Showing 45001 words to 48000 words out of 77516 words

Chapter 16 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

ita gabaWaya ta tsorata da yanayinsa.


"Lafiya dai Alhaji" Ta faWa lokacin da ta zo wurin nasa hankalinta a tashe.

Bai ce da ita komai ba sai ?ara ri?e kan nasa yake, yana ta karanto addu'o'i ya jima a hakan zuwa can ya yi shiru kamar ruwa ya cinyeshi, Hajiya kwa sai bin sa da ido take hannayen nasa ya cire daga kan nasa sai kuma ya tsaya yana kallon Hajiya Suwaida kamar dai yau ya fara ganinta.


"Alhaji sannu ka dawo dai dai?" Ta jefa masa tambayar tana mi?ewa tsaye daga sunkuyon da ta yi a kan sa.


Shiru ya yi bai yi magana ba, jim kaWan sai ?wa?walwarsa ta jefa masa wata tambaya.


"Ina Ru?ayya???"


A zabure ya tashi tsaye yana waige-waige kamar dai yana son ganjn wani.


"Alhaji mai kake dubawa ne" Hajiya Suwaida ta jefa masa tambayar cike da son jin amsar da zai bata.


"Ina Hajiya Ru?ayya?" Ta tsinkayi muryarsa a kunnuwanta ya jefo mata tambayar da ta sanyata rikicewa lokaci guda a maimakon ya bata amsar tambayarta.


Idanu ta zaro jin wata tambaya mai rikitarwa da rikita lissafi, tambayar da ta kaWa mata hanjin cikinta tambayar da ta ruWata tare d sanyata cikin wani zulumi marar misaltuwa saboda ita rabon da ta ji wannan sunan ma a bakin Alhajin sama da shekaru goma sha wani abu amma yau gashi da bakinsa cikin hayyacinsa yana ambaton sunan Hajiya Ru?ayya tare da neman inda take.



"Ina Afrah na ce miki amma kin tsaya kina wani abu da ban" Ya ?ara jefo mata tambayar da ta katse mata gabaWaya sa?ar zucin da take, tare da fara ?o?arin haWo kalmomin da za ta bashi amsar tambayarsa saboda jin tambayar tasa cikin wani amon muryarsa wanda ya Wauki shekaru aru-aru bai yi amfani da muryar ba.



"Ban...gan...ta...ba" Ta faWa muryarta na karkarwa hakan ne ya sanya maganar daddatsewa ta fito a ciccire.


Wani kallo Alhajin ya mata kafin ya fara takawa cikin izza da sarauta da ta gama ratsa jijiyoyi da jinin jikinsa, da sauri Hajiya Suwaida ta sha gabansa duk da a mugun tsorace take tana cewa.



"Alhaji ina zaka je ne? Ba ka ganin yanzu nan kan ka ke maka ciwo"


Hannu Waya ya sanya ya maidata gefe guda, ya cigaba da sakkowa daga step Win yana gama sakkowa ya nufi ?ofar fita daga falon, Hajiya Suwaida cikin ruWewa da fargaba ta biyo bayansa tana fatan Allah ya sa masallacinzai tafi duk da ta ji har lokacin ba a kira sallah ba.Cikin sanWa take biye da shi tana son ta ga inda ya nufa, abin da ta gani ne ya sanya ta ji wata irin muguwar faWuwar gaba wacce tafi wacce ta ji lokacin da ya ambaci sunan Ru?ayya (Afrah) ba komai ta hango ba wanda ya sa ta ji fitsari na bin ?afafunta saboda ruWewar da ta yi, Alhajin ba ko ina ya nufa ba illa part Win Hajiya Ru?ayya.


Bugun zuciyarta ne ya ?aru gabaWaya yawun bakinta ya ?afe, hatta numfashinta kokawa suke da ita saboda tsananin ruWewa.Part Win sa ya zama tamkar ma?abarta saboda yadda ya koma tamkar wata bola. Daker take iya Waga ?afafunta tana bin bayansa shi kuwa tafiya yake cikin marari da son ya ga ya ?arasa part Win masoyiyar tasa domin ya yi tozali da ita.



Tana zuwa dai dai wani ?arfe da ke jikin wani bango hanyar da za ta sadaka da part Win Hajiya Ru?ayya ta kama ?arfen ta tsaya saboda barazana da ?afafun nata ke mata na kasa Waukarta da suke neman yi.Nan ta tsaya tana kallon yadda zaninta ya ji?e da fitsari ta ma kasa sanin takamaiman tunanin da za ta yi bare har ta samu makamar abin yi, daga inda take tsaye tana hango shigar Alhajin part Win Hajiya Ru?ayya.


Alhaji kwa na zuwa part Win tun daga waje ya fara ganin sauyi dangane da part Win, kamar dai babu alamar ana rayuwa a wurin.Cikin fargaba ya fara dosar ?ofar da za ta sadashi da falon farko da ke cikin part Win Hajiya Ru?ayya. Yadda ya ga ?ofar a rufe amma ba ruf ba ba a ?arasa rufeta ba bare a yi tunanin an sanya mukulli, hannu ya sanya ya tura ?ofar amma ya ji ta ?i buWuwa alamu sun nuna ta daWe a haka dan kamar Sa ?asa ta tokare bayan ?ofar. Sai da ya zage ?arfinsa ya dinga tura ?ofar sannan ta buWu, kallon falon yake da mamaki ganin irin tarin ?urar da ke dan?are a falon hatta kayan kujerun da na kallon baka iya ganin komai sai ?asa da ta baibayesu, kafet Win ma tamkar ?asa ce a wurin dan ko alamarsa ba a gani, cikin Wacin rai da fargaba ya sanya ?afafunsa cikin falon hakanya shigo yana bin ko ina da kallo, ganin babu kowa sainkawai ya nufi upstairs da gudu ya hau faWuwar gabansa na tsananta dan ba ya so ya je bai tarar da ita ba domin ba ya fatan hasashensa ya zama gaskiya, domin a iya tunaninsa ya kasa tuna rabon da ya sanya Ru?ayya a idanunsa, ya manta rabonsa da ita jiya ne ko kuwa yau ne?

Yana hawa ya shiga bubbuWe Wakunan amma gabaWaya babu kowa a ciki yana fitowa daga ?ofar ?arshe ya dur?ushe a wurin cikin ?urar nan ya dage ?arfinsa ya ce


"Ru?ayya!!!" GabaWaya Sangaren ya Wauki amsa kuwwar muryarsa.

Amon muryarsa ne ya doki kunnen Hajiya Suwaida da ke ri?e gam da ?arfe tana ganin kamar idan ta saki ?arfen faWuwa za ta yi.Saboda yadda take a tsorace, tana cikin wannan ruWanin ta tsinkayo takun tafiyar Alhajin, tana Wago kanta ta hangoshi a firgici ya nufota, idanu ta fara zazzarewa tana ganin kamar ya gano cewa da sanya hannunta, kamar dai ya san ita ce ummul aba isin faruwar komai, tabbas idan har hasashenta ya zama gaskiya to yana ?arasowa sha?eta zai yi har lahira.


"Ina kika kai min Ru?ayya???" Ya jefo Sata tambayar tun kafin ya ?araso inda take ido ta ?wara masa tana hango tsantsar tashin hankali a tare da shi da alama ma baya cikin hayyacinsa.



MMN AFRAH=?
?>?p?=??




d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?


Page 4?? &6?? 4?? 7??




*GIDAN HAKIMI ?AN BURAN*



Hajiya Sakina ce tsaye a dining area tana jera kayan abincin dare, ta gama jerawa tsaf tana Wan goge kujerun dining Win, Mai gidan nata ne shi da Hafiz suka shigo cikin shirinsu na zuwa masallaci dan har an fara kiran sallah ma a wasu masallatan.


"Ammi wai har abincin ya kammala" Cewar Hafiz yana dariya.


"To acici ka dai bari ai ku dawo daga masallacin dai ko, kai ne sarkin ci" Ammi ta ce tana kallonsu da murmushi.



"Barshi ya ci ai dan shi nake nemowa" Abban nasa ya faWa cikin barkwanci.


"Yawwa Abba ci dama ai ba laifi bane" Hafiz ya ce yana kallon Ammi.


"Wato ma dan shi kake nemowa" Ammi ta ce tana kafe mai gidan nata da idanu.


"Har da ke mana" Ya faWa yana dariya ganin yadda ta yi dan ya ce dan Hafiz yake nemowa.


"Ka ce fa, ai da dan shi kaWai kake nemowa ni ma sai in daina dafa muku abincin in ga ko kwa ci abincin Wanye"


"Dafa abinci aiki ne dama" Ya faWa ckn sigar zolaya.


" Ba aiki bane bacci ne, shi yasa ma na ga baka iya cin abincin masu aiki"


"To gaki mai zanyi da abinci wasu masu aiki, ai za?in hannunki kaWai bai barin mutum ya ji WanWanon abincin kowa sai...


Kafin ya kai ?arshen maganar sai kawai suka ga fuskarsa ta sauya, yana yatsina fuska sai kuma suka ga ya dafe kansa.


Da sauri Ammi da Hafiz suka nufoshi, kafin su ?araso har ya dur?ushe a wurin Hafi ma na zuwa sai kawai ya yanke jiki ya faWai, wani ?ara Ammi ta fasa ganin su duka biyun sun shiga wani yanayi marar kyan gani dan a take ta fara tuniwa da yanayin da suka shiga lokacin naWin da suka je a fadar Sarki da aka maido mata da su basa hayyacinsu.Ai ita ma bata gama tantancewa ba sai jin kan ta ta yi yana juyawa take ita ma ta kwance a wurin.




?aran da ta saki shi ne ya janyo hankalin ?ar aikinta da direban gidan da wani mai ban ruwan fulawa, dan koea ya ji ?aran ya san ba na lafiya bane. A kusan tare suka shigo dan dama Wabi'ar gidan ce masu aikin gidan tamkar ?an gidan haka suke.Sun same su kowa dafe da kai sai dai kowa da abin da ke fitoww daga abakinsa na addu'a da ambaton sunayen Allah, wannan yanayi da suka samesu ya Waga musu hankali dan haka suke ta ?o?arin yadda za su tafi da su asibiti amma kuma ba a Wau wani lokaci mai tsawo ba suka dawo hayyacinsu sai dai su duka daga farfaWowarsu mutum Waya suke ambato wato Ru?ayya..

Daker Abban ya umarcisu da su gabatar da sallah kafin su tafi gidan Ru?ayyar dan su duka sun za?u su ganta dan sun kasa gane ko tuna rabon da su ganta, dan ko a waya basa son kiranta ita kawai suke son gani.Bayan sun idar da sallar dan a gida suka yi Abban ya ja su dan an fito daga masallaci lkcn, haka suka Wunguma direba yana jan motar Hafiz a gaba Ammi da Abban a baya.


Abba sai cewa direban yake ya yi sauri domin ganin Wiyar tasa yake son yi ji yake kamar ya fi su Ammi da Hafiz Win son ganinta ma.Suna zuwa direban ya yi horn mai gadi da hankalinsa ke kan radio yana saurara ya ajiyeta a kan bencin nasa da sauri ya le?a ganin motar gidan sirikin mai gidansa ya wangale musu get Win suka shigo yana Waga musu hannu.Ko gama parking direban bai yi ba suka fara buWewa suna fitowa kowa hankalinsa na ga son ganinta.



Hanyar part Winta suka nufa su duka, suna tahowa suka fara jiyo hayaniyar mai gidan yana ta amboton ina Ru?ayya.Mamaki da al'ajabi ne suka cika su jin su ma ita auka zo nema amma gashi nan shi ma yana nemanta to ina take? Kowa ya jefawa kansa tambayar a zuciyarsa.Tun kan su ?araso suka ashe da shi da matarsa Hajiya Suwaida ne, gabaWaya fuskokinsu cike da tarin tambayoyi ganinsu yasa Alhaji Sagiru ya nufosu tun kan su ?araso yana tambayarsu ina Afrah???


"Mu ma wurinta maka zo" Abba ya faWa yana kallon Alhaji sagirun.Dan dama abokai suke shi ne ya auri Wiyarsa dan zumuncinsu ya cigaba da Worewa.



"Ni da ina zan san inda take da zai sanyani a gaba yana cewa sai na nemota" Hajiya Suwaida da ee ta faman share hawaye take faWa, dan zuciyarta kamar ta faso ?irjinta ta fito saboda ba?inciki dan ita kukan daowarsu hayyacinsu take dan ganin dangin Ru?ayyar suna nemanta ya ?ara tabbatar mata da karyewar asirin, gashi so take ta keSe ta yi waya dan ta kamata a ce ta fara shirin Waukan mataki tun kafin Ru?ayyar ta bayyana dan ta san ita ma duka inda take in har tana raye to ta dawo hayyacinta, gwara tun kafin ta ji?a mata aiki ta sanya a ?ara matar da su kan su, su duka a ?ara nisanta tsakaninsu idan ma ta kama a kashe Ru?ayyar gabaWaya.


"Wai dama bata nan ne" Ammi ta jefa wa Hajiya Suwaida tambayar.


"Da safe fa ta fita unguwa shi ne fa har yanzu bata dawo ba, ni kaina bansan ina ta tafi ba" Hajiya Suwaida ta faWa cikin kissa da kisisina.

Shiru kowa ya yi, Hafiz kwa sai hararar Hajiya Suwaida yake dan ya san bata ?aunar ?ar uwarsa ko kaWan dama bai zama lallai kishiya ta ?aunaci kishiyarta ba kuma ma ba kowace mace ba ce za ta ce tana ?aunar kishiya sai dai ana samun masu zama da kishiya tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa sai dai ita Hajiya Suwaida tsanarta da ban take ?iri-?iri take nuna tsanarta a fili dan ba zai manta ba duk da ba wani wayo ne da shi ba amma kuma tabbas ya san lokacin da take nunawa ?ar uwarsa tsana a fili har da shi ma idan ya zo wajen Aunty Afrah.


"Ya aka yi kika san unguwa za ta je?" Hafiz ya jefa mata tambayar.

Idanun mutanen ta faka ta jefa masa harara kafin ta bashi ams da cewa.


"Na dai hangota ne za ta fita"

"Amma yanayin yadda na ga part Winta babu alamar akwai wata halitta da ta rayu a yau a cikinsa dan ko a shekaru bana jin Wan adam ya shig sashen , dan haka ya akayi bansan bata nan ba? Ya aka yi kuma kika ce yau ta fita da safe? Shin mai kike Soyewa dan nasan kin san komai dan haka ki faWa min gaskiyar ina take, tunda iyayenta ma ba su san inda take ba, da alama su ma a yau suka nemi inda take kamar yadda ni ma a yau na nemeta, ki faWi gaskiya idan ba haka ba kuwa in har na gano gaskiya na gane da sa hannunki sai na Waureki har igiya ta yi saura" Cewar Alhaji Sagiru yana nunata da yatsa.

"Billahillazi huwar rahmanu bansan komai ba, wato ni kamar bani da kowa shi ne za a ce da sanya hannu na a ciki" Ta faWa tana fashewa da kukan makirci.

Ammi kwa sai share hawaye take jin wai sashen Rau?ayyar ma babu alamar ana rayuwa a ciki, kenan ?arta ta Sata ta yi ko kuma mutuwa ta yi ko kuma kasheta aka yi.


"Hafiz kira min mai gadi" Alhaji Sagiru ya faWa rai Sace.

D a sauri Hafiz ya juya tun kafin ya ?arasa wurin mai gadin yake ?walla masa kira, mai gadi jin ana masa kiran mafarauta ya taso da sauri ya nufo Hafiz tun kan ya ?araso Hafiz Win ya juya ba tare da ya ce masa komai, bin bayansa ya yi cikin ruWani dan sai yake ganin ko garin buWe musu get Win ne ya yi laifi yana tsoron kar ya rasa aikinsa.



Suna ?arasowa Alhajin ya jefawa mai gadin tambaya.


"Mai gadi yaushe Hajiya Ru?ayya ta bar gidan nan? Kai ne a bakin ?ofa dan haka nasan kasan duk mai shiga da mai fita a gidan na domin sanin hakan ya rataya a wuyanka, yaushe rabon da ka ganta yaushe ta fita da wane lokaci ta fita tau tsawon wane lokaci?

Ido mai gadin ya fara rarrabawa jin duk tambayoyin nan shi ake jiran amsar su daga gareshi, ta ina zai fara bayanin wannan dan baya so shi ma ya shiga ciki mace mai tsohon ciki tana Wauke da cikin hakimi kuma jikokin sarki sannan babanta hakimi ?ar gata gaba da baya amma matu?ar ya shiga cikin cakwakiyar nan babu mai fitar da shi sai Allah amma tabbas zai faWi gaskiya ko dan karamcin matar a gareshi.


"Ana tambayarka ka yiwa mutane shiru?" Abba ya faWa yana kallon mai gadin ganin duk ya tsorata hakan na nuna masa akwai wani abu.


Hajiya Suwaida kwa fakar idanunsu ta yi take yiwa mai gadin gargaWi tare da nuna masa za ta bashi kuWaWe masu yawa in bai faWi gaskiya ba dan ta san ya san lokacin da Ru?ayya ta bar gidan amma kuma ba zai taSa ambata wani abu ba har sai an nemi hakan saboda wanda za su nemi sanin haka an mantar da su ba sa cikin hayyacinsu.


Mai gadin kallon Hajiya Suwaida yake yana kuma bin fuskokin sauran mutanen da ke wurin yana tunanin mai ya dace ya faWa gaskiya ko ?arya?



MMN AFRAH>?p?=?
?=??




d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?


Page 4?? 8?? &4?? 9??



*HIZBULLAH*


Tun da ya rufe Wakin nan bai buWe ba, har sai da aka kira sallar magriba da yake akwai masallaci daga can tsallaken gidan da suke.Duk da bai jin ?arfin jiki da na zuciyarsa a haka ya daure ya tashi daga kwanciyar da ya yi alwala ya yi ya buWe Wakin ya fito, hakan ya yi dai dai da fitowar Abulkairi daga nashi Wakin amma Hizbu na ganinsa ya haWe rai tare da Wauke kai yana jin Abulkairin na masa magana amma ya yi tamkar ma bai jinsa, har suka je masallacin suka dawo Waya a gaba Waya a baya ko jerawa Hizbu bai bari sun yi ba dan shi yanzu gabaWaya zuciyarsa ta Wauki laifi ta Worawa Abulkairi dan shi ne ummul aba'isin rashin gananwarsa da Ridallah da ace ya barsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login