Showing 9001 words to 12000 words out of 77516 words

Chapter 4 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

na secondry school, a lokacin Ridallah tana primary 5 dan dama lokacin da take primary 1shi kuma yana J.s.s 1. Yana zaman jiran fitowar jarabarwar su ta SSCE sai kuma wani mummunan abu ya faru, wanda ya yi sanadin wargaza gabaWaya farincikin sa da ma sanya mahaifansa cikin damuwa saboda halin da ya tsinci kan sa a ciki. A wata ranar asabar ce aka tashi aka nemi Ridallah da mahaifiyarta Baba Habiba aka rasa babu wanda ya san inda suka tafi, dan ko kaya ma ba su Wauka ba haka suka tafi gidan ma ko rufewa ba a yi ba.

Sosai Hizbullah ya shiga damuwa da ?unci na tashin hankali, dan yanzu ya daWe da gano cewa ba wai sha?uwace kawai tsakaninsa da Ridallah ba tabbas akwai wata Soyayyar soyayya a cikin zuciya, Umma Sadiya sun rasa yadda za su yu dashi sun yi lallashin sun yi faWan sun yu lallamin amma dai Hizbullah ya yi nisa sosai baya jin kira.Da yake lokacin da Baba Habibabta dawo gidan da ke kusa da na su Hizbullah, lokacin Hizbullah yana ?arami bai sani ba amma dai da wasu ?an rani ne a gidan mata da miji da yaransu to da suka koma garinsu sai Baba Habiba ta kama gidan dan dama gidan haya ne me gidan yake bayarwa haya.


Dan haka Umma Sadiya ta shiga masa bayanin duk yadda abun ya faru tun daga lokacin da Baba Habiba ta dawo gidan da zama lokacin Ridallah tana ?ar jinjira, sosai sabuwar haihuwa ce, to lokacin ne da Hizbullah ya ?yalla ido ya ga Ridallah sai yake zuwa gidan wurinta.Ganin halin da ya shiga har ta kai ga kwantawa jinya dan duk inda suke zaton za su gan su sun cigita amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa.Hakan ne yasa Malam Auwalu ya nemi mai gidan da Baba Habibar ke zaune domin jin ko daga ina Baba Habibar take tun da shi ya bata hayar gidan, amma abin mamaki mutumin yace wallahi bai san daga inda take ba, shi dai kawai abu Waya ya sani ma?ocinsa ne ya haWa shi da ita, shi ma kuma ma?ocin ba wai ya san ta bane kawai dai ta je wurinsa ne akan tana neman taimakon inda za ta zauna ko da gidan haya ne tana so wai mijinta ne ya rasu ya barta da tsohon ciki shine kuma bayan ta haihu ?an uwan mijin suka koreta akan wai ba za su bata gado ba, hakan yasa ta baro garinsu ta dawo nan.Shi ma tausayinta yasa ya haWani da ita na bata gidan ta zauna amma ko kuWin hayar baya karSa.



Wannan jawabi da Malam Auwalu ya zo da shi, shi ya ?ara saka Hizbullah a cikin matsananciyar damuwa, dan dama yana tunanin a wurin mi gidan za a samu Wan labarin garin da suka fito dan abi sawu to kuma sai aka samu akasin hakan.Da farko ma an yi tunanin ko kidnapers ne suka Wauke su amma daga bisani an fahimci ba haka bane.Duk wanda ya ga Hizbullah sai ya matu?ar tausaya masa saboda rabuwa da abin da ka sha?u ba ?aramin abu bane, akwai damuwa sosai duk ya ?are ya yi ba?i baya iya cin abinci kullum yana keSance a Waki dama ba wani abokai gareshi ba Ridallah ita ce aboki ?awa sannan ita ce komai nasa.Yanzu kwa da bata nan sai ya zama abin tausayi.Kullum yana Waki a rufe yana kuka rashinta ji yake zuciya da jijiyoyinsa ba za su taSa iya jure rashinta ba, idan son ganinta ya ciyoshi haja zai fita ya yi ta yawo wuri-wuri yana nemansu gani yake kawai zai iya ganinsu idan ya gaji da yawo sai ya ya je bakin ruwa ya zauna masu kamun kifi suna ganin kamar zuwa ya yi domin yake kallon yadda ake kama kifi amma shi bai ma san me suke ba gangar jikinsa ce a tare da su amma zuciyarsa ta lula duniyar tunani da jimamin halin da ya tsinci kan sa a ciki na rashin abar ?aunarsa ?anwarsa wacce ya sha?u da ita Ridallah.


A wannan hali da yake ciki ne jarabawarsu ta fito ya yi ?o?ari sosai, domin ya cinye jarabawar gabaWaya, amma shi ko murnar hakan ba ya yi sai dai iyayensa ne ke ta murna da farincikin hakan.Ganin hakan da Malam Auwalu ya yi, ya samu abokinsa Malam Iro da maganar halin da Hizbullah Win ke ciki, dan yana jin tsoro kar damuwar da yake ciki ta shafi karatunsa.Malam Iro ya baiwa Malam Auwalu shawara akan ya sanya Hizbullah ya cike scholarship ko Allah zai sa ya samu idan ya samu ya fita wata ?asar karatu zai fi maida hankali ga karatun nasa idan ya ga ya yi nisa da ?asar ma baki Waya ba kamar anan ba ko yaushe zai ke tunanin zai ganta ko zai haWu da ita.Wannan shawara ta yiwa Malam Auwalu daWi sosai dan yana ganin hakan shi ne mafita dan ita damuwa a cikin zuciya take babu wani wanda zai iya cirewa wani daga zuciya sai ko a taya mutum da addu'a akan Allah ya cire masa.


Duk da Umma Sadiya bata ?aunar Hizbullah ya mata nisa domin kuwa shi kaWai ne Wan da Allah ya mallaka mata, amma saboda suna so ya samu kyakkyawar rayuwa da ilimi mai nagarta hakan yasa suka amince masa ya cike form Win schoolarship Win amma a Sangaren Hizbullah shi dai bashi da wani zaSi dan shi komai yanzu ba ya jin daWinsa, sai dai baya so kwata-kwata ya bar ?asarsa ta haihuwa saboda ya san akwai Sarin jikinsa, mahaWar rayuwarsa burin zuciyarsa a cikin Niger'a wato Ridallah.


Cikin ikon Allah Hizbullah yana daga cikin wanda gwabnati ta biya wa karatu zuwa ?asar china, iyayensa sun yi matu?ar murna da sanya albarka a cikin lamarin.Haka aka yi ta shirye-shirye aka yi passport sannan aka masa biza da komai da komai har Allah ya kawo ranar tafiyar, ta Dutse da ke Jigawa State za su tashi haka iyayensa suka masa rakiya har airport Win ya yi sallama da iyayensa suna masa fatan alkairi suna kukan rabuwa da shi, shi kuma kuka biyu yake Waya kukan rabuwa da iyeyen nasa Waya kuma kuka rabuwa da ?asar da masoyiyarsa ke ciki tun da har yau babu labarin su Ridallah Win.


Haka su Umma Sadiya suka tsaya har sai da jirgin su Hizbullah Win ya tashi sannan suka baro airport Win.Sun sauka lafiya a inda suka samu masaukin su da aka ba su acan ?asar amma dai ba cikin makaranta suke ba gida ne wanda bashi da wani nisa da makarantar tasu, yawanci dama duk ?an Nigeri'a ne wanda gwabnati ta biya musu schoolarship, da wanda suka kusa kammalawa da kuma wanda shekaru biyu ya rage musu da ma wanda su ne ?an wannan shekarar.Gida ne mai tsari hawa -hawa wasu a sama wasu a ?asa Wakuna ne gasu nan kowa da nasa akwai kuma bayi a ciki har da kicin.A upstairs Hizbullah ya samu Waki bayan ya buWe da makullin da aka bashi ya shiga Waki yana ?are masa kallo akwai komai da komai a ciki haka ajiye jakarsa, yana le?a ko'ina sai dai akwai ?ura dan ba kowa ke zaune a ciki ba.


Yana tunanin yadda zai yi da gyara Wakin domin yana bu?atar tsintsiya da mopa, gashi baya so ya fita ya tambaya dan ya ga kowa harkar gabansa yake, Wakin da ke kusa da nasa kwa ban da kiWa babu abin da ke tashi a ciki.


"Barka da zuwa bro kai ma saukar yanzu ne?" Ya tsinkayi wata murya a bayansa.Juyowa ya yi domin ganin mai maganar, wani matashj ya gani wanda bai fi sa'an shi ba tsaye yana masa murmushi.Hizbullah duk da baya jin daWin zuciyarshi gashi kuma baya son yawan hayaniya, amma haka ya daure ya ?a?aro murmushi ya ce.



"Eh saukar yanzu"


"Ayya sannu da zuwa mu kam mun Wan wartsake gajiya, dan yau kwananmu biyu da zuwa"Matashin ya faWa lokacin da yake ?arasowa cikin Wakin.


Shiru Hizbu ya yi yana tunanin amsar da zai bashi dan shi bai saba da magana da abokai ba, babu wanda ya sani sai Ridallah, ita ce abokiyar hirarsa ita ce ke sanyashi nishaWi tun bata san me zata ce masa ba ya saba da gwalan gwalantun ta tun tana ?arama.Wata ?wallah ce ta ciko masa idanunsa da bai shirya zuwanta ba dama tun a jirgin yake cike da damuwa da alhinin baro ?asar da take.Haka yake ta tunani a jirgin har dai bacci ya yi nasarar Waukansa.


"Haba mazaje ya da ?wallah haka, ai fa dama rabuwa da iyaye sai an kai zuciya nesa but be a man kar kake yarda wani na ganin hawayenka, za ka saba ne dan nima nan haka na wuni na kwana da tunanin gida amma yanzu da mun yi waya shikenan" Cewar matashin yana dafa kafaWar Hizbu.



"Ba komai ba kuka nake ba ai, kawai dai na tuna wani abu ne"


"Yawwa my bro sunana Abulkairi Abubakar ana kirana da AA ni Wan garin Kano,a unguwar hotoro haka kawai tun da na ga zuwanka na ji kawai ka burgeni ga Wakina can sai ka wuce shi za ka zo naka"

"Thank u, sunana Hizbullah Auwalu ni Wan jihar Jigawa ne a garin HaWejia unguwar ?ofar arewa"


"Masha Allah suna mai daWi "

Murmushi suka yi a tare, kallon Wakin Abulkairi ya yi ya ce

"Yanzu za ka ga mai gyaran wurin ya zo,kafin ya rufe bakinsa sai ga wani saurayi sanye da wasu kaya da alama ma,aikaci ne a wurin da tsintsiya da mofa ya musu sallama tare da gabatar da kansa a matsayin Waya daga cikin masu shara da goge -goge na gidan cikin harshen nasara.


"Mu je Wakina kafin ya gama gyara maka nan Win"Abulkairi yace yana kama hannun Hizbullah tare da Waukan jakar Hizbullah Win saboda kar ta yi ?ura suka fita daga Wakin suka ba mai sharar damar yin aikinsa.

?akin Abulkairi suka shiga, gabaWaya yanayin tsarin Wakin irin na Hizbu ne sai dai wannan a gyare yake tsaf, saSanin na Hizbu da babu gyara.akan Waya daga ckn kujerun suka yiwa kan su masauki, bayan Abulkairi ya ajiye jakar, frige ya buWe ya Wakko lemuka da ruwan roba ya ajiye a gaban Hizbu kicin ya wuce ya Wakko kofi ya kawo masa.Ganin bashi da niyyar Waukan drinks Win ya sha hakan yasa Abulkairi Waukan ruwan ya buWe ya tsiyaya masa a kofin ya mi?a masa tare da cewa.


"Haba bro ka saki jikinka dan Allah sai wani Wari -Wari kake ka kasa sakin jiki dani" Ya faWi hakan yana murmushi.Shi dai Hizbu bai ce komai ba ya mi?a hannu ya karSi ruwan tare da kaiwa bakinsa yana mai ambaton Bismillah, ya kafa kai ya shanye ya ajiye kofin.Yana ajiyewa Abul ya Wauki lemon ya buWe zai tsiyaya masa a kofi.


"Ka barshi haka ma "

"Kana nufin ba zaka sha lemon ba?"


"Eh "Kawai yace a ta?aice ya koma ya jingina da jikin kujerar ya lumshe idanunsa.

"Ka koma kan gado ka kwanta in bacci kake ji" Da yake Wakin kato ne daga can gefe akwai gado madai daici da wardrobe sai kuma kujeru guda biyu a tsakiya sai su frige kayan kallo da komai da komai na bu?ata haka kowane Waki yake, da kicin da bayi duk a ciki.




"Bana jin bacci" Hizbu yace cikin ?aguwa dan ya fara gajiya da waWannan tambayoyin.


"Na lura dai baka fiya son surutu ba" Abul yace yana murmushi, shi dai Hizbu idanunsa kawai ya lumshe bai kuma cewa ?ala ba.




Bayan mai gyara ya gama suka koma Wakin Hizbu Abul na ri?e da jakar, suna zuwa komai tsaf sai ?amshi ke tashi haka Abul ya zauna yana kallo shi kuma Hizbu ya shiga wanka.Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi, ya fitar da sauran kayan ya jera a cikin wardrobe Win ya fito da wayarsa daga aljihun jakar, sai ya koma ya zauna a kujera yana Wan danna wayarsa shi kuma Abul yana kallo dan da ya lura Hizbu ba ya son yawan magana sai ya ?yaleshi dan a tunaninsa ko gajiya ce ta sanya yake hakan bai san ba abin a jininsa yake, surutunsa na tashi ne idan yana tare da Ridallah.



_Bayan sati biyu_



Lokacin Hizbu har an zama ?a gari domin yanzu har sun fara zuwa school, an fara karatu ba kama hannun yaro, yanzu abotarsu ta Wan yi ?arfi da Abul domin Hizbu ya lura yana da kyawawan Wabi'u hakan yasa ya saki jiki dashi sai dai idan surutu ne ya yi yawa Hizbu bai biye mishi, shima kuma Abul da ya fahimci halin Hizbu ne rashin son magana sai yake ?yaleshi idan ?an kuramen suka zo.Yanayin zamantakewar su abin sha'awa basa shiga harkar kowa in ba gaisuwa ba bare kula ?an mata kowa yana yin abin da ya kaishi.


Duk da ba department Waya suke ba amma wani lokacin tare suke tafiya school, kowa sai ya nufi nasu Sangaren domin aiwatar da abin da ya kaishi.Hizbu yana waya da su Umma amma duk lokacin da zai kira su sai ya ji zuciyarsa ta masa rauni saboda tuno Ridallah, sannan duk lokacin da suka yi waya sai ya tambayi labarin Ridallah ko zai ji an ganta amma magana Waya ce ko yaushe babu labarinsu hakan na sanya ya ji duk damuwa ta dabai baye masa zuciya dan ba ya jin dai-dai da second Waya zuciyarsa za ta manta da Ridallah domin ita Win a cikin jininsa take.





MMN AFRAH=?
?>?p?=??


d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



Page1?? 5?? &1?? 6??




_Ridallah_

A ranar da za a nemi su a rasa da cikin dare, misalin ?arfe biyu da wani abu Baba Habiba ta je bayi domin yin fitsari sai kuwa take jiyo muryoyi na maza suna magana ?asa-?asa, duk da bata jin me suke cewa amma ta tsorata saboda a jikin katangar gidanta suke butar ta ajiye a hankali ta lallaSa ta fito daga bayin ta je jikin katangar gidan inda za ta fi sauraren me suke cewa dan dai ta sana tabbas akwai wani abu tun da mai zai zaunar da mutane har wannan lokacin suna magana kuma raWa-raWa, tana kai kunnenta kwa sai ta fara jiyo me suke cewa.


"Kawai mu haura ta katanga, tun da babu namiji a gidan daga ita sai ?arta ta, na ci alwashin sai dukanmu mu ukun mun musu faWe, dan ita yarinyar sai mun kasheta bayan mun mata fyaWen saboda Hizbullah, a kanta ya ?i amincewa da bu?atarmu yana ganin mutane a raine, to zamu gama da ita sai mu buWe ?ofar gidan mu fice kafin asirinmu ya tonu.


"Oga ka rabu dashi zai zo hannu ne dama saboda yarinyar nan da yake so shi sa bai amsa tayin ba, amma yanzu in ya ga an yi mata fyaWe an kasheta ta bar duniyar dole zai ?auna ce ka ya ke biya ma bu?atarka"?ayan shi ma ya amsa masa.


"Yanzu ga wancan Alhajin can ya yi dare inaga daga Hotel yake kasan shi mayen mata ne, bari idan ya shige gida sai mu haura tun da yanzu ma bai gan mu ba"


"Gaskiya ne yau akwai kwasar gara duk da ma dai mata ba wani damun mu suka yi ba, mun fi ?arfi a neman ?an uwanmu jinsinmu maza, amma saboda wannan mai taurin kan gwara mu afka musu tun d....

Cikin hanzari Baba Habiba ta baro jikin katangar jikinta sai mugun rawa yake, gabaWaya ta susuce hankalinta a mugun tashe yake burinta kawai su bar gidan kafin mazan su duru, Waki ta nufa Ridallah da ke kwance tana baccinta hankali kwance, hannun Baba Habiba har karkarwa yake ta Wago Ridallah tare da toshe mata baki, da yake Ridallah Win bata da wani magagin bacci ta buWe idanunta amma tsoro sai ya kamata ganin Babarta ta toshe mata baki, hannunta kawai ta kama ta sakko daga kan gadon ganin hakan yasa Ridallah gane akwai wani abu da ke faruwa.


Gani ta yi Baba Habiba ta nufi hanyar zauren ?ofar gida, duk cikinsu babu mai takalmi a ?afarsa, a hankali Baba Habiba ta zare sakatar ?ofar gidan suka buWe suka fita a hankali, suna fita suka zura da gudu babu kowa a titin saboda dare ne hakan ya basu damar gudu akan titi, gudu kawai suke ba su san inda suke saka ?afafunsu ba.A can cikin gidan kuwa mazan sun sami nasarar haura katangar su duka uku, shigarsu gidan ke da wuya suka fara duba Wakunan domin aiwatar da abin da ya kawo su, suna dubawa suka fahimci babu kowa a cikin gidan suka duba ?ofar gidan ganinta a buWe yasa suka fahimci cewa masu gidan sun gudu ne da alama sun musu laSe ko dai makamancin haka A take suka mara musu baya domin sun ci alwashin sai sun aiwatar da ?udirinsu a yau Win nan!


?arfin namiji da mace ba Waya bane haka gudu da juriyar da namiji zai yi ba lallai ne mace ta yi ba.Wannan dalilin ne yasa mazan nan suka fara hango su Ridallah da ke she?a gudu, sai dai akwai tazara a tsakaninsu.Baba Habiba da yake suna gudu tana waiwayowa amma duk da layikan unguwanni da suka yi canjawa amma sai da suka lura suna biye da su hakan yasa suna shan wata kwana kafin mazan su ?araso Baba Habiba tasa suka shiga cikin wani kwalbati wanda babu ruwa a ciki suka kwanta rubda ciki yadda ba za a gansu ba suna fata da addu'ar kar Allah yasa su gansu domin babu mai cetonsu sai Allah, gashi talatainin dare kowa yana gidansa yana bacci.



Mutanen nan na ?arasowa kwanar nan su duka ukun suka tsaya, suna ta waige-waige sai haki suke na gajiyar gudun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login