Showing 57001 words to 60000 words out of 77516 words

Chapter 20 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?


Page 5?? 8?? &5?? 9??



_IFTIHAL_


Mummy na fita a Wakin Iftihal ta koma ta zauna a bakin gado tana jin wani takaici na ziyatar zuciyarta ji take tamkar ta fitar da su daga cikin zuciyarta ji take ina ma Aunty ba ita ce ta haifeta ba da tabbas abin ya zo mata da sau?i, saboda ji take tamkar zuciyarta za ta buga saboda tsananin zadi da ciwo a ce mahaifiyarka ce sanadin lalacewar rayuwarka ita ce ummul aba'isin jefa rayuwarka wata hanya marar kyau tabbas wannan ba ?aramin abin ba?inciki bane kuma mugun tabo ne wana zai zauna har abada a zuciyarka zaman da ba zai taSa ?an?aruwa ba!


Tana rayawa a ranta cewa inama a ce kishiyar mahaifiyarta ce ta mata hakan da hajan ba zai dameta sosai ba domin ta san kishin wasu matan babu abin da ba ya sanya su duk da ita kishiyar mahaifiyarta ta lura tana da kyan hali da na zuciyar. Ita dai Amal tana gefe nan inda zaune ita Win ma duk abin duniya ya isheta lallai shirya ta Allah ce gashi dai a baya ko hasashen daina rayuwar da aka sanyasu a ciki basu taSa yi ba amma kuma gashi rana Waya kuma lokaci guda sun ji komai yana neman ya zama tarihi a rai da zuciyarsu tabbas shiriya ce Allah ya kawo musu ba tare da sun sanya cewa za su daina a kwana kusa ba.?aran buWe get da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? aka yi da kuma jin dirin motar Daddy shi ne ya sanya Iftihal mi?ewa tsaye daga zaunen da take, itama Amal tsayen ta mi?e tana mai ?arasowa inda Iftihal Win take ta dafa kafaWarta ta ce.



"Yanzu idan mun tunkari Daddy da wannan maganar me kike so mu faWa masa? Shin bakya tsoron wani abu ya faru?" Amal ta tambayeta tana kallonta da jajayen idanunta.



"Amal ya kamata mu tunkari matsalarmu kai tsaye ba tare da tsoro ko fargabar faruwar wani abu ba, ko ma mai zai faru sai dai ya faru amma a yau Win nan sai Daddy ya san duk abin da ke faruwa"



"To shikenan Allah taimakemu kar su ?ulla mana wata ma?ar?ashiyar da makirci kin san girma da hankali da kuma tunaninmu ba Waya bane da nasu"


"Allah ya fisu sannan kuma Allah bai barin zalumci babu abin da ya gagareshi" Iftihal Win ta faWi hakan tana sanya hannu ta share hawayeta tana jin ?arfin gwiwarta na ?aruwa tun da ta ambaci Allah ta san kuma lallai zai shige mata gaba.Cikin sauri ta fito daga Wakin Amal ta take mata baya, lokacin Daddyn har ya nufi part Winsa dan haka can suka nufa cikin sauri kamar ana tura su dan so suke kawai su aiwatar da ?udirinsu tun kafin shaiWan da shaiWanin mutane su ci galaba a kan su duk da suna ganin hakan ba abu bane mai yiwuwa.



A lokacin kuma ita Mummy tana can tana ta faman kiran wayar Hajiya Suwaida bayan ta yi ta kira ba a Wauka ba dan lokacin ita ma tana cikin tsaka mai wuya dan mai gidan ta ya jefawa mai gadinsu tambaya dan haka hankalinta tashe yake domin matsawar mai ya gadin ya faWi gaskiya to kuwa tata ta ?are.Bayan ta gaji da kiran wayar Hajiya Suwaida sai ta koma kiran wayar Hajiya Hauwa lokacin itama ta bar wayar a ?asa tana caji ta hau sama sai Safiya a falon tana jinnwayar na ?ara da ta le?a ta ga mai kiran ta taSe baki dan bata jin za ta iya Waukan wayar ta kaiwa Aunty dan yanzu duk haushinsu take ji dan haka tana jin kiran na ta shigowa ba ?a??autawa amma ta murWe kunneta ta cigaba da uzurin gabanta.Haka Mummy ta yi ta kiransu hankali a tashe domin su san abin yi amma babu wanda ta samu ya Waga wayar dan haka ta zauna daSas tana jin mummunar faWuwar gaba dan yadda ta ga idon yarinyar nan Iftihal wi?i-wi?i bata tunaninnakwai wani abu da zai taka mata birki wajen aiwatar da abin da ta yi niyya duk da dai tana tunanin kamar ba za ta iya aiwatarwar ba, tabbas tana ji a jikinta kamar dai dubunta ta kusa cika amma kwa in hakane tana cikin Suguwar matsala.


Su Iftihal na zuwa part Win Daddy Iftihal Win ta yi nocking sai da ya basu izini sannan suka tura ?ofar suka shiga, tsaye yake a tsakiyar falon nasa ri?e da gorar ruwan da ya Wakko a frige zai sha saboda ?ishirwa da yake ji dan yau daga wurin aiki wani uzuri ya wuce sai da ya yi sallah ma sannan ya taho gidan.



"Ku ne a tare haka kuka zo ganina daga dawowata kai abin birgewa" Ya faWa cikin zolaya dan Daddy akwai sakin fuska ga yaransa da ma mutane baki Waya.


Da gudu-gudu suka ?araso wurinsa suka rungumeshi tare da sakin kuka mai cin rai, hannayensa ya sanya yake Wan bubbuga musu bayansu cikin tashin hankali yake tambayar yaran nasa dalilin damuwarsu, dan yana matu?ar ji da tilon ?arsa Amal bare kuma ?ar amininsa Iftihal gabaWaya ba ya son damuwarsu yana matu?ar son ya basu kulawa duk da kasancewarsa ba mazaunin gida ba ko yaushe yana wurin aiki.

"Daddy sun lalata mana rayuwa sun cucemu cutar da ba lallai mu yafe musu ba" Amal ta faWa cikin kuka.


"Subhanallah! Mai ya faru shin su waye kuma mai suka muku?" Ya tambaya cikin tashin hankali dan ya lura ko ma mai aka musu to tabbas ya taSa musu zuciya tun da har suka tunkareshi da maganar kuma har suna zubar da hawaye to tabbas ba ?aramin abu bane.


"Iyayenmu Daddy" Iftihal ta faWa tana fashewa da kuka dan jin maganar take tana huda mata tsakiyar zuciya idan ta tuna har da sa hannun Aunty a lamarin ko ma ta ce ita ce babban sila matakin farko a faruwar hakan.


Da sauri Daddy ya janyesu daga jikinsa ya kaisu kan kujera ya zaunar da su har lokacin kuka suke kukan da yake taSa masa zuciya.


"Mai kuke son faWa ne? Mai suka muku da har ya sanyaku zubar hawaye?" Ya tamnaya yana binsu da kallo dan tunaninsa bai taSa bashi abin da suke son faWa ba ya dai fi tunanin ko wani abu da ban ne saSanin wanda za su faWa.


GabaWayanmu mun taso cikin gurSacewar tarbiyar wanda duk wanda suka yi sanadin hakan su ne wanWanda suka cancanta su kula da tarbiyarmu amma kuma sai aka samu saSanin hakan sun maidamu hajar da suke siyarwa su samu kuWi...tiryan tiryan ta kwashe komai ta faWa masa.


"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, subhanallahi, hasbunallahu wa ni'imal wakil" Cewar Daddy da ya zaune a ?asa a inda yake, yare da dafe kai jin kan nasa har wani jujjuya masa yake. Tsit falon ya yi sai sheshshekar kukansu , sai da Daddy ta ji kan nasa ya tsagaita masa sannan ya mi?e cikin zafin nama yana jin wani ?unci da raWaWi a zuciyarsa saboda tsananin damuwa da Sacin rai da suka yuwa zuciyarsa dirar mikiya, jin iriyar rayuwar da aka ginawa yaran, duk da ma dai Iftihal Win a hakan ta zo gidannnasa ya godewa Allah da ba a nan ta fara lalalcewa ba da bai san da wane ido zai kalli mahaifinta ba, amma Amal da take a tare da shi tun farko ammya aka yi bai taSa sanin halin da take ciki ba hakan ma har da laifin shugabannin makarantar da basu taSa sanar da shi cewar bata zuwa makaranta ba duk da ya fi Wora laifin a kan matarsa.


A hanzarce ya tashi ya buWe ?ofar ya fito, su ma yaran baya suka mara masa, bai zame ko ina ba sai Sangaren Hajiya Wasila, tana nan zaune ta yi tagumi da hannu biyu ta rasa ma wane irin tunani za ta yi, da ta kama wannan sai ta saka ta kama wancan, cikin zafin nama Daddy ya sanya hannu ya murWe handle Win ?ofar amma a maimakon ya tura da hannu sai ya sanya ?afa ya hangaza ?ofar har sai da ta bugu da bango ji kake gagaf, ?aran ne ya dawo da Mummy daga tunanin da take yi cikin tsoro da fargabar ganin Daddyn a wani yanayi ya sanya ta tashi tsaye a kiWime ganin wani yanayi da Daddy ke ciki na Sacin rai da bata taSa ganinsa a ciki ba, karkarwa jikinta ya fara yi tun kafin ma ya ?araso inda take, cikin Sacin rai ya nufeta kamar wani kumurcin maciji tamkar zai tashi sama haka ya taho, a take Mummy ta fara ganin Daddyn ya fara rabuwa bibbiyu uku-uku a take ta tsure nan take wasu hawaye da bata san da zamansu ba ta ji suna wanke mata fuska, dan zuwa lokacin ta gama fahimtar cewa ya ji komai yaran sun sanar da shi halin da ake ciki musamman ganinsu da ta yi biye da shi suna share hawaye kamar wanda aka gama yin jana'izar iyayensu yanzu.


Daddy na zuwa gabanta bai yi wata-wata ba ya sanya hannu ya Wauketa da wasu zafafan maruka har guda uku hakan ya yi sanadiyyar Waukewar jinta da ganinta na wucewar gadi, tun kafin ya fara magana ta dur?ushe a wurin ta kama ?afafunsa domin bashi ha?uri, cikin Sacin rai ya janye ?afafunsa yana janyewa ta yi ?o?arin maida hannayen nata kan ?afafun nasa aikuwa hakan ya ?ara tabbatar masa da maganar yaran duk da dama gabaWaya kalamansu basumasa kama da ?arya ba amma dai a ?alla ya yi tunanin za ta Wan musa ko ya Wan samu sassauci ashe dai maganar ta tabbata gaskia ce.?afar dama ya Waga ya sanya ya hamSareta sai da ta faWi wanwar sannan ta yi saurim tashi daga kwanciyar dan gudun kar ya taka mata ruwan cikinta dan yadda yake ganin yanayinsa yana kan dokin zuciya ne komai ma zai iya aikatawa dan da alama ma baya cikin nutsuwa da hayyacinsa.



"Ka yi ha?uri dan Allah ka yafe mini sharrin shiWan ne?" Ta faWa tana dur?usawa a kan gwiwoyinta tare da haWe hannayenta waje Waya alamar ro?o.



"Ashe baki da hankali, har kina tunanin bani ha?uri har kina neman in yafe miki to inaso ki sani ko da ace laifin da kika mini shi kaWaine zunubin da ya rage miki ranar lahira sai na yafe miki zaki shiga aljanna to wallahi ba zan taSa yafe miki ba kin cuceni kin kassarawa ?ata rayuwa bayan Wauki amanarta n dam?a a hannunki sannan ?ar aminina da yake ganin ya yarda dani ya Wakko ?arsa ya bani amana dan ta yi karatu saboda t rs damar yin hakan a hannun mahaifiyarta ashe gabaWaya bakinku Waya kuka taru kuka lalata musu rayuwa" Daddy ya ce cikin Waga murya yake magana dan jijiyoyin wuyansa har fitowa suka yi raWo-raWo.



Kuka Mummy ke yi kamar ranta zai fita ta rasa ma da wane kalamai za ta yi amfani wajen shawo kan Daddy tabbas gaskiayar bahaushe da ya ce ranar wanka ba a Soyon cibiya, lallai duk wani abu da aka ginashi a kan rashin tsoron Allah ha?i?a akwai ranar tonon asiri.Su ma yaran sai kuka suke ganin yadda Daddy duk ya fita hayyacinsa suna fatan kar wani ciwon ya sameshi sanadin Sacin ran nan, juyowa ya yi cikin sanyin jiki yana jin kamar ya dashe da kuka ya ?araso wajen yaran ya kama hannayensu suka baro Wakin Mummy, Wakinsu ya kaisu ya zauna ya lallashe su da nuna musu su Wauki hakan a matsayin ?addararsu, sannan ya faWa musu cewar zai je ya siyo musu ticket dan dole su kasance a Nigeri'a haka ya baro su ya fito tare da rufe musu ?ofar, Wakin Mummy ya koma ya tsaya daga bakin ?ofa ya ce


"Zan fita idan wani abu ya samu yarana wallahi! Sai na Waureki har igiya ta yi saura"Yana gama faWar hakan ya juya ya fito ya barta yadda ya sameta tana ta kuka kamar ranta zai fita, part Winsa ya koma ya Wakko mukullin motar, dan so yake a yau sai ya je ya musu jirgin zuwa Nigeri'a.Yana fitowa ya iske wasu samari da mai gadinsa suna ta sa'insa suna so su shiga cikin gidan shi kuma ya hanasu shigowa ya tsaya ya ri?e ?ofar.Tambaya ya yi sai mai gadin ke masa bayanin wai wata suke nema mai suna Ridallah kuma ya sanar da su babu mai sunan hakan a gidan amma sun dage cewa a nan gidan take dan an tabbatar musu nan ne gidan.Daddy na jin hakan ya gane su waye dan a cikin labarin da Iftihal ta faWa masa akwai labarin wasu samari da suka haWu yau kuma ta sanar da shi Wayan na kiranta da suna Ridallah, sannan kuma ya ga samarin ma da ganinsu sun masa kama da ?an Nigeri'a saboda haske tar kamar rana dan haka ya cewa mai gadin ya koma wajen zamansa shi kuma ya tambayesu wanda suke wanda suke nema aikuwa basu Soye masa komai ba sai ya ji labarin dai dai da wanda Iftihal Win ta bashi dan haka ya gane su ne.



"Tabbas wacce kuke nufi a gidan nan take duk da ba ita ce asalin wacce kuke nufin ba, amma ya aka yi kuka gane gidan nan?"


Abulkairi ne ya fara bashi labari tun daga Satan Ridallah, zuwa yau da suka haWu d ita ta ce ba ita bace da yadda abokinsa ya koma wajen bai sameta ba da yadda ya fara masa gaba dan ya hanashi ya bisu a Restuarant Win, da kuma yadda ya Wauki al?awarin nemo masa gidan su yarinyar a yau dan ya wanke kansa in yaso koma mai zai faru ya faru, hakan ya sa bayan Hizbu ya rufe ?ofar Wakinsa shi kuma ya fito ya koma Restuarant Win dan a lokacin da suka taho za su fito daga Restuarant Win daga can cikin wajen sha?atawar ya ji wani ma'aikacin wurin cin abinci mai sanye da uniform Win aikin wurin yana cewa

"A zaku biya kuWi fa na faWa muku har gidansu, dan yarinyar oga ma ce har wurinta yana aikena" To da yake lokacin hankalinsa a kan Hizbu yake sai bai kawo komai ba sai daga baya da ya nutsu wannan maganar ta faWo masa a lokacin da yake cike da neman mafita hakan ya sanya ya yi ta bugawa Hizbu ?ofa har sai da ya gaji ya buWe sannan ya masa wannan bayanin aikuwa a take Hizbu ya yarda suka fito suka ?ara komawa Restuarant Win suka baiwa matashin kuWi masu yawa ya kwatanta musu wajen dan har hotunanta ya nuna musu a wayar ogansa da ya Wakko wayar a Soye hakan ya tabbatar musu da gaske yake dan haka suka kamo hanya suka zo dan har no gidan ya basu.



Bayan Daddy ya saurari bayaninsu, haka ya shigar da su cikin gidan ya bayan sun zauna a babban falon sai ya kira su Iftihal Win ya gabatar da su ita dama Iftihal Win tana ganinsu ta shaidasu su ma sun yi mamaki ganin bata nuna komai ba, nan Daddy ya musu bayani cewa Ifthal Win ba ita ce Ridallah Win da suke nema ba saboda ya basu gabaWaya tarihinta har da hotunanta ya nuna musu wanda suka yi da iyayenta wani tana jaririya da wanda tana ?arama hakan ya sa suka yarda sai dai sun yi matu?ar mamaki musamman Hizbu nan dai Daddy ya ro?i za su je Nigeri'a da su dan akwai abin da yake son yi amma bai faWa musu ba sai dai a hasashensa na mai dogon nazari ya fara zargin Hajiya Hauwa a kan Iftihal musamman kuma da su Hizbu suka nuna cewa tabbas Iftihal Win na kama da wata sak hakan ya sanya yake so su je har da su domin yana son gano wani abu.


A washe gari Daddy ya gama musu komai da komai na biza, Daddyn Iftihal, Amal Mummy, Hizbu da kuma Abulkairi dan direct ma a Abuja za su sauka.Washe garin ranar kwa jirginsu ua Waga zuwa Nigeri'a suna ta hira abinsu Hizbu ji yake kamar da Ridallah yake tare Mummy sai tsiltsilla ido take dan ido ya raina fata.?arfe shida na yamma jirginsu ya sauka a garin Abuja waya Daddy ya yiwa wani abokinsa ya aiko masa direbobi da motaci biyu suka Waukesu, gidan su Iftihal suka nufa...


MMN AFRAH=?
?=??>?p?





d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?



Page 6?? 0?? &6?? 1??



Wajen ?arfe huWu da arba'in na yamma suka sauka garin sukeja duk da suna tsayawa su yi sallah a hanya har abinci ma suka ci a Restuarant ga gudu da suke tamkar su tashi sama.A ?ofar gidan da suka saba ganin Aminar lokacin suna zuwa dubata, direban ya faka motar dan dama shi ne ya san gidan sannan motar su Malam ma ta tsaya a bayan Wayar, sun firfito kafin suka fara nocking dan ?aramar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login