Showing 45001 words to 48000 words out of 191310 words
Chapter 16 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
Duk muna a cikin motar zaune nidai na kurawa sarautan Allah ido sai can aka bude motar duk da an bude ya dan dade bai fito daga cikin motar ba.
Can ya sauko katan mazan nan suka wani zo suka tsaya wurin motar wani ke fadin in fito na fito da sauri har sunyi gaba na bi bayan su.
Gap da zai shiga wayab shi yai kara ya tsaya a wurin yana amsa waya haka yasa na yanke shawaran fara shiga cikin inda ake taron.
Sai masu tsaron get din wurin suka hanani shiga wai sai na nuna masu pass dina wanda mutum yafi a kirga sun shiga ni ina wurin tsaye.
Har sojan dake kofan yana son ture da hannu biyu kyaleta tare muka zo ya bashi amsa bamu shiga ba saida akai muna bincike.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
1️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
JUMMA, AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLAH YA SADA MU DA ALHERUN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA UBANGIJI YA YAFE MUNA KURAKUREN MU AMIN YA ALLAHU, , , ,
YAR UWA LITTAFIN KUDINE DON DARAJAN ALLAH KADA KI KARANTA IDAN BAKI BIYA BANA FITAR MAKI DA HAKKIN RASHIN SANI NA FADA MAKI ALLAH YASA MU DACE AMIN, , , , ,
DARI UKU NE KUDIN SHI DON SHIGA GROUP ZAKI IYA TURA WA TA WANAN ACC 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN NA DARI UKU KACAL, , , , ,
Ina tsaye duk na kagu in shiga inga abinda ake a cikin dakin taron da nake ganin mutane kala kala suna shiga wasu ma ba mudulmai bane daga cikinsu..
Nayi kamar zan bi wani tawagan yan mata da naga zasu shiga sai sojan dake kofa ya kalleni yai warning dina da bulalan hannun shi .
Dole naja baya na tsaya ina mazurai da idanuwa tare da dan bin ko ina da kallon mamaki a wurin don gaskiya ban taba zuwa irin wurin nan .
Sojojin kofan na naganin shi ya gama waya bodyguard din shin sun sashi tsakiya suka fara jayewa a hanya suna girmama shi.
Hannu ya daga masu yana kokati shiga nayi saurin shiga cikin su da saurina don kada su barni gurin ban san yaya zanyi ba gashi tunda nazo banga wani wanda na sani ba a wurin.
Sojan ne yayi azaman riko ni sai ya juyo a hankali kamar mai rowan magana yace don't sojan yaja baya da sauri ya kame.
Wani iri naji kaina ya amsa lokaci guda ganin irin taron mutanen dake wajen gasu zaune saman kujeru masu kyau kowa yayi kwalliya gwanin ban shawa,a.
Ba zan iya sheda kowa a wurin ba idan ba karya zanyi ba saima ince kowa ya zubu muna idanune shigowan mu ashe ban sani ba mai magana ke sanar da shigowan dan mami dana biyo tawagan su.
Biye nake dasu a baya kamar jela har aka nuna mashi wurin zama wani table babba yasha kayan ado dana ciye ciye saman shi.
Da idanu yai nune sai wani ke ce min in zauna wai na dan kai zaune a hankali kamar yadda kowa ya zauna kaina na sade kasa.
Ba mami ba duk wanda ke dakin taron hankalin shi ya dawo garemu ne ance yaro da kudi abokin manya.
Wai ashe da Done nake zaune ban sani ba a wurin sai mamakin koni wacece wanda basu sanni ba suke yi.
Wa yanda suka sanni kuma suna mamakine meye hadina dashi muka shigo tare ni yar aikin gida abinda ko yan gida basu samu gatan hakan ba sai karamar yar aiki kamana.
Anci gaba da gudunar da shagalin da ake inda mawakan hausa dana sauran yare suke nuna bajintan su a wurin.
Ga masu rabon gifts suna faman rabawa table table don komai a wurin a tsare ake yin shi tun ina kallo har gajiya ya fara kamani don zaman kurame muke a table din mu.
Dan gara su dan motsi kadan zaiyi sai kaga daya daga cikin bodyguard din nan sun duka suna magana dashi a kunne.
Har lokacin da muka tashi sai dai mutane suzo su gaisa dashi su wuce yana zaune bai daga ba sai da zasu tafi ne dayan ke min magana kamar rada yana fadin in tashi mu tafi.
Haka na taso shike gaba sai ni a baya bodyguard din dun samu a tsakiya kusan ince shine farkon fita wurin da gani baison hayaniya don sai faman murza goshin shi da yake yi kadan kadan zai murza goshi har yakai ga mikewa muka fita.
Kamar yadda mukazo haka muka koma ba wanda yai magana a motar har muka kai gida ni ban ma sani ba saida naga mota na shiga gidan nasan mun kawo.
Aka bude motar zan fita na juyo inda yake zaune kamar ba zai fita ba nace na gode yaya don ban san sunan shi ba dan mami bako nake kiran shi dashi.
Ina hawa steps din ne naji muryan dayan bodyguard din shi na fadin hjy ga wanan wai ki dauka inji boss wai ashe abinda aka rabane a wurin daya yakai a mota shine yanzu suka ban.
Haka na shiga da jakkan niki niki don gifts din manya daban aka bada su ba irin wanda aka rabawa kowa bane wurin.
Daki mami nakai jakkar har biyu mai kama data matafiya shake da kayan da ban san ko meye a ciki ba na aje.
Hayaniya ne ya fara karde gidan lokacin har barci ya soma daukana don ban dauki hakan a komai a raina ni dai nasan ya taimaka min saboda halin kirki irin na uwarsa ya kaini naga buki haka na aje kawai a raina.
Sabanin sauran jama,an wurin dake tunane kala kala yadda aka ganni dasu kowa da irin nashi fassaran a ran shi.
Nikan ganin mami bata shigo ba yasa na kwanta kasa nayi filo da jakkunan kayan da nashigo dasu har barci ya daukeni hakana ban sanni ba a wurin.
Ko da mami ta dawo ta samu ina barci a dakin ta a kasa na dunkule a wuri daya kallon tausayi tayi min yadda na kwanta a maraice a kasa.
Sai taji komai da take son tambayana data dawo ya kawu a zuciyar ta bata tayar dani ba sai dai can hayaniyar suce ta tayar dani daga barcin.
Da sauri na mike ina fadin mami sannuku da dawowa maki ina murzan ido .
Sai mami ta juyo tana fadin tashi kikayi kuma koma ki kwanta nima a gajiye nake ai yanzu sallah zanyi in kwanta.
Mami me zan maki yanzu na tambaya ta juyo tana fadin bakiji mena fada ba ki koma ki kwanta abin ki dare yayi yanzu sosai.
Washe gari da safe na tashi kowa nata sallahfita nayi waje ca wurin famfo wajr inda na saba yin alwala nayi na dawo falo nayi sallah.
Na dan zauna don jiran mami ta idar kafin in kwatanta in tashi zuwa dakin tana zaune suna magana dasu anty safiya da anty sa,a da wata mata.
Gaidasu nayi na mike na shiga bandaki na fara wankewa kagin in hadawa mami ruwan zafi na fito yanzu sun karu a dakin yasa na fita na barsu a ciki na dawo falo saman kujera na takure a wuri daya .
A yadda na lura wasu daga cikin bakin suna shirin komawane a ranan garuruwan da suka fito dan yiwa mami kara sai yanzu nasan mami mutumiyar mutane ne sosai.
Yauwa zonan yar iska manya kawai mai mugun nufi dama nasan ba banza kika bar mami ba shegiya.
Na dago kai ina duban dawa anty Rufaida ke wanan magana haka na fara waige waige ina duba sai naga tana nufo inda nake tana fadin .
Bada ke nake ba kin tsaya kina kallon mutane yar iska nuna kaina nayi da hannu cikin mamaki ina fadin ban san dani kike ba ai anty na mike tsaye.
Juyawa tayi haka yasa ba gane nufin ta nace anty mami zata nemeni yanzu don tace in bar nisa da ita jiya da kika sani diban ruwa tayi min fada.
Ke ni kike fadawa wani mami tace kibar nisa da ita kizo dakin mu yanzu ina jiran ki idan baki zoba kuma kin san sauran.
Juyawa nayi na kalli dakin mami kamar zanyi magana sai kuma na bi bayan Rufaida din zuwa dakin su.
Ina shiga takai min mangara a kai da niyar kaimin mari saina dafe ta samu kaina kallon mamaki nake mata don ban san abinda nayi mata ba haka ?
Ke yar iska yaya akayi kibi hero zuwa gurin jiya wai tana zare min idanuwanta waje tana son jin amsa daga bakina.
Shiru nayi don bansan abinda take magana a kaiba lokacin ra kara maimaita tambayan ta nayi shiru Nazira tace idan ma ke manyace kici kanki kisha bakin ruwa don bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane.
Sai wace akecewa rubby tace wanan ai na fada maku snake ce a ciki ku ga kyau ga daukan hankali ga duk wanda yasan abinda ake kira da matar manya.
Don Allah rubby ki daina wanan maganan haka karta dauka ita din wata tsiyane can ta ban amsa kawai don jiya shegiya ta hanani barci da dadi duk na rufe ido yar iska nake gani a cikin su.
Turo kofan da akayine ya dauki hankalin kowa a dakin ba kowa bane sai anty zulfa yar gurin kanin mahaifin su Rufaida tana fadin ke kina nan ga mami can na kira ki.
Ban tsaya jin komai ba na mike na bar dakin da ssuri na nufi dakin mami na dauka zatayi min fadan haka sai naga sabanin hakan tana fadi yauwa zainab don Allah zauna ki hada min wanan kayan kafin in fito wanka zan tafi dasune in sallami mutanen yola don karfe tara jirgin su zai tashi.
Na amsa da to mami tana fadin ki saka komai daya daya a cikin ko wani jakka tana fadin haka ta shige ban dakin.
Zama nayi na saka kayan kamar yadda mami ta umurce ni inyi mata tana fitowa ta zauna shafan mai tana umartana dana bude jakkunan ta gani.
Har ta gama shiri a gurguje tana fadin in kwasa zuwa cikin motar ta dake wajen gidan fake na na aje sai ga driver yazo yana fadin za a saka a cikin motar ne nace eh mami tace in kawo nan zata fito yanzu.
Sai gata mun hangota suna tafe suna magana ta kawo inda nake tsaye take fadin idan kin gyara dakin zeey ki mayar min da sadkokin ida muka dauko su jiya.
Sai kin dawo mami na bata amsa ina juyawa zusa cikin gidan kai tsaye dakin na shiga na samu mami ta barshi a bude.
Gyara komai nayi tsab na shiga ban dakin a gurguje don nayi wanka sai dai kuma har lokacin ina tunanen abinda su Rufaida sukai min wanda bansan akan me suke magana ba akai.
Mami ta dawo bayan bakin nata sun tafi nan kuma ta shiga sallaman masu tafiya a mota don komawa kaduna.
Suma tana daki tare da su anty safiya da kannenta biyu suna kasafa abinda ake bawa masu tafiya.
Zuwa karfe biyu gida ya koma sai mu kadai a cikin sa sai kuma kannen mami da basu tafi ba suna daki da anty salma wace sai yanzun na fahinci akwai mahaifiyarta a cikin su ashe don basu da kama sosai da uwar da mutum zaiyi saurin gane hakan.
Mami ta tashi don yin sallah azahar saboda dan barcin daya dauketa a lokacin don gajiyan dake jikinta.
Nima na danyi barci bayan gyara falon gidan danayi duk da girman falon amma hakan bai dameni ba na tsaya na gyara shi fes.
Ina zaune ni kadai a katon falin sai tv dake aiki jefi jefi nake dan mayar da hankali wurin kallon abinda akeyi a ciki.
Eyyeh zama ma kikayi saman kujara ke nan ke gaki mara ta ido ko a gidan ku akwai irin sane halan da zaki zaunawa mutane harda dora kafa sama.
Ina sauke kafan naji muryan Anty Aisha na fadin me kuma tayi yanzu dan ta zauna kawai a kasa kike son ta zauna ke nan .
Aisha baki san wanan munafukar yarinyar bane wallahi sai ta dinga yin abu simi simi kamar wata ta Allah can da ita nan ko munafukace ta gaske.
Ku daina yin hakan mana yarinyar nan bata da wani aibun da za,ace kuna mata haka ai tana fitowa daga daki dauke da chip's tana ci a hankali ta nufo wurin mu.
Wai kin san wanan bata aje kanta a kusa ba jifa jiya harda mannewa yaya J zuwa wuri dinner.
Kin san yan kauyen nan da bakin shishigin tsiya ko ya akayi ma tabi bayan shi ko tsoro babu.
Wanan she most go back to her village kafin rigiman ta ya fi nan don wallahi ni gaba daya nama tsaneta kwata kawata wallahi.
Haba haba Aisha tace cikin muryan ta na sanyi irin nasu meye a cikin har kina fadin kin tsaneta haka yarinyar nan she is good and beside mami tana jin dadin zama da ita sosai so kima bar wanan magana kada ku hadu da mami.
Ta mike tana fadin ashe na kusa barin gidan nan don ba zan iya zama da wanan yar iskan ba da take neman nuna ita watace a gidan nan.
Har abi yakai can haba bai kamata ba kina fadin haka kan zainab don ba ruwan mu da ita don Allah kada hakan ya jawo wani matsala mai girma.
Ina laifin wanan yarinyar a nan itace fa dazun ta gyara falon nan haka muna sharan barci a daki ita bata huta ba.
Tace a fusace ni dai bana son ganin ta gidan nan ne tare damu I just hate d girl wallahi.
Aisha tayi murmushi tare da daukan chip's din ta tasa a baki kafin tace ni banga wani aibunta ba wallahi.
A gadarance tace tana wa mutane shishigi da yawa a gidan nan ko don tana ganin mami na kama matane oho ?
Ru,faiidaaahta fada a wani irin yanayi kamar mai warning din ta sai kuma taci gaba da cin abinda ke hannun ta ba tare data furta komai ba kuma .
Juyawa Rufaida tayi a fusace tabar falon ta bita da kallo tana girgiza kai kafin ta dago ta dubeni inda nake tsaye a rakube tace zauna.
Ba bata lokaci nayi kokarin zama kasa don warning din da rufaida tayi min dazun kan kujeran da har ta zagi gidan mu.
A, a kasa zaki zauna zauna a nan tana nuna min gefen da take zaune na girgiza kai tare da fadin akan hawa kujera yanzu anty Rufaida ta zageni.
To ai yanzu ni nace ki zauna ko ta fada cikin rashin damuwa sai dana danyi jimm kafin in zauna a saman dayan kujaran a takure daga bakin kujeran don ban yarda na zauna ciki sosai ba kada kuma a kara zagan min iyayyena wanan karon.
Kaina a kasa sai wasa nake da yan yatsun hannuna jin ta kira sunana yasani dago kai na dan kalleta kadan tare da kara sunkuyar da kaina a kasa.
Sai naji ta dan sake murmushi tare da fadin feel free with me zee I am not like Rufaida OK.
Na kula baki da walwala a gidan nan ko yaushe kamar a takure kike ina son sanin damuwan ki idan ba matsala.
Jin tayi shiru yasa na dago kai na dan dubeta kadan ni take kallo a lokacin ganin na kalleta ta dan daga min kai tare da fadin ke nake saurare zainab.
Ta sake fadin tell me meye matsalan ki ne meke damuwan ki ko yaushe kike a takure ?
Ina son sanin menene sirin kin san ABU A CIKIN DUHU SIRINE, jin haka yasa na dago kai na dan kalle ta tare da fadin sirin me kuma Anty Aisha ?
Sirin rashin jittuwan ki dasu mana nake son sani sai da dalilin ai hakan ke faruwa.
Da kyat na bude bakina na nace banda matsala a komai sai dai su anty Rufaidane suke yawan takura min har tana zagina da iyayyana don kawai taga nazo yin aiki a gidan su.
Zagi kuma zee koda yake koni yanzu naji yadda kukayi ko dukan ki zata iya ai a yadda ta nuna din .
To wai me ya kawo hakan a tsakanin ku ne don na kula tunda na dawo hutu da abubuwan dake faruwa a gidan nan.
Ko kina tunanen wani abune ya jawo hakan ke a tunanen ki zainab don naga dai ba shiga harkan su kikeyi ba ke a gidan nan.
Idona ya kawo kwalla nace sai nake gani kamar don irin yadda mami take min ne sukewa haushin hakan don mami bata daukeni yar aiki ba kamar yarta ta daukeni ta jini.
Sai suke ganin kamar ban cancanci hakan ba tunda nidin ba jinin ku bane da mami zata sakani a jikin