Showing 69001 words to 72000 words out of 77516 words

Chapter 24 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

ce kuwa tsufa ya kamashi lokacin da za su yi arba da juna.Sanin da ta yi yana raye ne ya sanya take siyana kaya tana ajiye masa dan ta nuna masa yana nan daram a ranta tana jiran ranar da za su haWu, hakane yasa ta ajiye masa kayan jarirai tana sawa a ranta cewa zai dawo gareta ne tun yana jariri ama ina! Hakan bai sa ba, a haka take siyana kaya mataki-mataki na yara har kawo girmansa na matashi kuma ko a yau akwai kayan da za su masa bila adadin manyan kaya ne ko ?anana shaddodi ne ko yadika, babu kalar kayan da babu turaruka da dai sauran abubuwa agoguna huluna zobuna komai da komai Momma ta ajiyewa Wan nata.


Juyi ta yi a kan gadon nata tana ?ara tunano kaWan daga abubuwan da ta gani an canja mata Wanta, dama a garinsu Kano ta haihu, saboda lokacin EDD Winta ya kusa cika sai tafiyar gaggawa ta samu Abie zai bar ?asar zuwa ?asar India ganin irin mugun kishin fa Aunty ke nunawa a kan cikin jikin Momma ko Soyewa bata yi ?iri-?iri take nunawa musamman take takurawa Abie wai da gangan ya?i mata ciki saboda ba ya son ta amma ya yiwa matar so wacce yake son ya haihu da ita, tun yana nuna mata ta yarda Allah ke bayarwa kuma bai manta da ita ba zai bata nata rabon.Ganin ba ganewa take ba ya ?yaleta, aikuwa tafiyar na samunsa ya ce gwara ya kai Momma Kano in ya dawo sai ya Wakkota gudun faruwar wani abun. A Sangaren Aunty kwa farinciki ta yi jin tafiyar da Abie zai yi hakan ya sa ta ?udurci aikatawa Momma mummunan abu, tana fatan Momma ta haihu kafin ya dawo ta yiwa kanta alwashin sai ta san yadda ta yi ta samu dama ta matsewa abin da Momma za ta haifa hanci ta hanyar hanashi numfashi har sai ya daina motsi ma'ana ya mutu! Ta yarda a ce ta yi kisan kai a kan a ce ta bar abin da aka haifa ya rayu, ta san hakan dai dai yake da Waukewar numfashinta.Kwatsam sai ta ji wai Wauketa zai yi daga gidan ya kai ta danginta hakan ba ?aramin ba?anta mata rai ya yi ba dan haka ta yi al?arin ko ma ina ne za a kai Momma sai ta san yadda ta yi ta biya bu?atarta.

Babu wanda ya san ?udurinta haka da Abie ya tashi tafiya ana gobe zai tashi ya kai ta Kano ya mata bankwana suka rabu ba dan sun so ba saboda suna ?aunar junansu kuma banda tafiyar ta dole ce babu abin da zai sa ya tafi ya barta.Tun da Abie ya bar ?asar Aunty ta sanya numbobin bibiya a number Abie tun daga kafafun sada zumuntarsa har na wayar da zai ke yi saboda ta san me ake ciki dangane da haihuwar Momma, ta hakan kwa ta yi ta samun abin da take so.

Momma ganin dare ya tsala ta tashi ta yi alwala ta shiga gabatar da nafiloli a kan Allah ya warware ?ullun nan cikin sau?i ya dawo mata da Wanta a ce nata ne, tun da ta idar da sallar ta shiga karatun qur'ani da ?ira'arta mai daWin sauraro har sai wajen ?arfe huWu ne da rabi ne sannan ta Waga hannu ta rin?a jero addu'o i, bata tashi daga sallayar nan ba har sai da ta gabatar da sallar asuba.

A Sangaren Hizbu ma haka ya kwana bai rintsa ba ganin Malam Idi ya tashi yin nafila shi ma ya bi sahu suka yi tare dan dama shi Malam kullum ne sai ya tashi sallar dare saboda matu?ar tsadar lokacin, lokaci ne da Allah ke sakkowa sama ta Waya yana neman wanda ke da bu?ata ya amsa sama.Amma Abulkairi kuwa tun bayan dawowarsu part Win da aka saukesu da ya kira gidansu ya sanar musu cewa suna Nigeri'a saboda an samu Ridallah ko faWa Babansa bai yi ba saboda sun san tsakaninsa da Hizbu kuma kaf gidansu babu wanda bai san da labarin Satan su Ridallah Win ba.Baban Hajiya Hauwa kwa takaici da ba?inciki fa zuciyarsa na abin da Wiyarsa ta aikata duk da ya san cewa matarsa a na da sa hannu a komai amma dukansu masu laifine tabbas da sai ka yi dace da samun mace ta gari sannan ne za ta baiwa ?a?anka tarbiya dan uwa ita ce tushen samar da tarbiya ta gari idan kuma baka dace ba sai dai ka yi ha?uri k Wauki hakan a matsayin ?addararka.Abbah direba kuwa dama shi direba ne idan ya yi tafiya mai nisa ya Wauki shata dama ya saba kwana idan wurin da nisa dan haka waya kawai ya yi ya sanar da matarsa kwana ya kamashi ta masa fatan alkairi.Shugabar gidan marayun kwa bata da aure tun sanda mijinta ya rasu bata ?ara yin aure ba Mamarta kawai ta yiwa waya t sanar ata halin d ake ciki, direbanta ma waya ya yi ya sanar.

Babar Hajiya Hauwa kuwa kwanan ido biyu ta yi kamar yadda ?arta ta yi kwana ido biyu saboda tunanin hukuncin da za a zartar musu na abin da suka aikata.Mummy kuwa duk da na sani ya dabaibayeta na abin da ta aikata.Abie daker ya runtsa yana ta alhinin abubuwan da suka faru yau kamar a mafarki.

Momma na idar da sallah ta fito d duku -duku ta kira ?an aiki suka shiga kicin suka shiga shirya abinci, misalin ?arfe goma saura kowa ya hallara mazan a kan dining matan kuma aka shimfiWa musu table mart a tsakiyar falon aka karya kowa da abin da yake sa?awa, Momma sai satar kallon Hizbu take wanda tun da ya du?a ya gaishesu ya nemi wuri ya zauna duk ta lura da sanyin da jikinsa ya yi, tana ta jin babu daWi a ranta.Ridallah kawai ta lura ya sakarwa murmushi ita da Iftihal da suka du?a suka gaisheshi a tare tana gani har da dafa kan Ridallah ya yi sai dai tana jin daWi da Ridall??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ah ta zama farincikin Wanta ta lura yana ?aunar yarinyar sosai, daga an Wan jima kuma sai ta kalli Hajiya Ru?ayya da ke ta kallon ?an biyunta tana murmushi kana ganinta ka san tana cikin farinciki, haka ma Baba Habiba duk da tana Wan jin babu daWi a ranta a rabuwa da za ta yi da Ridallah amma a gefe Waya tana jin dai da Ridallah ta haWu da ?ar uwarta da kuma mahaifiyarta, ga kum mahaifinta da ke hanyar zuwa Abuja lallai wannan abin ta taya Ridallah farinciki ne saboda ko ita da bata da dangi yanzu tana jin babu daWi duk da cewa ta Wauki hakan a matsayin ?addara. Hajiya Hauwa da Hajiya Wasila sai sunkuyar da kai ?asa suke dan abincin ma ba wai suna ci bane dan basu da nutsuwar cin abincin ma sai dai cokula kawai suke juyawa a plate Win, musamman Hajiya Hauwa da ke ji kamar an tsamota a ruwa ga mahaifinta da yake ta faman harararta daga ita har mahaifiyarta sun kunyata a cikin jama'a.


Misalin ?arfe Waya da wani abu na rana su Hajiya Suwaida motocinsu suka sauka a cikin harabar gidan Abie, sun tarar da mutanen gidan da ba?in gidan sun idar jam'in azahar suna zazzaune da jiran isowar tawagar ba?in nasu na Jigawa. Abie ne ya je ya shigo da su har falon da kowa ke zaune, suna shigowa Alhaji Sagiru sai kalle -kalle yake suna shigowa aikuwa idanunsa suka sar?e da na masoyiyarsa Hajiya Ru?ayya itama a take ta sauke nata idanun a cikin na mai gidan nata.


Tasowa ta yi daga inda take zaune ta tunkaro inda yake dan shi ma nufota ya yi cikin wani irin yanayi, har tuntuSe ta yi suna zuwa suka rumgume junansu a lokaci guda suna jin bugun zuciyoyinsu kana ganinsu ka san an shiga ha??insu abin tausayi tabbas in ba mutuwa ba wa zai raba masoya amma sai gashi mutum Wa adam ya rabasu tswon shekaru ba tare da sun sanya junansu a idanuwansu ba hasalima shi mijin an Wauke masa tunaninta, Hajiya Sakina da Alhaji Sunusi, har da Hafiz tsayawa suka yi suna kallonsu tare da mutanen wajen cikin tausayawa suna ganin Alhaji Sagiru ya fisu bu?atar ya fara kasancewa da ita kafin su iyayenta domin a hannunsa matsayin matarsa take lokacin da ta Sata ta bar hannunsu tabbas su ma suna bu?atarta amma sai suka dakata amma fa hawaye sai sunturi suke a fuskar Hajiya Sakina.Hajiya Suwaida kuwa ji take tamkar ta ?arasa ta yi ajalinsu baki Waya daga Alhaji Sagirun har Hajiya Ru?ayyar ji take ko da mafarki take idan ta farka babu ita babu komawa baccin dan ganin Alhaji Sagiru rungume da Hajiya Ru?ayya ba ?aramin tashin hankali ta shiga ciki ba.Matar da ta daWe da goge shafinta a doron ?asa ta Wauka ma ta daWe da mutuwa da ciwon hauka ashe dai tana nan a raye wato har hankalinta ya dawo jikinta!

Bayan sun saki juna suna ta murna, da sauri Hajiya Ru?ayya ta ?arasa wajen mahaifiyarta Hajiya Sakina suka rungume juna tare da sakin kuka kowa na wurin sai kallonsu yake ckn tausayawa.Alhaji Sunusi sai murmushi yake, suka samu wuri suka zauna.Hafiz ne ya ?arasa wurin nasu ya sanya hannu ya dafa mahaifiyarsa Waya hannun kuma ya dafa kafaWar yayar tasa ya ce.


"Alhamdulillah!!! Godiya da yabo sun tabbata ga Allah da ya nuna mana wannan rana Allah ?arawa annabi daraja" Ya faWa yana kallonsu da murmushi.


"Amin ya rabbi" Ammi da Hajiya Ru?ayya suka faWa tare da duka mutanen falon.Sakin juna suka yi Hajiya Ru?ayya ta juya wajen ?a?anta da idanunsu ke kansu suna hawaye ta ce


"Ridallah Iftihal ku zo nan" Ta faWa hawaye tare da murmushin farinciki a fuskarta lokaci guda.Tasowa suka yi hannayensu sar?e da na juna suka tako zuwa wajensu.Alhaji Sagiru idanunsa da numfashinsa ne suka tsaya cak! Ganin ta kira wasu yara ?anmata masu kama Waya kuma masu tsananin kama da ita, addu'a da fatan da yake shi ne Allah yasa dai zatonsa ya zama gaskiya dan shi lokacin da ya shigo bai lura da yaran ba hankalinsa a kan matarsa. Yaran na ?arasowa wajen idanun Ammi suka zaro Hafiz ya tsaya baki sake yana kallonsu Abban Hafiz kwa tsaye ya tashi daga inda yake.


"WaWannan su ne ?a?an da Ru?ayya ta haifa da cikin da ta bar gidan mijinta" Cewar Malama Zainabu dan ganin Hajiya Ru?ayya ta kasa bayyana hakan saboda kunya.A zabure Alhaji Sagiru ya tashi tsaye a take wasu hawaye masu zafi suka zubo masa a lokacin da idanunsa suka sauka a kan jininsa mallakinsa ?a?ansa yana jin wani farinciki ya baibaye zuciyarsa ashe shi ma yana da ?a?a har biyu, a take ya zube a ?asa tare sa sanya goshinsa a ?asa yana mai godiya ga ubangiji.Hajiya Sakina kuwa rungume jikokin nata ta yi a tare tana jin tamkar za ta haWiyesu dan murna.Hafiz hannayensu ya kama ya ri?e cike da jin daWi tabbas babu abin da za su ce sai godiya ga Allah!



To fa sai Hajiya mai gayya mai aiki hhhh wato Hajiya Suwaida saukar maganar cewa ?a?an Ru?ayya na sauka a kunnuwanta idanunta kafe a kan su ta yanke jiki ta faWi sumammiya.


Alhaji Sagiru na Wagowa daga sujadar da ya yi ya tafi wurin da aka jera abinci ya Wakko gorar ruwa mai sanyi yana zuwa ya buWe gorar ya she?e mata gabaWaya ruwan, a gigice ta tashi zaune tana ?if?ifta idanu wata uwar harara Alhaji Sagiru ya aika mata, gabaWaya kowa na wurin sai da ya murmusa da yanayun da Hajiya Suwaida farfaWo take ?if?ifta idanu, aikuwa idanun Hajiya Suwaida suka sauka a kan Hajiya Hauwa da Hajiya Wasila ma da halin da suke ciki bai hanasu murmusawa ba wani takaici da ba?inciki ne ya turnu?eta.Wata uwar harara ta gallawa Hajiya Hauwa dan gani take ta raina mata hankali ...





NEXT PAGE=???=???=???=???



MMN AFRAH


d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?



Page 7?? 0?? &7?? 1??


Su Umma Sadiya na sauka a tasha suka kira Hizbu suka sanar masa sun iso Abie ne ya sanya direba da Hizbu suka tafi suka Wakkosu a tasha tun da suka shigo Umma Sadiya da Baba Habiba suka rungume juna, cikin farinciki suna jin daWin ganin junansu. Ita ma Ridallah zuwa ta yi ta kwashi gaisuwa sosai Umma Sadiya ta ji daWin ganinta amma abin da ya bata mamaki shi ne ganin wata da ban da ta yi kama da Ridallah Win duk da cewar ta ganeta ita ce wacce Hizbu ya ce ya ganta a China wacce ya yi zaton Ridallah ce amma dai kamannin nasu ya yi yawa haka ta amsa gaisuwar Iftihal tana ta kallonta hatta Baban ma mamakin kamannin nasu yake yi.Dama sun yi sallar azzahar a hanya dan haka komai ya yi tsit.Abie ne ya umarci Baba Habiba ta bada labarin yadda aka yi ta tsinci Ridallah nan ta shiga bada labarin tiryan-tiryan har ?arshe sosai abin ya Waurewa Hizbu da Umma Sadiya da kuma Baba kai sai su ma mutanen Dutse da suke jin abin da ya faru cikin jimami.Tana gama faWa shi ma Abba direba ya faWi nasa labarin yadda ya tsinci Iftihal ya mi?ata hannun hukuma suka kaita gidan marayu da kuma yadda ya haWu da Ru?ayya jiya a gidan Malam Idi sosai labaran ke taSa zukatan masu sauraro saboda abin kamar almara.


Yana kammalawa sai ita ma Shugabar gidan marayun ta bada nata labarin yadda aka yi Hajiya Hauwa ta je ta Wauki Iftihal har kawo jiya.Malam Idi ma ya bada labarin yadda aka yi ya samu Hajiya Ru?ayya a halin hauka da kuma warkewarta har kawo jiya da komai ya bayyana.Yana gamawa Baban Hajiya Hauwa ya dan?ara mata wata muguwar hararar da ta sanya ta sadda kai ba tare da ta shirya ba ya ce


"To Babbar munafuka ke kuma sai ki bamu labarin yadda kika yi naki rashin imanin da kuma rashin tsoron Allah a kan yarinyar"Ya faWa yana kallonta tare da tsareta da idanunsa.Du?ar da kai ta ?ara yi tana jin nauyi da kunyar mutanen da ke wurin ga mahaifan yarinyar da kunya ta buWe baki ta bada labarin yadda aka yi ta gurSata musu rayuwar yarinya.



"Ko ni ubanki kike so na bada labarin" Ya faWa cikin zafin rai ya tashi ya yi kanta a harzu?e tamkar zai hauta da duka, saboda haushi yake ji da takaici a ce ?arsa ce ta aikata hakan.Daker aka ri?eshi tare da bashi baki sannan ya ha?ura ya zauna yana jin zafi a zuciyarsa.
Cikin sanyin murya ta shiga bada labarin kamar yadda mahaifiyarta ta bayar tun daga ranar da ta yi ?aryar tana da ciki da ranar har kawo yau Win nan.


"Dama nasan da kamar wuya ace uwa ta aikata hakan ga ?arta ta cikinta tabbas ko ba ga ?arka ba ?alilan ne za su aikata wannan Wanyan aikin, na godewa Allah da ba ke bace mahaifiyata dan na san wata rana zuciya za ta iya Wibana in kasheki har lahira saboda abin da kika mini" Iftihal ta faWin hakan cikin Sacin rai tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.Momma da ke kusa da ita ce ta shiga lallashinta, duk da Iftihal ta san cewa Ru?ayya ce mahaifiyarta amma sai yanzu da Hajiya Hauwa ta bada labarin ta ji wani takaici da ba?inciki.


Hajiya Ru?ayya ma duk da jiya a gabanta mahaifiyar Hajiya Hauwa ta bayar d labarin amma yanzu da aka maimaita jin irin rayuwar da ?arta ta shiga sai ta shiga share hawaye, shi ma Alhaji Sagiru idanunsa ne suka yi jawur dan ba dan yana jin kunyar Abie ba sai ya tashi ya Wauke Hajiya Hauwa da marin da sai ta gwammace kiWa da karatu.Abie kuwa kunya ta sanya ya rasa bakin magana, tana kammalawa Daddy ya kalli Mummy ya ce



"Saura ke algunguma" Ya faWa yana harararta yana jin dana sani babu adadi a cikin ransa na aurenta.A take itama ta shiga bada labarin yadda ta lalatawa Amal rayuwa kasancewarta ?ar mijinta sak abubuwan da Hajiya Hauwa ta yiwa Iftihal, har zuea inda aka kai mata Iftihal ta haWasu da Amal Win ta Wora daga inda ta tsaya kawo yanzu.Suna gamawa Alhaji Sagiru ya sanya Hajiya Suwaida ma ta bayar da labarin yadda aka yi ta yiwa Hajiya Ru?ayya kishiyarta asirin ta haukatar da ita tare da yadda ta sanya aka musu turen aljani su biyar wanda zai sanya su manta da junansu, Alhaji Sunusi, Hajiya Sakina, Hafiz, Hajiya Ru?ayyar sai kuma Alhaji Sagiru.Da kuma tadda take da sanya hannu wajen yin haWin gwiwa na Wakko Ifthal a gidan marayu da kuma lalata rayuwar Ifthal Win.


Kowa a wurin mamaki yake da irin rashin imani na matan uku wanda suka kasance ?awaye, lallai mata wani abun idan suka yi ko sheWan sai ya sara musu tare da jinjina musu.

"To ke ai baki gama bada naki labarin ba muna so ki warware mana yadda aka yi yaron nan Hizbu ya tashi a wani waje a hannun iyayen da saSanin mahaifansa" Daddy ya faWa yana kallon Hajiya Hauwa dan ya ga Abie ya rasa ta cewa.Zuciyoyi da yawa ne suka buga, zuciyar Momma, Hizbu, Rida, Baba Habiba, Abie, sai kuma uwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login