Showing 54001 words to 57000 words out of 191310 words
Chapter 19 - ABU CIKIN DUHU BY MAKAWA By abooks.com.ng.txt
mami ta sauke ajiyan zuciya ta fara magana.
Da farko ke Nuriya a kanki zan fara don ba zan tsaya kina fada min magana cikin rashin mutunci a gaban diyana ba haka.
Don dan kuka shike jawa uwar shi jifa, sai dai kinci albarkacin darajan abu biyu da kike ci gareni har kullun a wurina.
Shine auren dana da kuma kasancewar ki uwar jikokina a yanzu wanan damar kike ci har kullun a wurina don ba zan so saka matar dana a gaba idan ba haka ba ke kinsan wani abin ko ance kiyi min shi ba zakiyi shi ba duk da kudin da kike takama iyayyen
Sai yaya mamud ya dukar da kanshi don ya gane me mami take nufi da maganan ta saboda halin Nuriya a ku)un magana ya taso itace bata da gaskiya.
Mami taci gaba da fadin saidai zanso ki gane cewa ba zan lamunci aibanta mi diya ba ko zargi su a kan zina.
Mami ni kar,a laka min abinda ban fada ba fa a nan don kawai ana jin zafina kowa ya taso sai yace banyi daidai ba .
Don hakane nake nisantar kowa a gidan nan hakan baiyi ba har sai wani ya takaleni kuma inyi magana ace banyi daidai ba.
Yanzun wanan mara galihun tafini daraja da kima a wurin ku ake nufi tunda itace mai gaskiya ke nan don kawai taimin ba daidai ba na hukuntata.
Who are Nuriya who are you by the way har kina wani fadin tayi maki laifi kin hukuntata akanahi ke kika dauketa aiki a gidan nan ko wurin ki take.
Ke ba zaki iya yin aiki ba ki zauna da masu aiki kuma kin hana hakan saboda bakin kishin dake damun ki.
Mikewa tayi tana fadin na hana ka dauki yar aiki mamud don ban so kai din ban yarda da kaiba da har zan dauko wata yar aikican in aje wurina.
Daga yau na hana kowa saka wanan yarinyar aiki ko taba lafiyan jikinta wallahi wallahi ko yaya nake da mutum a gidan nan ranan zai hadu da fushina.
Wanan yazama na farko na karshe a gidan nan da wani zai kara taba lafiyan wani zainab yace kamar kowan ku nan dan haka a bani guri ban son wani magana kuma daga yau.
Tana fadin haka ta mike zuwa dakin ta a fusace yayin da nake durkushe a gefe kujera tafiyan mami Nuriya ta mike tana fadin wallahi mu zuba da kowa a gidan nan kan wanan yar iskan kowa ya tabani tabashi zanyi.
Binta da kallo sukayi kafin su dawo da kallon su gareni inda nake rakube ina hawaye don tashin hankali dana gani ranan.
Da hannu ya nuna min hanya na mike simi simi na basu wuri yaya mamud ne ya kawar da shirun da fadin.
Ni Nuriya zata watsawa kasa a ido haka kwata kwata banji dadin zaman mu da ita kullun a cikin fitina muke.
Yau ma nasan haushi fadan da nayi mata na gyaran wuri ne ta sauke akan yar mutane haka.
Bai bari dan uwan ya gama zancen shi ba ya mike zuwa dakin mahaifiyar su data shige ranta a bace ya sameta dakin.
Shiko yaya mamud yaci gaba da fada da matar shi ranshi a bace yake fadin.
Ya mike yana fadin nasan maganin yar iska ai bazata zan mata a gidan nan sai ta gane bata da wayau.
Saidaya shige jalal ke fadin kamar da gaske din zai iya hakan yanzu kila hakkuri zaije ya bata.
Suma mikewa sukayi zuwa dakin mahaifiyar tasu suka samesu a nan suna wani hira da dan lelen nata a gurin.
Karfe biyar na bar dakina zuwa na mami don gyarawa ita kadai na samu a dakin da sallama na shigo dakin na duka har kasa ina gaida ita kafin in dago don fara aikin dakin.
Kinsha maganin dana aika akai maki dazun take tambayana nasha mami na fada ina wasa da yan yatsun hannuna a hankali.
Kamar zata sake magana sai kuma tayi shiru taci gaba da duban takardan dake hannun ta ko ina na dakin saidana gyara kafin in fito dakin kusa magariba yayi nan na samu matar da aka dauka don shara tazo ta fara aikin ta .
Don faruwan avi mami tasa a kawo mata yar aiki wanan mai sharan bahaushiyace ita don ina gaida ita take amsawa naji hausanta na gane ita din bahauace ba kamar matan nan biyu gwarawa masu girki bane.
Tun ranan shakuwa ya shiga tsakanin mu da matar da ake kira da hannatu yar ktsinawa irin matan nan ne da suka dade da fitowa bariki don har sigari take sha a boye.
Nima dai rabon in gan tane a cikinyanayin yasa na rutsa da ita can bayan daki ta labe tana shan abinta na juya da sauri zan koma naji tana fadin a cikin kokarin kashe tabar da sauri yar hjy kamar yadda take kirana dashi.
Ina nan ina wanan jarabar tsiyar da muka sawa kanmu ina dai ba zaki fadawa kowa ba halin da kika sameni wanan zancen.
Da sauri na girgiza kai tare da fadin indai nice babu maijin wanan a abakina insha Allahu ina kokatin wucewa don natsani warin taba a rayuwana.
Duk dan dakata min inzo har lokaci bata yarda dani don ta fahinci jikina yana rawa a lokacin.
Ina kallo ta ballo goro daga haban zanin ta tura baki tana taunawa ta kakabe zanin inda ta zauna a kasa tana fadin wanan abin ya zama muna jaraba a rayuwa.
Kinsan a zamani mu idan budurwa takai budurwa har bata shan sigari to bata cika wayayyan mace ba ke nan.
Tun wanan lokacin mula koyi wanan cacan kashi kudin don ko nairan ka ta karshe ke nan sai ka fitar kaya zakaji dadi.
Ni dai a kage nake na bar wurin nake fadin dama ban ganki bane a cikin gida sai nayi tunanen ko kina nan shine na biyo ki.
Yo ai ina nan kedai jarabarce ta motso min shine nazo indan rage zafi kai.
A tare muka jera zuwa cikin gidan idon ta mirsisi kamar bata sha komai ba taci gaba da sha,aninta
Cikin sati daya kawai mun saba da hanne wace na lakawa mama hanne nake kiranta da hakan don girmamawa .
Zama da mama hanne yasani cikin farin ciki da walwala sosai don zata zauna tayi hira dani kamar sa, anta nake gun ban iya bata amsa har yakai yazu ina bata zamu zauna tana ban labari ina kwasan dariya.
Da sunan kwana hudu sai gashi mun share wata a abuja lokacin ne mami ta fara shirin ziyaran kaduna.
Wanda gaba dayan mune zamu tafi gidan a yadda naji suna fada mahaifiyar mami ce bata da lafiya shine za a tafi gaida ita.
Shiri sosai mami keyi don zuwa gida nikan nafi kowa murnan hakan kamar ance damun isa zan tafi ancau ne ranan.
Ni kan na dauka yaya Jafar ya koma inda ya fito ne ashe wai tafiya sukayi tare da su jamal sai kwatsam gasu sun dawo ana saura kwana daya mu tafi kaduna.
Mama hanne kan tunda tayi arba dashi tasha jinin jikin ta a zaton ta wai yanayin sa yai kama dana yasanda tunma dataga security din shi ta kara tsurewa da al,amadin shi.
Take tambayana nake fada mata dan mami ne amma ni ban san aiki da yakeyi ba, ta sake fadan mutum.haka ba yar dariyan nan ko fara,a a fuskanshi.
Dariya sosai nayi har ina dukawa a inda nake zaune sai kamshin turaren shi mukaji lokaci guda.
Key din shi yake miko min ba tare da yayi magana ba, amma na gane me yake nufi dakin shi yake so a gyara mai ke nan.
Yana miko min ya juya ya futa a cikin wani irin tako na mazan zamani da suka suka san ta kan duniya sosai yake tafiyan.
Ban tsaya jiran komai ba na mike don cika umurni duk da mami ta hana inyiwa kowa wani aiki ita da kanta takan umurceni da inje in gyara mai dakin nasa.
Tura kofan nayi na shiga dakin da sallama duk da nasan ba kowa a daKin hakan bai hanani inyi sallama ba.
Idonane ya fara arba da wani kwalba dake aje saman table din dakin nasa ga abin cikin sa an zuba a kofi ansha an aje rabi.
Da mamaki nake kallon abin don ban taba ganin kwalban abin sha irin sa ba nidai na fara kawar da takardun dana gani a saman wani table naji an turo kofa da karfi an shigo dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
🦅 ABU CIKIN DUHU 🦅
1️⃣7️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YA ALLAH KA GAFARATA MUNA ZUNUBBAN KABA MU IKON AIKATA ALHERI A RAYUWAN MU DUNIYA DA LAHIRA AMIN.
DO MIN SAMUN LITTAFIN NAN CIKKAKE ZAKI IYA TURA DARI UKU TA WANAN ACC 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN MTN NA DARI UKU KACAL NAGODE UBANGIJI YA HORE YA BADA IKON BIYA ALLAHUMA AMIN ALLAH, , , ,
Idona a kan abin ina dan juyawa a cikin kofi naji wanan tsawan daya daka min sai da hanjin cikina ya kada don tsoro lokaci guda.
Allah ya gyara ban sale cup din ba ya shigo ya karbi abinsa yana mai bina da wani kallo mai kamar na tsana.
Wayace ki taba min wanan ya fada rai bace kamar da gangan na taba mashi abin bashi ya turoni dakin in gyara ba.
Dan marairaicewa nayi ya karbi abin shi zuwa daki sai gashi ya fito da cup din ban san inda ya juye abin ba.
Fita yayi daga dakin ba tare da yayi min magana ba hakan ya bani daman yin aikin a tsanake.
A gurguje na gyara komai duk da hakan dakin ya gyaru da kyau na kulle masa na fito na kai key din dakin mami.
Nikan don doki har na shirya kayana tafiya kawai nake jira washe gari na zata tun safe zamu wuce sai naga sabanin hakan.
Saida yamma bayan la,asar muka bargidan zuwa filin jirgin ashe da jirgi zamuyi tafiyan kuma.
Karfe shidda na yamma duk muna gida a lokacin har na bude dakin mami ina gyara don tun tafiyan ta dakin a rufe yake.
Sai yau da muka dawone ta miko min key na bude duk da a gyare muka barshi da zamu tafi hakan bai hana yadan yi kuraba.
Na gyara har bathroom na fito zuwa dakina shima na gyaro na shiga wanka dongon riga silk mai adon kamfala ne na dauko daga cikin kayab da anty Aisha ta bani na saka.
Saida nayi sallah har isha,i na fito falon don yunwa da nake ji lokacin in samu abinda zanci a cikina.
Suma mutanen gidan gaba daya a falo na same su saman dining suna cin abinci mami da yaranta maza su hudu sai yan matan mami din gaba dayan su har anty Aisha.
Simi simi na fito na zo diban abincin wasun su suka kuro min ido hannuna rawa na dibi abincin ina jin mami tana waya tana fadin muna kaduna yanzun haka.
Insha Allahu da safe zamu shigo Igabin naji tana fadi haka yasa na san zasuyi tafiya washe gari saidai ban san ko dani bane.
Diban abincin na juya zan wuce naji muryan yaya Jafar na fadin ke saida hanjin cikina ya kada don jin muryan shi saidai ban tabbatar ba ko dani yake don kaina na duke na basu baya.
Na kara takawa gabana na mumunan faduwa da ban san dalilin haka ba duk lokacin danaji muryan yaya jafar din duk da ina tsron kowa a gidan saidai nashi yafi yawa a zuciyana.
Ko dan ganin kowa ma yana shakarshi ne a gidan don tsare gida irin nasa .
Haka naci gaba da takawa cikin karfin halin zan tafi dakina inda na saba zama inci abinci hankali kwance zuciyana cike da addua nake tafiya.
Ya sake fadin come and join us ina zaki da abinci ga kowa nan a zaune hakan yasa nasan lalai dani yake magana na juyo a hankali.
Yana rike da cibin abinci da yake ci a hannun shi ya rike baikai a baki ba gabana na faduwa yace.
Daga yau a nan zaki rika cin abinci tare da kowa kinji abindana fada maki yana nuna min kujera da hannun shi .
Kai na gyada mai, tare da nufar gurin kujeran dake saiti da inda yake zaune babu kowa saman kujeran na zauna.
Idanuwan yan matan gidan duk a kaina bama su kadai ba har mami dake waya a lokacin idonta yana kaina.
Ko ban daga kaiba nasan akwai idon dake kallona a lokacin don jikina ya bani hakan ba ido daya ba ba biyu ba kodana dago kai duk idanuwan su na a kaina suna kai cibin abinci a bakin su.
Tundana zauna ya maida hankali gun abincin dake gaban shi hankali kwance yake kai cibi a bakin shi a hankali .
Daga mami har ya matan dama su jamal suka dago ido a sukwane suna kallon shi shiko ko a jikin shi.
Sai juya cibin dake hannuna nakeyi na kasa sakin jiki inci abincin yadda ya kamata a wurin.
Yadda kika san guba haka nake hadiyan abincin ba wai don baya da dadi ba don hadine na musanman akayi don zuwan su yau din su mama kande suka girka abincin mai rai da lafiya.
Mikewa yayi tsam mami tace har ka gama cin abincin ke nan ko rabin plate fa baka ci ba ba tare daya juyo ba yace mami iam ok zanje na kwantane.
Allah tashe mu lafiya mami tace yace amin yana tafiya sai jalal yace but yaya security dinka za a fada masu sutafi ke nan tunda ka shige ko ?
Na sallamesu tunda muka fito massalaci dazun idan sun gama zasu tafi ya bashi amsa yana tafiya da dan sauri kamar mai uzuri.
Mami ma bata dade ba wurin ta mike tabar falon sai mazan da suma suka mike lokaci daya falin ya rage mu kaida a ciki.
Duk lokacin danayi yunkurin dago ido sai in samu ana aika min da wani irin mugun kallo da tsana dan dama salma da Aisha su ba kallon tsana bane saidai kallone mai kama dana mamaki lokacin.
Amma dai yarinyar nan kina da sa, a yau kece yaya hero ke ba umurnin zama a saman table kici abinci tare da kowa a gidan nan.
Ke ko ba dole ba tunda ta iya makirci kamar ta mutu ta mairaraice ita gata Allah ba dole ta bashi tausayi ba Nazira ta fada
To kodai kin zauna a cikin mu ba a dai taba canza maki suna daga zainab yar aikin mami zuwa diyar gidan nan kamar kowa Rufaida a fada .
A, a, za a yi kiranta ki da yar gida mana duba yarda yan kwanakin nan gaba daya tayi fresh da ita haka duk sai suka kalloni lokaci daya.
Nagaji da cin fuska na mike don barin wurin, dama abincin ya fita min rai lokaci daya na dauki plate din zuwa kitchen.
Ina ruwan ba saban ba yau har wanan ce zata bar abinci haka bataci don samun wuri.
Ban kara fitowa dakin ba don na gamawa mami komai itama nasan ta gaji ta kwanta tunda akwai tafiya garesu washegari.
Nasan da zancen tafiyan mami don naji tana waya kan tafiyan yasa na tashi da wuri na nufi dakin ta koda abinda zata sakani a lokacin.
Aikuwa iba shiga dakin na samu ta fito daga wanka saida nayi mamakin hakan don bata ko tsaya jira inzo in wanke bandakin ba ta shiga.
Gaisheta nayi na nufi bandakin har ta karasa shirinta na dawo na fara gyara don ko kadan ban kawo dani za a tafi tafiyan ba don banga alaman hakan ba.
Hankali kwance nake aikina ina shiryawa maki kaya kamar yadda ta umurceni inyi mata anty Aisha ta shigo dakin tana gaida mahaifiyar nasu.
Bayan dun gaisa mami ke fadin ina fatan kin shirya dai don banson bata lokaci ga tafiya kin sani dai.
Mami wani shiri zanyi kauyefa zamu tafi banga abinda zan shirya bani ko haka zan iya tafiya ai ta fada cikin zolaya.
Mami tace da ita ai kauye garine don akawai yan Adam a ciki na dauka dai daji zaki tafi ai ta kwashe da dariya don tasan ta tabo mami din .
Gaba dayan mu zamu tafine mami ta tambaya tana kallon mahaiyar nata lokacin da ni kuma nake masu dan murshi don jin amsan da mami din ta bata.
Naji mami tace eh dake da yan uwanki maza ba na fadawa kowa tunjiya don kada yau su kawo min wani zance na daban.
Hae su Nazima ta sake tambayan mahaifiyar