Showing 1 words to 3000 words out of 74305 words
Chapter 1 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
*Dr HANEEFAH* 👩🏼1
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Bismillahir-rahmanir-rahim
Darasi ake musu amma hankalinta baya kan abinda ake koyarwa musu, zubawa malamin idanu tayi kamar mai fahimtar abinda ake. Qararrawa aka kada domin canza malami fitarsa ke da wuya itama ta tashi domin bin bayansa nan take hadiza da ta lura da yanayin da tashiga tabita a baya.
Nesa da ajinnasu tayi sannan ta samu wani lungu ta tsaya, hawayene kebin kuncinta sai taji an dafata kafadarta. Ganin hadiza yasa ta fashe da kuka sosai tare da sulalewa ta zauna kan wani dutse, kuka take sosai hadiza bata ce da ita komai ba, ganin ta saida kuka da kanta hadiza tace haba haneefah duk abinda ya faru hakuri zakiyi tare da cigaba da addu'a yariga ya wuce kuka da damuwa bazai zamto solution ba, murmushin takaici haneefah tayi taga aminiyar tata tace hadiza ba lamarin nazir ke damuna ba nasan ina sonshi ya yaudareni yayi aure lamarin abbanane har yanzu bansan me zan mishi na birgeshi ba, sun hadani da abbana kullum cikin ganin laifina yake bansan mezanyi in wanke kaina ba, cike da tausayi hadiza tace kada ki damu Allah na tare take duk daren dadewa gaskiya zata bayyana, abinda nake so dake ki kwantar da hankalinki, ki dage da karatu insha Allah wata tana sai labari da irin wannan kalamai hadiza ta rika kwantar mata da hankali suka koma aji.
Alhaji hamisu shine mahaifin haneefah sannan umma salamatu itace mahaifiyar haneefah. Haifaffun garin kano ne,Yana da mata biyu hajiya hafsa(inna) da salamatu (umma). Inna yaranta takwas biyar mata uku maza salim shine danta na farko, bilkisu, zainab, jibril, zuwaira, Ibrahim, shukra da sadiya sannan yaran umma Nana khadija itace babbar yarta sai ahmad, haneefah da kannenta biyu amal da bintu.
Alhaji hamisu adaline tsakanin matansa da yaransa yanada rufin asiri daidai gwargodo domin ma'aikacin gwamnatine, bayi da buri kamar yaga yayanshi sunyi karatu badon su zama wani abuba, domin duniyar yanzu karatu nada muhimmanci arayuwar dan adam.
Inna ta daurewa yaranta gindi wajen yin abinda suka ga dama shiyasa sam basu aje hankalinsu wajen yin karatu ba kullum cikin bin yan mata suke matan ko dakyar suka qarasa karatunsu na sakandari aka aurar dasu sai kannensu qanana shukra da sadiya haka yan maxan karatu yaga garesu suka nuna aure suke so aka aurar dasu banda ibrahim. Akullum alhaji hamisu yana takaicin halin yaransa domin shi mutum ne mai son karatu domin yasan muhimmancin sa amma babu yadda zayyi tunda haka suka ga yafi musu.
Itako umma ma'aikaciyace, macen kirki marason magana sannan takasance ta tashi tsaye kan tarbiyyar yaranta da ilminsu hakan yasa take gaban goshi wajen maigidanta, hakan yasa inna kishiyarta ta dauki alwashin sai ta tarwasa su, Allah cikin ikonsa lokacin Alhaji yayi retired, rayuwa yayi halinsa, yau akwai gobe babu hakan yasa yacanza makarantun yayanshi izuwa na gomnati.
Umma su biyune gun mahaifan su, yayarta hajiya lubna. Tun suna qanana Allah yayiwa haifinsu rasuwa mahaifiyarsu ta dauki dawainiyar karatunsu har lubna ta kammala ta samu miji tayi aure, yanema mata aiki a ma'aikatar ilmi hakan yasa ta samu kwarin gwiwar dauko kanwarta taci gaba da karatu ta kammala har tasamu miji tayi aure. Lubna yaranta bakwai hudu maza auwal, sadiq, musa, khalifa uku mata muhibbat, humaira da amina. Auwal, muhibbat da humaira suna da aure da yaransu. Duk dukiyar da Allah ya azurtasu hakan baisa sun sangarceba, duk sun kasance yara masu tarbiyya. Sannan burin umma da mama suga kan zuri'arsu a hade. Cikin ikon Allah sun girma suna kaunar junansu.
Haneefah yar shekaru 17 aduniya yarinyace mai biyayya da hankali, sannan takasance yarinya mai barkwanci, bata son raini sannan bata kaunar ta rainamutane, saurin fushi gareta ga saurin hucewa sannan yarinyace mai tsananin bincike kan abinda tasa gaba, ga ilmi. Yarince mai son kwalliya tare da yin duk wani gyara na diya mace, tana matukar son abubuwa daya shafi mata, sannan ita ba kyakykyawa bace ba mummuna bace JININ KYAU GARETA domin ta iya kwalliya. Haneefah itace yar gaban goshi gun mahaifiyarta da yan uwanta suna matukar ji da ita, hakan yasa bata da tamkarsu kullum burinta son faranta musu da wuya kaga sun samu sabani tsakaninta da su domin burinta kullum su hade kai. Yarinyace mai saurin shiga rai duk inda ta zauna tana dibar jama'a saboda yawan fara'arta, hakan da inna ta fahimta shine ta dada karkatar da hankalinta ga haneefah domin lalata mata rayuwa.
Kishi sosai inna da yaranta suke nunawa umma, duk da haka umma bata bi takanta ba saida taga sun fara shiga rayuwar yaranta ta soma taka musu birki, duk da haka saida tayi nasarar bata sunan haneefah gun abbanta. Haneefah komai tayi baya birge abbanta hakan yana damunta ga yan uba sai wahalar da ita suke, duk da wani lokaci ba raga musu take ba shakkanta suke.
A haka ta soma soyayya da wani matashin yaro mai suna nazir, tana sonshi sosai domin ya hadu iya haduwa. Tana matukar sonshi domin irin mutananne da basu iya so ba, akarshe ya auri wata duk da abin nadamunta kawai ta watsar dashi tare alkawarin bazata qara yarda da wani namijin ba... Amma burinta gyara tsakaninta da abbanta
*Dr HANEEFAH* 👩🏼2
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Gidane babba amma an rabawa kowa mashiganshi tun daga bakin gate. An taso daga makaranata ta hade kan kannenta suna tahowa tare dashike tsakaninsu da makaranta babu nisa, dai dai sunzo shiga gida taga yaya jabir da abokinsa suna tsaye idanu sunyi jajaye, daganinsu kwayoyi suke sha ta girgiza kai cikin takaici tare da cewa Allah shiryeku tayi nasu gidan su shukra ma suka shige.
Bayan shiganta sahabi yadubi abokinsa jabir yace aboki ya maganar haneefah saifa shareni kake da zarar na kawo maganarta cike da maye jabir yace ai dama so nake ta kammala makarantarta tunda yanzu tana ss3 amma tunda ka matsa ku daidaita tsakaninku inyaso agudanar da biki inta kammala cike da zumudi sahabi yace to shikenan nagode. Zai juya ya tafi jabir yace anjima ka dawo daga zarar an idar da sallan magriba, yace zan dawo daukeda murmushin mugunta jabir ya shige nasu gidan.
Agajiye tashigo gida bayan sun taso daga islamiyya ta tarar da yayarta a kitchen tana girki tace sannu Dr da aiki yau baki dawo gida da wuri ba, tace bari kawai yau muka fara fita asibiti shine kumayi yamma inaga kullum haka zan kasance, haneefah tace tab yanzu a asibitin zaki iya wuni wlh nikam bazan iyaba, cike da zolaya tace toh accounter haneefah, ta hada girar sama da kasa tace bayan kunce sai dai na zamo Dr, to wai dukka zamu hadu a fanni daya ayyakamata mu karanta abu daban-daban cike da murmushi nana tace zamu karanta health line amma fannin kowa daban kinga..... Tun kafin ta karasa takatseta tace nidai bazanyi ba yadda nake burin accounter zanyi ko banyi ba.... ta gyada kai tashige ciki nana namata dariya.
Bayan ta idar da sallah tana lazimi amal tashigo tace ana sallama dake a wace, tayi mata nuni data tsaya ta kusa kammalawa, bayan minti biyu tayi fatiya cike da tsoro tace waye? Abokin yaya jabir cike da mamaki. Sallama tayi ya amsa cike da murna yace nasan zakiyi mamakin ganina amma ba abin mamaki bane, inasonki kuma da niyyar aure nazo bude baki zatayi magana taji an bude gate, kallon da taga abbanta nayi mata ne yasa hankalinta ya dada tashi bai ce da ita komai ba yayi wucewarsa cike da bakin ciki tace wlh kaci sa'a, ko kunya bakaji ba wai kana sona? Toh wlh nakuma ganin kafarka cikin gidannan ta kyada kai ta wuce.
Zama tayi bakin gado ta rasa mezatayi, tunani kala-kala yanzu kuma wani hukunci za'a yanke mata? Cikin wannan hali nana tazo ta tarar da ita tace haneefah yau meya faru? Me kika gani? Yanzu nakaiwa abba abinci yake surutu yaushe zaki gyaru, imma auren kikeso kituro amma shiya fita hakkin ki wajen ganar dake, har dan shaye shaye kika kawo masa gida ransa ya baci sosai, nasan bazaki aikata haka ba sai dai turosa akai, nan take haneefah ta dago kai idanunta cike da hawaye, murmushi tayi tace ba komai Allah na tare dani, cike da tausayi yar'uwar tata tace kada ki damu zaizo yagane gaskiya cike da bacin rai haneefah tace yaushe? Tun na taso yataba saurarona? Komi aka fada mishi daukawa yake, yazama dole in masa biyayya da zan entar da kaina damuwar da nake ciki.
Tunda ta fara magana ta kafa mata idanu, tabbas tananuwa haneefah so amma tana tare da kyakykyawar tarbiyya data bata bazata iya aikata irin wadannan abubuwan ba. Taqaraso ciki ta zauna kusa da haneefah tace in fada miki mafita? Tace eh umma zanyi, umma tace toh yazamto mai biyayya gareshi tare da kusanto farin cikin shi ko da ke zai baqanta miki rai, kinsan farin cikin sa yaga kuna karatu sosai, inaso ki kwantar da hankalinki kiyi karatu sosai domin fita da saka mako maikyau sannan ki hada kanki da yan uwanki duk da su ba hakan take agun suba, sannan ki dage da addu'a sosai kan Allah yaraba ki dashi lfy last one shine ki daina damun kanki, ki kawar da kanki kinji? Ta rungume ummanta insha Allah zanyi ta shafa kanta that's my haneefah.
Tun daga wannan rana haneefah ta kudurci aniyar yin karatu, ta tattare hankalinta gurin kararu tare da dagewa da addu'a. Ta fita harkansu inna duk da dama ita ba shiga tsabgarsu take ba.
*** *** *** ***
Kwanci tashi ba wuya cikin nasara haneefah ta zana jarabawarta na SSCE kuma ta fito da saka mako mai kyau cike da farin ciki ta nunawa mahaifinta shima ya yaba mata sannan ta ce tana da ra'ayin tafiya nursing ganin yadda ta dage yasa shi farin ciki tare da yi mata alkawarin zai nema mata. Ranar haneefah tayi farin ciki ganin mahaifinta na farin ciki haka yan uwanta suma sun taya ta.
Alhamdulillah ta fara ganin sassauci gun mahaifinta kuma cikin ikon Allah ta samu admission a nursing, tare da kawarta hadiza. Farin ciki ba'a magana gun haneefah, kowa ja mata kunne yake akan tayi karatu cike dajin dadi tace da yan uwanta duk abinda kukeso ina so bazan baku kunya ba.
Hakan ko akayi, hadiza da haneefah an dage basu dauki sabbin kawaye ba domin sun aminta da juna sosai dukkaninsu ma'abota son karatune duk da anason kawance dasu amma basu bawa kowa dama ba. Sun tashi daga aminai sun zama yan uwa. Hadiza kyakykyawace sosai domin tafi haneefah da kyau tun suna ss1 hadiza ta aminta da haneefah dakyar ta shawo kanta suka zama aminai, domin haneefah ita kowa natane.
Cikin nasara suka cinye shekara daya da rabi saura daya da rabi sannan a asibiti zasu karasa. Babu matsalar da haneefah ke fuskanta kamar rashin iya turanci sosai, ta iya amma bazata dade tabayin shiba wato kadan-kadan takeji, tana iya karatu sannan ta fahimta amma mayarwane bata iyawa, wannan matsalar na damunta.
*Dr HANEEFAH*👩🏼 3
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Zaune take tana nazarin wasu littattaifa nana tashigo tace sannu da kokari tace yauwa atakaice tace me kike dubawa ne? Tadanja tsaki tace gobe zamu fita asibiti kuma inaga ranar ante-natal (awon cikine) kinsanni da surutu Amma kada abani topic da ban kware akaiba, nana tace inaga za'a baku kuyi takaitaccen jawabi kan awon cikine, mata diyewa in sun fara zuwa awon ciki kalilanne suke kammalawa harsu haihu, hakan ko bashi da kyau sannan da dama basa son shan magani kamar yadda aka kayyade musu hakan na kawo matsala musamman in mace tazo taihuwa, kamata yayi in mace ta lura tana da juna biyu ta rinka ziyarar asibiti ba fashi harta sauka lfy, in munajin kanmu babu matsala bamusan yaushe matsalan zata auku ba bari in takaita miki yadda zaki jawabi
Bayan kinyi sallama tare da tambayarsu kowa lfy saiki soma bayani kamar haka; Zamuyi bayanine akan awon ciki ga wadda bata taba haihuwa ba kuma tana jinta kalau, ya dace tayi gwaje-gwajen da akeyi a awon ciki sannan sume akeyi a awon ciki?
Yana da kyau sosai ko da kalau kike jinki ki je a gwada lafiyarki yayin da kike da juna biyu, musamman ma idan na fari ne. Wannan shi ake kira awo. Bari a yi miki bayani mai dan gamsarwa game da awon. Awo wata hanya ce ta amfani da gwaje-gwaje, domin tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta da kuma gano matsaloli da ke tattare da yanayin juna biyun, don magance su
da wuri tun kafin su zama alakakai. Wato dai hanya ce ta kariya daga galabaita a yayinda ciki
ke girma ba kuma lallai bane a auna kowanne a ziyararki ta farko, a’a yau a duba wannan, wani zuwan a duba wancan. A wasu matan da aka ga juna biyunsu ba shi da hadari sosai, ba lallai ne a
auna komai ba. Ga abubuwan da aka fi aunawa a zayyane: Na farko ana auna tsayin mai ciki domin duk matar da tsayinta ya gaza mita 1.5 tana cikin hadarin yin doguwar nakuda. Don haka sai a sa alama a katinta cewa wannan matar idan ta zo haihuwa a shirya sosai, ko da doguwar nakuda za ta kamata. Sai kuma nauyi, wanda idan ya wuce misali shi ma ana kyautata zaton ko dai mai juna biyu ta iya samun hawan jinni, ko ciwon suga a wannan lokaci na ciki. Domin wasu matan a
lokacin ciki suka fi samun wadannan ciwuka ko da ba su gada ba, kuma yawan nauyin mace kan
sa a fara tunanin hakan. Kamata ya yi mace mai ciki ta rika kara rabin kilo na nauyi a mako guda da zarar ciki ya fara tsufa. Amma idan aka samu nauyin da ya wuce wannan, an san akwai matsala. Sai kuma awon cikin shi kansa. Duk sati ciki ya kamata a ce yana kara kwatankwacin santimita guda, don haka ana aunawa ne a gani ko jariri na girma yadda ya kamata ko kuma a’a. Idan awon ciki bai kai daidai watannin cikin ba, to yaro ba ya girma sosai, kuma akan dauki mataki, idan kuma awon ya wuce yadda ake so to shi ma yana nuna wani abu daban, wato ko dai cikin tagwaye ne, ko jariri na girma fiye da yadda ake so (kamar yaran mata masu ciwon suga), wanda hakan kan jawo doguwar nakuda. Za ta iya kasancewa kuma ruwan da yaron ke ciki ya yi yawa sosai, wanda shi ma alama ce ta illa a jariri. A wannan lokaci akan hada da hoton scanning da zai nuna halin da jariri da mahaifa suke ciki. Na hudu sai a auna bugun jini don a tabbatar ba hawan jini a tare da mai ciki. Idan akwai a ba da magani da sauran shawarwari. Sai kuma a tura mace auna yawan jini. Saboda bukatar da jariri ke da ita na wani kaso na jini, kowace mai ciki sai an duba yawan
jininta a gani ko isasshe ne. Akan ba da magungunan karin jinni, ko ma shi kansa jinin daidai da bukatar matar. Akan ba su shawara su rika yawan cin nama da koren ganye, saboda suna daga cikin abinci masu kara jini sosai (suna dauke da sinadarin iron). Sai kuma a auna yawan suga. Shi ma don a tabbatar matar ba ta da ciwon suga, idan kuma
akwai a fara ba da magunguna. A lura cewa da hawan jinin da ciwon sugan da aka samu a
lokacin ciki za su iya warkewa bayan an haife
cikin, ko kuma su ki warkewa. Sai kuma a ce mai juna biyu ta ce ta yi
fitsari a kwalba, don a gwada sinadaran da ke
cikin fitsari. To a nan ma ana iya gano ko akwai
matsalar ciwon jijjiga ko na suga a jikin matar.
Wadannan su ne muhimman abubuwan da ake aunawa. Ban da tsayi, kusan duk abubuwan da
aka zayyana a sama ba sau kadai ake aunawa
ba, wato kusan duk zuwa sai an sake aunawa saboda lokacin da ciki ke kara tsufa, lokacin
hadarinsa ke kara yawa. Allah baku ikon zuwa ya saukeku lfy
*Dr HANEEFAH*👩🏼 4
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Saiki shirya da amsar tambayoyi domin baza'a rasaba, haneefah dake kallon nana tace yanzu haka mutum zai tayi? Wlh ni bazan iya cigaba da health ba ,innayi gaba canza abuna zanyi. Nana tace kici gaba yar uwa, al'umma na bukatar irinku, ke yarince mai tausayi sannan zaki aje uzurinki domin wasu na tabbata zakiyi taimako, haneefah tace wannan shine dalilin naki? Ayyuka da dama al'umma na bukatar taimaka amma ai lfy yafi koma cewar nana.
Haneefah tace yauwa sis yaushe zamusha bikine Allah duk na kagu kinga kin gama makaranta. Nana tace da saura, abba so yake muyi karatu sosai haneefah tace haba nana ai karatun da kikai is ok, aiki yarage miki fa! Haneefah ina matukar so naga nacikawa mishi buri, in kikai la'akari da yanayin gidannan cikin yaran inna babu wadda karatunsu yayi zurfi, duk da yakasance bayida arziki irin na baya amma yana mana kokari sosai, inason nayi aure kuma umma tanaso amma zan bari ba yanzu ba sai nayi MBBS zaro ido haneefah tayi tace kina da kokari, shine ko kula samari bakyayi? Eh bazan kula kowa ba sai naga komai ya dai-daita.
Ajiyar zuciya haneefah tayi tace haba nana, kin dan samu karatu ai saiki godewa Allah, bakyaga irin yadda kasarmu take ciki? Wace yar talaka kikaji tana MBBS duk yayan masu kudine sannan aure ai baya hana karatu, ina mamkin wasu iyaye da suke dagewa yaransu akan sai sunyi karatu koda sun nuna aure suke so, dayawa yara suke shan wahala wajen danne kudurinsu su faranta ran iyayensu, wai shin karatun boko meyake so ya zamane? Yadda mutane suka dauka muhimmanci suka bashi, zakiga yaron da ya iya turanci yana kokari anfi tarairayarsa amma ba'a kula da na addini ba, yaro daya dace ya taso addininsa yasani amma yafi sanin kan boko, zakiga wasu yara masu shekara 7 basusan banbancin tsakanin wuta da aljannah ba amma an hada suda tv babu abinda basu sani ba. Muyiwa kanmu fada kamata yayi