Showing 21001 words to 24000 words out of 77516 words

Chapter 8 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

tana shigowa ta faWa jikin Auntyn nata tare da sakin wani kuka.Bayanta Hajiyar ya shiga bubbugawa tana lallashinta har sai da ta samu ta yi shiru sannan ta shiga kora mata jawabi kamar haka.

"Ki daina kuka Iftihal babu abin da zai faru kuma ma gidan da zai kai ki na san matar gidan kuma ?awar Hajiya Suwaida aminiyata ce dan haka ba za ki takura ba za ki yi duk abin da ranki ke so, dan kin san su dama maza ba mazauna gida bane bare ya takuraki shi abokin Abien naki.Hajiya Suwaida za ta kirata ta mata jawabi dalla-dalla.

Wani daWi ne ya ziyarci zuciyar Iftihal Win ta rungume mahaifiyarta ta cikin farinciki dan dama ita a rayuwarta ta tsani takura bare yanzu da idanunta suka buWe ba ta jinnza ta Wauki kulle a gida kamar wata matar aure.Haka dai su ka yi ta tsara yadda komai zan kasance idan Iftihal Win ta je Chaina maimakon a gan su suna Sacin rai sai aka ga saSanin haka saboda aun riga sun samo mafita basu da matsala.

A Sangaren Hajiya Suwaida ma ta kira Hajiya Wasila ta rattaba mata bayani, aikuwa ta ji daWi dan dama mijin nata ya faWa mata cewa abokinsa zai kawo ?arsa Waya tilo gidansa domin ta yi karatu.Jin cewa kuma ?ar gidan aminiyar ?awarta ce kuma ga ?udurinsu kuma ita ma fama ?ar harka ce dan haka kwa suka ?udurta neman kuWi sai sun ga abin da ya turewa buzu naWi.

Suna gama wayar Hajiya Suwaiba cikin azarSaSi ta kira aminiyarta ta labarta mata yadda suka yi, daWi a wurin Hajiya Hauwa kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha.




d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YATINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?




NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




PAGE2?? 5?? &2?? 6??



_Umma Sadiya_


Zaune take akan tabarma bayan magriba, Malam Auwalu ne ya shigo Wauke da sallama amsa masa ta yi tana masa sannu da zuwa, zaunawa ya yi akan tabarmar ita kuma ta tafi ta kawo masa abincinsa tuwon masara da bushashshiyar kuSewa.Ruwan da ta Wakko masa a wata ?ar roba mai faWi ya wanke hannayensa, mi?a masa ta yi ya yi Bismillah ya fara ci suna Wan taSa hora yana ta yabon daWin da girkin ya yi.

"Wallahi lamarin yaron nan yana Waure min kai, duk da dai nasan halin da zai tsinci kan sa a ciki sanadin Satan su Ridallah amma yadda na ga ya Wauki abin ya girmama kar abin ya taSa karatun sa" Ta ?arasa faWa tana kallon Malam Win da ya dage sai cin abincinsa yake da alama daWin ya wuce inda ake zato.

Sai da ya kai lomar ?arshe ya ture kwanon da ta zuba masa a ciki gefe sannan ua wanke hannunsa da bakinsa ta mi?a masa ruwan da ta zuba masa a ?aramin kofi ya karSa ya sha sannan ya fara bata amsa.


"Duk maganganun ki haka suke amma sai dai babu yadda za a yi Hizbullah ya ki maida hankali a karatu sanadin damuwar da yake ciki, ke kan ki kin san halinsa baya wasa da karatu duk da yana da damuwa a ransa amma haka ba zai sanya ya yi watsi da abin da ya kai shi ba"


"Hakane Malam amma yadda ya damu ne abin ke tsoratani wallahi kullum fa sai ya kira ya fi a ?irga yana tambayar an gan su ko an samu labarin su"


"Wannan duk ba wata matsala ba ce kuma ke kan ki kinsan irin yadda ya sha?u da yarinyar a yadda ma ya yi ai ba ?aramin ya?i ya yi da zuciyarsa ba kuma kiran da yake yana tambaya kar ki Wauka wani abu yana yin hakan ne da ya samu sau?i da salama a cikin zuciyarsa saboda Allah kaWai ya san yadda yake ji abin da nake so kawai mu ?ara dagewa da addu'a akan Allah ya bayyana su, kuma duk lokacin da ya kira ki rin?a kwantar masa da hankali"

"Wannan haka yake, kuma insha Allah za mu cigaba da addu'a kuma zan cigaba da kwantar masa da hankali dan ya samu nutsuwa ya yi karatun"


"Yawwa to Allah mana jagora su kuma Allah bayyana su"

"Amin amin" Ta faWa tana tashi ta shiga kwashe kayan da ya ci abincin.



_GAGARAWA L.G_


Tafiya take wasu dandazon yara biye da ita suna tafi suna mata wa?a.

"Mahaukaciya ta Wan Bala,mahaukaciya ta Wan Bala" Haka suke ta faman faWa suna tafi suna dariya haWe da tsalle-tsalle ita dai bata musu komai ba hasalima kamar ba da ita suke ba dan ita dama bata faWa bare kuma yanzun da take tafiya kamar a gabaice ma take da alama wani abu na damunta, a daidai wata kwana kawai sai gani suka yi ta yanke jiki ta faWi cikin razana da tsoro yadda suka ga ta yi yasa yaran ja da baya suna cewa.


"Ta mutu!!! " Suna ta maimaitawa, a guje duk suka fara watsewa suka barta anan yashe da yake layin babu mutane sosai shi yasa babu wanda ya gan su bare ya san mai ya faru.

Malam Idi mai almajirai ne tafe shi da wasu almajirai guda huWu daga gonarsa suke suka yi aiki shi ne suka taso ganin magriba ta kawo kai, dan dama da yamma ne suka koma gonar saboda daman sun je da safe.Kwanar da suka shawo sai ganin mace suka yi kwance a ?asa cikin hanzari Malam Idi ya yi kan ta tare da almajiran nasa, haka yasa almajiran suka kamata da yake matasa ne da Wan girmansu kuma dama a layin gidan nasa yake.Haka yasa suka kai ta har cikin gida yasa matarsa Malama Zainab ta shimfiWa tabarma da yake ita ma mace ce mai kirki ko yadda jikin mahaukaciyar yake bata ?yamata ba bare ta ce ba za a Wora mata ita ba akan tabarma.


GabaWaya Malama Zainab ta ruWe da ganin mahaukaciyar dan duk tunaninta ma mutuwa ta yi, Malam Idin ne ya shiga kwantar mata da hankali akan ba mutuwa ta yi ba haka aka watsa mata ruwa Malam Win ya shiga tofa mata addu'a cikin iko da hikimar ubangiji sai ta kawo hankali.Tun da ta falka take ta bin su da ido, amma bata ce komai su kuma dama sun san mahaukaciya ce dan suna ganinta a layin duk da ba wata hauka tuburan take ba sai dai kana ganinta kasan tana da gushewar hankali.


Ganin alamomin yunwa a tattare da ita yasa Malama Zainab zubo mata abinci ta kawo mata, Malam Zainab na ?o?arin ajiye mata abincin sai ta sanya hannu ta warci kwanon abincin, cikin sauri ta sanya hannu tana ci hannu baka hannu ?warya, Malam sai jijjiga kai yake alamar tausayi Malama Zainab kwa ban da hawaye babu abin da ke zuba daga idanunta saboda tsabar tausayi da kuma ?ara godewa Allah da take da ya iyota cikin masu hankali lallai komai Allah ya baka yana daga cikin baiwar ubangiji.

Dan mutane da dama ba sa gane baiwa da ni'imar da Allah ubangiji ya musu ba wani kullum bashi da burin da ya wuce suke kallon wata Winbin dukiya da gidaje da tarin motoci da Allah ya baiwa wasu, suna mantawa da hatta lafiya da Allah ya basu babban arzi?i ne.Lafiya idan aka karSeta daga bawa aka jarabceshi da rashinta, sai ki ga duk tarin dukiyarsa ya ?arar da ita a neman magani amma lafiyar bata samu ba shi yasa idan Allah ya baka rai da lafiya to ka gode masa duk wani abun duniya samamme ne kuma ?ararre matu?ar kana da rai da lafiya da rufin asirinka ka Wauke idanunka daga kan abin duniyar mutane Allah kai ma yana sane da kai wani ma abin da zai ci gagararsa yake amma kullum cikin godewa Allah yake Allah sa mu da ce.

"A gaskiya Malam sosai wani imani ya ?ara shiga ta ganin halin rashi na hankali da matar nan take ciki, lallai rai da lafiya, hankali ji da kuma gani su kaWai Allah ya baka to ya baka babban kyauta! Duk da waWan nan abubuwan da na lissafa abin tambaya ne ga duk wanda aka baiwa su" Ta faWi hakan ?walla na cikowa daga idanunta ganin yadda mahaukaciyar ke cin abincin ko na bakinta bata cinyewa ba take ?ara tura wani.


"Wannan haka yake Zainabu amma mutane ba ma la'akari da hakan kuma wasu ba sa amfani da abubuwan wajen gyaran lahirarsu, suna duk abin da suka ga dama da su"

"To Allah ya ganar da mu gaskiya, ya bamu ikon amfani da baiwar da ya mana ta hanya mai kyau"


"Amin" Cewar Malam yana sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, tare da kallon mahaukaciyar da ta kammala cin abincin ta yi wurgi da kwanon, ta shiga waige-waige da alama ruwa take nema.

"Zainabu ki Wakko mata ruwa "

"To Malam" Zainabun ta ce tana tashi ta Wakko ruwan a wani kofi mai Wan girma ta mi?a mata madadin ta sha ruwan sai kawai ta karSa ta ajiye sai kuma ta sanya ?afa ta ture ruwan ya zube gabaWaya a ?asa.Kallan kallo aka shiga yi tsakanin Malam da Malama Zainabu dan ita Malamar har wani tsoro ta ji ya Warsu a ranta, ita kuwa mahaukaciyar ko a jikinta ta tashi ta nufi randar da ta ga Malama ta kwalfo mata ruwa har ta buWe sai kuma ta rufe da ?arfi har murfin ya yi ?ara da yake wani farantin silba ne ?arami aka rufe randar dashi.

Sai da ta je kan randar ta ?arshe da yake randunan uku ne ta buWe ta sanya kofin da aka kai mata ruwan da shi ?asan sa ma akwai ?asa haka ta dulmiya ta kwalfo ruwan da ta fito da hannun nata gabaWaya ya ji?e dan har hannun ta sanya a randar ta Wakko ta kafa kai ta sha sai da ya ishe ta, sannan ta dangwarar da kofin a wurin ta juyo ta dawo inda ta tashi ta zauna. Su Malam dai kallonta kawai suke.

"Uhmmm Malam tun da ta warware kuma ta ci abinci dama ina ganin yunwa ce ta sanya ta faWi, ai sai a nuna mata ?ofa ta tafi ko?" Cewar Malama Zainab tana kallon Malam Win da ya yi shiru kamar mai wani nazari.


Shirun dai ya yi bai bata amsa ba har sai da ta ?ara maimaita masa maganar sannan ya huro da iska daga bakinsa, sai kuma ya ce.

"Hakane Zainabu amma ba wai na ?i ta taki bane sai dai ni ma akwai abin da nake hange wanda nake ganin kamar ke baki hango ba, inaso dan Allah ki bani haWin kai mu ri?e matar nan a gidan nan" Ya ce yana kallon Malama da ta yi saurin mi?ewa tsaye cikin kaWuwa.

"Me kake faWa haka Malam? Mahaukaciyar kake cewa ta zauna a gidan nan, haka kawai ba sanin halinta ba muka yi yo da Allah na tuba mahaukaci ma ai ba a saka shi a lissafi ba son ta je ta cutar da mu" Malama Zainab ta ce tana kallon inda mahaukaciyar ke zaune tana ta wani kurta layi da yatsanta a ?asa sai wani maganganu take da baka gane ko fahimtar me ma take cewa.

"Haba Zainabu ya kamata ki fara saurarata ki ji manufata kafin ki yanke hukunci, kuma insha Allah za mu ajiyeta ne dan mu taimaka mata mun yi hakan da kyakkyawar niyya da yardar Allah babu abin da za ta mana"

"To ina sauraranka Allah kuma ya sa haka"Ta faWa tana komawa ta zauna.

"Amin" Ya ce kafin kuma ya Wora wata maganar.


"Haki?a Allah yana baiwa bayinsa baiwa haka kuma yana jarabtarsu ta duk inda ya ga dama, amma cikin iko da hikimar ubangiji na gano wani sirri tattare da matar nan, Allah ya bayyana tare da nuna mini wani Soyayyen al'amari a tattare da ita"


"Me kake so ka ce ne Malam" Malama ta katse shi.


"Inaso in ce miki wannan matar ba wai da haukar nan aka haifeta ba, asalima ba mahaukaciya ba ce daga baya abin nan ya sameta, tabbas akwai wani sihiri a tattare da ita" Malam ya faWa idanunsa kafe a kan mahaukaciyar da zuwa lokacin kuma kawai Waga kai take yi sama tana saukewa ?asa.

?an?ance idanu Malama Zainabu ta yi ta kalli matar tana son gano abin da Malam Win y faWa amma kuma bata ga komai ba dama ta yi zaton hakan dan tasan bata da baiwar da mijin mata yake da shi"Yanzu Malam kana nufin ka ce min matar nan da asali ba mahaukaciya ba ce, kenan ta taSa zama da hankalinta?"

"Tabbas haka nake nufi, kuma na ?udurci taimaka mata insha Allahu za a dace za ta dawo ras kamar bata taSa yin haukar ba"

"Amin ya Allah, kai duniyar nan abin tsoro ce wallahi wannan wane irin rashin tsoron Allah ne da kuma son duniya za a mayar da mutum mahaukaci kawai yake yawo a gari kai Allah ka karemu sharrin mutum da aljan"Malama Zainabu ta ce tana jijjiga kai.

"Amin, ke dai bari rayuwar yanzu sai a hankali"

"To Allah tayamu ri?o ya bata lfy"

"Amin, yanzu abin da nake so da ke wancan Wakin da ake sanya kayayyaki, za a kirawo almajirai guda biyu ko uku su kwashe su haWa a Waya Wakin, sai a gyara mata ta zauna a ciki"

"To Malam, amma wani hanzari ba gudu ba kan ganin za ta yadda ta shiga Wakin kwa?"

"Eh za ta shiga yanzu kafin su gama gyarawa akwai wani magani da zan yayyafa mata a jikinta zai taimaka wajen shigarta Wakin"

Da "to" Malama ta amsa masa.

Kafin meye wannan almajiran Malam sun shiga gyara Wakin, ita kwa mahaukaciyar tana nan kwance a inda take da Malam ya watsa mata maganin anan ta Singire tana bacci, har sai da Waki ya zama tsaf sannan aka shimfiWa tabarma da ?aramar katifa, tana falkawa Malama Zainab ta nuna mata Wakin cikin ikon Allah kwa babu abin da ta yi kawai shiga Wakin ta yi ta zauna tare da mi?e ?afa duk da baccin dama ba wani isarta ba ya yi da alama, Wakin kawai take bi da kallo.


_Bayan sati biyu_


Jiki ya yi kyau sosai dan har sai da Malam ya mata addu'a ya kafeta a cikin gidan dan gudun fita saboda tana ta yun?urin a barta ta fita, yanzu ma duk haukar ta yi sau?i sai dai ta zauna ta yi shiru, ko aiki Malams Zainab take a tsakar gida sai ta fito ta zauna a ?ofar Waki take ta bin Malamar da ido duk inda ta yi.

Yanzu jikinta ma fes yake saboda hatta kan ta sai da Malama Zainab ta wanke mata shi ta gyara mata ta tufke mata, saboda ta fahimci bat son kitso da an kama kan sai ta rin?a jijjiga kai alamar bata so.Kayan Malamar ne yanzu ma a jikinta dan har wanka take mata sosai sau?i ke samuwa shi kwa Malam kullum ciki haWa rubutu da maganin ita ce gashi yana jin daWin yadda Zainabun ke yiwa matar ba kyara ba tsangwama.






d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YATINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?




NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...




PAGE2?? 7?? &2?? 8??



_Ridallah_


Karatu ya kankama sosai ta maida hankali a karatun ta dan yanzu duk class Win nasu babu wacce ta fita ?o?ari Malamai har mamakin irin ?o?arinta suke saboda iliminta har nema yake ya zarce ajin da take.Ko yaushe cikin nazari da duba litattafai take babu ruwanta da shirme ko biya ?awaye ?awarta gida Waya Anisa Bello ?ar garin Dutse ce ita ma yarinya ce mai ?o?ari da haza?a shi yasa ma tasu ta zo Waya da Ridallah.


Shugaban makarantar shi ne ya mata siyayyar madara cornflakes da makamantan su, tabbas Principal ya yi musu alkairi da ba za su taSa mantawa ba saidai Allah ya biyashi. Baba da inna Rahma suka mata sauran siyayyar kayan yaji da mai da sauran abubuwan bu?ata yanzu ta zama ?ar makaranta, hankalinta kwance dan kullum sai ta ga su Baba hakan ke sa ta ji kamar ma ba boarding school take ba.


Da yammaci ne garin ya yi luf kamar akwai haddiri saboda lillimi da ake yi, zaune suke a ?ar?ashin wata bishiyar maina suna kan sallayar da suka shimfiWa ga litattafan da suka Wakko nan domin yin karatu, saidai Ridallah ta buWe nata littafin a zahiri idan ka ganta zaka Wauka karatun take amma a baWini ba wai karatun take ba kawai dai tana kallon littafin ne amma ko rubutun bata iya karantawa sai hoton Ya Hizbullah kawai take gani yana mata murmushi hakan yasa idanunta suka ciko da ?walla saboda kwana biyun nan sosai tunaninsa ke addabarta tana ta ?o?ari ta yakice tunaninsa da son ganinsa daga zuciyarta amma hakan baya samuwa.Anisa da ta ga wani wuri bata fahimta ba a cikin littafinta tana so Ridallah ta mata bayani ta Wago tana mata magana tare da nuna mata rubutun. Amma duk maganar da take mata bata ko da kalli inda take ba bare kuma ta san ran za ta bata amsa.


Sororo ta tsaya tana kallonta ganin hawaye na Wiga a kan littafin da ke hannunta, hannu ta sanya ta taSota, figigit ta yi tana kallon Anisa tare da sanya hannu ta goge hawayenta.


"Haba ?awata mai yake damunki ne haka har da kuka, ko Babanki kika tuno da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login