Showing 84001 words to 87000 words out of 191310 words
Chapter 29 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
aini ita din ce chooice dina sai ta karasa girman ta a gurina don ni a hakan da take yayi min daidai.
Jafar kada ka mayar dani abokiyar wasan ka idan kai tayi mani ba, , , ya mamud ne yace mami please.
Ki barshi ya zabi abinda yake so a rayuwan shi tunda shine zai zauna da ita bake ba kada a tillasta mai yayi abinda baiso a dawo ana dana sani daga baya kuma.
Hjy tacs fada mata dai dan nan ko kai zataji maganan ka tunda ni ban kai matsayin da zan tsawata mata ta saurare ni ba
Hjy bawai haka bane na lura yaron nan rainawa mutane wayau yake son yiwa mutane tunda mun tursasashi yayi aure bari ya zabo wace bata yuyuwa a gareshi yanzu ya rama abinda mukai masa ko ?
Wallahi mami tunane baikai ga hankan ba itace dai din naga tana daidai da rayuwana ita kuma din nake so a matsayin a bokiyar rayuwana.
To ban yarda bami ta fada a hasale tana mikewa hjy tace iyami dawo ki zauna mu kai karshen wanan maganan a nan tun wani bai kaiga ji ba.
Shiko jafar jikin shi ne yayi sanyi lakwas don bai taba tunanen mami zata dauki abin da zafi haka ba.
Ya mamud ne ya kawar da duk wata magana ta hanyar fadin tunda ita ka zaba din ba laifi ga hakan saidai yana da kyau itama muji ta bakinta ai idan tana son ka shike nan aurene mami ba wani abuba ai.
Mai yuyuwa kai itace zabinka ka ganta kana sonta a haka karamar ta ita kuma yarinyar ba kai mata ba a ranta .
Kaga ba zamuyi mata dole ba a kanka a matsayin na yar amana a wurin mami din don haka sai muji ta bakin ita yarinyat kuma.
Ban gane abinda kake nufi ba mamud mami ta fada tana kallon yaya mamud din taci gaba da fadin kaima kasan tunda ya tursasa mata ai bazatace batayi ba tunda duk mace ko banza neman irinsa takeyi.
Mata ma masu aji da ilimi da wayewa suna binsa su sameshi yana gudu sai akan wanan yar kauyen yarinyar idon ka zai sauka sai dai idan kana da wani manufane a kan hakan dai.
Banda manufar kome mami ita din ce nagani nake kuma so a hankan don banga wani matsalan da zaisa a hanani aurenta ba a tare da ita.
Mtss mami taja wani matsiyacin tsuki tana fadin Jafar kana son bacin raina da jefa yarinyar nan ga fushi wallahi.
Mami kiyi hakkuri yanzun nan zan kira ita yarinyar a gaban sa muji ta bakinta idan tace ta yarda dashi shike nan mami sai ki masu fatan alheri a rayuwan su.
Me zata fada tunda tana son shi mamud karka mata fa yar kauyece dama nema tafito yi a birni kuma ta samu a yanzu.
Gashi ta samu wanda darajan ta da kimarta baikai ta samu ba a yanzu, abinda bata taba tsamanin samun shi ba sai tace maka a a kuma ?
Mami please ayi hakkuri aji ta bakin ta idan ta amince ai masu fatan alheri shiyafi yanzu.
Mamud na fada maku yarinyarce bana son ya aura gaba daya don haka abar wanan na zancen tambayan ta please mamud.
But mami ni kuma ita din nake don banga wata da hankalina ya kwanta da ita ba bayan wanan din.
Jafar idan ma tausayinta ne yakaika fadin kana son ta ai ba sai ka furta kalman aure a tsakanin ku ba kana iya taimaka mata ta hanya da dama basai wanan hanyar ba daka fito dashi wai auren ta zakayi.
Jafar dake ta faman latsan wayan hannun shi tankar ba da shi ake zancen ba sai lokacin ya dago kai yana fadin.
Mami bawai taimakonta kawai nakeson yi ba ni kawai dai auren ta nakeso nayi dan tayi min a raina yana magana a cikin daure fuskan shi.
Daga inda hjy take zaune tace da kyau na mijin duniya kai mamuda kira muna yarinyar muji na bakinta yanzu.
Na bar gurin da suka sameni zaune don abincin ya gagara ci gareni don haka na dauka na kai kitchen.
Daga nan ne na tsaya don yin wanke wanken kayan da akaci abincin safe gasu nan an tara birjit don bakin da akayi gidan.
Maganan da mami tayi nake son in fara kiyayyewa da tace in dinga zama a cikin su lami da kande sune yan aiki irina.
Ina tsaye na fara tara kayan ne lami na faman sakamin albarka don haka suke min duk lokacin da nashigo zan tayasu wani aiki daya shafesu.
Muryan yaya mamud ne a kofan kitchen din yake fadin ke zainab zo mami na magana dake a dakin hjy.
Yana tsaye ya tokare hannayen shi a kofan shigowa kitchen din yayin daya zubamin idanuwan shi sai tausayin yadda ya sameni ya kamshi.
Juyawa yayi ya fara tafiya haka yasa na dauraye hannaye da sauri nabi bayan yaya mamud din ina jin wa yanda ke falo zaune na fadin.
Yar iska yarinya yau zakici uban ki gidan nan don yarinya kin tarowa kanki bala,i da hannun ki.
Idona ne ya kawo kwalla don ban kaunan abinda zakai a zagi iyayyena ko kadan saboda sanin daranjan su da nakeyi suko yan gida mami zagi a wurin su ba bakin komai bane a wurin su.
Zaune suke su hudu a dakin mami hjy ya mamud dashi gabana ne ya fadi don ganin su har lokacin a dakin .
Sallama nayi cikin yar siririyar murya hjy da ya mamud suka amsa min mami kan kai ta dago ta dan kalleni tare da kawar da kanta ga kallona.
Zauna a nan ya mamud yace dani yana nuna min wuri daga gefen kofa da nake tsaye saina kai rusunne da sauri ba tare dana zauna ba kamar yadda ya bukaci inyi din ba.
Kaina kasa ya mamud naji ya kira suna sai na dago kai a hankali na kalleshi yace mun kirakine muji ta bakin ki a kan wani maganan daba musan dashi ba tsakanin ki da jafar gashi zaune.
Ya nuna min shi da hannu sai lokacin na dan saci kallon Jafar din da idonshi sun kada a lokacin da gani shima yana cikin bacin rai ke nan.
Jafar ga yanan ya gabatar muna dake a matsayin wace zai aura kamar yadda mami ta bukaci da yakawo mata, matar da zai aura a yanzu.
Da sauri na sake dago kai nakai kallona ga Jafar din da shima a yanzu nice yake kallo da idanuwan da suka kade mai lokaci guda.
Don haka muke son jin ko kin amince da wanan ra,ayin nasa kema kin shirya da zaki aure shi kamar yadda ya bukata dake.
Dukar da kaina nayi kasa don ban san amsan daya dace in bada ba a wurin ga gardadin dayai min tun daren jiyan a mota ina tunane.
Ga mami dana hango tsanata saboda wanan zancen daya taso tsakanina dashi mami ta canza min gaba daya daga dare zuwa wanan lokacin kamar ba mami bace a gabana.
Don ba wanan yanayin na tausayina data min yau a gare ta ko kadan illa tsana karara da take nuna min a fuskanta.
Kiyi magana ke muke saurare ya mamud ya fada yana kallona don jin amsan da zan basu a lokacin.
Kai na fara girgizawa a hankali na samu na bude baki da kyat ina fadin ban san da maganan bani koma na sani ya jafar ba sa, an aurena bans shi don matsayina dana iyayyena baikai ko na yaron shi ba yaya.
Tunda na fara magana ido kowa ya zuba min sai mami dake fadin nikan nayi mamaki ina hankalin zeey da yatafi har take shirin tafkamin wanan kuskuren duk, , , ,
Dakata iyami ke a matsayin ki na uwa kin taba ganin inda aka tsiye yarinya haka wai ana tambayanta zabinta kai tsaye.
Kiwa Allah kiwa yaran nan adalci iyami tunda ni yanzu ba magana ta kike ji ba ban isa ba ko dan nima din banda mutuncine tunda nima daga kauyen nake ko ?
Yarasulu hjy me ya kawo wanan zance kuma har kina danganta kanki da hakan Allah ya gani ni ba manufa ke nan ba ta fada tana kallona az cikin yanayin daba zan iya fassarashi ba a lokacin.
Ke tashi ki tafi ya jafar ya fada a tsawace kuma ranshi bace ga wasu jijiyoyin kai da suka mai jasur a goshi abu fa farar fata sai suka mike sukai wani layi layi a saman goshin shi kamar mai tsananin ciwon kai a lokacin.
Da gani hankalin shi gaba daya a tashe yake mai a lokacin zainab jeki abinki ya mamud ya sake fada da sauri na mike nabar dakin.
Don dama a kage nake dana bar aurin saboda rikicin da nake hangowa a idanuwan su wurin.
Ina barin dakin kitchen na nufa har ina hadawa da tuntube don sauri saboda gaba daya na gama tsoracewa da lamarin nasu ga baki dayan su.
A daki kan hjy ta tubure tana fadin ya mamud yazo ya mayar da ita dakin ta ba zata zauna inda ba,a san darajan ta ba.
Hankalin mami ya tashi tsohuwar taci gaba da fadin yaron nan yace ga zabin shi ta yaya bayan kun gama tsorata yarjnya tun safe yanzu za a kirata ace ta fadi ra, ayinta a gaban kowa ?
Ke lokacin da akai maki aure haka mukai maki mami tace hjy kina dai son ganin laifina ne yanzu.
Wanan shawaran yaran nan sukazo da shirmen su a gaban kifa akai komai yanzu don Allah hjy kada kija zancen nan inda bai kai ba.
Yarinya dai tace ba zatayi dashi ba final Allahu akabar don kuma hankalin ki ya bata yanzu sai kikaji dadin hakan ke.
Allah na tuba ashe gaskiyane mace komai tsufanta wayau ta ragagge ne.
Ke yanzu har kina murna yar da kika raina kike gani ba a bakin komai ba ta iya budan baki a gaban idon ki yau tace maki batayi da dan naki da kike dauka wani kayan gabas a wurin ki.
Niyi tir da wanan hukuncin da kika bari yaron nan ya yanke a gaba me zan zauna inyi tunda banda sauran kima a idon ki.
Gidan ki nazo zaki iya min duk wani rashin da, a don yanzu kina ganin ke kin isarwa kanki a komai sai dai da badon jafari ba da sai ince yarinyar nan zainabu ta burgeni sosai .
To jinin ka jinin kane banji dadin yadda ta watsawa jafarin kasa a ido ba a gaban kowa don kawai tsoron idon ki data gani a daure kin sakar mata na mujiya .
Wanan maganan kuma sai yasa mami ta ji daci a zuciyar ta da kyat dai ta samu ta shawo kan yar tsohuwar ta fasa tafiya saidai mami bataji dadin yadda tsohuwar ta dauki zafi da ita ba haka.
Ya jafarko tunda ya fita ya bar mami da su ya mamud a dakin ya bar gidan tun mami bata damu da rashin ganin shi ba har dare yasa ta tambaya ko ina ya shiga haka bai dawo gida ba don hakan ba dabi a shi bane yin dare a waje .
Har yakai ta fara tambayan duk wanda ya shigo gidan a cikin mazan dake gidan amsa dayane dai daga shi har security din shi fun safe basa gidan.
Ta kira wayan shi yafi a kirga wayan ba ya shiga kwata kwata ba, a samun shi gaba gaba daya ranan.
Tunane kala kala mami tayishi ga zafin yarinyar daya mamaye mata rai gaba daya taji ta tsani yarinyar tana dana sanin daukoni dayi ta jefa a cikkn iyalin ta.
Gashi kuma hjy ma a nata ban garen haka ya jawo masu matsala da ita don tana matukar son mahaifiyar nata sosai.
Gaba daya gidan sai yai min zafi a yan kwanaki biyun nan babu wurin wanda nake dafawa inji sanyi kowa tsanata yake a gidan ga baki daya.
Sai gurin hjy kawai ita kuma yanzu ba zama muke sosai ba idan na shiga dakin sai zanyi wani abu don ina gudun mami tashigo ta sameni a ciki zaune yasa na koma kitchen wurin yan aikin da dukkan mu kawomu akayi gidan don aiki.
Hjy tayi fadan hakan har ta gaji ta saka min ido ta kyale ga yadda lamarin ya juye muna.
Ga zagi da nake sha a gun yan matan gidan a yanzu yayi yawa har takai ranan Rufaida tayi min mari biyu masu kyau.
Saida anty Aisha tayi mata fadan hakan kan su dan sasautamin don Allah tunda ba laifina bane shine ya ganni yace yana sona ai.
Ba nice na leke mashi ba kuma yanzu ba wanan zancen budan bakin Rufaida sai cewa tayi Aisha kece baki san halin yan kauyen nan ba.
Mudake tare dasu muka san halin su basu shigowa gari sai sun shirya an asirce su yadda duk namijin daya gansu ba zai iya kawar da idon shi a kansu ba meye ba a yi yanzu halan.
Gasu da sihiri mai dafi da kaifi wanda in basu ba kainan dan birni kace ai maka saidai aci kudin mu ga banza.
Tace au hakane nima fa abin yaban mamaki ace wai duk wanan baiwa da jin kan na ya jafar ga ilimi da wayewa amma ace wai zee yake so shi .
Wanan to zarcin da suke min ne yasa hankalina ya kara dagawa sosai a gidan naji ina son komawa kauyen mu baki alaikum ba tare dana fadawa kowa ba.
Sai dai kuma ina jin tsoro don ban san kan garin ba kada in fita ni kadai a ganni ba kauya a saceni.
Tunda na fara jin ana fadin jibine tafiya Abuja na fara funane a raina don nagama yankewa kaina hukunci .
Gara kawai in gudu in koma gida ko ta kan anty safiya data kawoni da itama tazo tayi min tas kan wanan zancen a gaban mami ta wanke tas wanda nasan hakan tayi shine don kawai ta wanke kanta a wurin mami din.
Saida na bari hjy tayi barci na mike na fara hada kayana a cikin jakkata inayi ina juyowa ina kallon ta kada ta tashi ta ganni.
Aiko ban tsira ba don ashe idon ta biyu tun dana fara take kallon abinda nakeyi.
Juyowan da zanyi sai ganin ta nayi zaund ta kura min ido kaduwa nayi don ban zaci hakan ba na dauka tayi nisan barci a lokacin.
Ikon Allah yar nan me kike kokarin yine karda ace guduwa kike son yi daga gidan nan sai kawai na durkushe a wurin ina kuka ina fadin hjy gida zan tafi.
Babu mai sona a gidan nan mami ma fushi take dani har su anty Aisha da nake dan dafawa naji sanyi yanzu itama bata sona suncewa asiri nakeyiwa mutane suke sona.
Sai naga tsohuwar ta danyi murmushi can kuma tace kai yaro dai yarone ke in banda abinki dama ai duk wanda Allah ya mayar sani abu a duniya saiya fuskaci kalubali mai tsanani kafin ya taka nasaran shi.
Ba wanda ya tsamaci haka gareki sai gashi kwatsam Allah ya doraki a kan kowa dake gaban ki ga yanzu sun san da sani ke din yar bawaice kinga dole ko su nuna hassadan hakan gareki
Yanzu kinga mayar da kayan nan kafin gari ya waye wani ya shigo dakin nan yasan abinda kikai kokarin aikatawa har makiyan naki suji suyi maki dariya.
Hjy Abujan ne da za a koma ban son zuwa gara dai in tafi tun muna nan kusa da gida.
Yar nan ashe haka kike da gardaman banza ko dai kin san inda Jafarin din yake ne ?
Hakan data fada yasani fadi wallahi hjy babu komai a tsakanin mu ban san komai ba game dashi.
To wanan tafiyan da zakiyi ne zai sa a kara zargin ki a dauka kun hada baki dashine kan ki gudu hakan kuma na iya jefa iyayyen ki dake a cikin wani mawuyaci hali.
Kallon ta nayi da mamaki tace kwarai kin dai san iyami na da halin da zata sa a daure kowa naki a kasan nan ko.
Tsoron maganan da hjy ta fada ya kamani sai na kara fashewa da wani irin kuka tace kinga ki shiru kin san yanzu darene kada wani yajiyo mu a waje.
Na maki alkawari muddin ina raye zan tsaya maku har burin ku yaci ka duk da naga kin sare kin ji tsoron barazanan uwar taku har kina fadin shine ya tsara hakan.
Da sauri nace wallahi hjy ban san komai ba a kan zancen nan ni dai kawai komai da yace nayi a wurin nayi.
Da haka har ta shawo kaina muna dan hira kafin ta mike ta shiga ban daki ta dauro alwala tana fitowa nima na shiga don