Showing 33001 words to 36000 words out of 74305 words
Chapter 12 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
biyu da table a tsakiya.
Gidan ya tsaru sosai, Raihana tace saura bedroom amma ki rufe idanun ki kafin mushiga. Idanunta a rufe suka tura kofar suka shiga, a hankali ta bude idanun ta, neman numfashinta tayi ta rasa dalilin abinda idanuwanta suka hango mata.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼35
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Murmushi yake wadvda ya bayyana fararen hakoransa cikin fararen kaya, adon kayan da baki a jiki sai hularsa da agogon hannunsa baki, yayi matukar kyau sosai cikin hoton. Gefen hoton ta gani su biyune cikin mota yadan matso kusa da ita ya dauke su randa bazata taba mantawa ba, randa Momy ta nemi alfarman rabuwa dashi.
A hankali ta soma tafiya tana goge hawayen da ke fita a idanunta harta karaso inda hotunan suke. Ta tsaya tana murmushi tace Yusuf ka sanar dani, muddin dan Adam yana son zama wani abu a doron kasa zai zamo sai dai niyyarsa kadanne, in suna yake nema zai zamo, ka sanar dani cewa koda mutumin da banza ne mutum zai zama amma ba so daya ko sau biyu da aikatawa zai samu suna ba, yau da gobe har zai kasance cikin matakin da yake nema, yau gashi ni Haneefah ban nakai matakin da na samu gidan kaina, mota da albashina amma banyi farin ciki dasu ba, cikin shekara biyu nasan abubuwa da dama! Tabbas komai sa kaine muddin mutum yace zayyi abu zayyi sai dai bayyi niyya ba, ban manta da kai ba kana cikin raina Yusuf! Yaushe zaka iso gareni? Ina zaman jiranka. Nan ta fashe da kuka mai tsanani ta sulale ta fadi a kasa tana ci gaba da kukan ta.
Raihana da ta aikata hakan sai taji babu dadi. A hankali tazo ta durkusa gabanta tana share mata hawaye tace kiyi hakuri banyi tunanin abin zaikaiga haka ba, gani nayi a duk sanda kika dauki wayarki kina kallon shi kinajin nishadi wani sa'in inga kina hawaye shiyasa na tura hotunansa wayana nakai akai enlarging nasu amma kiyi hakuri zan shire su kidaina kuka.
Haneefah ta tsaida kukan tace aa kada ki ciresu inason kayana kuma nagode da kikai haka, banyi niyar sanar dake ba amma ya zama dole in sanar dake wannan bawan Allah. Nan Haneefah ta sanar da ita komai game da Yusuf ta qara da cewa ina zaman jiranta duk sanda taga ya dace na auri danta zata zo ta nemi alfarman in aure shi.
Raihana tace gaskiya abin akwai ban tausayi amma mesa zata tauyewa danta hakki? Babu kyau ga iyaye dan sunga dansu na musu biyayya su juya su yadda suke so... da sauri Haneefah ta katseta tace danta ne tana da ikon yin komai akansa.
Raihana tace duk da haka zamanin yanzu dole kabi yaro da hankali, ita daji dadima ta samu mai mata biyayya! Allah shirye mana zuri'armu. Naga kuskuren ki daya Haneefah.
Haneefah ta dago ido tana mata kallon tambaya? Tun farko kuna addu'an Allah tabbatar muku da alkhairi, toh kun rabu mesa bazaki dauki hakan cewa shine mafi alkhairi ba? Yakamata kici gaba da addu'a Allah kawo miki mafi alkhairi arayuwarki tunda kun rabu bawai zaki ci gaba da addu'a Allah kawo shi ba. In bai zoba ya zakiyi?
Nan Haneefah ta shiga tunani, maganar Raihana gaskiyane toh amma ya zatai da sonshi da ke adda barta? Mafita shine ta kawar da wannan son, wani sashe na zuciyarta na mata gargadi da hakan. Cikin kankanin lokaci taji tunani ke son rikita mata kwakwalwa. Tashiwa tayi tabar gurin.
Har dare Haneefah na abu daya, da gaske Yusuf sun rabu kenan? Ina! Nasani zaizo yana sona. Raihana data lura da ita tace nasan abune mai yuwa agareki kiyarda da abinda nace amma arayuwa anason bawa yakasance baya riko kan al'amarin duniya ki barwa Allah zuciyarki kawai.
Tashi tayi ta fita a dakin. Zaune tayi cikin kujerun alfarman dake falo tana tunanin anya ko zata iya kasance da wani? Nan ta soma ambaton Allah ya duba mata wannan lamari. Tashi tayi ta dauki qur'ani ta soma karantawa, a hankali ta soma jin sassaucin kuncin da take. Murmushi ta soma yi tana kallon qur'ani.
Rufewa tayi ta daura kirjinta tana cewa nagode maka Allah da ka yini musulma kuma makaranciya, rayuwata da zuciyata na hannun ka, ka zabanin abinda yafi alkhairi. Tana kaiwa nan ta kwanta ta soma barci.
Cikin mafarki taga Yusuf yana mata murmushi, gani daya ta masa taga ya rame yace da ita Haneefah kada ki barni ina bukatar ki pls! Firgigit ta tashi tana waige- waige. Ganin agogo tayi karfe uku, tashiwa tayi ta dauro alwala tafara nafiloli.
Bayan sun idar da sallah asuba taji wayarta na ringing, tana dagawa taga Abba. Da sallamar ta ta amsa suka gaisa tare da tambayar mutanen gida? Abba ya amsa da kowa lafiya ya qara da cewa dazu yar'uwarki tazo lafiya, kema muna miki fatan kizo lafiya duk da Mubarak ya sanar dani halin da kike ciki, ki kwantar da hankalin ki yadda kikaje lafiya haka zaki zo lafiya.
Murmushi tayi tace Abba nagode, zan kasance mai farin ciki muddin ina biye da albarkan ku. Allah miki albarka Haneefah. A hankali tace ameen sukai sallama.
**** **** ****
Jiran driver yake yazo ya tafi da shi airport domin wucewa gurin aikin sa. Rahma ta fito cikin sauri ta nufo shi tace ina zaka? Airport zanje ya bata amsa, zaka iya kiran mum na ta iso domin driver yaje daukan ta a airport.
Yusuf yace ok kafin bari inje in karbi sim na dana bada amin welcom back. Rahma tace kada ka dade domin akwai maganan da nake so nayi dakai in mum ta zo, bataji me yace ba ta nufi bangaren Momy.
Ganinta yake cike da mamaki ko mesa bata son fitarsa yau. Ya dau hanyar gate sai kuma ya tuno sim park nashi dake wardrop, ya juya dakyar yake tafiya har ya isa sashen shi.
Rahma najin qarar tsayiwar mota tayi sauri ta fito ta tare mum, janta tayi zuwa sashen su. Mum ta dubeta tace ai kya tsaya in gaida yayartawa ko? Rahma tace mum wllh sai kin saurareni kafin ki gaisa da kowa suka nufi sashen su.
Momy jin kanwarta bata shigo ba yasa tace bari ta lekata ko dai lafiya? A falo ta samu Aisha zaune tana kallo tace taso muje mu dubo umman ku nusaiba naji shiru bata shigo ba.
A tare suke tafiya har suka iso gurin motar sukaga wayam. Aisha tace Momy ina suke? Momy ta kira driver tace ina bakuwar daka kawo? Driver yace Hajiya Rahma tazo sun nufi sashin su tare. Momy mamakine ya kamata tace da Aisha su wuce sashen nasu.
Abinda kunnuwan su suka fara jiye mu sune yasasu daka tawa da shiga falon.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼33
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Kevin ya dubeshi sosai yace duk wadda suke 100level su kadai suka damu zuwa asibiti, mu qara musu kwazo ta hanyar nuna musu hanya koya kace Rohan? Yace great idea tashi mu bisu dan nasan can zasu nufa.
Su Haneefah basu tsaya ko ina ba sai bangarensu, suka tarar a kulle dan haka suka wuce laboratory nan suka tadda a bude. Bayan sun gaisa da wani ma'aikacin da suka tarar suka ce muna bukatar tayaka aiki amma mu dalibaine... Nan ya zage yafara gabatar musu abubuwa tare da amfanin kowannen su. Sun kusan awa daya suka nufi gynecology. Nan sundan san jama'a suka ci gaba da daukan lecture. Su kansu baturen yadda su Haneefah suke daraja su ne abin yake burgesu har su koya musu abubuwa da dama.
Su Kevin sanin basa department nasu yasa suka nufi inda zasu same su. Zaune su Haneefah suke gaban wata staff tana musu bayani akan abinda suka gama treatment. Suna fahimtar bayaninta sosai.
Jin anzo an zauna kusa da su ta dago ido tana kallon shi. Shima kallon nata yake yace me kukeyi anan bayan nan ba bangaren ku bane? Tsab ta ganeshi, wadda ya taimaka da ID card nata daya fadi a airport. Baturiyarce ta kallesu tana dariya tace kunbiyo colleagues naku ne? Toh sunzo karin ilmine wannan bangaren domin naku bangaren kulle yake.
Kevin yace taso muje mu bude sai muyi karatu tare. Haneefah batayi niyan tashi ba Raihana ce taja hannun ta suka tafi. Sun bude department nasu suka kaisu gurin manyan na'urori nan su Haneefah suka bude baki sai kallo.
Kevin ne ya soma magana yace ni sunana Kevin daga nan garin nake wato London, wannan kuma Rohan daga India yake. Department namu daya amma muna gaba da ku, muna kallon kwazon ku wajen zuwa asibiti duk da ba'a fara fitar daku ba, sau tari muna ganin ku a library atakaice duk cikin daliban wannan shekaran kune kusan na farko wadda suka san meya kawo su wannan makaranta, hakan yasa muke son shiga rayuwarku mubaku wani abu game da abinda muka sani amma sai da yardan ku.
Haneefah ta kalli Raihana cikin harshen larabcin da bata kore ba tace nifa ki tashi mutafi tsoron su ma nake ji, ya za'ai mufara karatu da maza?
Raihana tace su suka ce da yardan mu amma mesa bazamu basu dama ba tunda karatu kawai suka ambata.
Rohan yayi murmushi cikin harshen larabci yace daama zaku bamu duk da mutanen yanzu ba'abin yarda bane amma in kun damka kanku Allah amanar kanku babu abin sharri dazai fuskance ku sai alkhairi.
Haneefah taji wani bala'in kunya kamar kasa ta tsage ta shiga, dama yana jin larabci? Kevin ne ya katse mata tunani da cewa mun iya yaruka daban-daban cikin shekaru biyu, in bakwa shiga cikin mutane abubuwa zai barki, bawai zakiyi mu'amala dasu sosai ba kawai dan ki fahimci wani abu game da abu na rayuwa.
Rohan yace mu musulmaine, Kevin ne mahaifinsa christer, tun yana karamin ya musulunta, mahaifinsa ya yarda da musuluntarshi amma yanemi alfarman ko da zai musulunta kada ya canza sunshi domin takwaran kakan shine. Ni kuma dukkan gidan mu musulmaine dan haka kada kuyi shakka mu yan uwanku ne.
Raihana tace Alhamdulillah, ai yazo da sauki, mun amince Allah saka da alkhairi. Rohan ya dubi Haneefah yace bakice komai ba? Haneefah tace ba komai Allah shige mana gaba.
Sannu a hankali Haneefah ta gama sanin bangaren karatun da wasu bangaren da ba nata ba musamman gynecology, sannan tana jin dadin tarayya da Rohan da Kevin domin duk abinda ya shige mata duhu tana samu bayani sosai gurinsu. Sannan sun fahimce Rohan da Kevin ana matukar ji dasu domin ba kananan dalibai bane domin suna matakin karatun masters ne, bangaren addini ma sun rike addini basa shaye shaye da sauran munanan dabi'u, hakan yasa kansu ya dada haduwa su hudu.
Su Haneefah anyi nasaran shiga 200level. Sun gama exams nasu na 2nd semester sun shiga na 3rd a wannan lokaci dukkanin dalibai anturasu asibitoci. Zaune suke bayan sun gama ganin wasu patients, Haneefah tayi shiru tana tunanin yadda zata tafi Egypt wajen Nana domin nan da jibi za'a yayesu kuma tunda Dr Mubarak ya tafi bai sake zuwa ba. Raihance ta tabata tace an shiga meeting tashi mubi su.
Gurine da cika da manyan likitoci da manyan dalibai bangaren radiography, wani daga cikin baturai manyan mazauna gurin ya tashi ya soma bayani yace ina mika gaisuwata da ko wannen ku, ba tare da bata lokaci ba zan gabatar da abinda yasa mukai taro na gaggawa, aka hasko wani hoto yace wannan sabon case ne wadda yazo mana a jiya, munyi yadda zamuyi domin gano abinda yake damun wannan amma abin yaci tura, mu kuma bama so mu mayar dashi batare da gano abinda ke damun shi, dan haka muna jiran duk wadda zai iya gano wani abin.
Haneefah dariya yaso kubuce mata amma tayi shiru domin yadda gurin yayi tsit, azuciyarta tace yau na tabbata baturai mayu ne, basu ga komai ba amma sai sun tabba akwai abu. Zaune a inda take ta kurawa hoton ido domin ta soma hango matsalar. Kusan minti goma babu wadda yayi magana hakan yasa ta daga hannu alamar tana son magana, Raihana tayi saurin saukar da hannun ta amma tuni an bata damar tashiwa tayi bayani.
Jama'ar gurin baki daya kallon su ya koma gunta, ita dai Haneefah a hankali take taku harta iso inda aka hasko hoton ta juya kallon jama'an. Cikin nutsuwa ta soma bayani yadda abin yake da yadda mafitar zata kasance muddin akai aiki yadda take ganin haka ne, sannan ta karasa bayani da cewa ayi hakuri innayi kuskure domin kasancewa ta daliba.
Komawa zatayi ta zauna taji an soma tafi, juyawa tayi taga wani tsohon bature wadda take tsammanin shine mai asibitin, ganin haka yasa dukkanin gurin suka soma tafi. Baturen ya tashi yace wannan case na taba treating nashi shekaru goma da suka wuce kamar yadda wannan yarinyar ta fada, nayi mamaki da kike daliba har ilmin ki ya kaiga nan duk da haka kin samu karin girma a mtsayina na mai wannan asibitin zaki fara aiki.
Murmushi Haneefah tayi tace nagode amma bazan iya aiki ba domin karatu ya kawoni. Ji tayi ance zaki iya. Da sauri ta juyo dan jin muryar Dr Mubarak, ya karaso yace ranka ya dade zata iya domin karatuma a karkashin ku take bale aiki.
Baturen yayi murmushi yace kusameni a office anjima bayan awa daya. Nan meeting ya tashi mutane suna zuwa mata domin tayata murna da nuna kwazonta. Ita dai tsananin mamakin zuwan Dr Mubarak tayi. Bayan sun fito ne suka samu guri suka kebe.
Kallonta yake sama har kasa, habayane jikinta Brown colour sai tayi rolling da black gele, ba wani makeup ne tayi ba amma tayi kyau sosai. Dr Mubarak kallonta yake kamar ya hadiyeta duk da yasan barrister ta fita kyau amma kyan Haneefah dabanne. Ganin yayi shiru yasa Haneefah tace Dr sannu da zuwa kawar da kai yayi sannan ya hada rai.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼36
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Rahma tace mum hakuri na ya kare, farin cikin ki nake so nayi aurennan don kina son samun jikan da zai gaji Yusuf, toh Yusuf yayi hatsari ya samu matsala bazai sake haihuwa ba, sai kisan yadda za'ai na fita nabar gidan naje na auri wadda.....
Umma Nusaiba ta toshe mata baki da hannuwa tace so kike ki tonamin asiri , yar uwan tawa zan duba cikin ido ince abaki takarda saki sabida danta baya haihuwa? Yanzu bazaki rufawa dan uwanki asiri ku zauna ba?
Cikin kuka rahma tace Mum wallahi bazan iya zaman gidannan ba, ba so na yake ba, kuma ai dama bada niyyar zama nazo ba cemin kikai inna haihu zanbar gidan, mum na hadu da wadda zai so ni kada kisa nafara bin maza da aure na wlh nagaji da zaman gidannan.
Mum na kokarin buge mata baki taga Yusuf ya fito daga bedroom. Durkusawa har kasa yayi ya gaisheta, bai nuna mata ya ji dukkanin abinda suke tattaunawa ba. Ganin bata amsa ba ya tashi ya nufi hanyar fita, turus yayi ganin Momy da Aisha bakin kofa.
Momy ce ta kamo hannun sa ta shiga dashi falo har gaban Rahma. Tace wannan kike kira juya? Kinyi babban kuskure, sannan bazanki ya sake kiba, bazan so ki kasance kina bin maza da auran ki ba.
Ta juya ga Umma Nusaiba tace da kingayamin wannan shine manufarki akan da na ban biye miki ba, wannan shine sakayyar da zakimin matsayina na yar uwarki? Ciki daya muka fito fa? Dubi yadda ya kama sanadiyyar janye auren da na sashi yayi kawai saboda yarki takasance cikin farin ciki da samun soyayyar da na. Babu abinda zan iya ce miki, ta dubi Yusuf tace rubuta mata takardan saki...
Zayyi magana tace ban lamunci kace min komai ba nina ce kayi. Nemo takarda tayi ta mika masa ya rubuta mata saki daya. Momy ta karba ta mikawa Rahma tace zaki iya tafiya ki auri duk wadda kike so, sannan kin horar da mahaifa irin mu masu son hada yara aure musamman maza, darasine agareni sannan ke kuma nusaiba nan gaba ko hijabine kada ki bata zabi kinci sa'a nakasance yar uwarki mai rufa miki asiri. Inkin huta zaku iya barin gidana. Tana kaiwa nan ta juya ta fita.
Aisha ce ke biye da ita har bedroom, ta zauna kan gado ta dafa kanta tace Aisha ni wace irin uwace? Dubi abinda najawowa Yusuf, yanzu da wani ido zan dube shi? Nina jawo masa rashin auren zabinsa gashi zabin nawa sun zubamin kasa a ido har suka kiran da na juya!
Aisha tazo kusa da ita tace Momy ki daina fadin haka, nagode da Allah daya bayya gaskiya dan nasan innice nazo na fada miki bazaki yarda ba amma tunda gaskiya ta fito shikenan, ke uwace abin alfahari agaremu, domin kin mana abinda bazamu iya biyan kiba, abinda nake so dake neman lafiyarshi zamu ci gaba da yi tare da yi masa addu'a. Da wadannan kalamai Aisha ta kwantarwa Momy hankali.
*** *** ***
Zaune yake aiki ya gagaresa ya kurawa hoton Haneefah ido yau shekara biyu kenan da rabuwarsu, yana son dakkowa Momy maganar Haneefah amma tsoro yake domin bayason wani abinda zai taba tsakaninsa da Momy.
Wayarsa ce ta soma ringing ganin Aisha ce ya daga tare da sallama tace yaya albishirin ka yace goro. Salma ta haihu namiji mai kamar ka! Dariya yayi yace haba weekend dinnan zanzo ashe inga young engineer, sukai sallama ya ajiye wayar.
Lumshe ido yayi yana rayawa a ranshi yaushe Haneefah zata fara haifa masa nasa yaran? Ya Allah dan girman zatinka ka bamu ikon kasancewa a inuwar ma'aurata. Haka yake ta kissimawa aranshi har lokacin tashi yayi yabar office ba tare da yayi komai ba.
Bangaren Momy kuwa damuwa tashiga sosai, da kanta ta yanke shawarar tafiya gidansu Haneefah domin neman afuwarta sannan ta dawo mata da soyayyarsu.
Batayi tunanin tafiya ko ina ba sai gidan Hadiza, domin acan ne tasan zata samu address din gidan su Haneefah. Parking tayi bakin gate din ta shigo a hankali. Knocking daya tayi akazo aka bude mata.
Hadiza ba karamin mamakin ganinta tayi ba, bata hanya tayi ta wuce. Bayan ta zauna sun gaisa Hadiza ta tashi ta shiga kitchen domin kawo mata ruwa. Tsayawa tayi tana