Showing 126001 words to 129000 words out of 191310 words
Chapter 43 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
kama mami dake zaune tana aiki saijin sunan dan nata tayi a matsayin babban bakon su na ranan a hankali mami ta zare glass din dake idon ta tana mamaki don bai fada mata cewa sun gaiyace shi ba .
Kowa dake falon ya mayar da hanlalin shi wurin sauraren hira da akeyi da ya jafar din a sannu ake masa tambayoyi yana bada amsa mami sai girgiza kai kawai take a cikin burgewa.
Bayani ne na irin business din su ta yadda zasu tallafawa kasa a samu cigaba hakan daga kasashe daban daban na duniya.
Ko wanan haskawan ya kasance sunyi nasaran shigo da na,urori n wutar lantarki da zata karawa wutan kasan haske ba tare da ansha wahalan wutan neper ba a kasa.
An dauki lokaci ana hiran falon yayi tsit hjy tsohuwa ke fadin ni wanan da an barni sai nace jafari ne ai don kamar su datayi yawa sosai.
Aisha dake gefe zaune ta nade kafafunta saman kujera taja tsuki tare da fadin dama wa kike kallo a tv idan bashi ba yanzu.
Yayin dasu jalal suka hau mata dariya daga inda suke zaune suma suna kallon shirin tambayan da aka jefo maine yasa mami ta daka masu tsawa akan suyi shiru su saurara.
Mai hira dashi yace mr jafar mu,azu mahadi laire kayi namijin kokari sosai wurin shigo muna da wanan kayan a kasan nan babu abinda mu yan kasa zamu ce maka sai godiya da kira ga irin ku matasa da suyi koyi da irin halinka a taru a gina wanan kasan ta farfado daga faduwan tattalin arzikin da take barazanan shiga a yanzu.
Sai tambaya na karshe da zamuyima a yanzu ko enginer namu zai dan fadawa masu kallo da sauraren mu shekarun sa nawa ?
Sai lokacin ya danyi murmushi tun fara hiran dashi tare da fadin iam just talatin da bakwai nake nema a yanzu.
Matan ka nawa a yanzu ido ya dan lumshe kafin ya bude ya kalli mai tambayan ya furta matana daya sunan ta zainab bello Anchau .
Itace matarka ta farko mai tambayan ya tambayeshi a cikin dariya sai ya dan lumshe idanu kafin ya waresu a hankali yace cikin murmushi itace auren namu baikai three days ba ai yanzu da mukayi.
Don aurene na siri da ba kowa yasan da faruwan hakan ba sai yan kalilan ya fada yana gyara zaman shi.
A daidai lokacin da mai hira dashi a tv ke fadin wow zanso naga wanan lucky girl din datayi nasaran sace zuciyar matashi kamarka da kasa ke alfahari dakai haka.
Daidai lokacin ne a falon mami kuma abubuwa suka faru da dama a wurin don ba mami kadai ba har yayanta dake zaune a falon saida suka mike tsaye a cikin fargaba da tashin hankali.
Hjy dai da ba turanci takeji ba sai binsu da kallon mamaki takeyi tare da mikewa tsaye itama tana fadin wai meke faruwane haka ?
Don ganin yadda mami ta sake kofin glass din daga hannunta ya tarwatse a gurin lokaci guda tana batun fita hayacin ta a take.
Tambayan su take meke faruwane haka a gigice Aisha na fadin ina wanan ma aiba zai taba faruwa ba wallahi wanan ai jawa kai raini ne da wullakanci.
Ya jamal ne dake kan mami da take kokarin kiran waya hankali tashe ta kasa sai jalal ta mikawa wayan ya kira matashi ya juyo yana fadawa hjy cewa.
Wai ya J ne ya fada yanzu sunyi aure da zeey kwana uku daya wuce din nan a razane tsohuwar tace aure ?
Haka ya fada yanzu hjy a duniya kin kuma san halinshi baya magana biyu shi hakan ne tunda ya iya fadawa duniya kai tsaye.
Shike nan hjy ta fada iyami kin kai ga yadda kikeso da yaran nan Allah ya gani yaron nan baida hakkin ki ko kadan.
Shiyasa ubangiji yai maki hakan kina raye ki ci barnan ki da hannun ki ba sai gobe ba ace mutum ya tsaya yana jayayya da hukuncin Allah haka ?
Allah ubangiji yasawa aure albarka ya kore shadan da shedanu a tsakanin yaran nan kuma Allah ya basu zuria masu albarka, , , , , haba hjy.
Aisha da ta raba hankalinta gida biyu ke fadi haka ki duba kikaga yanayin da mami take ciki da kike wanan maganan.
Ga kuma wayoyin mami din dake ake ta faman kira a lokacin wanan na shigowa har ya katse ba a daga ba wani ya sake shigowa daga kawayen ta da yan uwanta.
Ban san meke faruwa a gidan ba ina dakin mu kwance ina karatu don jerabawan da muka fara zanawa yasa yanzu ban wasa da karatu na.
Don damuwan da tashin hankali bai hanani mayar da hankali ga karatuna ba.
Dan haya niya nake ji sama sama tunda ba tv ne kunne a dakin ba sai dan karan nauran sayin dake aiki dakin lokacin.
Kamar ance in fita waje zubur na mike daga kwancen da nake na zura takalmina dake kofan daki a fararen kafafuwana da yanzu suka samu hutun jin dadi sun kara fari da kyai kamar bana taba kasa dasu don hasken su.
Har nakai kofa naji wayana na kara najuya ina kallon wayan dake gefen filo ajiye na nufi wurin duk da ban debe tsamani ga kirana din ba shine dai.
Na dauka da sallama muryan shine ya sauka a kunnena yana fadin queen kina inane yanzu ba tare daya amsa min sallaman ba.
Dakin mu zan fita waje ne yanzu ka kirani kada ki fita nasan mami na gida yanzu akwai matsala idan kin fita yanzu wurin su.
Kirjinane yai wani irin bugawa lokaci guda nace a hankali matsala akan me kuma yaya yanzun nan na gaida ita a falo ai.
Na fada maki kada ki fita ki bari yanzun zan karaso gidan idan ma zaki fitone ki bari in shigo.
Jikina yayi sanyi yayinda zuciyana ya shiga fargaba da tsoron jin abinda ya fada din naji yana fadin al,amarin mai girmane zai faru a yanzu tsakanin mu da mami don yanzu nagama fadi a tv an daura min aure dake.
Aure na fada da dan karfi kafin in wurgar da wayan saman gado inje kasa a sulale don firgicin abindaya fada din.
Shike nan wanan mutumin yaja min tashin hankali da fitina a rayuwana don me zai fadi haka a duniya dole mami ta dauka ai gaskiyane ke nan.
Kamar an tsikareni sai kuma nayi zubur na mike na kwasa da gudu zuwa falo ban tsaya sauren gargadin da yaimin ba a wayan.
Ina fitowa falon naja na tsaya turus don yadda gaba daya suka zubo min idanuwan su a falon lokaci guda.
A hankali nake kokarin takowa zuwa garesu naji Aisha da mami sun daka min wani irin tsawa kusan lokaci guda suna fadin ke dakatanan gurin kada ki yarda ki karoso wurin nan bakar manya kawai Aishan ta fada.
Hannu mami ta daga min itama tana fadin barta tazo ta fada min abinda ban sani ba tunda ta zamax munafuka tsakanina da dana.
Idona runtse hawaye ya shiga tsiyayya a idon nawa na kai kasa ina fadin mami bazan taba munafurtaki ba a rayuwana.
Idan nayi maki laifine don Allah ki yafe min mami idan kinyi fushi dani mami ina zan saka raina.
Rufa muna baki yar iska ba kauyan banza bakar manya mai nacin tsiya kamar karya wace, , , ,
Tas tas Jamal ya kwashe Aisha da mari biyu masu kyau sai data duka a inda take zaune tana jefo min zagin.
Mami ta dago da zuman ramawa Aisha marin yayi saurin kaucwa a inda yake tsaye ta hanyat jada baya kadan mami ke fadin ka mareta saboda wanan yarinyar jamal.
Mami bakiji irin mugun zagin da take zagin diyar mutane dashi bane ita waya zageta haka ko meye laifin zeey a cikin zancen nan yanzu wace ke gida always tare daku.
Shiru sukayi a dalilin shigowan yaya jafar da ya mamud gidan ya mamud da tun kan ya karaso yake fadin meke faruwane kuma yana kallon mami ya kuma juyo inda nake gurfane ina sharban kuka ya sake juyawa wurin da Aisha ke zaune yana fadin wai meya farune haka wai ?
Wani irin ashar mami ta wulwulo ta duramin a tsorace na jada baya na makure a jikin bango jikina na kyarma hankali a tashe ban daina kukan da nakeyi ba har lokacin.
Mami ta sake daka min wani uwar tsawa tana umartana da nadawo gaban ta take na mike jikina na kyarma na dan karaso inda suke zaune ita da Aisha.
Ya jafar din ya samu wuri a gefen mami yakai zaune a cikin kwanciyan hankali yanayin shi yake.
Banyi aune ba naji mami ta fisgeni da karfi nakai gurfane a gabanta da sauri ya jafar din yace subbahanallahi this is bad mami meye laifinta a wanan zancen.
Wani kallo mami ta watsa mai kafintayi kukan kura ba wanda yai aune da ita lokacin takai min mari uku masu kyau a fuskana saida duk diyan nata suka mike tsaye don firgita.
Ban samu bakin yin ihu na don gigicewan danayi a lokacin sai idanuwana da suka firfito waje kamar mai shirin bankwana da duniya .
Ta koma inda ta taso tana fadin mara mutunci kawai kin cuci kanki wallahi ni baki cuceni ba zainab.
Dama an fadi tsintarciyar mage bata taba zama magen gida sai ta hada da halin sata ashe zancen da ake fada min inyi hankali dake a yadda nasakaki a jiki ba karya aka fada ba.
Har lokacin falon yai shiru kowa yana sauraren ta taci gaba da fadin wallahi yau ba zaki kwana min a gida ba har in maganan nan gaskiyane ya fada.
Kuma yanzun nan ba sai anjima ba zaki barmin gidana babu ruwanki da wata zuri,ata yar iska.
Kije can ku karata da tsitanki keda tambadaddun iyayyen ki da suka sakoki a cikin duniya suka watsar dake haka.
Kai haba mami this unfear wallahi yarinyar nan ina ta sani a garin nan da za ayi mata wanan irin koran kare haka bafa itace mai laifin nan ba dankine mai laifi mami ya mamud ya fada rai bace.
Tsam ya Jafar ya mike tsaye ba tare da yayiwa kowa magana ba a wurin ya nufo inda nake gurfane ina rusan kuka .
Dakatar dashi mami tayi ta hanyar fadin jafar kana taba ta wurin nan saina tsine maka yanzun nan .
Jin hakan ya dakatar dashi daga niyar tabanin da yayi da farko yana shafan kanshi a hankali batare dayayi magana ba ya juya ya zauna inda ya tashi din.
Wani marin mami ta sake kaimin saida ya yunkura daga yadda yake zaune kamar zai tashi a lokacin.
Iyami kina da sauran hankali kuwa hjy da take zaune tayi mutuwan kasko a zaune ta fada rai bace.
Kai na girgiza don jin muryan hjy din nace wallahi hjy ban san komai ba akan laifin da ake nufin na aikata yanzu.
Yi muna shiru munafukan banza da wofi kawai wa zaki kawowa rainin hankali a nan bayan kun asurce min da mugun alkaba,in kuna kauye.
Yanzun wani karya zaki fada muna kin dauka bamu san me iyayyen ki suke maki bane a can gida kin rikita min kanda na rasa gane kansa gabaki daya.
Hannu na dora a kai tare da girgiza kaina ina fadin wallahi mami ban taba tunane ko wayau aikata hakan ba ga kowa balle wanan da ake tuhuman na aikata din yanzu.
Yadda ta zaburo zata kara makana yasa nayi wurin hjy da sauri na kankame a jikinta ina fadin hj ki ceceni ku mayar dani wurin iyayyena don Allah wallahi ban aikata komai da ake nufin munyi ba asalima iyayyena basu san wanan zancen ba .
Mikewa yayi zubur tare da fadi cikin wani tsawa enough ya tsaya yana bin kowa dake falon da kallo na dan second kafin yace indai ba kasheta kuke son yi ba please mami ku barta hakana.
Nina mai lafi ba yarinyar nan da bata san komai a wanan zancen ba don nina ganta nace ina sonta a duk yadda kuke ganin take ni tayimin a hakan.
Hannu ya mika ya wufci hannuna daya daga inda nake gurfanen ya mike dani tsaye tare da nufar hanyar fita waje dani.
Kon binshi nayi da karfi nake fadin mami ki taimakeni ki cece rayuwana kada ki bari ya tafi dani don Allah mami kicece rayuwana nima yarkine mami.
Jin ya rikoni da karfi yana kokarin jana da karfi mubar falon da karfi na fara fadin innalillahi wa,innalaihim raji,un mami kada ki bari yaya ya tafi dani don Allah.
Ganin mami bata ko kalleni ba yasa na juya wurin hjy ina fadin hjy ki taimakeni kada ki bari a cutar dani hjy.
Hannu hjy ta mika mai tana fadin jafari miko min yarinyar nan nan kaga dai uwarku ta nuna yar nan yau bata kwana mata gidan nan .
Mami ta juyo a fusace tana fadin hjy bafa zanbar yarinyar nan gidan nan ba yau taje can ta hadu da yan duniya irinta su dace.
Nasani iyami yar ba zata kara awa daya ba a gidan nan ko ince ba zamu kara awa daya ba a cikin gidan dani da yar nan.
Kai mamuda jeka ka da dan uwanka gamu fitowa ke kuma tashi ki shiga ki hado duk wani abin bukatanki dake gidan nan.
Na dan tsaya nawa hjy ta daka min wani uban tsawa na mike tare da dan dingisa kafata da yai min nauyi ina shiga dakin naja na tsaya daga kofa ina bin dakin da kallo kamar yau na fara shiga dakin.
Jin takon tafiya an nufo kofan dakin yasa da sauri na matsa wurin wardrobe dina na bude na fara fitar da takarduna sai wayana dana dauka na tura a school bag dina.
Hjy ta shigo a cikin wani irin yanayi dakin wanda ban taba ganinta a cikin shi ba ta nufi wurin jakkar kayanta tana kokarin dauka da karfin Allah.
Da sauri na karasa wurin ta na fada saman jikin ta ina fadin hjy idan kinyi haka kamar nice sanadin hadaki da yarki Allah ba zai taba yafe min ba kan hakan.
Ni ba donke zan bar gidan nan ba yau don kare mutunci da martaba na haihuwa gun yar dana haifa da idon ta ya rufe a gabana take wanan irin tujaran da nuna dan adam ba kowa bane a wurin ta.
Kamar yadda ta rantse nima haka yau din nan ba zan kwana a gidan nan ba sai mu tafi dake duk inda Allah ya nufa mu kwana a can.
Ina ji ina gani ban iya tabuka komai ba hjy ta fice da dan jakkar ta a hannu ta nufi falo dashi simi simi na biyo bayan ta dauke da jakkar school dina wanda shi kadai na iya dauka a gidan lokacin.
Kowa na tsaye cirko cirko a falon yanayin su babu dadi mami ke zaune ta sada kanta kasa a cikin wani irin yanayi na damuwa dkn bansan abinda ya faru ba bayan barina falon lokacin.
Yanzu da gaske hjy tafiya zakiyi don wanan maganan zaki bar gidan nan ai koshi yaya din baice hakan gaskiyane ba har yanzu.
Amma ke kin tashi kin hada kayan ki wai gida zaki bari saboda an taba yar dakinki ko ?
Kada ka kawo min diba albarka ta fada tana kallon jalal da yai maganan a lokacin a hasale kafin ta juya wurin ya mamud tana fadin mu tafi ka kaimu titi ka barmu a nan zamu samu na Annabi da zai iya taimaka muna daga sama do na Allah basu kare ba a duniyan nan.
Ta juyo inda nake tana fadi shige mu tafi kafin su halaki a gidan nan don an mayar dake bare.
Simi simi na zo na wuce a gaban su duk suka bini da kallo mami bata iya cira kai ta dago daga duken da kanta yake ba ga wayoyin ta suna ta kara naji jamal na fadi Aisha ki kashe wayan nan ga baki daya don Allah su daina damun mu haka.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
3️⃣8️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
FATAN ALHERI GAREKU MASOYA UBANGIJI YA SADAMU DA ALHERUN SA YA TSARE MU DAGA AIKATA SABO KOMAI KANKANTASHI AMIN, , ,
Nagode yan uwa da adduan ku gareni ubanginji ya yayewa dukkan musulmi damuwan shi a duk inda yake Allahuma Amin.
Sai bin hjy nake a baya tana jaye da hannu ina faman share hawa da hannuna daya.
Min karaso security din ya jafar suna tsaye cirko cirko a gaban gida suna dakon mu da fitowan mu kokarin amsan jakar dake hannu mu suka shiga yi lokaci daya.
Zuwa wurin motan da suka riga suka bude kofufinta tun kan mu iso wurin motar kofan yana a bude suna jiran isowar mu.