Showing 63001 words to 66000 words out of 74305 words

Chapter 22 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5183

tana kallonsa taga duk ya canza, hannayensa ta gano empty dan haka tace dashi ka shiga ina zuwa. Kasa motsawa yayi yana kallonta har tazo ta wuce ta nufi inda jakarsa take ta dauko ta nufi gida shima yana biye da ita.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼62


Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖


Nana tana dariya ta mike tashiga ciki. Tana shiga Yusuf ya tashi da sauri yazo kusa da abokin nashi ya fizge wayar hannun as yana cewa da wani suna kayi saving lambarta?


Abdullahi dake dariya sosai yace Sis Haneefah. Gudun kada yayi mistake ya tura ta WhatsApp yana cewa nagode nizan wuce.


Dr Abdullahi ya tsagaita da dariyar da yakeyi yace aa tsaya mu tattauna kasan yanzu mun zama so close, yanzu dai kabarta ta karasa karatun da kafin ku tare


Wani kallo ya watsawa Dr yace shekaru nawa muna jiran wannan rana? In ma taro ko occasions kuke son yi mun yafe, nasan dangi sun shaida aure ,saiku jira in muka haihu saikuyi komai.


Dr Abdullahi ya kuma kwashewa da dariya yace kada kayi haka, itama bazata ji dadi ba kabari sai tadawo Nigeria saiku tare aganina hakan zayyi amma yanzu da wanne zata ji? Ya qarasa maganar da zolaya.


Shidai Yusuf shiru yayi yana jiran isowar contact. Yana gani ya mike yana cewa nizan wuce mayyuwa bazamu hadu ba domin cikin satinnan zan wuce London. Abdullahi yana ta mishi tsiya akan kada ya soma amma ko kula abokin nashi bayyi ba.


Bayan ya koma gida ya nufi falon Abba ya tarar Momy na can. Murmushin jin dadi tayi da taga dan nata cikin walwala. Bayan ya gaida su sai kuma yayi shiru yana sosa keya.


Abba abu kadan ya fashe da dariya ya kawar da idanun nasa zuwa kallon tv. Momy da ta gano shi tsaf tace yakamata ka soma shirin tafiya can London ko zaka jirata tazo ne?


Karaf ya sako baki yace dama inason fara shiri gobene, shine nace bari inzo in sanar da ku. Momy tace ai hakan yayi kyau sai zuwa gobe ka shirya zuwa Abuja.


Yusuf ya kalli Abba dake kallon tv yace Abba gobe nake son wucewa. Abba yace Allah kiyaye hanya amma inason tarewarta yakasance inta kammala karatun ta, tunda kadan ya rage saika bari ta kammala amma zaka iya zuwa ku gaisa.


Toh shikenan ba komai Abba. Zai tashi Abba yace a gidan da kake zaune yanzu zaku zauna ko akwai wani plan naka? Aa Abba a sabon gidana.


Abba yace babu damuwa, zan karasa maka sauran ginin sauran shirin kuma mahaifiyarka da sauran yan uwanka yazu karasa cikin nutsuwa tunda har yanzu akwai sauran lokaci. Godiya Yusuf yayi ya tashi ya nufi sashin sa cikin sauri. Momy tabisa da kallon tana binsa da addu'a.


Ya gama shirin kwanciyarsa tsaf ya hau kan gado ya kwanta rike da pillow ya kurawa lambar ido. Shiga WhatsApp yayi ya duba lambarta yaga tanayi. Dp ta ya kurawa ido, itada Raihana, Kevin sai Rohan. Sunyi matukar kyau musamman Haneefah domin gani yake tafi mishi kowa kyau.


Wayarta na ringing harya katse bata daga ba domin bacci ya soma daukarta. Ganin an sake kira yasa ta dauki wayar da nufin ta sa a silent taga lambar Nigeria ne. Ganin batasan lambar ba yasa ta daga tare da yin shiru.


Shima shiru yayi. A hankali ta furta wanene? Shiru yayi ya lumshe ido jin muryarta. Ta sake maimaita tambayar tare da cewa banaji fa.. shima a hankali ya furta DEARIE


Idanuwanta ta bude baki daya jin muryar shi, ta nemi bacci ta rasa amma ta dake ta qara tambayar wanene? Murmushi yayi yace in hukunta ni zakiyi kada ki hukunta ni ta wannan fannin bazan iya jurewa ba.


Wani irin farin ciki ke ratsa illahirin gabobin jikinta, kasa magana tayi ta lumshe ido tana sauraronsa. Jin yayi shiru yasa ta fashe da kuka


Hankalinsa ya soma tashiwa yana tambayarta meya faru? Lallashin duniyar nan yayi amma taki shiru, ganin hakan yasa ya soma bata hakuri amma nan ma taki shiru, da kanta ta katse wayar ta kashe baki daya tana murmushin jin dadi.


Shima hankalinsa a tashe tunaninsa baki daya ya karkata gari ya waye ya soma shirin tafiya amma wannan daren bai iya runtsawa ba farin ciki sosai yake tare da godewa Allah.


Da safe dakyar ya kai karfe tara ya nufi gidan su Haneefah. A waje yayi parking yana kokarin fitowa yaga Ahmad da yaya jibril. Sallama ya fito yayi musu suka amsa. Bayan sun gaisa ne Ahmad ya mishi iso zuwa falon Abba shi ko jibril ya nufi gida sanar da Abba yayi bako domin gidansu ya kwana.


Kasancewar su Amal sun fita yasa Ahmad da kanshi ya kawo masa ruwa tare da yiwa Umma magana dake shirin fita aiki.


Har kasa ya sauko gaida Umma, Umma da fara'arta ta amsa tare da tambayar mutanen gida? Duk suna lafiya, ya qara da cewa Umma ina nemawa mahaifiyata afuwa.... bai karasa ba ta katseshi da cewa babu koma ya wuce, ai komai lokacine sai yanzu Allah ya nufa babu komai Allah hada zuciyarku ya baku zaman lafiya. Cike da murna ya amsa da ameen.


Sukai sallama ta fita. Bai jima ba Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya dauko da maganar afuwa Abba ya masa nuni da komai ya wuce fatan zaman lafiya ya musu tare da yi masa nasihar akan rayuwa baki daya.


Yusuf yaji dadin lafuzzan mahaifan Haneefah, hakan ya qara masa qimar Haneefah a idanunsa. Ya sanar da Abba yana son tafiya gurin Haneefah. Fatan tafiya lafiya da zuwa lafiya yayi mishi.


Agurguje yaje gida ya tattara abin bukatarsa ya nufi Abuja daukan excuse gurin aikin shi.


**** ****


Zaune take tayi shiru ta zubawa takar dun gabanta ido, duk da irin karatun dake gabanta hakan bai hanata tunanin sa ba. Meya hanasa kiranta? Sau daya ta gwada kiransa amma bai daga wayarba.


Raihana cikin tsokana tace an zama ma'aurata amma ana yawan tunani. Bata ce da ita komai ba ta dauki wayarta tayi dialing number shi amma bata samun sa. Ji tayi kamar ta jefar da wayar ta tarwa tse.


Suna cikin haka wata balarabiya ta nufo su ta sanar dasu lectures suke dashi yanzu.


Bayan ya sauka a airport batare da bata lokaci ba ya nema taxi domin yana da address dinta. Da murmushi ya nufo kofar ta ya danna qararrawa amma yaji shiru, ya dauki tsawon minti goma yana haka amma ya tabbatar babu kowa domin ba'a bude kofar ba.


Nesa da gidan kadan yayi yanemi guri ya zauna yana kallon mutanen da suke zarya. Kusan karfe tara na dare babu alamarsu gashi gajiya da yunwa ta addabeshi, ruwa ya ciro cikin kayansa ya sha.


Karfe tara da minti arba'in suka yi parking. Sunzo daidai zasu shiga Raihana ta ja ta tsaya ta hangosa yana bacci kasancewar gurin haskene tamkar rana.


Haneefah ma ta tsaya tana kallon inda Raihana ke kallo, da sauri ta mika mata takardun hannunta ta nufo shi da sauri. A zaune yake ya lumshe ido tamkar mai bacci, tausayinsa taji ganin wahala tattare dashi a tunaninsa bacci ya soma.


Tsugunowa tayi tana tunanin yadda zata tashi daga bacci, jin motsi yasa ya bude idanunsa a hankali yana kallonta. Da sauri ta mike zata juya shima ya mike da sauri ya fara binta amma yakasa cewa komai.


Juyowa tayi tana kallonsa taga duk ya canza, hannayensa ta gano empty dan haka tace dashi ka shiga ina zuwa. Kasa motsawa yayi yana kallonta har tazo ta wuce ta nufi inda jakarsa take ta dauko ta nufi gida shima yana biye da ita.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼63


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Basu tarar da Raihana a falo ba dan haka ta ajiye jakarsa ta nufi dakin da zata sauke shi ta shiga gyarawa. Bayan dakin yayi fes ta nufo falo amma ta kasa karasawa. Ta rasa me zata fara ce masa dan haka ta tsaya nesa da mashigan falo.


Kusan mintuna goma tana tsaye taga Raihana ta fito. Ajiyar zuciya tayi tace pls inkin je falo ki mishi iso zuwa dakin shi


Tsaye Raihana tayi tana kallonta tace nifa na dauka kuna daki, nemo ruwa na fito ashe ko masauki baki kai shiba kuma kinsan nisan Nigeria a London akwai gajiya..


Haneefah ta wuce ta shiga daki batare da tace mata komai ba a zuciyarta tana cewa ni nasan gajiyar da ya dauko amma bansan me zance dashi bane.


Raihana tashigo falon da fara'arta tana cewa irin wannan zuwan bazata haka? Shima murmushi yayi baice komai ba yana ware idanu ko zai ganta. Tsaf Raihana ta gano shi ta tashi tace yazo masauki. Yana shiga ya lumshe ido yace ina kike? Shiga toilet yayi.


Tunda tashiga daki ta kasa zaune sai zarya take. Tana jin budewar kofar Raihana tazo da sauri tace kin kaishi? Raihana har dariya abin yabata sannan ta amsa da eh, yana jiranki, sai.....


Tun kafin ta karasa ta fita da sauri ta nufi kitchen. Cikin mintina kalilan ta dafa masa abinda zaisa abaki, ta hado masa da fruits ta aje kan try ta nufi dakin da yake. Duk da gabanta ba karamin faduwa yake ba amma yazama dole ta je inda yake domin bazata barshi da yunwa ba.


Sallama tayi taji shiru, ta dauki kusan minti biyar tana sallama amma ba'a amsa ba. A hankali ta bude kofar ta shigo da sallama amma bata ga kowa ba, da sauri ta ajiye abinda ke hannunta ta fice a dakin.


Tunda yaji sallamarta yake sauri amma kafin ya fito babu ta fice a dakin. Da sauri ya nufi inda try yake ya bude su, murmushi yayi ganin abinda ta kawo masa yace delicious!! Tunani tare da farin ciki ke ratsashi wai yau shine zaici abincin Haneefah a matsayin matarsa? Murmushi ya kuma yi ya tashi yayi sallah sannan ya zauna cin abinci.


Rabonshi da yaci abinci ya koshi har ya mance amma yau har kari yake nema. Bayan ya kammala komai ya zauna tare da zubawa ko fa ido ko zata shigo amma shiru. Tam yasan bazata zo ba dan haka ya tashi ya lallaba ya kwanta domin bacci da yake ji.


Itama haka abin yakasance agun nata, farin sosai tayi da ganinsa amma bazata iya komawa gurinsa ba domin tambayar kanta take me zata ce dashi? Ga murmushin jin dadi da baya yankewa a fuskarta.


Raihana tace ni kada ki dame ni da wannan murmushi in zaki tashi ki tafi to, in ko so kike in bar muku gidan ne zan iya komawa hostel


Da sauri Haneefah tace na daina yi hakuri, muyi karatun mu. Cike da farin ciki na musamman tayi karatun ta.


Washe gari da safe ta tashi tayi breakfast sannan ta shirya domin fitan safe zasuyi. Bayan sun shirya ta dauki karamar ta karda tayi rubutu ta ajiye daidai kofar Yusuf tana murmushi suka fice.


Tunda yaji tashiwar mota yadan suna suka fice, bai kawo komai aransa ba yaci gaba da kwanciyarsa sai kusan karfe goma ya tashi. Bayan yayi wanka ya shirya ya bude kofa ya fito domin zuwa kitchen.


Yana bude kofa yaga karamar takarda an ajiye biro akai kada iska ya dauke shi. Saka hannu yayi ya dauka domin bazai wuce sakon sa bane yaga an rubutu:


_Ina fata ka tashi lafiya? Ya gajiyar hanya? Nasan kana tattare da gajiya shiyasa banyi yunkurin bude maka kofa ba domin nasan kana bacci. Na fita makaranta breakfast naka na falo, a huta gajiya_


Murmushi yayi tare da kissing paper yace Allah dawo dake lafiya. Ya nufi falo ya tarar da lafiyayyun breaskfast ya soma ci. Bayan ya kammala ya tattara kayan ya tashi ya nufi kitchen. Zaga gidan yafara yana nazarin yadda akai ginin, gidan ya mishi kyau gashi ba babbane sosai. Bayan ya gama yazo ya kunna tv ya soma kallon news.


Zaune suke suna karatu dayan uwanta amma hankalinta ya soma tafiya gida, ganin karfe daya yakamata ace sunje ta dafa masa lunch. Tun kafin tayi magana Raihana tace mu zamu wuce gida sai zuwa gobe.


Daya daga cikinsu tace haba Raihana da wuri haka? Raihana tace daliline yasa, sukai sallama suka tashi.


Bayan sun iso gida sukai parking Raihana ce agaba, da sallama ta shiga falo. Ganin Yusuf zaune yasa ta nufi inda yake da fara'arta tana gaisheshi. Shima gaisheta yayi yana tambayarta ya karatu? Tace Alhamdulillah.


Yace Allah taimaka ya amsa da ameen. Suna dan taba hira Haneefah ta shigo da sallama, ta kasa kallon inda suke zaune tace wani kalma tayi wucewarta. Raihana baki bude take kallonta harta shige Yusuf yace inkin shiga ciki ki turomin ita.


Tunda ta shiga taji kunya ya lullubeta, mesa nayi haka? Tana cikin tunani Raihana tashigo cike da mamaki tace Haneefah lafiyarki kuwa? Nifa nakasa gane kanki, keda kanki kike wahalar da kanki? Mutum yazo tun daga garin ku mai nisannan amma kinkasa ce masa ya yadawo? Koma menene kije yana kiran ki.


Jin yana kiranta yasa taji babu dadi, maimakon ita taje ba sai ya nemeta ba. Jiki babu kwari ta nufi banda ki ta watsa ruwa ta fito ta shirya cikin mintuna kalilan ta fice ta nufi falo.


Wayam ta gani bayanan, hakan na nufin yana dakin shi. Kamar zatayi kuka ta nufi dakin shi. Knocking daya tayi taga an bude mata kofa, da sallama ta shiga amma taji shiru. A hankali ta shigo dakin tare da maimaita sallama.


Daga bayanta taji an amsa tare da rufe kofa. Da sauri ta juya tana kallonsa. Shima kallonta yake cike da tsananin so.


Dukkaninsu sun kasa cewa junansu komai, a hankali ya tako yazo dab da ita, ganin haka yasa ta soma ja da baya. Tsayawa yayi yana kallonta yakacewa komai. Sulalewa tayi ta zauna kasa tana furta ina yini


Baice da ita komai ba, ganin yayi shiru a hankali ta dago idanunta suka hada ido. Abinda taganine yasa gabanta ya fadi tare da mikewa.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFA* 👩🏼64


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Hawayene cike a idanunsa wadda yake kokarin zubowa abinda bata taba gani ba. Bakinta na rawa tace meyafaru? Bani bace ko?? Da sauri ya matso kusa da ita tare da rike hannayenta yace na rokeki ki daina fushinnan, zan iya jure komai amma banda fishin ki, bani da laifi cikin al'amarin nan sannan in kika duba mahaifiyata ce bani da zabi da ya wuce inbi umarnin ta, amma badan raina ya so ba, ina sonki kina so na kada wannan abin yasa mu wahalar da kawunan mu bakisan yadda nake jiba lokacin da na rasaki amma yanzu Allah ya qara hadamu plss ki huce....


Kasa karasa maganan yayi ya lumshe ido sai ga hawayen dake makale ya zubo. Haneefah tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta. Itama fashewa da kuka tayi zata gudu ta fita ya rikota. Tsayawa tayi tana kokarin fizge hannunta domin kukan yaci karfinta amma yaki sakinta dan kanta ta tsaya hakan taci gaba da kuka.


A hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta yana cewa shikenan tunda nine bakison gani nizan koma inda na fito. Cikin kuka tace a'a


Yusuf yace toh me abin kuka? A hankali tace farin cikine yamin yawa amma ni ina sonka, ban taba kawo araina ina da sauran rayuwa tare dakai ba, yau gashi lokaci daya mun kasance tares. Alhamdulillah ya furta a hankali, nima ina sonki sosai Haneefah mukasance masu godewa Allah... kokarin kwace kanta take ya saketa yana kallonta tace lunch zanje in girka maka.


Murmushi yayi yace akoshe nake domin jinki atare da ni... da sauri zata fita ya rikota a tsoroce ta tsaya domin da gaskenta tsoro take ji.


Zagayowa yayi zuwa gabanta, ganin yadda ta sauke kai ya saketa yace jeki... tana fita yabi bayanta da murmushin jin dadi yana kara godewa Allah cikin zuciyarsa da ya azurtasa da abin kaunar sa wato Haneefah a matsayin mata.


Kamar jiya abinci mai kyau ta dafa masa amma tsoron kaiwa take, ta dauki ita da Raihana ta wuce dakin su. Bayan takai tazo ta dauki nashi ta nufi dakin shi tayi knocking ya amsa ta shigo a hankali.


Zata juya ta fita yace ina zaki? Ganin ta tsaya bata ce komai ba ya ta so da kansa yazo yace bazaki zauna muci tare ba? Nan ma tayi shiru ganin yana kokarin riketa ne tace a'a naka ne ni naci nawa.


Ganinta a tsoroce yace toh zauna ki tayani hira. Rashin son jayayya yasa ta koma inda ta ajiye abinci ta fara zuba masa. Duk wani motsin ta akan idonshi, ji yake tamkar ya maido ta ciki amma ya lura kamar a tsorace take.


Bayan ta gama ta samu guri ta zauna ta sunkuyar dakai domin jikinta ya bata idanunsa na kanta. Ya soma cikin abinci, yace yaushe exams naku? Next month ta bashi amsa. Farin ciki ya bayyana a fuskar shi yace ashe kun kusa.


Tace eh amma zamuyi sati uku that's mean sai upper month zan gama. Yace good. Ya zakiyi da aikin ki? Bazanci gaba da aiki dasu ba, zan san yadda zamuyi mu rabu lafiya.


Dauko wayarsa yayi ya nuna mata hoton kyakykyawar yarinya yace wannan itace diyar Aisha sunanta Ra'ima. Haneefah ta karba tana murmushi tace Allah raya ta ya amsa da ameen.


Garin mika masa wayar ya tsanta ya taba wayar nan ya canza zuwa hoton sa rike da jariri. Nan da nan hawaye ya ciko a idanunta tace ya sunan babyn ka? Kallon hoton yayi yace ba nawa bane na salma ne, ni bani da yara amma inshaaww Allahu mun kusa samuwa ni da ke.


Shiru tayi tana kallon hoton tace yaran Rahma nawa? Murmushi yayi yace har muka rabu bamu haihu ba.


Cike da mamaki ta dako kai tana cewa rabuwa? Wacce kenan? Yace already tayi aure, tun shekaru uku da suka wuce. Mamakine ya cika Haneefah amma bata kuma cewa komai ba.


Ya gama cin abinci ta soma tattarawa zata fita yace inkin kai ina son ganin ki. Kamar yadda ya bukaci ganinta ta shigo ta same shi zaune kan gado da alama yana jiran isowarta. Nesa dashi ta zauna a kasa. Murmushi yayi yace ta so ki zauna nan ya nuna mata kan gado.


A hankali tazo ta zauna dan nesa dashi ta sunkuyar da kai. Yace Alahmdulillah, aduk abinda dan adam zayyi kada ya gajiya da godewa mahaliccinsa, yau gashi ni da ke mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login