Showing 78001 words to 81000 words out of 191310 words
Chapter 27 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
fara ratsa kunnuwana.
Na fada maki tun gida wanan wuri akwai yan uwan mahaifina akwai na mahaifiyan mu kin sa wasu wasu baki sansu ba.
Don haka duk abinda wani ko wata zasu fada maki iyakarsu dake murmushi kada ki yarda ki wani abinda zai ba dani a gurin duk yadda nace dake haka zakiyi.
Zanso idan mun zauna zandan rika jan ki da hira ke kuma kina murmushi a cikin wayewa kada ki yarda ki nuna min kauyancin ki a nan.
Idan kinyi abinda nake so kin taimaki rayuwan ki har na yan uwanki nan gaba sai duniya tasan da diya mace ma yace kamar kowa.
Yana fadin haka ya dan yun kura kamar zai tashi daga wurin dai kuma ya dawo ya zauna tare da fadin nasan mami zata bincikeki idan mun dawo gida kice da ita ni kike so idan kuma kin ki ruwan ki wanan duk abinda mami zatayi ki nuna mata ni kike so.
Yana fadin haka ya juya ya bude motar ya jefa kafanshi daya waje tare da juyowa hana fadin ki dakata an fito in bude maki motar aikin ki ya fara daga yanzu ke nan.
A zuciya na amsa cikin damuwa da tsoron me haka ke nufi ke nan ga yanayi ya canza a lokaci guda duk murna da daukin da nakeyi in shiga wurin bukin inga irin kallon da su Rufaida zasu min sai naneme shi na rasa don yadda nake jina kamar wata mara lafiya dani.
Daga haka ya fita a motar ya bani gabana na faduwa don har lokacin na kasa hada maganan shi wuri daya in gane me yake nufi da hakan.
Kayan jikin shi kawai abin kallone don ina kulla yana sha,awan fararen kaya don duk kyau tufafi farin kala zai saka a jikin shi.
Yau ma rigace da wando da ban san ko na wani yarene ba sai yar karamar hula fara mai zagaye a kanshi rigar tana da aninaiya a gaba manya dasu har uku sai wani adon zaiba na manyan zane da akaiwa jikin rigar.
Idan nace wurin taron nan gaba daya ba wanda yakai haduwa banyi karya ba don yadda kyaushi da kayan jikin shi suka kara haska wurin.
Don yayi matukar kyau yau fiye dama kullun ko dan yau adon buki yayi ya kara haskawa haka oho sai na nemi nawa kwalliyan na raina kaina a wurin.
A hankali na fito daga motar tsikar jikina yana wani tashi yarrr daga kaina har zuwa kafana dole badan naso ba muka jera har muna hada kafada a yadda muke tafiyan.
Da sauri na dan jada baya don yadda muka manne mind your self OK ya fada ba tare dako na bayan mu sunji yai magana ba.
Buki bidiri birede wurin ya cika ya batse don tun daga ganin haraban kai ma kasan yau babu kama hannun yaro sai dai muce Allah sa a watse lafiya.
Saida muka dan tsaya a wajen na yan mintina kafin a bude mu shiga kamar an bada sanarwa shigan mu don idanuwan da sukayo kan mu can.
Masha Allah mai sanarwa ya fada kunsan kaduna da izala ko dan gala yana izala kaduna kowa sunna Allah yasa muga Annabi Allahuma amin.
Kamar in shige kasa in nutse dan kunyan abinda mc din ke fada a kanmu da shigowan mu hakan ya kara jawo hankalin kowa gare mu.
Tafiya muke guda guda wanda zai nuna muna inda zamu zauna yana gaba security din shi suna daga bayan mu.
Kwalliyan da gyaran da mai kwalliyan tayi min yasa basuyi saurin gane nice ba kunsan yadda kwaliya yanzu ke canza siffan mutum lokaci daya tundai in an hadu da wace ta iya tsarawa.
Haka muke ta tafiya kafada da kafada har zuwa wanan table da aka tana da don mami da iyalin ta a wurin.
Tunda naga yan gidan na soma kokarin sunkuyar da kaina kasa don nauyi da kunyan su daya kamani lokaci daya saboda kallon mamakin da suke muna gaba dayan su.
A, a, a ya J yau yar mami ne haka ka, , , , hannun daya daga mai yasa jalal ya kasa karasa abinda yai niyar fada sai ya zagaya ya ja min kujera tare da dan nuna min in zauna.
Nakai zaune a hankali godiyana yau ga Allah da baiyini mai garaje ba sai sanyin jikin nawa a yau yaba da kala a wurin.
Saidana zauna ya zagaya ya zauna a dayan kujeran a daidai lokacin da mc ke fadin yanzu dai kujeran hjy iyami ya gama haduwa tare da sanar da shigowa ya Jafar da bayanin ko waye shi da kuma inda yake aikin sa sai kuma ya kara da fadin.
Sai bride to be insha Allah kamar yadda kuke ganin wa yan nan masoya sun shigo muna da haske mai haska gidan kowa a wurin nan.
Ya jafar ya dan rankwafo inda nake yana fadin kinji me mc din nan ya fada game damu ko ?
A dan razane na dan sake murmushi yake na bude bakina da mai kwaliyan nan ta fesa min wasu abubuwa tare da wani sweet na tsotse tun a gida sai hakan yasa bakina fitar da wani kamshi mai ma,ana har yana jin shi a hancin shi lokacin.
Sai ka dauka kai dake kallon mu kaga masoya na asali a wurin yadda muke mami kan imani ya hanata magana da kawar da kai daga garemu.
Ba mami ba har yaran ta da muke zaune gaba dayan su sun kasa boye mamakin su a wurin ;
Hakama sauran kujerun dake kusa dana mami din inda yan uwane da abokan arziki suke zagaye damu a wurin kowa imanin ganin hakan.
Rufaida tunda salma tace waike baki ganeta bane zee ce yar mami fa yarinyar mami dai da muka bari a gida.
Ai bata san lokacin data mike tsaye ba tana fadin kutumar uban nan zeey zeey dai zeey yar aikin mami dai.
Amma wai yaya hakan ya faru dama yarin yar nan haka take ashe ?
Shike nan dama Ruby ta fadi hakan gashiko yanzu hakan ya tabbata muna nan shekara da shekaru muna dakon wahala ashe ?
Yau ga wata yar kauye mara asali da tushe tazo ga banza ta sameshi a saukake a wanan lokacin muka danyi wanan magana Rubby tace ku duba ku gani wallahi soyayya sukeyi ki duba yadda suke nuna kauna a gaban mami.
Kai haba ina wallahi sam sam wallahi ina hakan ba zai taba yuyuwa ba muna zaune wata banza kamar zee tazo ta kwace muna shi.
Tunda kowa wurin nan cikin ku zaman jiran ya zabeta takeyi haka kawai zamu kyale muna kallo wanan yarinyar kauyen ta rushe muna plain din mu.
Humm yazu na yarda da zancen ki Rufaida yarinyar nan matsafiya ce ta sace zuciyar mami yanzun kuma ga wanda ko a zato bamu taba kawo hakan ba a ran mu wai yaya J zai kali wanan banzan yarinyar yar aiki ya kyasa.
Wallahi da sake sam hakan ba zai taba yuyuwa ba kan sai dai inda wata manufa yazo da ita wuri nan wanan kan na yarda kai koma dashine wanan yarinyar ta gama shammatan mu yau.
Da hannu aka kira Nazira daga table din da iyayyen su mata ke zaune ciki harda uwar nazira din dake zaune da matan yayyun ta a wurin.
Tana zuwa ta dan duka dafata matar tayi tana fadin wai wanan yar yar gidan waye a garin ko kuma a kasan nan ?
Wanan mama baki ganeta bane zeey ce yar mami mawa mami hidimar nan muma abinda mukewa magana yanzu ke nan a can.
Mami tace Jafar wai me nake ganine nan haka meke shirin faruwa ne wai haka ta tabaya tana tsure shi da idanu babu ko kakautawa a wurin.
Please mami kada kiyi wani motsi a nan idan mutane yana a kan ku yanzu don Allah mami kibar komai har a koma gida.
Jafar din baiyi magana ba sai murmushi yakeyi yana fadin surprise mami aina fada maki zan baki mamakine da zabina a yau ko ?
Please ya J gaji me ya mamud ya fada ai so a daina wana maganan a nan please Aisha ta fada kanta na duke kamar ba itace ke magana ba.
Daga inda Nuriya ke zaune kusa da mijin ta take fadin wai mamaki a nan kuma aka kare gun yar , , , ,
Hannu mami ta daga mata yasa tayi shiru bata karasa maganan da zata fada ba lokacin taja bakinta tayi shiru.
Koda aka kira mami tashi tayi friends din ta suka mara mata baya sai da ya bari an dan rage muka tashi zuwa wuri mami tayi niyar juyawa tabar wurin kafin mu iso saida wata kawarta ta dan rada mata kada tayi hakan don Allah.
Kudin daya saka min a yar jakan hannuna nima na bude jakkan ina likawa mami din ya dan rada min zakace mudin wasu masoyane na gaske sai ji mami tayi mun rungumeta a lokaci guda.
Masu photo suka shiga daukan mu a cikin karfin hali mami ta rungumomu a jikin ta don kawai ta kawar da hankalin kowa ga zargi komai a wurin kanmu baki daya.
Saidai na ciki na ciki a zuciyar mami don in ma wasa jafar yai mata haka dani wasan yayi yawa haka don hankalinta ba karamin tashi yayi ba da ganin hakan.
Tsoron ya Allah shine kada wanan abin ya zama gaskiya ga jafar don zuwa yazun bataga alaman wasa a idanun dan nata ba yau.
Daga inda nake na dan dago ido na saci kallon mami din dake tsaye suna magana da wata kallon da taimin yasani jin wani irin ba dadi a raina.
Haka yasa na fara shan jinin jikina gabana sai faduwa yake uku uku riko hannuna naji anyi daga bayana yasa na dago da sauri yayane dan rankwafo yana rada min zaki gaisa da abokainane gasu can .
A haka muka bar wurin yana rike da hannu na har inda ya barsu kai maginet wanan irin zabin naka a ina kashiga kasan nan ka samon wanan pretty girl din.
Suka shiga wasa shi duk su ukun yana tsaye kimkam ko murmushi baiyi kamar an tsayar dashi a wurin dole.
Muryan wani daga cikin su ke fadin dole mc ya bamu fili mu gwadawa duniya farin cikin mu da zabin ka.
Bai tsaya jirab komai ba ya nufi wurin mc tun kan ma ya dawo inda muke mc yasa muna wakan tare da sanarwa zamu fito fili abokan JM nason su nuna mai farin cikin su da wanan ranan.
Ance ana buki da dollars ranan koda bansan darajan kudin ba nasan masu daraja ne wanan kudin yadda wurin ya dauki ihu ga baki daya ya jafar yana rike dani da hannu daya.
Dayan hannun kuma yana cikin aljihun wandonshi muke takawa a hankali sai photuna ake zuba mana babu kama hannun yaro.
Sai daya gaji yaja hannuna ko ya fahinci ina gab da bashi kunyane don kiris ya rage in duka in cire takalmin dake kafana kada in fadi.
Daurewa kawai nakeyi a hakan sai gashi yaja hannuna mu fita daga hilin wasa bama nan ba kawai gaba daya dakin taron muka bari lokaci guda security dinshi na biye damu duk inda muka saka kafan mu a wurin.
Maroka suka sakashi gaba yana rike da hannu na har muka fice daga dakin yayin da suka dan sarara muna ke nan.
Wani iska mai sanyi naji ya dokeni sai da nayi wani irin ajiyan zuciya kamar an gafarta min a wurin.
Mota muka shiga ba wanda yai magana a cikin to nima me zance nida nawa umurni kuma in aiwatar don dole na.
Sai da muka shigo unguwar ne ko ina yayi tsit alaman dai dare yayi sosai a lokacin duk mutane sun shige gidajen su.
Mota na tsaye kofan gidan mami din ana jiran maigadi da akewa horn ya bude get din gidan naji yana fadin kin taka matakin farko a cikin shirin mu.
Yanzu saiki shirya mataki na gaba shine amsa tambayan mami a gareki kaina na fada maki abu daya nake so dake shine.
Idan mami ta tambaye ki a kaina ki fada mata nine nace ina son ki nasan zata tambayeki ke kina sona ko bakya sona ?
Kada ki manta da amsan dana fada maki dazun ki basu idan sun maki wanan tambayan.
Kai na gyada don ba bakin bashi amsa don duk a cikkn fargaban abinda zai faru idan mami ta dawo nake yi.
A kofan shiga gidan ma mun dan jima ana buga kofan kafin lami ta bude mana daga ciki don su aka bari jiran gida dakuma hjy dake dakina.
Har dakin ya kaini tsohuwar na zaune saman sallaya taji shigowan mu take fadin a, a har kun dawo ke nan eeh gatanan na dawo maki da ita ya fada yana wucewa bai yarda ya tsaya a dakin ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
2️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
UBANGIJI ALLAH KA KAREMU DAGA SABA MAKA TAKO WANI HANYA A RAYUWAN MU ALLAHUMA AMIN, , , ,
Gaba na faduwa ina tsaye ban iya gusawa a inda nake ba tunda ya bar dakin jin muryan hjy ce data juyo gareni tana fadin.
Yar nan lafiya kuwa hawaye ne yazo min lokaci daya nayi karfin halin girgiza mata kai ina daga kafa da kyat nace ba komai hjy.
A cikin karfin hali na karasa cikin dakin ina kokarin aje jakkar dake hannuna da naji ya kara min nauyi a wurin.
Bandaki na nufa tukun na fara sake fitsarin tsoro daya taru mi a mara na dan dade tsugune ina sake shi kamar ba zai tsaya ba lokacin.
Na dade a zaune ina tunane kafin in samu inyi tsarki in fito daga bandakin duk jikina a sabule har lokacin yau kan nasan na taro mach a gidan mami wanda mai fitar dani sai Allah.
Ni da wani ido zan kalli mami dashi wai yau ni zainab yar aikin ta ke ikirarin zama sarakuwar mami a duniya.
Ni zainabu wani hali da rikici na jefa kaina a ciki aikin dana sani daga baya ke nan yake zuwa don nayi dana sanin yarjewa yaya Jafar bukatan shi yafi sau dubu a wurin.
A gurguje na shiga dakin mami a cikin daren nan don daya saura na dare a lokacin na gyara ko ina na dakin ban tsaya ba don kada mami ta riskeni a ciki na jawo kofan ina dawo na haye kujera dama na cire kayan jikina tun kan in shiga dakin mami din.
Tundana kwanta ba dunkule a cikin hijabina ban yarda nayi ko motsiba wurin.
Ina jin hjy na magana tana fadin su a can zasu kwanane har wanan lokacin basu dawo ba haka.
Shiru nayi kamar ina barci haka yasa ta kyaleni sai can na fara jin hayaniyan mutane a gidan alaman an fara dawowa ke nan daga dinner din.
Can aka turo kofan dakin da karfi ana kiran sunana muryan Aisha ce sai naji hjy na fadin yau naga sha shanci a gidan nan.
Zaki turo kofa haka babu sallama to boyar taku tayi barci tunda yaron nan ya dawo da ita don da alaman a gajiye takema ko da ta shigo.
Mami ke kiran ta yanzun nan a dakin ta ta fada a cikin wani murya da ban santa dashi ba sai ranan.
Kada ki soma ki tada yar nan daga barcin nan kije ki fadawa uwar taku tayi barci tun dazun inji ni haba kowa fa rai gare shi kamar kowa ace mutum ba zai huta ba haka dare ai mahutane ta fada cikin bacin rai.
Ina jin lokacin data rufo kofan hakan yasa nasan ta tafi na sauke wani iri ajiyan zuciya daga kwancen hjy taci gaba da fada ita kadai a dakin.
Sai muryan sallaman mami tana fadin hjy ashe baki barci ba ina zanyi barci kuna waje har wanan lokacin iyami.
Ki duba lokaci fa karfe nawa yanzu zaku biyewa shedanu kukai lokacin nan a waje dare fa mahutun muminine don a daren yake raya rayuwan shi walau ta hanyar barci ko na samun ganawa da ubangijin shi a natse.
Wallahi hjy taron ne ba, a fara da wuri ba tana magana hankalinta na inda nake kwance zata tayar dani .
Yar nan tayi barci tun dazun haba ku rika sauwaka mata hakana tana iya kokarin ta gidan nan yanzu sha shan yarki ta shigo tayar da ita.
Koma me zatayi ita Aishan tai maki mana baku bari yaron ya samu albarka a wurin ku saboda karyan zamani har yaushe kamar Aisha za ace ba zata iya aikin da wanan yar zata iya maki ba.
Ba aiki zatai min