Showing 36001 words to 39000 words out of 77516 words

Chapter 13 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

a kan kowacce mace bayan mahaifiyarsa a rayuwarsa, wanda ya ?udurta zamar miki bango abin jingina a rayuwarki, wanda zai ri?e miki maraicinki ya kyautata miki ya zamar da ke sarauniya har iya ?arshen numfashin da Allah ya Waukar masa, mai yasa Ridallah, mai yasa zaki min haka, mai yasa bakya tausayin mai ?aunarki da gaskiya!!! " Yana kaiwa ?arshen maganar ya dur?ushe a wurin yana sakin wani kuka mai tsuma zuciya, dan gabaWaya sai yau ya ?ara sanin ba zai iya rayuwa in ba Ridallah, ha?i?a ?aunar gaskiya wata aba ce mai wuyar ?an?aruwa daga zuciya sai dai kullum take ?aruwa tana hauhawa a zukatan masu yin ?auna dan Allah ba masu yin soyayyar yaudara ba soyayyar da babu komai sai sha'awa da tarin yaudara.


(TSOKACI ki nutsu da kyau ki gane mai ?aunarki da gaskiya, wanda ke son ki da aure ba waWannan samarin ba wanda babu komai a ransu sai yaudara ba komai yake so ba sai jikinki bashi da buri kullum sai yadda zai yi amfani da kalamai da kuma kaifin harshe wajen jan hankalinki ki mallaka masa kan ki da zarar kuma ya samu abin da yake so da ke da bola duk Waya.Mutuncinki shi ne ribarki shi ne ribar iyayenki kada soyayyar shan minti tasa ki siyar da darajarki ta ?a mace darajar iyayenki da ta ahalinki bakiWaya.Bayan nan darajarki ita ce mutuncinki da ta ?a?anki domin kema uwa ce wata rana ki zama wacce ?a?anki za su yi alfahri da ke a matsayin uwa domin duk abin da kika yi ?a?an nan naki fa zasuyi kin ga kin jefa rayuwarsu a matsala, saurayin da zai ke taSa miki jikin ki wallahi wallahi ba mai ?aunarki bane! Allah tsaremu daga azzalumai).



Tausayin Hizbullah ne ya shiga zucouar Abulkairi ji yake ina ma yana da iko da ya cikawa Hizbullah burinsa ko dan kasancewarsa mutumin kirki amma tabbas rangwame irin na raWaWin soyayya sai wanda ake yin soyayar domin shi, shi ne zai iya faWawa masoyin kalamai wanda za su tausasa zuciyarsa, ha?i?a wannan aikin Ridallah ne sai dai shi ya masa addu'a akan Allah warware wannan ?ullin da ya sake tunkaro rayuwar Hizbullah.A hankali ya ?arasa kusa da shi hannu ya sanya ya dafa kafaWarsa ya Wan ran?wafo ta gefensa ya ce




"Haba Hizbullah ka zama namiji mana"



"Wane namiji kuma kasan zafin so kwa Abulkairi? Kasan yadda nake ji kwa yanzu, kasan halin da zan cigaba da kasancewa yanzu da na yi tozali da wacce soyayayarta ta rayu a cikim zuciyata tun ALA?AR YARINTA, soyayyarta ta girma a raina ina bege da muradinta, duk da bana ganinta amma hakan bai rage ko kaWan na daga soyayyar da nake mata ba, ka sanya kan ka a matsayin ni yau gashi na gan ta amma ta nuna bata ma sanni ba har tana iya Waga hannu za ta mareni, Ridallah nutsatstsiyar yarinya kamila wacce tun tana ?arama nake rainonta da Wabi'u masu kyau amma yau na ganta a wani yanayin marar kyan gani ko wannna kaWai ya isa tashin hankali a gareni"

" Na sani Hizbu, na sani bu ne mai ciwo abu ne mai girma amma ha?uri da dangana shi ne babbar mafita...


" Ha?uri da dangana su kaWai ba zan samu sau?in a zuciyata ba sai dai addu'a kaWai ce za ta sanya na samu salama" Ya katse Abulkairi ta hanyar yin maganar cikin ?araji tare da fashewa da kuka mai ciwo.

Zagayowa gabansa Abulkairi ya yi gaban Hizbu shi ma ya zauna a ?asan, tare da zuba masa idanu shi ma a take nasa idanun suka ciko da hawaye tausayin abokin nasa ya tsarga masa a cikin ?o?on zuciyarsa ji yake ina ma bai ri?eshi ya hanashi tahowa wajensu ba, dama ya barshi ya cim musu da duk hakan bai faru ba duk da yana ganin da ya barshi ya tarar da su Allah kaWai ya san abin da zai faru, dan ba ya so Hizbun ya je ya yi abin da zai taSa masa karatunsa.


Zabura Hizbu ya yi, ya mi?e tsaye shi ma Abulkairin

mi?ewa ya yi ya sha gabansa da ya ga yana ?o?arin bin wata hanya da ban


"Wai ina za ka je ne?"

"Taxi zan samu na tafi gida, so nake kawai na jini a kwance jj nake ?afafuna ba za su iya Waukana ba saboda halin da zuciyata ke ciki, idan aka jima ma zan iya faWuwa ka rabu da ni dan Allah'


" Wane irin gida kuma Hizbullah mu da za mu koma scul, ka san fa ba mu gama da scul Win ba yunwar da kake ji yasa muka baro makaranta saboda ka ce ba ka son siyan abincin restuarant makarantar ba sai dai mu zagayo wannan Restuarant Win ka ga ganin babu nisa da scul Win muka zagayo kuma maimakon mu koma sai ka ce gida za ka tafi?"


" Ka bar maganar scul Win nan kawai"

Shiru ya yi yana nazarin halin da abokin masa ke ciki tabbas ko shi ya fahimci ko da sun koma scul Win Hizbu babu abin da zai iya taSukawa, hakan ya sa ya tare musu taxi suka shiga dan shi ma ba ya jin zai iya barinsa a halin da yake ciki ya tafi gidan shi kaWai gwara dai ya kasance a kusa dashi ko zai samu sassaucin a cikin zuciyarsa kuma idan yana kusa da shi Win zai rage zurfin tunani a maimakon idan shi kaWai ne tunanin zai yi yawa sosai.


Suna zuwa gidan ya hau sama da sauri ya buWe Wakinsa ya shiga ya rufo ?ofar ya sanya mukulli, dan haka Abulkairi na hawo wa saman ya murWa ya ji ?ofar a kulle cikin sanyin jiki ya koma ya buWe nashi Wakin ga shige, sai a lokacin ma ya tuno sun bar handout Win a Restuarant Win kai kawai ya kaWa ya shiga yin wasu hidimomin.



Hizbullah kwa na shiga ya wuce ya Wakko Wankunnen da flower da Ridallah ta bashi ya shiga kallon su yana maganganu shi kaWai dan shi duk gani yake kamar ya rasa Ridallah dan shi duk tunaninsa Ridallah ce Iftihal Win.




MMN AFRAH=?
?>?p?=??


d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?


Page 4?? 0?? &4?? 1??


*IFTIHAL*


Suna fitowa ita da Alhajin daga Restuarant Win ta ja ta tsaya, shi kuma ganin tana wani shan ?amshi tana haWr rai sai duk ya ji ba daWi, amma hakan bai sanya ya ji kp da haushinta ba shi dai kawai so yake bu?atarsa ta biya.


"Kinsan fa wani abokina da ke zaune a nan ne ya sanya direbansa ya kawoni yanzu kuma sai dai mu shiga taxi mu je Hotel Win in kama mana Wakin da za mu huta ko baby?" Ya faWi hakan yana wani murmushi tare da washe ha?ora sai wani lasar baki yake kamar wani tsohon maye.?asa ta yi da glases Win nata ta masa kallon up nd down ta sauke idanunta a kan ?aton tumbinsa tari guda kamar mai cikin wata tara, Wauke kai ta yi gefe tare da maida glases Win nata yadda yake ta Wago wayarta ta duba time.


"No kar ma ki yi la'akari da wannan cuki ba wai tsufa bane ya sanya y yi girma hakan tsabar cin daWi ne da kwanciyar hankali kinsan idan akwai kuWi to mutum bashi da matsala sai wacce ba a rasa ba"


"Ok ni ai ka san daga gidan talauci na fito"


"Ba haka nake nufi ba baby, inaso na sanar da ke yau idan ki ka tashi tafiya za ki tafi da ma?udan kuWaWe wanda kowa sai ya san kin yi tarayya da wanda ke matashin kai da kuWi" Ya faWa yana washe baki.


Jin ba ta ce komai ba ya sanya ya ?ara cewa


"Mu je ko muna Sata lokaci" Dan shi gabaWaya wannan shan ?amshin da take burgeshi take yi sabod yana son ya ga mace mai aji ya fi son hakan dan an fi daidaitawa da shi.


Ita ta fara yin gaba, ganin ta nufi wajen wata mota da ke fake a wurin ya gane cewa da mota ta zo, hakan ya ?ara tabbatar masa da babban yarinya ce saboda har mota gareta ta kan ta.Suna isa ta sanya mukullin ta buWe ta shiga wurin direba ta zauna sai dai ?afafunta a waje suke, jakarta ta jefa kan Waya sit Win mai zaman banza, shi kuma cikin sauri ya nufi Sangaren mai zaman banzan zai buWe ya shiga sai washe ha?ora yake kamar gonar auduga.


Iftihal na ganin ya gewayo ta maida ?afafunta cikin motar ta rufe ?ofar, gabaWaya ta kulle motar Alhajin na kama ?ofar zai buWe ya ji ta a kulle, ?wan?wasawa ya yi amma maimakon ta buWe sai ta sauke glass Win ta sanya hannu ta yi ?asa da glases Win fuskarta ta masa wani kallon ?as?anci ta ce



"Malam ka bar min jikin mota tun kafin in tasheta in yi gaba in kuma yi reverse in kwasheka kuma na kwashe banza wallahi"


"Haba baby wace irin magana kike haka? Idan ma wasa kike ki bari kar kisa ruwana ya hau, dan na gama Wora rai a kan ki wallahi"


"Za ka ga wasa da zarar na take ka, kuma sai dai hawan jininka ya tashi ba wai hawan ruwa ba"

"Dan Allah ki buWe in shigo mu tafi...



"Kai na fasa zuwa ko ina da kai" Ta katse shi.


"A haba dai haba baby ya zaki min haka"


"Bani da lokacinka" Tana gama faWar hakan ta Waga glass Win motar, ta mata key, Alhajin kuwa ya daddafe motar har sai da ya ji ta fara tafiya, ya ja baya ganin ta fisgeta da sauri ya tare taxi ya bi ya ce mai taxi Win ya bi bayan motar, tun suna bin bayansu har suka nemi inda motar ta yi suja rasa aikuwa Alhajin kamar ya cinye direban taxi Win sai masifa yake masa da turanci dan ba jin hausa yake ba daga chinanci sai ko turanci.Shi dai ha?uri yake bashi yana faWa masa cinkoson motoci ne ya sanya motar ta Sace masa, haka dai ya kaishi wani hotel ya yiwa wata waya dan ya rage zafi da ita saboda Wora rai Allah sa mu fi ?arfin zukatanmu.


Iftihal kwa da ta lura da bin da su Alhajin ke mata dan dama tana ganinsa ta mudubi lokacin da ya tsare taxi Win, a haka ta yi ta yaudararsu har ta yanke ta wata hanya inda ta Sacewa ganinsu.Gida ta nufa tana jin zuciyarta ba daWi, tana yin parking ta nufi Wakinsu ta shiga ta samu Amal zaune tana a kan gado tana waya jefa jakarta ta yi a kan gadon ta cire kayan jikinta ta Wakko wata yaloluwar riga iyakar ?waurinta ta sanya ta kwanta rubda ciki ta jin ranta na mata wani zafi wanda ta kasa gane dalilin hakan dan ta rasa mai ke damunta, dan ita yau Waya kawai ji take duk ta tsani rayuwar da take yi, tun da ta gane saurayin da ta haWu da shi a restuarant ya gane ta masa kama da wata a fuska amma ba a halayya ba kenan ita halayyarta marar kyau ce? Kenan ita ba dan kama da take masa da wata ba a fuska da bata da wani kyan hali da har zai sa a tunkareta, tabbas ta ji a yau tana sha'awar a ce ita ma wani zai iya yin abin da ta ga saurayin nan na yi a kan wata wato soyayyar gaskiya lallai hali mai kyau shi ne jigo a rayuwa shi kima da kuma martaba, amma ita mai ya sa babu wata hanya da aka nuna mata mai Sullewa? Sai dai gurSatacciyar hanya kuma matar da ita ce mahaifiyarta ita ya dace ta sanyata a hanya madaidaiciya amma kuma sai aka samu saSanin hakan, shin ina mafita a ina amsar tambayarta take mai yasa Aunty ta zaSa mata wannan rayuwar akan ta sanyata a hanyar da za ta zama abar kwatance kuma abar sha'awa ga ko???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?wa da kowa?


Wasu hawaye ne suka shiga zubo mata, bayan hannunta ta sanya ta goge shin mai yasa bata taSa jin ?yamatar halayyarta ba sai yau Win nan? Mai yasa bata taSa jin abin da take aikatawa ba dai dai bane sai yau Win nan tabbas an sanyata a a hanyar marar Sullewa.Tana a haka har aka fara kiran sallar magriba.

Wayarta ce da ke cikin jakarta ta shiga ringing amma har kiran ya katse bata Wauka ba, Amal da ta kwanta bayan ta gama wayar da take ta juya mata baya tana chart ta ce



"Wai malama bakya jin wayarki ta cikawa mutane kunne in ba za ki Wauka ba ya kaSata ki kashe dan ni ?aran ya gundureni"


Shiru ta mata bata tanka mata ba, mamaki ne ya cika Amal jin Iftihal Win bata ce komai dan ta san dai Iftihal ba ta taSa barin ta kwana kana faWa mata mafana za ta baka amsa dai dai da kai, amma kuma abin mamaki yanzu ta shareta.Juyowa ta yi dan ta tabbatar idonta biyu ko kuma bacci take, amma kuma mamakinta bai ?aru ba sai da ta ga idanunta biyu buWe.


A dai dai nan wayar ta sake wanj wani ?aran da alama wani kiran ne ya shigo bayan na farkon ya katse.



"Iftihal ni kam ko dai baki da lafiya ne?" Amal ta jefa mata tambayar tana tsareta da ido dan ita bata ma lura da hawayen da ke ?ara kwaranyowa daga idanuna Iftihal Win ba.Baki ta taSe ta juya ta yi kwanciyarta, ita kuma Iftihal Win jin ba a da niyyar daina kiran wayarta ta ne ya sanya ta tashi zaune dan kiran na katsewa wani ke shigowa kuma ta san babu mai mata wannan kiran a kai- a kai sai Auntyn ta dan samarinta da abokan hulWarta kowa ya sani ba ta son damu dan in ka dameta da kira ma tana iya yanke ala?a da kai saboda ita ?a'idarta ce idan har ka mata kira Waya biyu ka ga bata Wauka ba to ka bari idan ta ga dama za ta bi kiran.


Cikin sanyin jiki ta tashi ta buWe jakarta ta Wakko wayar, tana shirin danna ok kiran ya katse sai ga wani koran ya shigo a take, kamar yadda tunanin nata ya bata kuwa Aunty ce tana kallon sunan sai da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata.?aukan kiran ta yi ta kai wayar kunnenta amma ba ta ce komai ba.




"Iftihal haba ina kika shiga tun Wazu sai kiranki nake amma shiru babu amsa, shi ma Alhajin na masa kira ya fi goma amma bai Wauka ba daga ?arshe ma wayar aka kashe, ko har yanzu baku baro Hotel Win bane kuna hutawa?"

Wani takaici ne ya rufe gabaWaya zuciyar Iftihal jin wai mahaifiyarta ce ke mata tambaya a kan cewa har yanzu tana Hotel tana hutawa tare da dadironta, shin mai yasa bata taSa jin zafin tambayar nan ba sai tau tun da ba yau ne ta fara mata makamanciyar tambayar nan ba? Shin ita wace irin mahaifiya gareta shin anya kuwa Aunty ta cancanta ta zama uwa, duk da an ce mahaifiyarka ko mahaukaciya ce uwa ce a gareka amma maj yasa ita tata mahaifiyar na da hankali amma ba na tunani ba tun da duk wata uwa ta gari ba za ta so ta ga rayuwar ?arta ta lalace ba, lallai kowacce uwa mahaifiya ce amma ba kowa ce mahaifiya ba ce ke zama uwa ta gari ga ?a?anta.


"Wai Iftihal ya kika yi shiru ina ta sauraren ki fara min bayanin yawan kuWaWen da kika cafko mana a wurin Alhajin Allah, amma sai in ji kin yi shiru" Aunty ta katse mata tunanin.


"Ni fa ba ma tare da shi" Ta bata amsa a ta?aice.


"Allah sarki my Ifti ki ce har kin koma gida wato kun rabu da shi kowa ya kama gabansa, yo ai dama tun da kowa ya samu abin da yake so sai a raba garun, shi ya samu biyan bu?atarsa ke kuma kin samo mana kuWi, wato kasuwa ta watse Wan koli ya ci riba" Ta ?arasa faWa rana wata dariya.


"Ni fa Aunty ba mu aiwatar da wani abu ba, dan ni ko Hotel Win ban je ba kawai dai na fasa yi...


"Ke! Dakata dallah ya ina miki magana kina sako min wani zancen banza da wofi" Auntyn ta katseta cikin ?araji.

Shiru Iftihal Win ta yi ba ta ce komai ba.


"Wato duk yadda na shirya wannan haWuwar taku sai da kika yi yadda kika yi kika ruguzata, wato duk irin yadda na so mu samu abin arzi?i mai tarin yawa sai da kika yi fatali da damar da kika samu, shin kin san waye wannan mutumin kin san irin tarin dukiyar da yake da ita, shin wai ma wace mai hure kunne kika haWu ta hure miki kunne dan tana ba?inciki ko kuwa Amal Win ce ta hanaki dan tana ganin bata da irin waWannan Alhzan?" Saurin juyawa ta yi ta kalli Amal da ke danne- danne a wayarta ba ta ma san me ake yi ba.


"Ni fa babu wanda ya hanani ni ce kawai na ga hanyar ba ta da ?ofar da za a bi a Sulle shi yasa na fasa ...


"Shin yau shaye-shaye kika yi Iftihal?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login