Showing 3001 words to 6000 words out of 77516 words

Chapter 2 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

jiran fitowar Alhajin, gaishe da su ya yi cikin girmamawa suka amsa cikin sakin fuska jakar hannun Hajiya ya karSa ya jiya ya tafi ya bar su suna sallama, sai da ta ga tafiyar su tana Waga masa hannu shi ma yana Wago mata duk da akwai Wan tazara daga part Win zuwa parking space amma suna hango junansu ana wangale get motar na fita Hajiya Azima ta juya ta koma ciki domin ta gyara masa bedroom Win nasa na upstairs inda suka kwana dan bedrooms a saman ma guda huWu ne sai dai Waya wanda suke kwana Alhaji da Hajiya Hauwa Waya kuma inda yake kwana da Hajiya Azima kowacce da Wakin da ya zamana shine turakar da take kwana da miji dan basa sharing na turaka sauran biyun kuma kawai dai an ?awata su ne da kayayyakin Waki amma ba wai ana kwanciya a ciki.


Tana dawo wa bata tarar da Hajiya Hauwa a dinnig area Win ba ta koma part Win ta dan kowacce akwai ?ofar da za ta sada ta da part Win ta, sai kuku yana kwashe kwanuka, ya gaishe da ita ta amsa masa tare da hayewa sama domin yin gyaran dan ita a tsarinta bata yarda ?ar aiki ta gyara mata turakar mijinta ba saSanin Hajiya Hauwa da mai aiki ke gyara mata.



Hajiya Hauwa rai Sace ta ?arasa part Win nata dan har lokacin bata daina jin haushin faWan da Alhajin ya mata a gaban Hajiya Azima sai dai ta sha alwashin sai dai ya yi falansa ya gama amma dai ba za ta taSa yin abin da yace ba ko da ta fara ba zai Wore ba.Mai aikinta Safiya ta samu tana ta faman goge -goge cikin girmama wa Safiya ta mata barka da dawo wa amma ko inda take bata kalla ba dama ita ma bata sanya rai cewa za ta amsa mata ba dan ta san hali, shegen wula?anci ne da ita.



MAMAN AFRAH=?
?

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page 7?? &8??




Hajiya Hauwa upstairs ta nufa tana zuwa ta kama ?ofar Wakin Iftihal ta buWe kwance ta ganta akan gado tana cikin bargo fuskar ta ce kawai a buWe sai baccin ta take hankali kwance.Wata uwar harara take bin Iftihal Win da ita daga ?arshe ta doka wani uban tsaki tare da rufo ?ofar da ?arfi ta juya ta koma nata Wakin, Iftihal kwa da ke ta bacci bata san abin da ake ba.Tana shiga Wakin ta ta cire Waurin Wan kwalin da ta yi wanda ake kira ture ka ga tsiya wuri ta nema a bakin gado ta zauna har lokacin ranta na ?una ta rasa yadda za ta yi da Hajiya Azima kullum maimakon ace Hajiya Azima ta zama bora a wajen miji amma kullum ita ce mowa ita ce tauraruwa ita ce abar so ita duk faWi tashin da take yana tashi ne a banza, kullum Alhaji cikin ganin laifinta yake a gaban Hajiya Azima sai ya tsinkata yana mata faWa tabbas da sake dan ba za ta saSu ba wai bindiga a ruwa.


Mi?ewa ta yi da sauri kamar wanda aka tsikare ta gaban mirror ta je ta tsaya tana ?arewaa kan ta kallo tamkar dai yau ta fara ganin siffar kan ta a madubi.So take ta gano muninta so take ta hango makusar ta so take ta ga ta inda Hajiya Azima ra kere mata, kyau diri iya kwalliya ko me? Amma bata hango hakan ba duk da ta san cewa bata kama ko da ?afar komai ba na Hajiya Azimar ba amma ta san ita ma tana da nata abin yabon, gashin kan ta, ta ?urawa ido ganin shi iya kafaWarta ko gama sakko mata bai yi ba sai kuma ta tuno gashin Hajiya Azima da ko Wan kwali baya iya rufeshi har gadon bayanta yake sauka ga santsi da she?i, ai hakan da Hajiya Hauwa ta tuna sai kawai ta mi?a hannu wurin kwalaben turaruka da ke jere akan madubin ta Wakko wata kwalbar humra ta Waga ta jefawa madubin a take ya tarwatse wani ?ara da gabaWaya part Win ya Wauka komawa ta yi ta zube akan gadon har lokacin zuciyarta na tafarfasa.




Safiya da ke gyaran kicin ta jiyo ?aran fashewar abu a hanzarce ta fara hawa step Win domin zuwa ta ga ko menene dan alamu sun nuna kamar ba lafiya ba.Tana gama hawa upstairs Win ta fara waige-waige tana son gano inda ?aran ya fito amma bata gano ba kukan Iftihal ta fara jiyowa da sauri ta nufi ?ofar Wakin ta tura ?ofar dan dama idan ranar girkin Hajiyar ne idan Hajiyar ta tafi part Win Alhaji to fa ita ke kwana da Iftihal amma a Wakinta da ke kusa da na Iftihal Win da basa kwana a Waki Waya idan kuma ba girkin Hajiyar bane a Sangaren su na ?an aiki take kwana.


Iftihal Win ta hango zaune akam gado ta du?un?une kan ta a cikin bargo tana takure a wuri Waya tana ta kuka, da sauri ta ?arasa wurin Iftihal Win tana kiran sunan ta sannan ta sanya hannu ta yaye bargon aikwa Iftihal Win ta faWa jikinta da sauri tana ?ara fashewa da wani kukan.



"Wayyo Safiya dan Allah ki kai ni wurim Aunty tsorata ni ake da wani irin ?ara"Cewar Iftihal Win tana ?an?ame Safiya.



"Ki yi shiru babu komai anan ni ma na ji ?aran amma da na zo ban ga ta inda ?aran ya fito ba"



"Ke ma kin ji kenan ni dai ki kai ni wajen Aunty tsoro nake ji"


"To taso mu je tana Wakinta"


Sakkowa Iftihal Win ta yi sai da na duba da kyau sai ma na ga ba wata babba ba ce duka bata fi shekara huWu ba, hannun ta Safiyar ta kama amma Iftihal ta ce ita dai ba za ta tafi da ?afarta ba, sunkuyawa Safiyar ta yi Iftihal Win ta hau dan dama da wuya ka ga Iftihal na tafiya da ?afarta rai da rai sai dai a baya, haka suka nufi Wakin Aunty, nocking Safiya ta shiga musu amma abin mamaki bata bada amsa ba jin shiru yasa Safiya tura ?ofar dan dama haka take sai ka yi ta mata nocking ta ?yaleka.

Kwance suka sameta ta kifa kan ta a jikin filo da alama kamar tana cikin damuwa daga bakin ?ofar da Safiya ke tsaye da goyon Iftihal suka ga gabaWaya madubin da ya tarwatse a Wakin, da mamaki Safiya da Iftihal suke kallon madubin sai lokacin suka fahimci ?aran fashewar madubin ne ya cika part Win har ya tsorata Iftihal.


"Aunty"Iftihal Win ta kira sunan Hajiya Habiba tana ?o?arin sakkowa daga bayan Safiya.

Shiru bata amsa mata ba

"Kar ki sakko dan kar ki taka madubin"Safiya ta ce tana ri?e Iftihal Win dan yadda madubin ya Sata Wakin ko ina ya tarwatse Iftihal Win za ta iya takawa.Duk bidirin nan da ake Hajiya Habiba bata ko Wago kai ta kalle su ba.A hankali Safiya ta bi ta gefen tana taka in da babu madubin har dai ta ?arasa bakin gadon ta sauke Iftihal Win akan gadon, ?arasa wa Iftihal Win ta yi ta faWa kan Aunty ta tungumeta ta baya tare da kwantar da kan ta a bayan Auntyn.Ita dai Safiya daga haka ta fita Wakin domin samo abin da za ta gyara wurin.


"Aunty ke kika fasa madubi?"Iftihal ta jefa mata tambayar.


A hankali Aunty ta zame Iftihal Win faga bayanta ta tashi zaune suka fuskanci juna.Iftihal Win kallon idon Auntyn take ganin ya yi jawur kamar dai kuka ta yi.


"Haba Iftihal ya za ayi in fasa madubi abu na je Wakkowa shi ne ya fashe"



"Amma kuka kika yi?"Ta ?ara jefa mata wata tambayar.

"Kai na ke ciwo shi sa kika ga ya yi ja"


"Sannu kisha magani"

"Yawwa na sha magani ma"

Iftihal kan ta ta kwantar akan cinyar Auntyn, sai kuma Auntyn ke shafa kan nata , shiru suka yi babu wanda ya ?ara magana.


"Aunty yau ma bazan je school Win ba?" Iftihal ta jefo mata tambayar.Auntyn na ?o?arin bata amsa Safiya ta turo ?ofa ta shigo Wauke da tsintsiya da abin kwashe shara wurin ta shiga gyarawa sai da ta tabbatar ya gyaru babu sauran wani madubin sannan ta fita daga Wakin.



"Yanzu time na zuwa school ya wuce, ba a son mutum ya je makaranta a makare saboda bulala malam ke yi amma ki bari za ki je"Cewar Auntyn tana cigaba da shafa kan Iftihal Win.


"To shikenan, amma dai gobe zan je"



Shiru Auntyn ta mata har sai da Iftihal Win ta sake mata magana sannan ta ce.





"Kar ki damu"




"Zan je?" Ta sake jefa mata tambaya.


"Ki bari yanzu bana son surutu kai na yana Wan sara min"


"Sannu " Iftihal ta ce tana tashi zaune daga kwancen da take tana kallon Aunty cike da tausayawa.



"Yawwa ai kaWan-kaWan ne ma " Aunty ta ce tana Waukan wayar ta ta kira telephone da ke falon ?asa, Safiya na Wagawa ta ce.


"Ki zo"Kawai ta ce ta katse kiran.


Da sallama ta shigo Wakin bayan ta yi nocking an bata izinin shiga.


"Gani Hajiya" Safiya ta ce lokacin da ta dur?usa a gaban gadon da Aunty take.



"Ki Wauketa ki je ki mata brush ki mata wanka sannan ki bata abinci ta ci" Auntyn ta faWa tana mi?a mata Iftihal .



"To Hajiya an gama" Cewar Safiya tana juyo bayanta Iftihal Win ta hau suka fito daga Wakin.

Bayan ta mata brush ta mata wanka sannan ta shiryata tsaf cikin riga da wando ?an kanti pink clour masu matu?ar kyau ta gyara mata kan nata sai she?i yake, haka ta goyota suka sakko ?asa ta zaunar da ita da akan kujera, kicin ta shiga ta Wakko mata soyayyen dankali da ?wai sai soyayyen plantain.A kan center table ta Wora ta Wakko kayan shayi ta haWa mata tea mai kauri ta zuba abincin ta shiga bata a baki, suna cikin haka sai ga Aunty ta sakko daga saman ta zo ta zauna ta Wora Waya kan Waya dan zuwa lokacin ba ta ko so ta tuno da Hajiya Azima dan tun da ta yi kuka sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi remote ta Wauka ta canja tasha zuwa arewa 24 sannan suka sakarwa juna murmushi ita da Iftihal.




Ita dai Safiya ba abin da ta ce tana baiwa Iftihal abinci har sai da ta juyar da kai gefe alamar abincin ya isheta.Ajiye fork Win Safiya ta yi ta Wakko kofin me tea Win da ta haWawa Iftihal a hankali ta shiga ?o?arin bata dan gudun yin kuskure dan kaWan da aikin Hajiyar ta mareta koma ta hanata albashi wannan watan.


"kar ki bani tea Win da kai na zan sha" Cewar Iftihal tana mi?a hannu ta karba, Safiya ganin an karSeta sai ta shiga tattare kayan abincin, ta gama haWawa za ta Wago daga sunkuyen da take aikwa Iftihal ta Wauki wannan shayin da ke hannunta ta watsawa Safiya a jikinta har fuskarta sannan ta ce




"Bana shan abu mai zafi bayan haka bana son ana cika min madara "




Wani haushi da mugun takaici ne ya mamaye Safiya ga tea Win da zafi bai huce amma sai ta cije sai dai ta yi ?o?arin dam?e hannun ta domin ta ayyana a ranta ko za ta rasa aikinta yau sai ta naushi Iftihal a bakinta domin sai ta nuna mata cewa bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, sannan Wan adam Allah ya Wauka ka shi dole ma ta nuna musu kuWinsu ba shi bane tun da ba za su iya yiwa kan su abu ba dole dai talakan shi zai musu, hannu ta dun?ule tana duba in da ya kamata ta kaiwa mugun naushi a jikin Iftihal Win.





MMN AFRAH=?
?>?p?=??



d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page9?? &=??




Wata tsawa da Hajiya Hauwa ta dokawa Safiya ita ta dakatar da ita daga shirin dukan da take ?o?arin ta kaiwa Iftihal, wani tsoro ne ya ziyarci Safiya dan sai a lokacin ta ji a ranta cewa lallai da ta kaiwa Iftihal dukan to tabbas da ta yi babban kuskure, dan wata?ila kafin ta rasa aikin nata sai ta fara rasa ranta dan tsaf Hajiya Hauwa za ta mata dukan mutuwa akan Iftihal.


"Wace irin marar hankali ce ke in ban da jakanci da jahilci maimakon ki yi saurin tafiya Waukan mopa da ruwa ki zo ki goge wurin shi ne kika tsaya kina kallon Iftihal Win sai ka ce wanda ta yi wani abu, ko dan baku san darajar kuWi ba saboda baku da su shi yasa za ki bar min capet da ruwan shayi a jiki sai ya dafe ya?i fita" Aunty ta ce tana wani zazzare ido tana bala,i.


"Ki yi ha?uri Hajiya yanzu zan gyara" Safiya ta ce tana Waukan kanukan ta nufi kicin domin ta ajiye su, ga wani zafi da raWaWi da fuskarta da ?irjinta ke yi dan shayin akwai zafi amma saboda rashin imani na Hajiya Hauwa maimakon ta tausaya mata shi ne take mata faWa bayan Iftihal ya kamata ta yiwa faWan amma saboda sangarci da kuma ganin suna da kuWi za su iya taka kowa ma hakan ya sa ta zamar da ?arta ta sangartacciya.Sai da Safiya ta tsaya ta share ?wallar da ta zubo mata tana da na sani akan aiki a ?ar?ashin Hajiya Hauwa da bata da mutunci ko kaWan bare tausayi, bata koyi da sobar zamanta Hajiya Azima mata mai kima da darajanta Wan adam pan aikinta tamkar ?a?anta haka ta Waukesu ba kyara ba tsangwama.


Tana ta sa?ar zuci ta dawo falon Wauke da mopa da burket da ta haWo ruwa mai Wauke da morning fresh, ta shiga goge wurin, lokacin Auntyn na lallashin Iftihal akan ta yi ha?uri za a haWa mata wani tea Win marar zafi sosai marar madara da yawa.Wani haushi da takaici ne ya turnu?e Safiya tana Allah wadaran naka ya lalace ace maimakon uwa ta zama turba na gina rayuwar ?a?anta akan hanya daidaitacciya mai Sullewa wajen basu kyakkywar tarbiya amma shi ne ita Aunty ta zama mai bada gudunmuwa wajen taSarSarewar tarbiyar ?arta, babu abin da yarinyar ta sanj sai sangarta.



"Dalla malama ki yi sauri ki gama ki haWa mata wani tea Win"Cewar Auntyn cikin zafin rai.



"To Hajiya" Safiya ta amsa mata, bayan ta Wakko freshner ta fesa a wurin saboda ?arnin madarar sannan ta Wauke kayan da ta yi amfani da su wajen gyara wurin, kicin ta koma ta Wauki gishiri ta shafa a wurin da aka watsa mata shayin dan da alama ma kamar wurin zai tashi, bayan ta shafa sai kuma ta wanke hannunta ta sake haWa shayin marar zafi sai dai yana da Wan Wumi sannan ta fito ta zo ta dur?usa ta mi?awa Iftihal Win, tun da ta ce da kan ta za ta sha.



?in karSar shayin ma ta yi tana kallon tv, kamar ma ba ita ake baiwa shayin ba, Auntyn kwa tana kallo ko ta yiwa Iftihal Win magana.



"Ga shayin na sake haWa miki"Safiya ta ce da ta fahimci bata da niyyyar karSa.

Banza ta yi da ita, can kuma a shela?e ta karSa, kurSa Waya ta yiwa shayin ta Waga ta watsar da shi, ta yi jifa da kofin ya tarwatse dan dai ma akan tiles ne ba akan capet ba.Safiya kai ta sunkuyar tana jin a ranta cewa lallai neman halal da wuya musamman a ?ar?ashin wanda ba su san kima da darajar Wan adam ba.Hatta Hajiya Hauwa ranta ya matu?ar Saci da abin da Iftihal Win ta yi amma saboda bata so ta nuna mata hakan duk da cewa ita ce ta Sata yarinuar gashi bata son kwaSarta sai kawai ta danne zuciyarta ta ce.



"Wai Safiya baki san aikin ba? Komai sai an faWa miki kenan? Ba za ki kula ki gyara wurin ba sai ki wani sunkuyar da ka kamar mai yin zaman tahiya yayin gabatar da salla.



"Ki yi ha?uri Hajiya yanzu zan gyara" Haka Safiya ta share wurin wurin ta goge tas, sannan ta Wore wasu ayyukan dan wuni ake ana aiki ba kama hannun yaro.


Da daddare zaune suke su duka iyalin gidan a dinning area domin gabatar da dinner, Hajiya Azima sanye take da wani leshi purple colour an mata Winkin buba ta Waura Wankwalinta ta sanya sar?a da Wankunne na gwal sai she?i suke ga warwaraye da zobuna sai zuba ?amshi take tamkar dai mai shirin zuwa wani gagarumin biki ko suna. Hajiya Azima mace ce mai son ado da kwalliya gata da matu?ar tsafta, hakan shi ke ?ara wutar soyayyarta a wurin mijinta yake kuma ?ara rura wutar tsanarta a wurin sobar zamanta Hajiya Hauwa dan ta tsani duk wasu abubuwan da Hajiya Azima ke yi.


Alhaji, Hajiya Azima sai Hajiya Hauwa su ne a wurin kowa zaune yake Iftihal kawai ake jira a fara cin abincin domin komai ya kammala dan kuku ya shirya musu komai da komai duk da kasancewar Hajiya Azima mai son take yin girki da kan ta amma fitinar da Hajiya Hauwa ke tadawa yasa Alhajin dakatar da ita, dan dama ita duk ranar girkinta ita ce ke yin girki, ita kuma Hajiya Hauwa sai dai aci girkin kuku dan dama bata wani ?ware a girki ba gata kuma da son jiki, to idan Hajiya Azima ta yi girki ranar girkinta sai Hajiya Hauwa ta ringa sanabe tana cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login