Showing 69001 words to 72000 words out of 74305 words

Chapter 24 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5183

yar'uwa. Da sauri ya shiga falo. Ganin rahma da Umma nusaiba yayi suna zaune.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼66


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Shi kadai tasan zai iya aikata mata hakn. Kulle kofan yayi ya tsaya bakin ko fa yana kallonta tare da harde hannayensa a kirji.


Shiru tayi ta saukar da kai kasa domin kwarjini ya mata sosai ga bala'in kunyar sa da take ji. Baice da ita komai ba yana kallon ta.


Ganin shirun yayi yawa ta dago ido suka hada, fuskarsa ko murmushi babu. Tace kayi hakuri ni fa.... yace me kikamin da zaki bani hakuri? Ni kallon ki kawai nakeson yi tunda ke baki bukatar kallon mijinki.


Hawayene suka taru idanunta tana kokarin zubda su ya jawota tare da rungumarta ya soma lallashin ta yace shikenan me abin kuka godewa Allah zamuyi a wannan rana. Congratulations my dearie, proud to have u in my life.


Lumshe ido tayi ta kwanta a jikinsa sosai tace am sorry dear sai yau kazo min inata jiranka, i really missed u.... yayi sauri dago ta yace da gaske? Zatai magana taji Raihana na kiranta. Da sauri ya saketa ya bata hanya ta wuce yana murmushi.


Bayan sun gama cin abinci Kevin ya bukaci suyi masauki a gidansa domin gidan Haneefah bazai ishe su ba. Kafin su tafi Dr Mubarak yace yana son kallon Dr Michael.


Raihana tace in akan maganan aikin Haneefah ne ina son biyo ku. Mota biyu suka ciko suka nufi asibiti amma basu same shi ba, Kevin ya musu jagora zuwa gidan sa.


Babban gida ne wadda yake kunshe da dukkanin abin bukatan rayuwa, duk fadin gidan Dr Michael da dan sa ne kadai ke rayuwa ciki sai masu aiki. Suna shiga yana shirin fita. Yana ganin Haneefah ya fadada murmushin sa tare da tayata murnan gama karatu.


Shiga ciki yayi dasu yana cewa yanzu nake shirin tafiya. Bayan an gaisa Dr Mubarak yace kamar yadda is sanni ni yayan Haneefah, mun gode da kulawar da kuka bata har ta kaiga wannan mataki amma yanzu muna so ka sallameta a aikin ta.


Da sauri Dr Michael yace dalili? Dr Mubarak yace saboda inta koma aure zatai sai dai intayi auren mijin da ta aura yana da sha'awar zuwa nan saiku sake daukan ta aiki amma in har baku sallameta ba hakan zai jawo matsalar da bazata sake zuwa ba.


Dr yace bana bukatar matsalar da zai hanata zuwa, Haneefah yarinya ce karama mai kwazo ina da tabbacin ko mijinta zai barta tazo.


Haneefah tace sir ina bukatar sake zuwa amma in bakai yadda yayana yace ba hakan zai kawomin matsala domin al'aldunmu daban da naku.


Dakyar baturennan ya amince ya sallami Haneefah. Murna kowa yake a haka suka je gida domin sanar da Abba.


Bayan sunje sun sanar da su sunyi farin ciki sosai dan haka suka soma shirin tara kayansu domin koda yaushe zasu iya suce su tashi.


Gidan Kevin babba ne sosai, wadda kowa is samu daki daidai. Haneefah na makale da Umma, tana sane da Yusuf amma tasan inta koma Nigeria bazatayi cikekken sati uku a gida ba za'ace ta tare gidansa dan haka take moran umman ta son ranta.


Kullum suna cikin fita su zaga iyaye guraren tarihi da ban mamaki da, sanin da Raihana da Haneefah sukayiwa London ko Dr Mubarak sai da yayi mamaki. Iyayensu sunyi farin ciki da karatun su domin babu wani abin aibu da suka aikata sai dai ma yabon yaransu da ake.


Ana gobe Raihana zasu wuce Dubai Haneefah duk taji babu dadi,dukkan su suka zauna jugum sunyi shiru. Basusan ma an kwankwasa kofa ba ganin Ummi da Umma sukai. Zama sukai suna lallashin yaran nasu suka ce ai dan an rabu yau har abada suna tare.


Washe gari har airport suka raka su, dukkansu suna kuka har suka rabu. Yinin ranar Haneefah taji babu dadi domin sunyi zaman amana da mutunci da Raihana, bazata taba manta ta ba. Suma suka soma shirin zuwa Nigeria.


Tun tafiyar Raihana, Haneefah ta zamto abin tausayi domin bata da hira sai na Raihana. Bata iya hira da kowa sai na Raihana. *_Zumunci domin Allah ba karamin abu bane_*


**** ****


Misalin karfe bakwai motar su tayi parking cikin gida. Kowa na tsaye yana jiran shigiwarsu. Suna sauka a mota akayo kan Haneefah ana mata oyoyo.


Itama murnan ganin yan uwanta ta rungumesu tana farin ciki. Ko zama su Dr Mubarak ba suyiba suka ce zasu wuce gida, Yusuf ma yace su sauke shi a gida. Duk hankalin Haneefah na kan Yusuf har suka fice daga gidan.


Kowa na murnan zuwan ta, so da kauna annuna matashi, inna da yaranta babu magana anata hidima. Hadiza ta zo ita da ummulkhairi da kaninta sadiq, Haneefah tayi murna sosai kullum tana cikin dangi ko wayarta bata kula ta nemi sim card ba amma masoyin nata na nan cikin zuciyarta tana son kiran shi.


Bayan zuwan su da kwana uku Nana ta haifi danta namiji. Ranar suna danta yaci sunan surikinta wato baban Dr Abdullahi.


***


Da yamma misalin karfe hudu. Zaune take tana nazari ciwon da takeji a karkashin maranta, tunani take abinda take boyewa ya kusa bayyana amma in har yasameta wani magani zata sha? Gashi tun da tazo bata samu zama ba bale Yusuf yazo su fara maganar tarewarta ko dai yayi fishi ne? Itama bata kira shiba.


Mukewa tayi ta dauki wayarta ta nufi dakin Nana, ta tarar bata nan. Daukar wayar Nana tayi ta saka lambarda kwana ki yakirata dashi ta soma kira.


Zaune yake ya kurawa hoton ta ido. Yau kusan sati biyu amma ko saya basu yiba. Tunani yake yadda zai tunkareta da maganar tarewarta gashi gurin aikinsu an damesa da kira, gini ya kare.... yana cikin tunani yaji ankirashi a waya kamar bazai daga ba amma ya yadaga tare da yin shiru.


Jin sallamarta yasa ya lumshe ido tare dajin wani bakon abu na ziyartan zuciyarsa. Baice da ita komai ba ta kareshi gaishe shi.


Sai taji bata kyauta mishi ba tace kayi hakuri ban samu zama bane amma.... bance komai ba amma kina bani hakuri, in har kina son na hakura zan so ganin ki zuwa anjima.


Shiru tayi sannan tace ina gidan Nana amma zuwa gobe zan koma gida. Yace zanzo anjima misalin karfe takwas. Katse wayar tayi jin wani abu na sokinta a ciki amma tayi shiru tana nazari.


8:00pm


Duk da ciwon da take ji amma ta daure ta shirya domin tana bukatar ganin masoyinta. Wayar Nana na hannunta taji an kira, tana dagawa yace ina kofar gida ina jiran ki ya katse wayar.


Mikewa tayi zata sako hijabi Nana tace gun mijin naki saikin dauki wani hijabi? Karba tayi ta mika mata gele tace kitafi da wannan. Haneefah ta karbi gelen domin bata son dogon surutu, so take taje ko gaisawa ne saita komo domin abinda takeji ya soma yawaita.


Hangota yayi ta fito sanye da gele, kasancewar gurin da haske ya kare mata kallo, light makeup tayi. Ganin zata koma yasa ya hasko mata huta tare da kashe wa a lokaci daya kasancewar inda yake da duhu.


Haneefah ta nufo inda yake zata bude kofar gaba taga an bude kofar baya. A sanyaye ta shigo ta rufe motar. Shiru yayi yana kallonta


Dakyar tace dashi ina fata ka yini lafiya? Lafiya ya amsa. Yadda ya amsa yasa ta dago ido tana kallon shi, wannan karon ba ita yake kallo ba alamun kamar yana fishi da ita.


Kokarin bude motar ta fita ya kulle motar da remote dake hannunsa. Juyowa tayi tana kallonsa shima kallonta yake. Yace, ban samu ganinki ba tun da muka zo, baki kirani ba yanzu da kuka zo ko minti goma bakiyi ba zaki koma?


Ta sunkuyar da kanta, kamo hannunta yayi yace yanzu kin zama matata, kin gama makaranta ya dace ace mun fara maganan tarewarmu..... kayi hakuri ba laifi bane tana magana tana kokarin kwace hannunta


Shima yace in kina son na hakura bani minti biyar zan hakura.... kafin tace wani abu ya dora bakinsa kan nata, kuka ta saka marar sauti, saida taji ya saka hannayensa cikin riganta ta soma kuka. Kokarin zuge zif na rigarta yake cikin kuka tace dan Allah kayi hakuri zan koma gida.. baice da ita komai ba yarungumeta tareda mata rada a kunne yace saikin amince nan da kwana uku zamu tare inba haka ba bazan kyale kiba.


A tsorace ta tureshi tace nidai kai hakuri... sake rufe mata baki yayi da nashi.... wasa sosai yake da ita bai ankara ba yaga ta fadi jikinsa sumammiya.


Shima a tsorace ya dagota amma yaganta ta koma, yace shikenan na kyaleki tashi Haneefah... dagota yake amma sai yaga ko motsawa bata yi.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼69


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Tana cikin wannan hali taji ana konkosa kofar falo. Shiru tayi domin Yusuf yace kada ta bude kofa sai ta tabbar wanene.Tsorone ya lullubeta ta zo daf da kofar tana tambayar wanene?


Yusuf yace nine. Jin muryarsa yasa ta bude kofar da sauri, tana budewa ta rungumesa tare da fashewa da kuka tana cewa ina ka tsaya inata jiranka.Kamshin turarenta ya bugi hancinsa ya shaka tare da lumshe ido yace yi hakuri dearie motatane ta baci ko gyarawa ban samu ba.


Rungumeta sosai yayi yace sorry nabarki ke daya ko, gani nazo bazan kuma ba. Rungume da ita yashigo ya rufe kofa. Har bedroom suka je a haka. Saida suka zauna bakin gado yake kallonta. Kura mata ido yayi tamkar zai maidata ciki ya nemi gajiyan da ya dauko ya rasa.


Ita kuma ta tashi tashiga bandaki hada masa ruwan wanka. Duk motsinta yana kallonta har tazo ta soma taya shi rage kayan jikin shi. Kasa hakura yayi yajawota jikinsa yana shakar kamshin jikinta yace kullum kara kyau kike.


Kwanciya tayi jikinsa cike da shagwaba tace aika fini kyau... bata karasa ba taji ya kwantar ta kan gado. Ganin abinda yake shirin yi tace pls ka tashi na hada maka ruwa


Da sauri yace pls dear yau zaki tayani? Zaro ido tayi ya tashi yana yar dariya yace matsoraciya kada yauma ki sumemin. Yana shiga ta tashi ta ciro masa kayan da zaisa ta dauki nata ta nufi dakinta dashi.


Bayan ta fito daga wanka ta shirya tsaf cikin nighty daya tsaya mata iya gwiwa. Ta kama kanta da ta fashe jikinta da turaruka ta fito.


Zaune ta samesa ya shirya yana amfani da laptop. Tunda ta shigo ya kura mata ido, ya rasa ya zayyi ga abinda yake ji cikin zuciyrsa. A hankali ta'iso tace dare nayi yakamata kaci abinci. Babu musu ya taso suka nufi dinning table.


Bayan sun gama cin abinci ta fara hamman bacci. Suka kashe komai suka nufi bedroom. Kwance take a girjinsa tana kokarin bacci, yana shafa bayanta a hanakali har ya sauko da kanshi daidai fuskarta yace pls dearie yau kada ki suma.


Yadda yayi magana harta ji tausayinsa amma tace ka gaji sosai bacci kake ji ka kwanta kayi baccin ka. Ganin bazai samu hadin kai ba yasa ya lumshe ido amma ya qara budewa a hankali yace pls dear watan mu biyarfa nayi kokari ai. Tsananin tsorone yasa tajuyar da kanta bangare daya. Tanaji yana mata magana amma tayi shiru kamar mai bacci, shima shiru yayi yana cije lebe.


Tabbas Yusuf yayi kokari amma tsoro take ji. Gabanta ne ya fadi data tuno tsinuwar mala'iku ga matar da taki amincewa da mijinta. A hanakali ta juyo da kanta ta kwanta a kirjinsa, rungumota yayi sosai a hankali tace tsoro nake ji. Shi kuma yace shikenan kiyi baccin ki, ke kadai nake bukata gashi nasameki.


Cikin sanyin murya tace na amince. A hankali ya dagota suna fuskantar juna yace kin amincemin? Gyada kanta tayi alamar eh tana kokarin hawaye. Bai kara ko second daya ba ya soma mata salon da ta mance wani duniya take.


**


Bayan ya fito daga wanka ya nufi gurinta tare da taimaka mata suka nufi banda ki, kin amincewa tayi ya mata wanka dolensa ya kyaleta ya fito. Mamaki ne ya cika shi abinda ya gani, da sauri ya canza bedsheet din ya gyara, tana fitowa ta nemi magani ya kawo mata tasha sannan ta kwanta.


Bacci take hankalinta a kwance. Shiko ogan sakata agaba yayi yana kallonta, tsananin kaunarta ne ke fizgeshi musamman inya tuno a wanni da suka gabata. Tashiwa yayi ya soma nafilfilu tare da nuna farin ciki da godiya Allah daya mallaka masa wannan baiwar tasa.


Dakyar ta tashi sallar asubah, domin ya zame mata jiki bata taba barin wannan lokaci ya wuceta sai rashin lafiya mai tsanani ko tasha magani mai karfi. Tana idarwa ta koma bacci, shima yana zuwa daga masallaci ya kwanta rungume da Haneefah.


Kusan karfe tara da rabi ta tashi, ita kadai ta gani hakan na nufin yana falo. Daurewa tayi ta mike tashiga toilet. Ta sake hada ruwan zafi ta shiga ta zauna sannan ta tashi tayi wanka. Daure take da towel tana nazarin kayan da zata saka domin bazata irin na jiya ba duk shi yaja mata. Riga mai dogon hannu zuwa gwiwa da dogon wando ta nemo, duk cikin kayan shine mai dama dama, ta dauki hula ta saka. Ta feshe jikinta da turare tare da shafa powder da man baki. Gani tayi light makeup din ma ya canzata, tana shirin fita shi kuma yana shigowa. Da sauri zata koma yayi saurin jawota ta fada jikinsa. Daukarta yayi sai kan gado, tsoro ya dada lullubeta kada ayi gidan jiya.


Kamar yasan me take tunani ya kwantarta a hankali yayi kissing nagoshinta, babu shiri tace pls kayi hakuri bani da lafiya.


Cike da tsokana yace warkewa zakiyi da zarar' na mik.... mikewa tayi tana kokarin boye kanta cikin kirjinsa. Murmushi yayi yana shafa bayanta tare da cewa wasa nake miki, ina fata kin tashi lfy? Kunya ya lullubeta tace ina kwana? Ya amsa cike da farin ciki ya mata ya jiki?


Shiru tayi tare da yin lamo a kirjinsa. Lumshe ido yayi, yana matukar jin dadi aduk lokacin da takasance a kirjinsa. A hankali yace nagode Haneefah, a kullum ke dabance, a kullum salon ki kara yawaita soyayyarki da kimarki yake aguri, all these years u keep ur self for me? Nayi sa'a a duniya tabbas dukkanin wani bawa daya fawwala komai nasa a hannun Allah alkhairi na biye da lamarinsa.


Haneefah tace tabbas maganan ka haka yake, nasan zamu sake kasancewa domin inada yakinin Allah maji rokon bayin sane, ta dago a hankali tana kallon shi. Kama hannuwansa tayi tace ni nasan nayi dacen miji, mai so na, wadda yake gudun bacin raina, wadda ra'ayinmu yazo daya tabbas nina kasance mai sa'a


Lallausan murmushi ya sakar mata yace me kike so a duniyar nan? Itama murmushi tayi tace kulawarka kadai nake bukata. Rungumeta yayi yace kin samu. Jinsu suke tamkar su hadiye juna tsabar SO.


Zaune suke kan dinning table suna breakfast amma taji bata kaunar zaman ma. Daurewa tayi suka karasa. A tare sukai komai, zaune suke taji ya kira office ya dauki excuse bazai samu shigiwa ba madam nashi bata da lafiya.


Haneefah taji dadin haka, a haka har bacci ya sace ta. Shiya kaita bedroom ya kwantar da ita. Yusuf kallon Haneefah baya isarsa. Haka yakasance cikin jinyarta.


****


Rayuwa ya dawowa masoya biyu sabuwa fil, Haneefah ta kauda kunya tana nunawa mijinta kulawa haka shima, ya bata dukkanin lokacinsa da kulawa, komai nasa Haneefah.


Zaman lafiya ke wakana tsakanin Umma da Inna haka yaranma kansu a hade.


Babu wadda yakai Momy ji da Haneefah, haka ga family gaba daya kowa Haneefah.


Burin Haneefah ya cika tsakaninsu lafiya da kowa hakan na mata dadi sosai sai dai haryanzu babu ciki, yanzu burinta bai wuce takai Umma, Abba da Inna saudia ba.


_Bayan wata biyar_


Zaune take tana jin tashin zuciya, yau breakfast nasu tayi toasting bread da kwai, tunani take ko warin mai ne ke sata jin tashin zuciya?


Shiga banda ki yayi yaga bata wanke ba bale ta hada masa ruwan wanka. Bayan ya gama shiri tsaf ya zo ya sameta a inda ya barta, zuwa yayi ya tsugunna gabanta.


Dago idanu tayi cike da hawaye tana kallonsa, da sauri zata mike bata ankara ba ta koma ta fadi.....


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼68


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


A hankali ya karaso falo ya tsugunna har kasa ya gaishe ta. Ta amsa cike da jin kunya.


Salma ce tace yaya yanzu Aisha ta kirani a waya take sanar dani labari mai dadi, amma Yaya sati daya ai yayi wuri


Momy dake zaune tana murmushi tace ai kun gama shirin ku tun wuri salma saura daukar amarya. Ganin Yusuf ya tashi ya shiga yasa salma ta bishi a baya.


Momy ta dubi yar uwarta tace, Yusuf da dukkanin yarana naki ne, abinda ya wuce yariga ya wuce sannan kin aikata hakan a kuskure sai dai a kiyaye na gaba. Babu yadda zanyi domin ba ni da wata yaruwa da ta wuce ki. Sannan bazan kyamace ki ba domin kin aikata hakan, fatana shine Allah yarabamu da duniya lafiya


Umma nusaiba ta goge kwallar da ta zubo mata cike da nadama tace nagode, insha Allah bazan kuma aikata makamancin haka ba.


Dukkaninsu suka kasance masu danne zukatan yan uwansu tare da addu'ar kore dukkanin wata sharri.


Labari yaje kunnen yan uwa na kusa domin umma tace walaima kadai za'ayi. Haneefah ta komo gida. Kuka ta zauna yi tana cewa wani irin shiri zatai a sati daya? Aunty Muhibbat dake zaune tace aike kin gama shiri domin auren naku tun yaushe? Ko kina nufin tafiyan da yake gunki babu abinda yashiga tsakanin ku?


Haneefah tace ni sau daya ya tafi kuma tunda nace yayi hakuri bai sake zuwa ba sai ranar graduation namu da suka tafi.


Mamaki suka shiga yi. Haneefah ta share hawaye tace ni yanzu Dubai nake son tafiya shopping, amin gyaran jiki amma lokaci duk ya kure.


Hadiza tace lokaci bai kure ba, indai gyaran jiki ne akwai wadda za'a miki kwana biyar kadai zaki haska, amma hakan ma ai kin canza Haneefah amma kuma yafi kyau a miki dilke, yanzu inna tashi daga nan zan wuce inje in dauko mai dilke, bayan kwana uku sai a miki kunshi tunda dilke muddin ana yinshi safe da yamma for you kam 3days ma is ok.


Sannan yanzu ki kira Raihana tunda taga shopping da kukai na auran Aisha saiki aika mata kudi ta miki...


Aunty humaira tace shopping a Dubai is not easy akwai kaya masu kyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login