Showing 27001 words to 30000 words out of 77516 words

Chapter 10 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

shi daga maganar da yake ya mi?e tsaye yana hangota tana nufowa inda suke, fosta ya yi dan hatta numfashinsa ji ya yi yana barazanar barin gangar jikinsa saboda Wimaucewa da kuma wani mugun bugawa da zuciyarsa ke yi da ?arfi kamar ya yi tseran gudu na kilo miter masu yawa.Idanunsa kwa ko ?iftasu ba ya yi har ruwa taruwa ya yi a cikinsu dan ba ya so ya ?iftasu ya nemeta ya rasa duk da yana ganin kamar a mafarki yake ganinta.
Abulkairi dai ya tsaya shi ma cikin mamakin abokin nasa sai ya kalli Hizbullah sai ya juya ya kalli wacce ya ga Hizbullah Win na kallo cikin tsantsar ruWewa, abin da ke baiwa Abulkairi mamaki wacce Hizbu ke kallo mace ce kuma Hizbu maza ma bai damu da kallonsu ba bare wasu mata ma da ya tsani zancen mace in ba zancen Ridallah ba ko na Ummarsa ba dan ko Abulkairi na yiwa Hizbu zancen tasa budurwar Bilkisu sai ya ce shi fa ba ya son surutu amma yau shi ne ke kallon mace ba Ridallah ba macen ma wannan mai kama da arnan dan gabaWaya jikinta babu alamar da za ta nuna akwai muslunci a tare da ita.


Tana dab da ?arasowa saitin inda suke Hizbullah ya dawo daga shork Win da ya shiga, cikin zafin nama ya tafi gareta yana zuwa kawai ya sha gabanta cikin wata iriyar murya ya fara magana.


"Ridallah dama kina raye? Ya aka yi kika zo ?asar nan? Yaushe kika yi watsi da tarbiyarki kike irin wannan shigar Ridallah, yanzu ace ko tunani na ma bakya yi kin manta da ni ina nan ina cikin damuwar rashin sanin takamai man inda kike, a raye ko a mace amma kina nan lafiya ?alaw hankali kwance kin...


"Wai ?wal?walwarka ta taSu ne? Ya daga ganin mace ka zo kana mata wasu surutai cikin gushewar hankali, shin ka manta ba a Nigeri'a kake ba? Ko kuwa wannan ta maka kama da bahaushiya dan Allah ka rufa mana asiri Hizbu" Abulkairi da ya ?araso gabansu ya ce yana bin Hizbu da kallon takaici, ita kwa Iftihal da ta langaSar da kai gefe idanu kanne fuska a yatsine dan ita takaici ne ma ya hanata magana dan tana jin komai su ne ke mata kallon kamar ba bahaushiya ba.


"Wai ni kake yiwa eaWannan maganganun? Shin ka Wauka bana cikin hayyacina to Ridallah ce wannan kuma ni nasan tana jin hausad shi yasa ka ga ina mata magana, kai...

?aran wayar Iftihal Win ne ya katse Hizbu daga maganar da yake ?o?arin ?arasawa.Kallonsu ta yi tare da banka musu wata uwar harara kafin ta buWe baki ta ce


"Dallah malamai ku ja jikinku a nan, ko an faWa muku nan ma Nigeri'a ce inda kuka saba yaudarar ?anmata to ko a Nigeri'a ai na wice ajinku da gani ma wannan gwabnati ce ta biya muku karatu kuka samu damar ketowa hazo"

Ta faWa tana gyara glases Win fuskarta.Baki sake Abulkairi ke kallonta jin hausa a bakinta kamar jakin garinsu Kano dan bai taSa tunanin ta san inda hausa ma take ba ganin hasken fatarta da kuma yanayin shigarta duk da musulman ma na irin shigarta a nan Win ma amma ko hula suna sanyawa su rufe kan su ko Wankwali amma ita haka gatsal kamar inyamura.

"Au bahaushiya ce ke ashe, to koma menene waye ma zai so mace irinki ko a ?afa aka Waura mana ke sai mun kunce, shi ma wannan dan bashi lafiya ne amma mai zai yi da ke ba zia taSa ?aunark...Hannu Hizbu yasa ya rufewa Abulkairi baki yana jin kamar ya hau shi da duka.

"Wai me yake skaa kake min haka ne ya za a yi macen dana fi ?auna duk duniya bayan uwata ka ce bana ?aunar...

Hannun da Iftihal ta Waga za ta Wauke Hizbu da mari Abulkairi ya yi saurin dam?e hannun shi ya dakatar da Hizbu daga maganar da yake yi

MMN AFRAH









Page3?? 1?? &3?? 2??




"Ridallah ni za ki mara?" Hizbu ya ce cikin mamaki yana ?an?ance idanu, dan shi ganin abin yake kamar almara, yana gani wai Ridallah Winsa ce ke nuna bata san shi ba har tana Waga hannu za ta mareshi taSWi lallai akwai lauje cikin naWi kenan dama ba son shi take ba? Kenan dama so ne na yarinta yanzu ta girma idanunta sun buWe ta manta da shi ta barshi shi yana fama da tunaninta kullum cikin kallon Wankunne da flower da ta bashi yake ba ya son ko kaWan ya manta da ita ko da na second Waya ne dan yana ganin ya ci amana ya ci amanar ?aunar da take masa da ma wacce yake mata baki Waya.

Kallon shi ta yi a raine tare da buga wani uban tsaki, ta fido wayarta da ke ta faman ?ara daga kiran ya katse sai wani ya shigo, tana dubawa ta ga Alhajin nan ranta ya ?ara Saci dan tana ganin duk shi ya jaza mata wannan bala'in da sun wucewarsu Hotel da duk haka bata faru ba yanzu gashi nan ya sanya wannan mai kama da mahaukatan yana kiranta da wani suna da bata ma taSa jin mai irinsa ba.


"Ina jinka" Shi ne kawai abin da ta ce.



"Ya na jiki shiru ko dama baki taho ba?" Alhajin ya tambayeta daga Waya Sangaren.



"Ka taho wajen hanyar fita ina wurin wani ya hanani tafiya" Ta ce dan bayan ta Waga wayar ma ta yi ?o?arin tafiya amma Hizbu ya janye Abulkairi daga gabansa ya je ya sha gabanta zai cigaba da jefa mata tambayoyi marar kai da ?afafu.Tana kashe wayar ta kalli Hizbu cikin takaici ta ce



"Za ka gane shayi ruwa ne dan sai nasa an kulleka an koya maka karatun da baka da ilimi a kan sa tun da baka da hankali" Ta ce tana Wauke idanunta daga kallonsa.



"Shikenan Rida na ji baki sanni ba kamar yadda kika nuna amma inaso ki faWa min ina Baba take shin tana raye? a nan ?asar take ko tana Nigeri'a?" Wani kallon baka da hankali ta masa ta Wauke kai dai dai nan Alhajin ya ?araso dan ta tura masa hotonta yana hangota ya ganeta.

Babban mutum ne dan da ganinsa ma ya haifi Iftihal Win sanya yake da wandon jeans da riga mai dogon hannu sai wani uban ?aton tunbinsa tari guda yana reto kana ganinsa kasan kuWi sun sami wuri sun tare.



"Baby Iftee menene hakan me ke faruwaa ne?" Ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta dan yana ganinta ya ji wata kasala ta baibayeshi, ganin irin shigar da ta yi mai bayyana surorin jikinta.


"Kalli wannan ba?auyen ne yake kirana da wani suna ya kafe dole ya sanni bayan ni ko a mafarki ban taSa ganin ko da mai kama da shi ba" Ta kai ?arshen maganar tana wani karkaWa jiki dan Alhajin ya ji daWin Waukan mataki.

Wani haushi da kishi ne suka turnu?e zuciyar Alhajin lokaci guda ya kalli Hizbu da ya babbake a gaban Iftihal ya ce


"Malam halan daga turu ka fito ko? Ka taSa ganin yadda ake ni?e mutum a maidashi dambun nama? To akan wannan yarinyar zan sanya a danda?a ka har sai cikinka ya haWe da bayanka, dan haka ka fita harkarta ko a mafarki babu kai babu ita" Yana kai ?arshen maganar yasa hannu ya hankaWa Hizbu gefe guda sannan ya kama hannun Iftihal suka juya suka fara tafiya dan maimakon su shiga ciki hanyar fita suka nufa, ya maida hankalinsa kwacakwam kan ta ita kwa sai wani rausaya jiki take dan ?ara Wauke masa hankali dan tana so ta samu kuWaWe masu yawa daga wurinsa dan Auntynta ta faWa mata cewa ta tabbatar ta yi iya yinta dan ta wanki gara.


Hizbullah ganin Alhajin nan ya ?ara saka masa damuwa kenan Ridallah ta ma wuce inda yake tunanin wato shigar jikinta kaWai da kuma yadda Alhajin nan ya kamata ya tabbatar da ta sanya kan ta a wata rayuwa dan da gani ba mijinta bane dn da mijinta ne da yace masa mai ya haWashi da matar aure? Yana hango sun shige ?ofar ta rufo cikin hanzari ya fara taku zai bi bayansu dan yau sainya ga abin da ya turewa buzu naWi ba zai taSa barin Ridallah ba, taku Waya biyu Abulkairi ya yi ya dam?i rigarsa dan shi abin na Hizbullah ya fara bashi tsoro dan ya tabbata dai Ridallah ta fara masa gizo.Duk da dai bai taSa ganin yarinyar ba ko a hoto bare ya ce ita ce ko ba ita ba ce dan Hizbullah memorinsa mai Wauke da hotunansu ya faWi a ranar da zai baro Nigeri'a dan haka yanzu ko hotonta bashi da shi, amma abin da ke baiwa Abulkairi mamaki me yasa bata taSa masa gizo akan duk mutane ba sai akan wannan lallai akwai ayar tambaya tun da dai yarinyar bahaushiya ce alamu sun nuna ?ar Nigeri'a duk da a yadda Hizbu ke bashi labari ba ya jin yarinyar za ta yiwa Hizbu haka amma kaidin mata yawa gareshi kuma rayuwa da burika suna canja mutum.


"Ka saka ni kar su Sace min"Hizbu ya ce cikin Sacin rai.


"Haba abokina ka dawo hayyacinka mana me yasa kake hakane, shin ?auna da tunanin Ridallah har zuciyarka ta fara Wakko fuskarta tana Worawa a gangan jikin wata kana yiwa wata kallon Rifallah?" Abulkairi ya faWa yana kama duka hannayen Hizbu da ?arfi ya ri?e dan ya ga sai fisga yake yana so ya ?wace ya bi bayansu.




"Abulkairi ka sake ni na ce idan suka Sace min sai ka gwammace baka sanni ba"Hizbu ya ce yana zazzare idanu dan ya kasa ?wace ri?on da abokin nasa ya masa saboda rauni da damuwar da ya tsinci kan sa a ciki sai ya ji gabaWaya ?arfinsa ma ya bar gangan jikinsa



*Gumel*


Ridallah har an shiga Senior secondry scul yanzu haja tana S.S 1 sun yi hutun first term dan haja yanzu tana gida hutu ake yi.Sanye taje da doguwar rigar jar atamfa an mata manyan fulawoyi ba?a?e da la'asar sakaliya ne, share tsakar gidan take cikin nutsuwa.Sai da ta gama sharewa tas ta kwashe sannan ta wanke ?afafunta da hannunta sai kuma ta je ta iza wutar da take dafa miya dan har ta gama tuwo, da ta gama wanke -wanke sai ta kwashe tuwon shi ne ta yi shara.

?akinsu ta nufa inda Baba Habiba take dan Mama Rahma ba ta nan ta fita unguwa gidan barkar haihuwa, zaune ta samu Babarta ta ta yi shiru shigowar Ridallah ya katse mata shiru da take yi.


"Wai Baba ko zafi bakya ji kin zauna a Waki ga tabarma can na shinfiWa miki a inuwa ki fita kisha iska amma kin zauna a Waki kamar boka" Cewar Ridallah tana murmushi ta samu wuri ta zauna a kan katifar da ke lailaye da shinfiWar wankekken zanin gado dan Ridallah ba dai tsafta ba komai nata tsaf gwanin sha'awa.


"Kawai dai na fi son zaman Wakin ne"Baba ta faWa cikin sanyin murya.



?ago kai Ridallah ta yi tana kallon mahaifiyarta ta dan kwata-kwata amsar ba ta gamsheta ba dan ba haka Babar ta saba mata magana ba musamman ma ta kan mata barkwanci su rin?a dariya abinsu.


"Baba wai ko bakya jin daWi ne yau tun safe nake ganinki cikin damuwa?" Ridallah ta ce tana matsowa kusa da Baba ta Wora hannunta a kan cinyar Baba, hannu Babar ta sanya ta ri?o hannun Ridallah ta ce



"Ridallah babu abin da yake damuna, kawai dai wani lokacin na kan tsinci kai na a cikin damuwa idan na tuno da mahaifinki" Ta faWa tana sanya hannu ta goge ?wallar idanunta.Ita ma Ridallah ?wallar ce ta ciko mata idanu jin maganar ta Baba ta sosa mata inda yake mata ?ai?ayi dan duk lokacin da aka yi zancen mahaifi sai ta tuna nata bare kuma aka yi magana a kan mahaifinta ta kan tsinci zuciyarta cikin rauni hakan yana tuna mata cewa ita marainiya ce ba ta mahaifi a raye dan ita ko a hoto ba ta taSa ganin mahaifinta ba kawai dai ta san Baba ta ce mata kamarsu Waya da mahaifin nata babu abin da ta bari na mahaifinta to idan ta kalli kan ta a madubi ta hakan take ganin fuskar mahaifinta a jikin fuskarta.



"Ki yi ha?ari Baba kawai mu cigaba da masa addu'a Allah lulluSesa da rahamarsa"



"Amin Ridallah" Baba ta ce tana rungumo Ridallah jikinta cikin tausayinta dan ita ba wannan tunanin mutuwar bane kaWai damuwarta akwai wata damuwar da ita kaWai ta san da ita ko Ridallah ba ta san da hakan ba.





Haka dai Ridallah ta cigaba da lallashin mahaifiyarta a haka har Iya Rahma ta dawo lokacin dab da magriba ne ta kaWa miyar sannan ta shinfiWa musu sallayoyi akan tabarma ta ajiye musu carbinsu aka sannan ta wuce ta yi alwala.Bayan sun gabatar da sallah suka Wore hirarsu har sai da aka yi sallar isha'i suka yi sannan Ridallah ta zubo musu tuwon su ka ci.


Haka suka yi hirarsu har wajen ?arfe goma ganin an kawo wuta sai Ridallah ta sanya musu gidan sauro a Waki da yake ita Iya Rahma a nata Wakin take kwana su kuma a Waki Waya, hakan ya sa ta shiga Wakinta su ma suka mata sallama suka shiga nasu Wakin.Bayan sun yi addu'a suka kwanta suna ?ar hirarsu har bacci ya yi awon gaba da su.


Cikin dare wasu samari guda uku suka diro daga saman katanga, sun tsaya suna ?arewa gidan kallo.

"Baaba ka san fa ba mu san Wakin da yarinyar take ba kar fa mu je ka hakewa tsohuwa" ?aya daga cikinsu ya faWa yana kallon wanda ya kira da suna Baaba.

"Kai fa gara ne wa ya ce maka a duhu za a aiwatar dole ai a haska fitila kuma ko ma ba a haska fitila ba ai babu yadda za a yi na kasa banbance tsohuwa da yarinya sai ka ce wani kai" Baaban ya bashi amsa.


"Mu shiga nan Wakin ka ga takalmi biyu da alama wannan ?aramin na yarinyar ne ka ganshi na soso mai Wan tudu" ?aya ma ya faWa yana washe baki, gabaWayan su suka bushe da dariya dan da alama ma ?an shaye-shaye ne dan daga maganarsu ma ana iya fahimtar su waye su.

"Fito da bindigar nan" ?aya ya faWa cikin raWa-raWa


"An gama Oga" Ya faWa yana Waga rigarsa ya fito da bindiga daga inda ya soketa a ?ugunsa.

KarSar ya yi ya jujjuyata a hannunsa yana dariya, su ma dariyar suka yi kafin suka Wunguma suka shiga Wakin da su Baba Habiba suke dan ?ofar buWe take hatta da labulen a Wage yake saboda zafi sai ?aran fanka da ke ta aikinta suka sai baccinsu suke hankali kwance.

Da fitilar wayarsu suka yi amfani suka gano makunnar ?wan Wakin suna kunnawa kwa haske ya gauraye Wakin, hango su Ridallah suka yi cikin net suna ta bacci Ridallah sanye da rigar bacci mai ?aramin hannu.







d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?



Page3?? 2?? &3?? 3??

Hannu Waya daga cikinsu ya sanya ya Wauki ruwa a wani jug ya zuba a hannunsa ya watsawa su Baba Habiba da ke bacci, gabaWaya suka tashi suna dube-duba Ridallah tana murtsuke idanu, a tare suka sauke idanunsu akan ?artan mazan da ke tsaye suna rarraba jajayen idanunsu sai wani wari ke tashi a jikinsu.


"Baby ya kike kallonmu a tsorace wurinki fa muka zo" Ogan nasu da ke ri?e da bindiga ya faWa yana washe baki.

"Subhanallahi! Dan Allah ku yi ha?uri ku rufa mana asiri" Baba ta faWa tana ?o?arin gyara Waurin zaninta dan har sun fito daga cikin net Win nasu.


"Tsohuwa idan ba so kike a haWa da ke ba ya kamata ki yiwa bakinki mukulli ki fito ki jira oga a waje ya kammala aikinsa"

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un! Dan Allah ku taimaka min"Ridallah ta ce a kiWime tana Wora hannu aka, dan lokacin ta fahimci abin da suke nufi dan har Ogan nasu ya cirw belt Winsa.


"Dan Allah ku yi hakuri ko me kukeso na baku zan baku amma kar ku keta haddin marainiyar Allah" Baba ta faWa tana dur?usawa a gabansu hawaye na zuba a idanunta.

"Ko ki fita ko mu fitar da ke da ?arfin tsiya, in kuma kina son gani akan idanunki a karSi amarcin kyakkyawar Wiyarki to zaki iya neman wuri ki zauna dan muma fita za mu yi"?ayan ya faWa yana karSar bindigar hannun Ogan nasu ya nuna Baba da ita, dan Ogan nasu ya raja'a da son Salle maSallin jikin wandonsa dan so yake su yi su gama dan gudun kar a samu matsala.

Cikin tsananin tsoro Ridallah ta kai kallonta kan bindigar da aka saita Baba Habiba da ita, wani abu ne ya Warsu a ran ta lokacin da ta kafe bindigar da ido, dan dama da ganin samarin nan ta san da wuya su mallaki bindiga dan kawai kana ganinsu kasan kawai ?an iskan unguwa ne irin masu dira gidajen mutane su saci waya da sauransu ba wasu ri?a??un Sarayi bane.Fakar idon su ta yi dama a tsugunne take ta kai hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login