Showing 15001 words to 18000 words out of 77516 words

Chapter 6 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

in ?ari tunani amma tunanin nawa baya kaiwa inda nakeso ya kai saidai na gaji na ha?ura"

Haka kwa za kake gajiya har abada dan babu wani abu da ?wal?walwarka za ta tuna, saidai ka gaji ka ha?ura, ta faWi hakan a ranta a fili kuma sai ta ce

"Allah sarki Alhajina nima bana jin daWin halin da kake kasancewa wallaho saidai dan ba yadda zan yi ne, amma ka yi ha?uri zaka daina watarana"

"To Hajiya Suwaida shi sa nake alfahri da kasancewarki mata ta"

"Ni ma ina alfahri da kasancewarka miji a gareni"

A haka ta lallaSashi ya shiga wanka ya shirya suka sakko ?asan tare, lokacin ma'aikatan gidan na ta hidima kowa ya kama aikinsa.


Alhaji sagiru Wan asalin garin Dutse ne, kuma Wa ne ga mai martaba sarkin Dutse, shi kaWai iyayensa suka haifa sai ?anwarsa da aka haifa a ranar ta mutu, yana da matar aure Hajiya Suwaida ita ma ?ar cikin garin Dutse ce sai dai Allah bai basu haihuwa ba.



Gidan Alhaji Sunusi


Hajiya Sakina ce zaune a falonta ta sanya kayan marmari a gaba sai tuffa a hannunta wanda ko gutsira bata yi ba, ta yi nisa cikin tunani sai tv da ke ta faman aiki.Hawaye ne ke kwaranya a idanunta amma saboda nisan da ta yi a tunanin ko share hawayen bata yi .

Hafeez ne ya shigo cikin falon sanye yake da t.shirt da wandon jeans ba?i sai ?amshi yake abinsa.Da sallama ya shigo falon mahaifiyar tasa, amma kuma sai jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ya tsinci mahaifiyar tasa a ciki, cikin sanyin jiki ya ?araso cikin falon har ya zo gabanta ya dur?usa amma bata ma san da zuwansa wurin ba.Da ido ya bi plate Win kayan marmarin da ke ajiye wanda tun lokacin da zai fita daga falon ya hangi Na'ima mai aikinsu ta fito daga kicin da ta yayyanka mata za ta kawo mata amma abin mamakin gashi har ya je ya yi wanka ya shirya duk Sata lokacin da ya yi amma har yanzu babu wani abu da ta ci daga cikin kayan marmarin sai tunani da ta tsunduma, a ciki shi yasa kwata-kwata ba ya so ta kaWaice ita kaWai saboda yawan tunanin nan gudun kar ma ya yuwa lafiyarta illa.Wata Soyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannu ya Wan taSa ta tare da cewa


"Ammi!"

Jin taSa ta da aka yi da kuma sunanta da aka ambata shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta kai ziyara.

Dubanta ta kai ga Hafeez Win, sai kuma ta yi saurin kawar da kan ta gefe jin lemar hawayen da ke kan kumatun ta, da sauri ta ajiye tuffar a kan plate Win sai kuma ta sanya hannayen nata ta goge hawayen tare da Wan jan hanci kaWan sannan ta ?a?alo murmushi tare da cewa


"Hafeez wai kana nufin har ka yi wankan ka shirya, ko dai ji?a-ji?a ka yi baka fita ba shi yasa ka yi saurin fitowa" Ta ce cikin zolaya dan kar ya mata zancen halin da ya tsince ta a ciki, saboda ko da zai tafi wankan sai da ya sha lallaSata akan dan Allah kar ta yi wannan tunanin, har da kunna mata tashar arewa 24 suna shirin mata a yau dan su Wauke mata kewa amma shi ne ya dawo ya same ta dumu-dumu tana aikin nata da ta saba wato tunani.



" Haba Ammi yanzu duk maganar da muka yi a gefe kika ajiyeta, kinsan ko kaWan bana son ganinki cikin damuwa, domin damuwa tana sanya ciwo, shi yasa in dai ba makaranta zan je ba ko wani uzuri mai muhimmanci ba na son na yi nesa da ke dan kar ki ke yawan tunanin nan"Hafeez ya ce lokacin da yake zaunawa daga tsugunnon da ya yi.



"Hafeez kenan sau nawa kake so na faWa maka cewa nima ba a son raina nake tunanin nan ba, kuma ma bana sanin lokacin da nake yin tunanin sai dai na tsinci kaina a ciki, dan Allah kake min uzuri mana wannan tunanin ya zame min jiki koma in ce ya zame mini abokin rayuwa!" Cewar Ammi tana sanya hannu ta share ?wallar da ta kwaranyo mata yanzu.



"Ki yi ha?uri Ammi, nasan da haka tun da abin nan ba ke kaWai ke yi ba nima ina yi haka Abba ma sai dai naki ne ya fi yin tsauri, Allah ne kaWai ya san dalilin wannan yawan tunaninnda yake nema ya zame mana kamar gado kuma abin al'ajabin ma babu wanda cikin mu zai ce ga wani abu da yake tunawa a lokacin da yake tunanin, sai dai idan wani tunain ne da ban za ka yi kuma ka tuna abin da kake son tunawa har ma ka yanke hukunci ko sharar idan akan hakan ka yi tunanin..Amma shi wannan dogon tunanin fa da ya zama kamar ibada sji baka taSa gane inda ka dosa bare ka san inda ka je sai dai ka gama bulayinka, ya tafi ya barka da damuwa a ranka.Tunani ne da ya sha ban -ban da wanda kowane tunanin da mutum zai gane irinsa sai dai mu cigaba da addu'a akan Allah kawo mana mafita"


"Amin ya rabbi" Ammi ta ce tana bin Wan nata da kallon so da ?auna tabbas kowacce uwa idan ta samu Wa mai biyayya irin Hafeez to tabbas ta yi dace.



Ganin kallon da take masa ya sakar mata murmushi tare da mi?a hannu ya Wakko tuffa Win da ta ajiye ya mi?a mata, karSa ta yi cikin jin daWi itama tana sakin murmushin ta kai bakinta ta gutsura, haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallar magriba, sannan Hafeez Win ya tafi masallaci itama ta shiga domin yin alwala ta gabatar da sallar tana so ta damawa Abban Hafeez kunun gyaWar da ya ce ta dama masa zai sha idan ya dawo domin ya je gidan abokinsa kuma ta san a gida zai ci abincin dare domin baya iya cin abinci a ko'ina sai a gidansa.





Maman Afrah>?p?=?
?=??


d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?



NA


MMN AFRAH


FIRST CLASS WRITER'S ASSO...



PAGE 2?? &1?? 2?? 2??




_Ridallah_


Tun komawarsu garin Gumel rayuwarsu ta sauya, Mama Rahma kamar yadda Ridallah take kiranta, ita ta sanar wa shugaban Boarding pri & Junior scul da take aikin abinci, akan ya mata alfarma za ta kawo wacce za ta maye gurbinta, cikin ikon Allah kuea sai ya ce dama akwai wacce ta rasu ba' a maye gurbinta ba dan haka ta bashi lokaci zai yi ?o?ari ya bada sunan Baba Habiba idan Allah ya sa tana da rabo ta za ta samu haka suka masa godiya da ?o?arin da ya musu suka dawo gida cikin farinciki.


Bayan mako biyu kwa aka nemi Baba Habiba akan ta fara zuwa wurin aikin, duk da wasu masu aikin acan makarantar suke kwana amma Mama Rahma da yake tana da kula da aikinta tana zuwa akan lokaci ga kuma cika ?a'idoji hakan yasa idan ta gama aikinta take tafiya gida ta kwana.Ita ma Baba Habiba ta nemi wannan alfarma kima da darajarsu da shugaban makarantar ke gani ya basu dama suke zuwa suna tafiya tun da a cikin gari suke, wannan ya sa su ma suka bada himma da kuma ganin basu yi duk wani abu da zai ruguje duk wata yarda da kuma dama da aka basu ba.


Kullum idan su Baba Habiba suna kicin suna aiki sai Ridallah ta samu wuri ta zauna ta rin?a kallon Walibai idan suna tafiya ajijuwa, gwanin sha'awa kowa sanye da uniform da socks da sandal sai abin ya rin?a birgeta tana jin inama ita ce, dan tana da son karatu amma gashi sun baro garinsu, hakan ya sa Ya Hizbunta ya faWo mata yadda suke tafiya makaranta ya kama hannunta ya yi ta siya mata duk abin da take so.Amma yanzu gashi wasu sun shiga tsakaninsu da shi, sun sanya sun baro garinsu sun dawo wani garin da bata ma jin daWin garin saboda babu Ya Hizbu a cikin garin.


"Kasan me Ya Hizbu?"

"A'a sai kin faWa "

"Inaso in yi karatu mai zurfi idan na gama in samu aiki"


"Allah sarki Ridallah, insha Allahu sai kin yi karatu har ya isheki, ni nan zan tsaya tsayin daka har sai kin cimma burinki, sannan in Allah ya yarda za ki samu aiki"

"Nagode Yaya na" Ta ce tana murmushi, shi ma murmushin ya mata.

Maganar da suka yi ana gobe za su baro Hadejia ta faWo mata, hawaye ne suka zubo mata ta sanya hannu ta share tana jin kewar Ya Hizbunta har cikin ranta, ashe burinta ba zai cika ba.


"Ridallah! Baba Habiba ta kirata da ta fito domin shanya gawayi.Da sauri ta Wago kan nata ta kalki mahaifiyarta ta da ke kallonta cike da mamaki, duk da dama tun da suka dawo Gumel tana kamata tana kuka idan ta tambayeta sai ta ce Ya Hizbu ta tuno.To itama Babar tana mata uzuri tun da ta san irin sha?uwar da suka yi, yo kuma abu ne mai wahala ace ta yakice tunaninsa lokaci guda duk da ta san dai ba lallai ne ta manta da shi ba har abada amma dai ta san mawuyaci ne ace sun ?ara haWuwa ma, sai dai bata taSa ganin tana yin kuka a wajen da jama'a ke kai kawo ba, ko a gidan takan kamata ne a Waki ta Soye kan ta tana kuka.


Ajiye ?aramin buhun hannunta ta yi wanda ra zubo gawayin a ciki, ta ?arasa wurin da Ridallah ke zaune ta zauna akan dakalin ita ma, hannun Ridallah Win ta kama da hannayenta biyu ta ce


"Haba Ridallah, har sai yaushe ne zaki daina yin wannan kukan kina zubar da hawayenki? Bayan kinsan cewa Hizbullah mun baro shi a HaWejia sannan bai san ma inda muka taho ba, bare ya biyoki amma sai ki zauna ki yi ta zubar da hawaye, abun har ya kai kina kuka a inda mutane suke ficewa kuma za su iya ganinki? Dan Allah ki sanyawa ranki ha?uri da dangana duk da nasan da wuya hakan amma daurewa za ki yi ko nima na daina tunanin halin da kike ciki idan da rabon ganawa wata rana sai ki ga kun gana ke da shi" Baba Habiba ta kai ?arshen maganar cikin sanyin murya tana kallon Ridallah da hawayen suka cigaba da sirarowa daga idanunta.


"Hakane Baba, amma ni yanzu ba wannan ya sanya ni kuka ba"


"Menene?"


"Kawai saboda na ga...

"Baba Habiba waye ya taSa ?ar lelen naki na ga kina ta faman lallashi?" Maganar principal Win makarantar ta katse Ridallah daga abin da take so ta faWa.

"Wallahi shugaba ka ganni da ita nima ban kai ga jin wanda ya taSo ta ba"Baba ta ce cikin jin nauyin shugaban makarantar saboda mutum ne shi mai kirki da girmama mutane.

Wurin ya ?araso yana murmushi tare da cewa


"?ar lelan Baba wa ya taSa ki?"

Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta.


"Ba magana ake miki ba?" Baba Habiba ta faWa tana kallonta.


"Dama fa..."Sai kuma ta yi shiru.


"Dama me?" Ya ce cikin lallashi.


"Dama da na ga uara suna tafiya aji shi ne ni ma na ji inason karatu" Ta kai ?arshen maganar tana goge hawayen idanunta.


"Kai! Allah sarki Ridallah dama akan karatu ne kika shiga damuwa, ni ma da na yi tunanin cewa Babar taki a sanyaki a makarantar nan maimakon kike zaune, to kuma sai nake tunanin ko bata da ra'ayi, amma yanzu tun da har kina so babu abin fa zai hanaki shiga aji in har ta amince" Ya ce yana goya hannayensa a bayansa.


"Na amince shugaba, ai ni dama daga ni har ita ba mu da burin da ya wuce haka, saboda Ridallah yarinya ce mai matu?ar son karatu, gata da haza?a tun da take ko ta biyu bata taSa Wauka ba a makaranta kullum ita ce ke Wauka na farko a ajin su"


"Allah sarki! To insha Allah za a sanyata a J.s 1 Win idan an mata interview mun gani, Allah ji?an mahaifin nata" Principal Win ya ce yana mai jin tausayinsu, dan Rahma ce masa ta yi mijinta ne ya rasu ?an asalin Malam madori ne sanadin mutuwar tasa ce suka dawo Gumel Win da zama dan Baba ta hana ace daga HaWejia suka taho dan bata so kowa ya san daga inda suke saboda wani dalili nata daban wanda ita ce kaWai ta san hakan.


"To mun gode ?warai Allah sa ka fi haka, Allah Wauka ka, ka ya albarkaci zuri'a" Baba ta faWa cikin farinciki.


"Amin ya Allah nagode ni ma da addu'a, kuma babu komai ai yiwa kai ne, ni zan mata komai kama daga litattafai da komai da komai"



"Nagode Baba shugaba Allah saka maka da alkairi, ya sanyaka a aljanna" Ridallah da ta tsugunna har ?asa ta haWe hannayenta a wuri Waya ta ce cikin murna da farinciki.



"Ba komai ?a ta taso mu je" Ya ce yana kama hannunta suka tafi can office Winsa.



Baba Habiba kwa tsabar farinciki ma ta rasa bakin magana, haka ta tsaya tana kallonsu har suka Sacewa ganinta sannan ta Wauki buhunta ta kama hanyar kicin. Dan so take ta je ta baiwa Rahma labarin wannan abin arzi?i da aka musu.



Sosai Mama Rahma ta ji daWi da wannan albishir




Principal Win office Winsa ya wuce da ita ya yi mata register da komai da komai, sannan ya Wakko mata uniform set biyu daga cikin uniforms Win da gobnati take bayarwa a rabawa Walibai.Ridallah sosai daWi take ji a ranta baki ya?i rufuwa sai kallon uniform Win take yi tana murmushi sai faman godiya take yiwa shugaba shi kwa sai cewa yake ta daina godiya, wani Malami ya kirawo yasa ya mata interview sosai suka yi mamaki daga Malamin har principal Win saboda yadda take bada amsoshi a nutse ko gaga ba ta yi sun gamsu da amsoshinta sosai dan haka principal Win ya ce ta je ta sanya kayan makarantar ta dawo, haka ta je Wakin su Baba da ke can inda Wakunan ma'aikatan kicin yake, duk da su, su Babar basa kwana a makarantar amma dai akwai Wakin da suke hutawa, haka ta je ta sanya kayan tana ta murna ta linke wanda ta cire Win ta nufi kicin Win.


Da murna ta je ta rungume Baba ita ma Babar rungumeta ta yi cike da farinciki dan ji take kamar yau take sallah tana son farincikin Ridallah haka kuma ta tsani ba?inciki ko Sacin ranta.Kowa a wurin sai dariya yake musu ganin suna murna gwanin sha'awa.Haka ta ce musu ta tafi aji, office Win shugaban ta je ya kalleta yana murmushi ya ce


"Ridallah an zama ?an makarantar kwana"

Cike da kunya ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana murmushi dan duk daWi ya cikata ta ?osa ta ganta zaune cikin aji tana Waukan darasi.

"To ga wannan" Ya ce yana mi?o mata wata jaka mai Wauke da dukkan littattafan da ake amfani da su a ajin da za ta je sai biruka guda biyu da mathset da komai da za ta bu?ata har test buke duk a ciki.

Idanu ta Wan zaro dan ita tsabar ruWewa da kuma murna ta ma manta da wasu abu littattafai.

"Gaskia shugaba ko dai ni za a baiwa nima in shiga ajin"Malamin nan ya ce cikin zolaya yana murmushi.


"Nawa ne waWannan" Ta ce tana mi?a hannu cike da ladabi ta karSa, tare da buWawa ta le?a ganin abin da ke ciki sai farincikinta ya ?aru akan wanda take ciki da.

"Allah saka maka da alkairi, ya faranta maka kamar yadda ka faranta mini" Ta ce tana kallon Principal Win cike da girmamawa.

"Amin ya rabbi, shugaba da da Malamin suka hala baki wajen faWa.

"Mu je na raka ki ajin " Malamin ya ce yana yin gaba ta juya ta bi bayansa.

"Allah bada sa'a" Ta tsinkayo muryar Principal Win lokacin da ta kai bakin ?ofar fita.

"Amin" Ta ce tana sanya kai ta fita daga cikin office Win.

Principal Win komawa ya yi ya jingina da jikin kujerarsa yana jin wani irin daWi da nishaWi a ransa dan a rayuwarsa yana son ya ga ya taimaki mutane, musamman yara, yaran ma marayu yana son sanya farinciki a zuciyar maraya, kasancewarsa maraya ya san zafi da raWaWin maraici hakan yasa yake ta ?o?ari domin ganin ya cire su daga wani ?unci ko ba?inciki ya sanya su a farinciki.



_Hizbullah_


Zaune yake a Wakinsa yana ri?e da handout yana karatu, sai kofin shayi Wan ?arami da ke kan Wan ?aramin faranti, jifa-jifa yana Wauka yana kurSa ya maya ya ajiye, yana cikin karatun sai ya ji Ridallah ta faWo Sasa a rai da sauri ya ajiye handout Win kamar wanda aka tsikara ya dafe kansa da hannu biyu saboda jin da ya yi ya sara masa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Ya ce yana wani runtse idanunsa da ?arfi jin yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ?arfi tamkar wacce ke neman agajin gaggawa, kan nasa ya saka ya sanya hannun nasa a ?irjinsa saitin zuciyarsa ya dafe tabbas Ridallah ita ce bugun zuciyarsa amma yanzu bai ma san inda take ba bare ya san halin da take ciki ba. Da sauri ya mi?e kamar wanda aka tsikara ya nufi inda ya sanya wayarsa caji ya Wakko ta maimakon ya dawo ya zauna a kan kujerar sai ya tsaya a jikin bango tare da jingina bayansa da bangon, a hanzarce ya shiga contact ya nemo lambar wayar Ummarsa ya shiga buguwa amma har ta tsinke ba'a Wauka ba, bai yi wata-wata ba ya sake danna wani kiran a karo na biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login