Showing 33001 words to 36000 words out of 77516 words

Chapter 12 - ALAKAR YARINTA Book Complete by Maman Afrah.doc

kamar wanda za a ce kamoshi ya gudu.Direbansa ne ri?e da rawaninsa sai zaginsa (Bafadensa) Ri?e da al?yabbarsa, cikin mamaki ta ?araso ganin suna masa sannu har ya zauna a kan kujera yana wani sauke numfashi sama-sama.



"Ikom Allah mai ke faruwa ne?" Ta jrfa musu tambayar tana bin su da kallo Waya bayan Waya.


"Eh dama, dama...


"Dama me? Na ce dama me ina tambayarku mai yake samesa kana min wani kame-kame?" Ta katsewa direban hanzari cikin ?araji.



"Kawai fa a wajen taron wannan ne shi ne ya ga wani Hakimi ?an buran shi da Wansa Hafiz to suna ?o?arin gaisawa ne dukansu kowa ya fara karkarwa su duka ukun har Hafiz Win suka dafe kan su, dama bayan an gama taron ne ana Wan gaggaisawa, sai kawai Sarki ya ce a saka su a mota kowa ya tafi gida" Bafaden ya faWa cikin girmamawa.



Wani murmushi ne ya sauka a kan fuskar Hajiya Suwaida jin wannan daddaWan labari amma babu wanda zai iya ganin murmushin nata saboda cikin hikima da gwanancewa da kissa ta yi.A hanzarce ta nufi Alhajin hankali tashe tana salati, tana jero masa sannu shi dai bai iya cewa komai ba dan gabaWaya sai wani gumi ne ke tsatssafo masa ko ta ina ga wani karkarwa da yake kamar mai zazzaSi.



"Kai Allah kaWai ya san mai hakan ke nufi" Ta faWa cikin sanyin murya.



"Wallahi Hajiya kowa ma mamaki yake hatta mai martaba ya jinjina al'amarin" Direban ya ce cikin jimanta abin.



"Allah dai ya yaye masa ya karesa daga azzalumai da sharrin duk wani mai sharri" Bafaden ya ce yana Wora al?yabbar a kan Waya daha cikin kujerun.



"Amin ya Allah, alfarmar annabi da alqur'ani" Direban shi ma ya ce yana ajiye rawanin a kusa da al?yabbar.



Shiru Hajiya Suwaiba ta yi ba ta ce amin ba.



"Hajiya bari mu je sai ya tashi ko" Suka haWa baki wajen faWa.


"To to to, sannunku da ?o?ari"


Suna fita ta bi bayansu da harara a ranta ta ce



"Amma na ji daWin faruwar hakan, ai ba za ku taSa gane junanku ba, duk wanda ya tarki tuno Waya daga cikinku to tabbas ya tarowa kan sa aradu da ka" Ta faWi haka a cikin zuciyarta tana maida hankalinta ga Alhaji da bacci ya Waukeshi a jigace.Haka ta Wan gyara masa kwanciyad da ke doguwar kujera ce ya Wan kishingiWa aka a duk da kasancewarsa babban mutum amma hakan bai hana kujerar Waukansa ba saboda irin manya -manyan nan ne.



Sai wajen ?arfe huWu da wani abu ya farka, kamar ma bashi ba dan ya dawo dai dai, sai da ya yi wanka ya yi sallar azahar da la'asar sannnan Hajiya ta gabatar masa da abinci, haka ya ci abincin mai maganin nan da ta barbaWa, yadda bai mata zancen haWuwarsa da ?an buran ba haka ita ma ta wagarar da zancen dan dama ba ?aunar zancen take ba shi kuma da alama ma ya manta da komai da ya faru.


Bayan sun kammala suna nan suna Wan taSa hira a take Hajiya Suwaida ta bijiro da bu?atar kuWi domin gwada sa'arta saboda tana so ta tabbatar da ingancin maganin.



"Alhaji dama inaso ka bani wasu kuWi saboda inaso in yi siyayya dan duk wasu abubuwam bu?ata ta sun ?are" Ta faWa tana masa wani kallo ?asa -?asa.



"Cikin Wan ruWewa ya ce mi?o min wayata a kan Tv stand "


Cikin Wan sauri ta tashi ta Wakko wayar a ranta tana jinjina aikin Malamin.Tana kawo masa ta tsaya jiran tsammani dan so take ya tambayeta adadin kuWin da zai mata bu?atun ta, dan bata so ya bata kuWi kaWan dan an ce in zaka ro?a ka ro?a da babban masaki...




"Kamar nawa kike bu?ata" Ta tsinkayi muryarsa ya jefa mata tambayar.



"500k ne "


"

Kina ganin za su isheki?"



"Sun isa" Cewar Hajiya Suwaida tana jin wani itin daWi a ranta dan tabbas magani ya fara aiki, dan tun da maganin ya karye ko 100k bai sake bata ba bare kuma har 500k.




?aran shigowar sa?o wayarta ne ya ?ara tsundumata cikin gogin farinciki, tana dubawa ta ga alert Win transper da ya mata.



"Godiya nake Ranka ya daWe"

"Ai babu komai" Ya xe yana tashi domin hawa sama dan yin alwalar magrib, yana hawa saman ta tashi ta koma part Winta, no Hajiya Hauwa ta kira a nan ta shig bata labarin abubuwan da suka faru, dariya suka kwashe da ita

.
"Kina lokacinki ?awata" Cewar Hajiya Hauwa tana dariya.



"Ke dai bari ?awata ai da sannu zai gane shayi ruwa ne"


"Ina yinki ?awata kin san ta kan tsiya, gaskiya kina wuta muna binki da fetur"


"Eh mana amma bar kani wutar na da baki kar mala'iku su ce amin"



"To na bari"


"Yawwa ko ke fa ai gwara dai ki ce ina aljanna ko"



"Hakane kam fatana nagari lamiri duk da baSa aikin aljannar'


" Za mu tuba ai"


"Allah ba mu iko"


"Amin"





Haka dai suka cigaba da tattaunawa daga ?arshe suka yi sallama.


*GIDAN ?AN BURAN*



Hajiya Sakina ce tsaye a gaban freezer ita da ?ar aikinta tana fitar da kayan marmari waWan da za a yanka, tana warewa domin mai aikin nata ta je ta ?ara wankesu ta kawo mata ta yayyanka, saboda ta gama haWa komai na abinci yana dining dan ta san mai gidan nata da tilon Wan mata yanzu suna tafe daga dawow daga wajen naWin da suka je fada.So take daga ta kammala ta je ta yi sallah dan ga lokaci ya kusa fan ta san suma idan sun dawo sai sun je masallaci sun dawo sannan za a ci abincin.


Bayan ta gama yayyankawa ?anana dan fruit salad ne ta haWa tana gamawa ta zuba a kwanon flastic mai zurfi ta sanya madara da ?an?ara sai Wan sugar kaWan, ta sanya murfin ta rufe, sannan ta markaWa mangwaro ta haWa lemon mangwaro bayan ta kammala ta zuba a jug tasa ?an?ara ta kai kan dinning ta ajiye sannan ta wuce domin zuwa ta Wan ?ara watsa ruwa saboda zadin da take ji, sai ta yi sallar, bayan ta kammala wankan tana ?o?arin yin alwala ta tsinkayo muryar mai aikinta ta shigo Wakin tana kiranta, jin yanayin kiran da take mata da alama kamar akwai matsala hakan yasa ta suturta jijinta ta fito, aikuwa ta ga ?ar aikin nata na nuni da hannu ta ma kasa furta komai.Da sauri Hajiya Sakina ta sanya dogon hijabinta na sallah da ke ajiye tare da sallaya a kan ?aramar loka, dan ba ta da nutsuwar da za ta tsaya sanya kaya.

Bayan ?ar aikin ta biyo dan gabaWaya ma ganinta neman gushe mata yake

Ta ruWe ta ma kasa tambayar ?ar aikin takamaiman abin da ke faruwa, ita ma kuma ?ar aikin ba ta san abin da ke faruwa ba kawai dai ta hango wasu dogarai guda biyu sun ri?o Alhaji, sannan direba da mai gadi sun ri?o Hafiz dan duk sai da aka shiga kafaWarsu. A can part Win Alhaji Sunusin an zaunar da Hafiz da Alhajin a kan kujerar sai aka jinginar musu da bayansu a jikin kujerar, a dai dai nan Hajiya Sakina suka ?araso ita da mai aikinta.


"Subhanallahi! Me ke faruwa da su ne? Ko guba aka zuba a cikin abubuwan da aka ci a wurin taron ne?" Hajiya Sakina ta faWa cikin gushewar hankali dan gabaWaya ta tsorata da yanayin da ta gan su.


"Wallahi Hajiya ba haka bane, bayan an kammala taron ne ma suka haWu da Sarkin ya?i daga haka kar ki ?ara kar ki raga, shi ne gabaWaya suka kasance a cikin wannan halin har gwara ma shi Sarkin ?akin a kan su dan su sai da mai martaba ma ya bada umarni dogaran nan su tayamu mu kawo su gida" Direban ya mata bayani ai ambaton sunan Sarkin Ya?i da ya yi sai da kan ta ya sara mata da mugun ?arfi har sai da ta dafe da hannu Waya sannan a hankali ta zauna.Ganin halin da ta shiga yasa ?ar aikin nata yin sauri tana mata sannu.Shiru ba ta yi magana ba sai zuwa can ta ce

"Yawwa"

Sai ta maida hankalinta kan mai gidan nata da Wan nata, ta taso ta zo garesu tana tambayar mai je damunsu dan har ta manta da labarin da direban ya bata hakan ne ya sanya kan nata ma ya saka mata.


Daga dogaran har direban da mai gadin kallon kallo aka shiga yi jin tambayar da ta fito daga bakinta, babu wanda ya sake wata magana dan su ma sun lura kamar akwai halin da ta shiga lokacin da aka faWa mata dalilin da ya sanya suka shiga wannan halin.Sallama dogaran suka musu tare da musu fatan samun sau?i, shi ma direban fitowa ya yu shi ma mai gadin ya koma bakin aikinsa.


Sun Wauki tsawon awa guda sannan suka dawo hayyacinsu, dan dama ba dai bacci suke ba amma yanayinsu kamar na wanda suka sha abin maye suka bugu.Ganin sun farfaWo yasa ?ar aikin nata ta fita ta koma bakin aikinta, ita kuma sannu ta shiga musu dan daga ita har su sun riga da sun manta takamaiman abin da ya faru.


Sun dawo kamar ma babu abin da ya faru dan abin kamar wani shafar aljannu, alwala suka yi suka yi sallah Alhajin ne ya ja su sallar har Hakiya Sakina dan lokacin har an riga da an idar da sallar azahar Win, bayan sun idar suka ci abincinsu cikin kwanciyar hankali suna taSa hira cikin farinciki da barkwanci.





"Sannu da zuwa Baba Malam Baiwar Allah ta faWa cikin girmamawa.


"Yawwa sannu Baiwar Allah, wanki ake"

"Eh"

"Ke dai bakya gajiya da aiki" Ya ce yana murmusawa.


"Kai ma dai ka faWa Malam ni ma yanzu na gama faWa"

"To ai shikenan tun da tana son yin aikin ai shikenn"

"Wlh kwa dan yanzu ma ta gama kwashe tuwo ta Wora miya, ni ce ma na ce zan ?arasa miyar daker ta yarda shi ne ta ?ara tsirar wanki" Malama Zainab ta ce tana Waukan ledojin da Malam ya iyo tsaraba, daga wani ?auye da ya je wurin wani babban Malami abokinsa domin su haWa wani magani da za a haWawa Baiwar Allah.


Bayan ya ci abincin dare suna hira a tsakar gida ya ce Malama Zainab ta Wakko masa wata ba?ar leda da ya zo da ita a hannunsa Wazu da ya dawo ya faWa mata inda ledar take dan Wazu ma da ya zo da ita a cikin aljihun babbar rigarsa dan maganin ne sanadin tafiyarsa tun bayan sallar asuba.

Bayan ta Wakko ya buWe ledar ya fito da gora mai Wauke da rubutu, sai kuma wani ?ullin magani ya ce


"Wannan rubutun da kike gani, idan aka zuba maganin nan ta sha na tsawon kwana uku to duk wani abu da ta manta za ta tuno da shi, ba ma ita kaWai ba matsawar sihirin mantuwar nan ya bar jikinta to duk su ma wanda aka musu tare sai ya bar jikinsu, domin su biyar ne aka yiwa sihirin duk da ban san sauran ba amma nasan ba za su wuce makusantan da ba saboda su manta da ita ba za su tuna da ita ba ma bare har su nemi inda take amma cikin ikon Allah komai ya kusan zuwa ?arshe kamar yadda haukar ta bar jikinta da izinin Allah haka ma mantau Win zai bar su" Cewar Malam Idi yana buWe gorar ya since maganin ya shiga zubawa a ciki.


"Alhamdulillah! Na yi matu?ar farinciki da samun wannan magani Allah ?ara muku sani da basira Allah kuma ya taimakeka ya baka ladan abin da ka yi" Malama Zainab ta faWa cikin farinciki dan tana jin Baiwar Allah tamkar ?ar uwarta ta jini iya zaman da suka yi na kusan shekaru uku da wani abu.


"Ai nake faWa miki maganin ne samun sassa?ensa akwai wahala, shi yasa gashi ba mu da bishiyoyin a nan wajen a can ma da na je sai da muka yi tafiya mai nisa kafin mu je ga inda muka samu bishiyoyin muka sassa?a, na daWe ina neman inda zan samu sassa?en amma ki ga cikin hikimar Allah yanzu da lokacin ya yi na samun lafiyar warakar mantau Win nata sai a abokina da na tambaya ya ce akwai a wajen ?auyensu ana samu, gashi dai mun haWo mun kuma rubuto ayoyin da za su taimaka sai da ya tayani duk muka rubuce sannan aka wanke aka Wiga nonon jikin bishiyar saboda kafin azo nonon ya ?ame, hatta sassa?en ma sai da ya sanya matarsa ta daka min"


"Kai gaskiya an gode Allah bar zumunci ya barku tare"


"Amin, ki mata magana ta fito ta sha maganin"


"To bari na kirawo ta tun da ta shiga ta yi sallar isha'i da ta idar ba ta fito ba ko kwanciya ta yi, ka san ba ta sakewa idan kana nan tana ganin girmanka" Malam Zainab ta faWa tana tashi ta kwashe kwanukan tuwon ta shiga Waki ta kira Baiwar Allah, bayan ta fito ta zauna a kan tabarmar da Malama Zainab take zaune, Malam ne ya tsiyayo maganin a ?aramin kofi ya mi?awa Malama Zainab ta mi?awa Baiwar Allah, Bismillah ta yi ta kafa kanta ta shanye dan ko WanWano maganin bashi da shi babu Waci babu komai haka ta shanye ta ajiye kofin tare da musu godiya, cikin jin daWi suka ce ba komai dan an zama Waya babu batun godiya sai dai fatan dacewa maganin ya yi aiki.



MMN AFRAH







d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

=???ALA?AR YARINTA=???

d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?d'?

NA



MMN AFRAH




FIRST CLASS WRITER'S ASSO...





*Alhamdulillah godiya da yabo sun tabbata ga Allah maWaukakin sarki da ya bani ikon sake zuwa da wani sabon littafina mai suna ALA?AR YARINTA yadda na fara lafiya Allah sa na gama lafiya, Allah bani ikon rubuta abin da mutane za su amfana da shi amin* .


Wannan littafi daga farkonsa har ?arshensa sadaukarwa ne ga aminiyar ?warai Meenatu mmn muhibba Boy & sadiq , alkairin Allah ya kai muku a duk inda kuke Allah ya bar ?auna tsakaninmud'?



Page 3?? 8?? &3?? 9??



*HIZBULLAH*



"Dan Allah Hizbullah ka nutsu ka saurareni, bana so ka sanya kan ka a cikin matsala, wannan yarinyar da ganinta ba yarinyar arzi?i ba ce bare kuma shi mutumin da suke tare zai iya maka komai idan ka bisu dan Allah abokina ka dawo hayyacinka" Abulkairi ya ce lokacin da ya ?ara ri?o rigar Hizbu daga baya da ya yi yin?urij bin su Iftihal.Wani ruwa ne ya ciko cikin idanun Hizbu saboda bai san da kalaman da zai yi amfani da su ba Abulkairi ya bar shi ya bi bayansu kuma ba ya so su Sacewa ganinsa gashi duk kan sa ya kulle baisan ta ina zai fara tsayawa yiwa Abulkairin bayanin cewa ita ce Ridallah Winsa da da yake kwana da rashinta yake tashi yake cike da damuwa a cikin zuciya da ruhinsa wanda babu wanda ya san hakan sai shi sai kuma Allah da ke ganin zukatan bayinsa.


" Ka yiwa iyayenka ka barni bana tsoron komai ya faru da ni matsawar zan cimmu su kafin su Sacewa gani na, ka bari zan maka bayani daga baya, saboda kasan dai idan har ta Sacewa gani na bani da tabbacin ?ara ganinta amma idan na bi bayansu a ?alla zan san inda take zaune"

Shiru Abulkairi ya yi yana nazarin halin da abokin nasa yake ciki, sosai tausayinsa ya kamashi domin ya ga rauni sosai a tare da shi bayan kuma ya san abokin nasa akwai dagewa da kuma jajircewa ba ya taSa bari mutum ya ga gazawarsa amma kuma yau gabaWaya rauninsa ya bayyana duk da dai dama ba abin mamaki bane a ga komai a tare da shi in dai a kan Ridallah ne, shi ya ma kasa gane takamai man inda batun ya dosa dan ya dai san wannan ba Ridallah ba ce duk da bai santa ba amma ya yadda yake bashi labarin Ridallah da irin soyayyarsu bai kamata ace ta nuna bata san shi ba ma tabbas akwai lauje cikin naWi akwai wani abu a ?asa da yake ganin kamar shi kan sa Hizbullah Win bai sani ba bare kuma shi d...


"Ka sakar min riga" Muryar Hizbu ta katse masa tunaninsa.Kafin ya ce wani abu Hizbullah ya ?wace rigarsa da ?arfi ya tafi.Sho ma bashi da wani zaSi da ya wuce bin bayan Hizbullah Win, lokacin da ya zo inda mutane ke cin abinci ya tsaya waige-waige ko zai ga Hizbullah Win dan kan meye wannan har ya Sacewa ganinsa amma bai ga ko da alamarsa ba hakan yasa ya bi ?ofar fita daga wurin ya fito waje, yana ta dube-dube bai ga Hizbullah Win ba tafiya ya lan fara yi aikuwa ya hangoshi can wajen parking space ya tsaya hankali tashe yana ta dube-dube.



Cikin hanzari ya nufi wurin abokin nasa, yana zuwa ya ga Hizbullah na zubar da hawaye yana ta magana shi kaWai


"Ridallah dan Allah kar ki min haka, ina sonki a hakan ma, babu wani hali ko yananyi da za ki tsinci kan ki a ciki wuya ko daWi kyakkyawan hali ko akasin haka babu wani bau da zai ragu daga cikin ?aunar da nake miki, ganinki da na yi yau ya ?ara rura min wutar son ki a cikin tai da zuciyata, amma ya aka yi kika ?ara tafiya kika barni bayan ni ba zan iya barinki ko da na lokaci ?an?ani ba amma ke kin tafi kin barni tsawon wasu shekaru yanzu kin dawo amma kika ?ara guje min? Shin kin san wani irin hali zan sake shiga ta dalilin hakan? Haba Ridallah mai ya sa za ki guji wanda ya fi ?aunarki fiye da kan sa a rayuwarsa? Wanda ya fifita son ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login