Wanka Amana ta fito tare da yin Sallar sa'asar ta shirya cikin Atamfa fara me zanen baki
Riga da skert dai dai ita Dinkin zamani tayi matukar kyau Sosai duk wanda ya kalleta sai ya
kara,tana fesa turare taji door bell,takawa tayi har kasa ta bude kofa Asiya ce da Autan Mum
suka kwada Sallama tare da shigowa, Amana da fara'a mutunci hade da karramawa ta tarbesu har palon Sama ta kaisu,suna ta
hira ta cika musu gaba da lemuka da ruwa hade da dambun naman kaza,
Asiya tace na girmeki nesa ba kusa ba ni Antynki ce amma ya zanyi matar yaya dole nace
miki Anty,dariya sukayi Amana tace ya Zama dole kuwa ko na fada masa ya zaneki.
Asiya tace rufa min asiri da masifar ya Alim akanki.
Yanzu dai ankon biki na kawo miki fa gashi kuma zan fada miki shirye shiryenmu sai kiji ko
zaki kawo idea,
Auta yace hmm Anty Asiya zumudi sai mijin ma ya rainaki wlh danma ya Ahmad ne me
hakuri,kin fiye zumudi,Amana tace jinji yaro da'allah rufe mana baki manya na magana.
Dariya sukayi duka,domin Autan Mum ya girmi Amana sosai.

Suna ta hira da tsare tsaren bikin Asiya sai ga Matar Ya Nura ta zo itama tare da mijinta
Nura babban yaya,nan suka kacame da hira da nishadi,Amana da Asiya suka jera abincin da
Amana ta dafa kala wajen uku,Asiya ta dauko wani mugun azababben foodflask guda hudu ta
kawo,Amana da Sauri tace ke yan mata wannan na me aiki me gayya ne,na Oga kwata kwata
ne,ko a Ido kin San na me girma Alim ne angon....kasa karasawa tayi saboda hada ido da
sukayi da ya Nura,wayancewa tayi da murmushi tana sosa wuya,Asiya ta sheke da Dariya tare
da matar Nura suna tsokanar Amana su Na Ogan zasu ci,
Amana ta kwashe flasks dinta ta mayar kitchen,ta bar musu nasu suma masu kyau amma ko
kafar na Alim basu kama ba,

Alim ne ya shigo palon da Sallama yagansu suna ta ciye ciye ana ta labari,
Dan Zama yayi suka gaisa yana musu sannu da zuwa Amma idonsa yana ga Amana yana
aika mata da kallo tare da harara wai bata je ta tarbeshi ba,
Kunya taji tare da dauke kai,ina zuwa Alim ya shige bedroom, Amana tana so taje wajensa
tana dan Jin kunya wai zata yi musu wayo tace Asiya Amarya bari na dauko miki wani abu ko
zai miki,zuruf ta shige dakin Alim,
Tana tafiya suka kama dariya wannan yarinyar da abin dariya take cewar matar Nura,Nura
yace ina ruwanki yan sa Ido,

Alim daga shi sai towel iya kugu zai shiga wanka,yaji Amana ta rungumeshi ta baya tare da
kwantar da kanta a bayansa,
Sai yanzu zaki wani zo,murmushi tayi yi hakuri kunya nakeji ta ya Nura,
To ya Nura tsaya ki gani shi a gabanki zaiyi abinda yaga dama da matarsa.

Muje kayi wankan kawai,suna shiga toilet yace sai ta shigo sunyi kuma ba iya wanka zaiyi ba
ta gane nufinshi kin yarda tayi tace ni bana son kara wanka ga baki munyi kuma dadewa
zamuyi fa,
Jeki to karki Dameni da Surutu kuma karki kara cemin kina son Aabid tafi, Amana magana
tayi bata fito ba kamar kunkuni,Alim yace me kikace,Amana tace a'a cewa fa nayi Allah zai
kawo ai,oh Allah ya taimakeki kuma idan banyi ba baza ki samu Aabid ba yarinya,
Dole ma kayi min na samu,toilet Alim ya shiga,Amana ta bishi ciki,to mene zaki kalle min
tsaraici kuma? Dariya tayi ba kallonka zanyi ba kayi wankanka,a toilet din ta nemi waje gefen
Bowl din wankan tayi zaman ta,Alim ya fara wankansa,tace haka akeyin wankan,shuru ya
mata,can baka sabulunba fa, Sabulun ya mika mata ungo karasa,hannu tasa zata karba ya jawota tana ihu ya tsundumata
ciki tare da danna shower ruwa shaaa ya jikata gaba daya,

Ruwan na zubowa ya tubeta gaba daya ya sake mata sabon wanka,sai kukan shagwaba
takeyi masa,
Sai da ya gama murzata son ransa da kyar ya hakura towel daya ya daura musu tana cikin
jikinsa kamar masu koyon tafiya suka fito ko mai bata shafa ba tasa doguwar Riga brown color
ta dan gyara fuskarta sosai sannan ta zurma hijab har kasa wai kar su Asiya su gane anyi wani

abu gashi har ta sake wanka ta canja kaya.tana fitowa suna kallonta suka San anyi wani abu
domin rigarta ana hangowa ba kayan dazu bane,

Auta a ransa yace kut Amma ya Alim jaraba ne daga dawowa shi yasa yake ta
kallonta,muma dai mayi auren nan,Alim da 3qtr da T-shirt ya fito suka fara hira,Amana ta kawo
masa abincinsa ta jera a gabansa ta cika gabansa tab,har yafi na bakin domin na Alim na
musamman,abin mamaki hattana kalar spoon din Alim daban ne ba irin na kowa bane, Alim ne ya kifta Ido Amana ta kau da kai,ya kara kashe mata Ido ta juya gefen Asiya,
Nufin Alim wai tazo ta bashi yaci abinci da kanta,ita kuma tayi kamar bata gani ba,

Su Nura suna kallon abinda Alim keyi,magrib na gabatowa suka ce zasu tafi har mota suka
rakasu,Auta da Asiya motarsu daya,Nura da matarsa ma haka,
Suna tafiya a hanya Alim ya dagata sama tare da sabata a kafada har cikin Palo,

Amana ta fara waec a cikin jerin motocin Alim ake kaita tare da securities sai ta gama suna
jiranta a dawo da ita gida,
Har ta gama waec suka fara Neco,
Tana gamawa ta shirya cikin tsadajjiyar motarta taje har kofar gidan Dan Uzuri,
Mutane da wanda suka Santa sun gaisa suna mamakin canjawarta domin basu gane Amana
bace sam, saboda da kyau da haduwa da tayi ana kallonta an San Naira ta ratsata,
Tambaya tayi ko dan Uzuri na nan,suka ce ai Dan Uzuri ya Dade a prison da kyar aka sakeshi
amma yanzu ya koma kauyensu da rayuwa,gida ta koma tana shiga Alim ta hango a Palo yana
kallon News tana zuwa ta kwantar da kanta a cinyarsa tare da mikar da kafafunta a doguwar
kujera yana mata sannu da gajiya har bacci ya dauketa.
Bikin Asiya yana ta gabatowa kuma Mum zata zo bikin Yarta sannan gidan Alim zata
sauka,Alim ya kira Mum suna hira,Mum tace bawa matarka waya mu gaisa,Alim dai a tsorace
ya mikawa Amana,Amana cike da ladabi kamar tana gabanta ta gaisheta,Mum cike da fara'a
suka gaisa harda Jan Amana da hira.
Alhaji Shehu da sauran kannen Sulemanu ne suka yo waya zasuzo gidan Amana suga
yarsu.
Murna wajen Amana ba a magana suma yanzu danginsu suna kulasu.Alim ta sanarwa shima
yaji dadi ko ba komai dangin matarsa ne.





Korafi ya karbu Maman Minat,godiya da tunatarwa.

AsmaBaffa.
✳CIRANIN AMANA✳



195-200



Official




By
AsmaBaffa







Kwana biyu tsakani su Baba Shehu da Ahj Sani tare da kannen Sulemanu,sai su Anty
Maimuna,Anty Sajida,Maryam da Sauran yayyen Su Amana mata,duk suka sauka a
Lagos,kwanansu daya suka tafi tare da sha tara ta arzikin da me gidan na Amana ya musu,su
Hamza kuwa da su Umman Amana sai bikin Asiya zasu tattaro suzo suma Asha biki dasu.
Alim ne ya dawo daga Office 5pm,Amana ta fito cikin hadewarta data saba me rikita
Alim,rungume abinta tayi kam tare da masa sannu da zuwa tana sakin murmushin dake kara
mata kyau,wani Apple Juice da ta hada da kanta ta dakko me zanyi a glass cup ta bawa Alim
dinta yasha yana santi,
kashe murya tayi tare da kara kasa da ita can kasan makoshi tace muje ayi wanka ko?
shagwaba ya fara mata ni nayi wanka da kaina fa? Sai kace marar gata,ni dai ki min da kanki
wani wanka na iya me kyau,

Dariya suka saki gaba daya Amana tana dariya ta dan tureshi shagwaba kullum ko? Alim
yaci gaba da shagwabarsa pls......mana ni ban iya wanka ba,yanda yake Abin Amana sai faman
dariya take tace muje to,da sauri yace ok ko kefa,
Tsayawa yayi kamar jariri ta cire masa kaya,ta kaishi toilet ta fara masa wanka,aka zo wanke

wuya Alim ma bai son a taba masa wuya sai ya dinga dariya kamar yaro, Amana tasan halinsa
tace daga wuyan na wanke, Yana dagawa tasa sabulu ai kuwa dama ta sani sai ya kyalkyale
da dariya tare da makale wuyansa,

Halinka kenan kara dagawa yayi ya kyalkyale da dariya tun kafin ta taba wuyan yake makale
abinsa,yana sorry to na tsaya,da kyar ya bari aka gama wankan.

Tazo ta fara shafa masa mai,Amana ta dan dakeshi a kafada cikin wasa,tsaya mana
joo....aka zo sa kaya yace shi Baza a sa masa kaya yau ba sai gobe,to da me zaka zauna? Ki
barni da towel dina nayi sallah fa saura magrib da Isha idan zanyi nasa kayan,
Kyaleshi tayi suka koma dining suna cin abinci,brush ta masa itama haka,

Chewgum ya zaro zai tauna a baki,Amana tace ina nawa?ka sanmin kaji ta fada kamar zata yi
kuka,a kan Mirror na gani na dauko,to nawa ne fa tun yaushe nake ce ma ka siyo min ko sweet

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login