Showing 6001 words to 9000 words out of 77516 words

Chapter 3 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

gishiri ya yi yawa ko dai an cika yaji ita ulcer ta za ta tashi kuma duk gassada ce dan ta ga Alhajin yana ta yabon abincin idan ana ci.Irin fitintinun da take yasa ya dakatar da Hajiya Azima da yun girki akan a bar kuku yana yi domin shi ma kukun nasu gwani ne a wurin iya girki babu abin da bai iya ba.



"Ke dai bakya gajiya da caSa ado kamar mai shirin zuwa gidan biki"Alhajin yace yana yiwa Hajiya Azima wani kallo ?asa-?asa.



Murmushi ta yi kafin ta ce



"Ai indai abu ne zan yi dominka bana taSa gajiyawa da shi, bare kwalliya ai ni kai ne gidan bikin nawa, matu?ar na yi abin da ya birgeka to tabbas kwalliya ta biya kuWin sabulu"



"Ai ba ma kuWin sabulu ba harda kuWin soso" Yace suna dariya su biyun ban da Hajiya Hauwa da ta cika ta yi fam sai bin jikinta take da kallo?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? sanye take da ba?ar doguwar riga sai Wankwalin rigar da ta Waura shi ya yi baya,ko Wankunne babu a kunnenta, ita dama ta gaji da yin wata kwalliya duk shigar da za ta yi ko wacce irin sutura za ta sanya sai ta ga bata yi mata kyau kamar yadda kayan ke yiwa Hajiya Azima.


Ji ta yi kamar ta tashi ta bar wurin saboda tsabar takaici kamar sun manta cewa tana zaune a wurin.Wata hararar ?asan ido take bin su da ita su duka biyun.



"Assalamun alaikum" Safiya da ke goye da Iftihal ta yi sallama.



Hajiya Azima ce ta amsa mata sallama, ?arasa shigowa ta yi sai da ta zo har wurin nasu sannan ta sauke Iftihal Win ta ja kujera ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita dan idan Alhaji yana nan ba ya bari a baiwa Iftihal abinci a baki cewa yake a barta ta ci da kan ta.




"Iftihal Wina barkan ki da dare" Alhaji ya ce yana kallonta da murmushi.



"Abie ina yini" Ta faWa tana rufe fuska dan ta san ya fala mata cewa yaro ne yake fara gaishe da babba amma ita mantawa take in ma ba Abie ya faWa mata ba idan sun haWu, mantawa ma take akwai wani abu gaisuwa saboda Hajiya Hauwa bata koya mata gaishe da mutane.



"Lafiya ?alaw my daughter bakya gaishe da mutane sai sun ro?a ko?"


Shiru ta yi tana rufe fuska da hannayenta.


"To ni kaWai za a gaishe dani ?"Abie ya jefa mata tambayar dan shi mutum ne shi mai son ya ga yaronsa ya tashi cikin tarbiya.


"Momma ina yini" Iftihal ta gaishe da Hajiya Azima dan dama Momma take kiranta.


"Lafiya law iftihal" Cewar Hajiya Azima tana sakar mata murmushi.


"Aunty ina yini" Ta juya tana gaishe da Hajiya Hauwa.


"Lafiya" Hajiya Hauwa ta amsa a ta?aice, a wani da?ile kamar an mata dole.

Daga haka Hajiya Azima ta shiga zubawa kowa abincin amma Hajiya Hauwa da kan ta, ta zuba nata, aka shiga ci Iftihal na ci da kan ta ashe dama rainin wayo ne ace komai sai an bata a baki dan tsabar sangarta.


A haka suka kammala cin abincin, Hajiya Hauwa ta riga kowa tashi ta bar part Win ma baki Waya, su kuma suka koma cikin falon suna hira abin su cikin farinciki Abie na tambayar Iftihal batun zuwa islamiya ta ce bata je ba anan take faWa masa yadda suka yi da Aunty da safe da ra mata zancen zuwa school.Ran shi ta Saci sosai da ya ji bata je islamiya ba hakan yasa ya Wauki al?awarin gobe da wuri zai fito domin Iftihal Win ta tafi makaranta dan ya fahimci cewa Hajiya Hauwa da gaske ba ta son barin yarinyar ta raSi ilimi kowane iri sai nuna mata soyayyar banza da shagwaSata na wofi wanda hakan bashi da wani amfani.


d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 11&12



_Washe gari_

Tun wajen ?arfe shida da rabi Abie ya sakko ?asa, ko Hajiya Azima bata sani ba dan bayan ya dawo daga masallacin asuba da suka Wan taSa karatun qur'ani sai suka koma suka kwanta shi ne bacci ya Wauketa.Part Win Hajiya Hauwa ya nufa, nocking ?ofar ya shiga yi amma shiru ba a buWe ba dan babu alamar motsin mutum ma bare ya sa ran za a buWe, wayarsa ya koma ya Wakko sannan ya dawo ya shiga kiran Hajiya Hauwa, sai da ya kira sau uku amma ba a Wauka ba.

Hakan ya sa ya koma ya shiga ta ?ofar baya wacce ake bi ta cikin kicin sa'arsa Waya ?ofar ba a kulle take ba amma a rufe take.Yana shigowa ya kunna fitilun sannan ya haura sama, Wakin Iftihal ya fara zuwa ya buWe ya kunna ?wan Wakin kwance take tana ta bacci abinta, tashinta ya yi sai kuma ya kira telephone na Sangaren ?an aiki, yace a turo masa Safiya ta zo sashen Hajiya Hauwa yanzu.Ba a Wauki wani lokaci ba sai gata ta zo ya umarce ta data yiwa Iftihal Win shirin makaranta.


Yana fitowa ya nufi Wakin Hajiya Hauwa a buWe ya samu ?ofar bata sanya makulli ba, yana buWe ?ofar ya kunna futilar Wakin, sai bacci take gabaWaya ta cika Wakin da munshari filon da ta yi matashin kai dashi ya shiga bugawa amma ko gizau ba ta yi ba.Kallo yake ?are mata da alama ma ko sallah ba ta tashi ta yi ba dan dama Hajiya Hauwa ibadar nan da sau?i dan mace ce wacce bata damu da ibadah ba.


"Hajiya, Hajiya, Hajiya"Sai da ya kira ta sau uku tana Wan bubbuga kafaWarta sannan ta yi wata mi?a tana, tare da saurin sanya hannu ta make masa hannu dan bata ma san wa ke tashin ta ba.


"Wai ba da ke nake ba, kamar wacce ta suma ko kuma mai baccin mutuwa sai wani magagin bacci kike kamar wata yarinya" Cewar Abie a fusace dan gabaWaya ransa a Sace yake.

"Alhaji kai ne" Ta ce tana mai tashi zaune tare da sakin wata hamma ko bakin bata rufe ba.


"Ni ne mana kin zo kin kwanta kina ta faman bacci, babu sallah ba salati, sannan baki ji na ce yau Iftihal za ta je makaranta ba, amma maimakon ki tashi da wuri ki sanya a shiryata shi ne kika kwanta kina baccin asara sai ta makara ki ce ba za ta je makaranta ba"


"Wai yanzu Alhaji akan shirin zuwan Iftihal makaranta kake waWan nan maganganun?"


"Ba dole na faWa ba kina so ki koyawa yarinya ?in makaranta tun tana ?atamarta"

Baki ta taSe ta fara jan jiki ta sakko daga kan gadon ta nufi hanyar bayi tare da cewa


"Koma dai makarantar neman lahira ce a barni in shiga bayi in fito in fara gaishe da ubangiji" Ta ce tana shigewa bayin ta banko ?ofar saboda ta tsani maganar zuwan Iftihal makaranta amma ta ga alama Alhaji ya kasa fahimta, dan gaka ma ta ?udurta a ranta cewa sai ta Wauki lokaci mai tsawo za ta fito daga bayi sannan ta san likaci ya ?ure dan bata da masaniyar Abie ya tashi Iftihal Win har ma ya sanya Safiya ta shiryata.


Kai Abie ya girgiza ya juya ya fito daga Wakin nata sai da ya bi ta Wakin Iftihal Win ya ga har an mata wankan ana sanya mata uniform sai murna take yau za ta je makaranta.


"Abie har an kusa gama shirya ni sai in yi sallah, ba sai na ci abinci ba ma dan kar lokaci ya ?ure"Cewar Iftihal dan bata son yau wani abu ya hanata zuwa makaranta.


"Kar ki damu Iftihal har kya ci abincin ma dan da sauran lokaci yanzu 6:50"


"Toh Abie" Ta ce lokacin da Safiya ta gama sanya mata ?aramin hijab domin ta yi sallah.Tana yin kabbara sai Abie ya cewa Safiya idan ta gama sallah ta kawo ta part Win sa domin ta yi break fast acan saboda ba ya so Hajiya Hauwa ta sanya su makara.Amsa masa ta yi ya juya ya sauka ya nufi part Winsa, lokacin kuku har ya fara jera wasu abubuwan na break fast akan dinnig Win.

Sama ya haura domin zuwa shi ma ya shirya sabida tafiya office.


Safiya ce goye da Iftihal sai ta rataya school back Win Iftihal Win a kafaWarta suka taho part Win Daddy, abin da take so ta zuba mata ta fara bata a baki.



Hajiya Hauwa ta daWe a bayi sannan ta fito ta yi sallah ko azkar bata yi ba ta tashi ta naWe dardumar sannan ta koma ta kwanta, sai da ta ga ?arfe bakwai da arba'in sannan ta taso domin zuwa ta tashi Iftihal ta san dai yanzu kafin ta kira Safiya ra shirya yarinyar har ta ci abinci lokaci zai ?ure sai dai a ha?ura da zuwa makarantar.


Tana zuwa ta tura ?ofar ta ga wayam babu kowa a Wakin, kofar bayi ta buWe shi ma ta ga Iftihal Win bata nan dan haka da mamaki fal a fuskarta ta fito daga Wakin tana tunanimninda yarinyar take da sanyin safiyar nan.?asan ta sauka nan ma bata nan, wayar Sangaren ?an aiki ta kira ta ce a turo mata Safiya domin ta je ta dubo ta a cikin gidan amma sai aka sanar da ita Safiyar ta fito domin amsa kiran Alhaji.A fusa ce ta kama hanyar part Win Alhajin tana fatan kar hasashen ta ya zama gaskiya tana zuwa kwa ta ga Iftihal ri?e da lunch box Win ta har direbanta ya zo za su tafi, Alhaji da Hajiya Azima kuma zaune a dinning area Win.


Wani ?aton abu ne ya tokare mata ma?oshi har yaushe ne Alhaji zai fahimci cewa bata ?aunar Iftihal take halartar makaranta tana da ?uduri mai girma akan yarinyar amma bata ?aunat yarinyar ta yi wano abi wai shi karatu.Tana ji tana gani hwkw Iftihal ta fice ita da Safiya za ta rakata wurin mota, Iftihal Win sai Wagawa Hajiya Hauwa hannu take amma ko ta kulata har sai da kowa ya fahimci hakan, shi kwa Alhaji ko ta kan Hajiya Hauwa bai bi ba ita ma Hajiya Azima banza ta yi da ita dan ta ga abin nata ya zama hauka, ace ?ar ?waya Waya amma ana hana ta zuwa makaranta ita ko kunya ma Hajiya Hauwar bata ji.


Ganin kowa ya shareta yasa ta koma part Win ta ranta na suya tana yin wani ?udirin akan lallai sai ta ?ara tashi tsaye dan ta ga abin na Alhaji ba ?arami bane ita kwa ta sanya a ranta cewa sai dai su yi ta fafatawa.


_ALHAJI HAMZA_

?an asalin garin kano ne a unguwar zoo road, iyayensa shi kaWai suka haifa,suna kiransa da Hamzan sa, ya tashi a garin kano tare da mahaifansa anan ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa zuwa digree Win sa.Iyayensa basu da wani arzi?i sai dai suna da rufin asiri, bayan ya kammala karatunsa bai samu aiki ba sai ya fara Wan sana'a har dai daga bisani Allah ya sa ya samu aiki a wani kamfani garin Abuja, hakan yasa ya fara zuwa wajen aiki yana dawo wa a week end, tafiya ta yi tafiya har ya samu ya samu Wan gida madaidaici ya siya ciki da falo sai banWaki haka ya dawo da mahaifansa kusa dashi suke zaune tare.



Daga baya yana ?ara samun buWi sosai domin Hamza ya kasance mutum mai gaskiya da ri?on amana hakan ya taimaka masa da wurin aikinsa suka ri?eshi da kyau sanadin gaskiyarsa, Har ake ?ara masa girma.Bayan ya sayi gida mai Sangare biyu sai mahaifansa suka ce ya yi aure haka kuwa aka yi ya auri budurwarsa Azima ?ar garin Kano ce sun daWe suna soyayya, da suka tare a sabon gidan su a Sangare Waya iyayen Hamza ma a Sangare Waya haka suke zaune lafiya dama Azima uarinya ce mai biyayya da kuma girmama na gaba hakan yasa zaman nasu yin ?ar?o.


Wata rana da ta zame musu rana mafi muni a cikin tarihi shine hatsarin da iyayen Hamza suka yi daga Kano zuwa Abuja domin sun je sada zumunci wurin ?an uwa da abokan arzi?i hakan ne ya yi sanadiyyar rasa rayukasu.Haka aka yi zaman makoki aka tashi sai dai mu ce Allah sa mu yi kyakkyawan ?arshe amin.



Shekaru kusan bakwai kenan su Hamza Allah bai basu haihuwa ba, gashi a lokacin har ya je ?asar India ya ?aro karatu, ga buWi na arzi?i ta ko ina amma kuma babu wani labari na haihuwa hakan yasa Azima ta Waga hankalinta amma shi Hamzan ke kwantar mata da hankali akan komai lokaci ne.Ya sake musu gida na gani na faWa domin yanzu shi ma ya mallaki kamfano ni da dama sai dai ma wasu su ci abinci a ?ar?ashinsa.Yanzu ma yana aiki a Waya daga cikin kamfanonin sa kuma mutanen da ke tate da shi suna jin daWin aiki da shi domin mutumin da ya san kima da darajar Wan adam



Watarana ya je Kano ziyara ya dawo sai motarsa ta lalace a Suleja, hakan yasa ya rasa yadda zai yi, wani gida da yake kan hanyar inda motarsa ta lalace mai gidan ya bashi tarbarma sannan ya bashi abinci har dai bakaniken da ya masa gyara ya kammala, sosai Hamza ya ji daWin karramawar da mutumin ya masa hakan yasa ala?a mai ?arfi ta shiga tsakaninsu duk da cewa mutumin ya haifi Hamzan amma haka suka ?ulla ala?a mai kyau, har ta kai Hauwa ta ?yalla ido ta ganshi hakan yasa ta Wauki alwashin sai ta aureshi duk da kasancewar mahaifinta talaka amma dai bata da buri da ya wuce auren mai kuWi, shi yasa da ta ga Hamza ce sai ta aureshi ko ta halin ?a?a, haka suka shiga suka fita ita da mahaifiyarta, sai da Hamza ya auri Hauwa.


Tun da ta tare a gidansa ta ga yadda yake ji da uwar gidansa hakan ya ?ara rura wutar kishi a ranta, ta ji duk duniya babu wacce ta tsana irin Azima haka ta sa a ranta ita ce za ta haifawa Hamza magaji dan ta zama tauraruwa kuma ta cusawa Azima haushi na rashin haihuwa.

Makkah kwa sai da ta je sannan hankalinta ya kwanta,dan ta tsani ta ji ana kiran Azima da Hajiya.

Zuwanta da wata biyar sai ciki ya Sullo a jikin Hajiya Azima, hankalinta ya yi matu?ar tashi haka suka dinga shigi da fice akan kar ta haihu amma cikin hikimar ubangiji lokacin haihuwa na yi ta haifi Wanta namiji a asibiti sai dai kwanan yaton Waya a duniya ya amsa kiran ubagiji.Murna a wajen Hajiya Hauwa ba a cewa komai sosai ta yi farinciki.Hajiya Azima kwa ta ji babu dali ganin yadda suka ?walla fa rai akan cikin har ma da Wan lokacin da ya zo duniya ita da Alhaji Hamza da duk wani masoyinta, amma haka suka fawwalawa Allah komai.


Sai da Hajiya Azima ta shekara shida da haihuwar Wan da ya koma, sai kuma ciki ya bayyana a jikin Hajiya Hauwa, sai wani iyayi da sanabe take wai ita mai ciki za ta haifi magajin Alhaji ya gaji dukiya, shi ne fa da cikin ya isa haihuwa ta haifi Amina ana kiranta Iftihal.Hajiya Hauwa tun da ta haifi Iftihal take zaton Alhaji zai juyawa Hajiya Azima baya saboda bata haihu ba sai ta ga saSanin hakan dan babu wani abu da ya canja hakan shi ne ke ba?anta mata tana ganin kenan dai duk da ta haihu bata samu martaba da kimar da Hajiya Azima ta samu ba a wurin Alhajin.

sai kuma ta fara zargin ko Alhaji ya fi ?aunar a haifa masa namiji, shi yasa take ganij bata samu wani matsayi da take son ta samu a wurinsa ba.Amma kuma daga baya dai ta fahimci Alhajin bashi da wani zaSi sai abin da Allah ya bashi ko mace ko namiji duk yana so hakan yasa take fatan Allah ya ?ara bata haihuwa ta haifi namiji duk da tana jin tun da Hajiya Azima bata haihu ba babu yafda za ayi ta haWa kan ta da ita duka da cewa mace ta haifa.

wannan kenan.



d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 1?? 3?? &1?? 4??



_Hizbullah_

Bayan shekaru biyar


Sha?uwarsa da Ridallah kullum ?aruwa take, hakan yasa gabaWaya bashi da wani wanda ya sha?u da shi sai Ridallah, bayan iyayensa Umma Sadiya, da kuma mahaifinsa Malam Auwalu,babu wani wanda ya sha?u dashi sai Ridallah Ita ma Ridallah haka ne a nata Sangaren in ban da mahaifiyarta Baba Habiba dan mahaifinta ya rasu sai mahaifiyarta kaWai ce a raye.


A haka suka taso ko yaushe suna tare babu abin da ke raba su sai bacci, tare suke zuwa makarantar boko tare suke zuwa islamiya, tare suke cin abinci tare suke komai idan Waya bashi da lafiya to Wayan ma haka zai wuni a kwance wani lokacin ma shi ma Wayan kamuwa yake da jinyar da Wayan ke yi wannan shi ne babban abin da ya ?ara sanya iyayensu ?arfafa zumuncin ma?otaka a tsakaninsu dan un ban da ma?otaka babu wani abu da ke tsakanin su na ?an uwantaka.


Rayuwa na ta tafiya, da kaWan -kaWan ranaku ke rikiWewa su koma sati, sati ya rikiWe ya koma wata da sannu su ma watannin ke haWuwa su bada shekara hakan ya kan sa shekarar ta haWu da wata shekarar har su bada shekaru.

Hakan ne yasa wucewar shekarun ya kawo mu lokacin da Hizbullah ya kammala karatunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login