Showing 24001 words to 27000 words out of 74305 words

Chapter 9 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5172

taji shiru bata dagaba, Dr yace ai yanzu darene kamar anjima zaki same su. Cikin sa'a ya tarar da abokinsa yayi masa jagora suka karbi admission, radiography suka bata. Dr baiso hakan ba amma haneefah tace ita tafison shima sai dai qasar zuciyarta gynecology take so.


An mata komai cikin sa'a , hostel ma sai da ya tabbata dakinsu daya da musulma tukun ya amince. Yadda haneefah taga Dr na mata zirga-zirga yasa ta dauki damarar karatu.


_(Masu karatu bari mu zaga muga halin da yusuf ke ciki)_
*Dr HANEEFAH* 👩🏼27


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Tsayawa yayi gaban yusuf yana kare masa kallo, yadda ya rame ya fita hayyacinsa. A hankali abba ya goge hawayen da suka zubo masa.


Kiran momy ne ya shigo take tambayar halin da ake ciki, yace yanzu haka gashi gabana kwance amma zamuyi kokarin kawo shi ko zuwa gobe. Shigowar Dr yasa ya aje wayar. Doctor yace nina likitan dake kula da lafiyar sa, wanene mahaifinsa ciki? Abba yace nine. Likita yace biyoni office.


Bayan sun gaisa ne yake bashi labarin yadda yusuf yazo hannun shi da irin raunin da yasamu, ya qara da cewa dama muna kokarin turashi teaching hospital dake zaria domin wadda yake daukan nawin treatment nashi ya bamu go ahead amma tunda kazo menene ra'ayinka? Zan tafi dashi kano inyaso sai ayi treatment din acan, sannan ka bani number wadda yaka wosa. Ya amshi number yafice.


Abba bai runtsa ba har gari ya waye. Dr yazo aka fara shirye shiryen kawoshi kano. Ambulance aka bada, batare da bata lokaci ba suka dau hanya.


A hanya abba yake sanar da kwararrun likitoci da ya sani kan suna hanya. Daki daban aka bashi, aka sake fara bincike akanshi.


Momy sunajin labarin zuwanshi dukkaninsu suka dau hanyar asibiti.


Kwance yake likitoshi ne kusan biyar a kansa. Bayan sungama dukkanin bincike suka fito daya daga ciki ya kira Abba.


Doctor yace dan ka ya samu rauni sosai, amma yanzu munyi masa taimakon da ya kamata, sai dai kafafunsa sun samu karaya sosai ta yadda tafiyar sa zai dauki lokaci, amma zamuyi iya bakin kokarin mu muga ya dawo dai dai.


Abba yayi wa likitan godiya ya fice. Tsaye yake kan dan nasa yaji turowar kofa, iyalansa ne baki daya suka shigo duk hankalin su a tashe. Babu wadda bai tausayawa Yusuf ba, musamman momy wadda take kuka sosai tasan yawan tunanine yasa shi har ya kaiga wannan hatsari, tana dana sanin abinda ta aikata. Kannen sa duk hawaye suke zubdawa na tausayin yayansu musamman aisha, rahma da kanta saida ta tausaya mishi ganin yadda ya rame kamar ba shiba.


Ganin kukan ba na dainawa bane Abba ya soma fada, addu'a zakui mishi ba zaku tsaya kuyi kuka ba, ku dubi halin da yake ciki ai abin godiyane ga Allah daya sada mu dashi... Allah tashi kafadarshi dukkansu suka amsa da ameen.


Da daddare Abba ya kira mutumin da ya taimakawa Yusuf, bayan sunyi sallama yake sanar dashi yadda akai yasami lambarsa tare da yi masa godiya, mutumin yace ba komai Allah bashi lafiya nima in na shigo kano zan nemeka. Sukai sallama.


Wasa-wasa yau satin Yusuf uku amma bai bude idanunshi ba. Iyalan gidan babu wadda yake cikin nutsuwa, kullum suna asibiti tare da dan uwa, yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke dubiya, duk wadda yaga Yusuf sai ya matukar basa tausayi domin kowa yana tuna alkhairi dake musu da son zumunci.


***** ******


Watan su daya da sati biyu cif yau a asibiti, amma Yusuf ko kifta ido bayayi. Misalin karfe goma na dare Abba ke zaune kusa dashi sai Momy dake dan nesa dashi, kannen sa ne aisha da Muhammad. Kallo daya zaka musu kasan basa cikin hayyacinsu, addu'a suke Allah bawa dan uwansu lafiya.


Momy da Abba tunanin ko su fitar dashi kasan waje suke amma babu wadda ya furtawa junansa.


A hankali Yusuf ya bude idanunsa, ganin wajen ya mishi haske sosai ya qara lunmshe idanunsa. Ya sake bude idanun a hankali harya waresu baki daya, Momy ce ta fara kallon sa, da sauri ta mike tana fadin Yusuf!!! Dukka ninsu suka nufoshi suna mishi sannu.


Shidai baice komai ba, dakyar ya iya juya wuyarsa yana kallonsu, zai bude baki ya musu magana amma tsaban radadin da yake ji bakin shi ya mishi nauyi. Tuno da abinda ya same shi yayi nan take ya rufe ido. Innalillahi wa'innailaihi rajiuun ya soma yi cikin zuciyarsa domin kasa furta ko da kalma dayane ya gagara.


Abba ne yace ku dakata mana, yanzu ya bude ido sai a abari likita yazo yayi bincike kafin a ce dashi komai. Nan Abba ya fita kiran doctor.


Bayan likita ya gama bincikensa ya cire robar da aka sa masa a hanci ya dubi Abba yace za'a iya bashi black tea yasha amma kada a dameshi da hayaniya, yin hakan komai na iya faruwa. Abba ya amsa da za'a kiyaye insha Allah. Bayan fitar doctor aisha ta hada masa tea kamar yadda doctor yace, tazo gaban shi ta zauna.


Yusuf yayi yunkurin tashiwa amma ya kasa, jinshi yake kamar ba shiba, baya iya motsa kafa da hannu. Aisha data lura da hakan a hankali tace kabari zan baka a kwance. Shiru yayi yana binta da kallo. Mika masa tea tayi da cokali amma yaki bude bakinsa.


Aisha tace yaya likitane yace a baka bude bakin ka. Hawayene ya soma sauka idanun Yusuf, yanzu ko bude baki ya gagara? Alhamdulillah! Yace gami da lumshe ido. Abba da Momy suka nufoshi lallashinsa suka soma. Bude ido yayi ya soma girgiza kansa a hankali.


Abba yace bazaka iya bude bakin ka ba? A hankali ya girgiza kansa alamar eh. Dukka ninsu suka soma furta innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun. Aisha ta kwanta kusa da kansa tana hawaye a hankali. Abba ganin halin da suka shiga yasa ya danne nasa hawayen yace haba, hakan zai daga masa hankali, muci gaba da addu'a, insha Allah komai zai daidaita, gobe in likita yazo saimu sanar dashi.


Aisha ta tashi tashare hawayenta ta soma kallon yayanta, tausayinsa take ji sosai ta shiga share mishi hawaye. Bude idanu yayi yana kallonta tace yaya kada ka damu, Allah zai sauwa ke maka kayi kokarin cin wannan jarabawar.


Murmushi taga yayi tare da lumshe ido ya bude. Tace har yanzu bazaka iya bude baki ba? A hankali ya daga mata kai. Ta shafa kansa tace do not warry dear, komai zai daidaita da izinin Allah.


Nan HANEEFAH ta fado masa arai, tabbas yasan tana can tana wahala karshema kuka take tayi, tsoronsa kada ta sawa kanta wani ciwo.. addu'a yayi Allah ka sauka kawa baiwar ka da bata jiba bata gani ba, ka bamu ikon juriyar wannan lamari da muka tsinci kanmu. Nan ya baza ido neman rahma ko zai ganta. Bai ganta ba, duban shi ya koma kan momy, ya sakan mata murmushi.


Isowa tayi gabansa tace kada ka damu muna nan muna tayaka addu'a, zaka samu sauki. Ya daga mata kai ya lumshe ido ya koma bacci. Sai da suka tabbatar bacci yake sannan Abba yace yakamata su koma gida dare yayi.


Bayan sun koma gida aisha ta nufi gun rahma. Bude kofar falo tayi taga bata ciki, sauri take taje tace mata Yusuf ya bude ido, turus tayi jin wayar da take yi.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼26


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Bayan an masa qarin jini binciken su ya tabbatar musu ya zamu rauni sosai. Bayan an masa taimakon da ya dace Dr ya fito domin sanar da mutumin daya yusuf halin da yake ciki.


Dr ya dubeshi sosai yace lallai yakamata mu samo yan uwansa, domin ya raunana sosai, munyi nasaran cire glasses da suka ke makale ajikinsa sannan ya zamu karaya a kafafunsa biyu da hannu daya, sannan kansa yayi mugun buguwa sosai ta yadda abinci ma bazai iya ci da kansa ba, sai dai mubasa ta hanci atakaice sai mun dauki hoton kwakwalwarsa mun tura asibitin psychiatric domin tabbatar da lafiyarsa.


Mutumin ya numfasa yace yanzu abinda nake so dakai ga numberta duk abinda kuke bukata ku sanar dani, yanzu zanje gidan qanwata in sanar da ita domin ni abuja zan wuce, insha Allah zamusan yadda za'ai munemo yan uwansa.


Dr yace ba komai. Yabi mutumin da kallo yana mamakin irin karamcin sa. Kamar yadda yafada haka akayi, ya hada kanwarta da likitan dake lura da yusuf, yace zata rika zuwa ta dubasa amma ya ware nurses da zasu zauna dashi.


Yau kwanan yusuf goma baisan inda yake ba, ko bude ido bayyi ba, likitoci suna iya kokarinsu. Ganin haka yasa mutumin yada hoton yusuf domin neman yan uwansa.


_Bari mu leka jama'an gida_


**** ****


Abba na ganin fitar yusuf da safe yasan ba lafiya bane. Ko momy saida taji abinda tayi mishi bata kyauta ba amma tana addu'ar Allah kaishi lfy.


Kwana biyar kenan hankalin su ya soma tashi, kullum wayar yusuf a kashe. Da daddaren ranan aisha taje dakin momy, zaune ta same ta bakin gado amma kallo daya za'ai mata asan hankalinta a tashe.


Aisha tazo ta zauna kusa da ita cike da damuwa tace momy kwana kinnan meyake damunki? Momy tace babu komai, ina tunanin yayankune tunda yatafi bai kira ba sannan inna kira bana samun shi.


Aisha ta tashi zaune tace momy nima inata kiransa amma bana samunshi, banyi tsammanin lafiya ba domin bai taba kashe wayoyinsa ba kuma..... abba ne ya shigo hannunsa rike da waya yace yusuf nake nema yau kwana uku amma ban same shiba, na aika yaron abokina gurin aikin nashi amma yace tun last wk baizo aiki ba, bana tunanin lfy.


Momy ne gabanta ya fadi tace to yanzu ya za'ai? Abba yace gobe zan bishi inji lafiya domin bai taba ko da kwana daya bai kirani ba. Allah sa dai lafiya cewar aisha


Washe gari misalin karfe goma sha daya jirgin su abba ya sauka, abokinsane ya aiko driver ya dauke shi, bai wuce dashi ko ina ba sai gidan dansa. A kulle suka tadda gidan, nan yacewa driver muje gurin aikin nasa. Sunjene aka tabbata mishi suma nemansa suke domin sunyi mamakin jin har yanzu bai komo aiki ba domin sanin da sukai masa shiba mai wasa da aikin sa bane.


Innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun abba yake furtawa. Kiran abokin nasa yayi yace bazai samu karasowa ba zai wuce kano amma da driver nasa zai tafi. Yace babu damuwa Allah kaisu lfy. Wayarshi yasa a silent sabida kada a dameshi da kira.


Ina yusuf yake? Wani hali yake ciki? Ya Allah ka tsaremin shi a duk inda yake. Tunani ne ya hana abba sakat. Jin gine yake yana kallon window har suka zo daidai inda yusuf yayi hatsari. Karaf idon shi yafada kan motar, zuciyarsa tayi mugun faduwa ganin mota duk da bai tabbata wace irin mota bane domin.


Da sauri ya tsaida driver sannan yafito ya nufi gun motar. Ganin yadda motar take yasa ya tausayawa wadda yake ciki domin ba lallaine ya fita da raiba. Zai juya ya tafi idanunsa suka sauka kan ID card, da sauri ya iso yaga ashe rabine domin rabin wuta ta koni saura gurin hoto wato passport.


Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuun ya furta da karfi, hankalinsa ne ya tashi sosai ganin hoton yusuf, ya dada juyawa gun motar ya kare masa kallo, sai yanzu ya tabbata motar yusuf ne.


Kasa dauke idonsa yayi har yazo kusa da motar yace... yusuf motar kace wannan! Yananan tsaye yaga wani tsoho ya taho gunsa yace mallam lafiya kake tsaye gun motar? Abba yace motar da nane.


Tsohon yace Allah sarki yau kwana biyar da hatsarin motar nan, tsohon ya kwashe labarin yadda akai aka cire mai motar da yadda wani bawan Allah yayi taimako aka nufeshi garin kaduna amma baisan da ranshi ko bayi da raiba.


Abba ya dafe kanshi dake sarawa, yace da tsohon nagode baba.Bayan yashiga mota yace da driver su tafi. Sun fara tafiya sai kuma yace mu tsaya garin kaduna.


Hotel abba yayi masauki. Sai da ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga ya kama daki. Yana shiga ya daga wayarsa yaga missed calls yawanci na momy ne. Abokinsa yakira dake garin kaduna. Bashi lbr abinda ya faru tare da neman alfarman neman mota domin neman gawan dansa.


Abokinsa yace ai baka tabbatar ba, dan kaga motar sa bai sa hakan ya rasu ba, yanzu da kaina zanzo mu zaga asibitoci nemansa. A sannan hankalin momy ya tashi, kuka take sosai ta kira yan uwansa ta gaya musu. Hankalin gidan a tashe


Abba da abokinsa sun yini wajen neman yusuf amma babu labari, hakan yasa hankalinsa ya dada tashiwa.


Zaune yake a falon a abokinsa yayi shiru ya zubawa tv idanu amma ba kallon tv yake ba, tunani yake ko dai yusuf ya rasu ne? Karaf aka hasko hoton yusuf, tsaye ya tashi yana nuna tv da hannu. Sauraron asibitin sukai sannan suka dauki mukullin mota suka fice.


Basu sha wahalan neman bangaren da aka ajeshi ba domin yana emergency, cikin hanzari suka fara bin dakuna har suka zo dakin shi. Nurse macece zaune kusa dashi, shigowarsu ya ta tashi tare da tambayarsu kosu wayene. Abokin abba ne ya sanar da ita tafita kiran Doctor
*Dr HANEEFAH* 28


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Durling na maka alkawari, bazan qara ko da shekara daya a gidannan ba, mum ce tasani auren sa nida shi ba son auren muke ba kaga ko babu maganan zama tare da shi, ok toh zanyi yadda kace......


Takaicine ya tokare wuyar Aisha, mayar aure tana waya da wani? Kuma tsaban rashin imani bata damu da rashin lafiyar dan uwanta ba? Komawa tayi a hankali ta maido mata kofar kofalon yadda ta samu.


Aisha shiru ta zauna bakin gado tana nazarin wannan lamarin, ganin haka ba mafita bane yasa ta tashi ta dauro alwala domin samin mafita gun mahaliccinmu.


Washe gari misalin karfe bakwai sun gama shiri tafiya asibiti, Momy tacewa Aisha taje ta kira Rahma su tafi, kamar bazata je ba ta nufi bangarensu.


Sallah ta tarar tanayi, sanda tajira ta idar tace Momy tace ki fito mu tafi asibiti, bata jira amsar taba ta juya ta fice.


Tsaki Rahma taja ta tashi tana gunguni ta fito. Gurin motar ta nufo ta gaida Momy a tsaye ko rissinawa batayi ba, Momy ta amsa da fara'a tace ai jiya ya bude ido shine nace bari mu tafi da safe, Allah sarki Allah bashi lfy cewar Rahma.


Aisha ta kalli Muhammad tace shiga gaba mutafi. A hanya babu wadda yayiwa wani magana har suka iso asibiti.


Tsaye suka sami Abba bakin kofar dakin, hakan yasa suka tabbar likita na ciki. Bayan sun gaishe shi ne yana kan amsawa likita ya fito yace Abba da Momy su biyoshi office.


Likita ya dubesu yace hakika danku yayi mummunan hatsari, sbd glasses sun shige jikinsa sosai, amma da ikon Allah yana samun saukin raunukansa cikin sauki. Sai dai matsalan yanzu shine muscles din fuskarsa ma'ana wajen yadda zai sarrafa bakinsa ya samu shock, ta yadda bazai soma magana ko motsa su sosai ba sai nanda wasu lokuta in magungunan da muka basa sun masa aiki, inko muka samu sabanin haka sai dai a masa aiki.


Abba ya numfasa yace muna godiya da kulawar ku garemu, Allah bashi lafiya. Suka ma likita godiya suka fice.


Aisha ce ta fara shiga dauke da kular abinci. Ta iso gare shi ta zauna gabansa, hawayene ke tsiyaya a idanunta. A hankali Yusuf ya bude idanunsa yana kallonta, murmushi ya sakar mata tare da girgiza mata kai da sauri ta goge hawayenta.


Yusuf yana son kama hannuwanta ya lallashe ta amma yakasa, yayi mata nuni da ido ta kama hannuwansa, ita ko ta dauka ce mata yake hannuwansa na masa radadi. A hankali ta dafe kansa tace kada ka damu zaka warke nan bada jimawa ba.


Ya lumshe ido yana jin wani irin radadi a zuciyarsa, lallai duniya abar tsoroce, yanzu kana lafiya anjima zaka rasata. Tunani yake yau shine a kwance baya iya komai sai kallo! Ya Allah kabani ikon komawa gareka kana mai alfahari dani.


Momy ce tashigo ta nufeshi tana murmushi tace Allah baka lafiya, kana cikin addu'a ta.


So yake yace Momy amma ya kasa, dubansa ya koma kan rahma da ko sallama batayi ba. Ganin kallon da yake mata yasa ta zo kusa dashi tace masa sannu, amsa mata da murmushi. Abba ya shigo yace shizai wuce sai yazo.


Da dare Abba yace yakamata yarannan su koma makaranta tunda anfara samun nasara kan lafiyarsa.


Haka ko akai, aisha da Muhammad sun koma makaranta, Momy ma tana leqa office amma ba aiki ke kaita ba. Momy ce ke kula da Yusuf sai Abba da yake kwana agunsa. Rahma ko kamar ba mijinta kuma dan uwanta ba, sai ance taje dubasa zata je, ganin haka yasa Momy ta kyaleta tace tunda ita batasan yakamata ba saita zauna domin tin yanzu ta fara dana sanin aurensu.


Duk wadda yazo duniyar Yusuf saiya tausaya mishi, ya rame sosai kamar ba shiba. Momy inta zauna tana kukan itace sanadiyyar shiga danta wannan hali domin tunanin fasa auren sane yaja masa hatsari. Amma ta dage da yiwa danta addu'a Allah bashi lafiya.


Yusuf ma kullum yana addu'a Allah bashi lafiya domin yana jin azabar ciwukan dake jikinsa. Sau tari zai lumshe ido kamar mai bacci amma tunanin Haneefah yake, da ita yake kwanciya da ita yake tashi. Duk da halin da yake ciki baifasa yi musu addu'a Allah hadasu matsayin ma'aurataba, SO kenan!


*****


Allah maji rokon bayinsa, yusuf yafara samun sauki domin har hannunsa yafara motsawa, maganar dai har yanzu bai soma ba.


Aisha ce zaune tayi shiru tazubawa yayanta idanu. A hankali ya bude ido ya juyo inda take, Aisha tace sannu da barci yaya, yanzu abokananka suka zo kana barci.


Murmushi yayi kamar yadda ya saba, duk da ba magana zai iyayi ba yace ina Momy? Ras maganan ta fito. Shi kansa yayi mamaki, yaya magana ka fara? Sake fada inji? A hankali yace ina Momy? Alhamdulillah ina iya magana! Dadine ya lullube Aisha nan ta fara hawaye! Zatayi magana Abba ya turo kofa.


Da sauri ta nufeshi tana nuna Yusuf takasa magana, Abba cikin tsoro da tashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login