Showing 15001 words to 18000 words out of 74305 words
Chapter 6 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
karshe yaji wayar a kashe.
Haneefah tana kwance tana kuka har kusan karfe sha biyu, tsabar kuka har kanta sarawa yake. Daga karshe ta dauko wayarta ta kunna domin muryar shi kadai zataji ta iya tsagaita kuka.
Zaune yake kan sallaya yana karatun Qur'ani mai girma yaji sautin wayar sa, yayi saurin dakatar da karatun da fatiha ya dauko wayarsa. Dadine ya lullubeshi ganin itane ya dauka tare da sallama. Shiru tayi bata ce komai ba.
Yace pls kiyi magana tun dazu nake tabinki arai, Allah sadai ba kuka kikai ba. Kiyi hakuri in har ban fada miki ba yazama wani abu daban shiyasa na sanar dake amma Allah baki hakuri, kinji? Katse wayar tayi sannanta tashi daga kwanciyar da nufi bandaki tayo alwala ta fito ta fara jero nafiloli sannan ta fara neman gafaran mahaliccinta kan ya yafe mata, ya bata ikon kadaitashi a zuciyarta da tsoronsa da soyayyar ma'aiki annabi Muhammad (S.A.W). Sannan tayi addu'a Allah tabbatar mata abinda yafi alkhairi tsakaninta da yusuf. Ta soma karatun qur'ani har bacci ya dauketa inda take.
Har an fara sallah a masallaci tukun ta farka, kasancewar batayi bacci ba. Da sauri ta nufi banda ki tayo alwala tazo tayi sallah. Bayan ta kammala ta jawo wayarta ta kunna ta shiga kira yusuf.
Dawo warshi daga masallaci kenan yaji kiranta. Yana dagawa ta gaishe shi ya amsa cike dajin dadi, yace pls dearie.... ka tseshi tayi tace ya wuce muddin ina sonka dole in tayaka yiwa momy biyayya, ko da tace bazaka aure niba na yarda. Farin cikinta shine hanyar shiga aljannar ka, niko ina alfahari tayaka ko wace irin biyayya domin inason ka gama da duniya lafiya. Dole nayi kishi saboda ina sonka! Son da banyi tsammanin yiwa wani ba, ban taba ko da mafarkin kasancewa irin wannan yana yin ba, sannan dabi'atane in raina ya sosu muddin banyi kuka ba banajin abin zai gushe amma da zarar na zubda hawaye, everything is over. Am sorry. Murmushi yayi yace am proud to have u, banida abinda zance.
Dariya tayi tace abubuwa da dama, naga tsarabarka nagode sosai sannan nayi matukar farin ciki, amma ai sunyi yawa? Babu wani yawa kin wuce haka haneefah, Allah bani ke matsayin mata. Tace ameen, ka kwantar da hankalin ka, kayi tuki cikin nutsuwa inka iso sai muyi waya ko? Toh shikenan ranki shi dade, saina kira.
Wani sanyi yaji aransa, haneefah yarinya karama amma rayuwarta so simple. Hannu ya daga yana addu'ar Allah mallaka mashi haneefah.
Itako bin wayar tayi da kallo, a hankali ta daura wayar a kirjinta tana cewa ina sonka yusuf. Sannan taci gaba da laziminta har rana ta fito. Abba ya shigo da safe umma ke nuna masa kyautar yusuf. Yabawa yayi yace a sufar lafiya.
Haneefah tana sake kallon kyautar tana murmushi. Tana son manyan wayoyi sai gashi Allah ya mallaka mata, a sannu Allah zai mallaka maka ni yusuf ta fada a hankali. Tasa wayar a chargy ta kama ayyu kan gida.
Bayan ta kammala ayyu kan gida tayi kwalliya, tayi kyau sosai. tasa daya daga cikin dogayen rigunan da yusuf ya kawo mata ta cire wayar a chargy ta kira bintu ta fara daukanta a hotuna. Tayi kala kusan goma ta qara canza riga da siket na atamfa Shi ma tayi hotunan dasu. Ta zabi guda biyar masu kyau ta tura masa ta WhatsApp. Bayan ya koma yakira haneefah yake sanar da isowarsa tace na tura maka sako ka bude ka gani.
Idonsane suka sauka kan hotunan, sun matukar yin kyau, ya tsaya wani kan rika da siket da bata da gele.. zubawa surar jikinta ido yayi ko giftawa baya yi. Lallai haneefah shiyasa kullum kike cikin hijabi. Farin ciki da godiyarsa ya nuna gareta, sannan addu'a Allah mallaka musu juna.
Dariya tayi tace ai nazama taka, fatiya da shaidu muke jira. Shima dariyar yayi yace Allah nuna mana
*Dr HANEEFAH* 👩🏼18
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Tun daga wannan lokaci alaqarsu ta dada nunkuwa, kullum kowa so yake ya faranta ran junan su.
Anje har adamawa ansa ranar aure rahma nan da wata daya. Murna gurin umma nusaiba ba'a magana, sai dada hura kunnen yar tata take da hudubar banza, ita ko rahma burin magaifiyarta zai kaita gidan ba zaman har abada ba.
Su haneefah an koma makaranta amarya hadiza ma ta fito. Haneefah ke tsokanarta har tagaji. Hadiza tace nidai bazaki ji komai abakina ba zaki gani da idonki in lokacin ki yazo.
Haneefah ta kawar da kanta ta danne zuciyarta kan auren yusuf, domin ta fahimci damuwar ta itace tashi, ita ko batason bacin ransa. Ita yanzu karatu tasa agaba, domin cike burin mahaifanta da mosoyinta.
Bangaren nana ma bata samun wata matsala abangaren karatun ta. Sai dai muce Allah basu ikon cimma burinsu.
Biki yazo momy sai shirye-shirye, shiko yusuf baisanma suna yiba. Kayan lefema momy ce ta hada, sannan rahma ta da meshi kan occation, shidai yace babu ruwansa haka ta hakura.
An daura aure amma ko ango bai halarci wannan aure ba. Momy tace ya aiko kudin jirgi a wuce da amarya rashin son gardama yace a kawo ta kano side nashi inyaso inya gama gyaran gidanshi sai suzo abuja.
Haka ko akai, aka kawo amarya kano. Haneefah har wata daya yayi yusuf baice an daura auren ba, hakan yasa taja bakinta rayi shiru.
***** ***** *****
Bayan wata biyu amarya na jiran ango bata sashi a ido ba amma yakan kiranta su gaisa. Momy ma in sukai waya yace zaizo, so yake in yazo ya koma da ita, hakan yasa ta saurara mishi.
Haneefah ko saura wata shida ta kammala makaranta, a sannan ta bukaci tafiya gidan aunty muhibbat domin cikinta ya tsufa.
Yau lahadi suna gida. Haneefah ta gama shara tana mopping sai yaron aunty muhibbat yazo da gudu tsantsi ya dauke shi kadan ya rage ya fadi yace auucchhh! Aunty haneefah badan kin rike niba da na fadi... tseye tayi tana kallonshi, bismillah zaka ce in kazo fadiwa ko wani abu daban? Mu haka muka saba fada! Muhibbat dake jinsu tace bari haneefah babu yadda
da su ba amma sunki dainawa.
Haneefah tace waya ce tun farko ki koya musu? Zakiga yaro shekaranshi shida amma baisan banbancin wuta da aljanna ba! Don ki tsoratarshi in kikace wuta bai sani ba sai spider man, wlh gomma ku farka, ya zamto yara su tashi da dabi'a ta addinin musulunci ba dabi'an wasu ba. Aunty muhibbat tace toh malama sakita cika ni da surutu. Gaskiyace saina fada.... jin sautin wayarta ta jefarda mop ta wuce amsar kiran masoyinta domin sautin shima daban ne
Sallama tayi suka gaisa, yace zaki iya fitowa da safennan ina kofar gida. Mamakine ya cika ta tace yaushe kazo? Jirgi na biyo. Ok ina gidan aunty muhibbat, saika karaso ta katse wayar. Bandaki tashiga ta watsa ruwa ta fito. Tsaf ta gama shiri yakirata tace ya shigo .
Zaune tasame shi a falo, taga ya canza mata yadan rame. Ta zauna nesa dashi, suka kara gaisawa yace inason ganin kine shiyasa na biyo jirgin safe nanda awa daya zan koma. Murmushi tayi tace nagode da ziyara nima kamar kasan kewar ka nake, ka wuce gida? Aa, mesa? Banason zuwa.
Shiru tayi tana ganinsa bata ce komai ba. Kasa hakura tayi tace meke damun ka? Me kika gani? Ka rame sosai.
Ya kalleta yace aure suka min, ina bin yadda zan sauke hakkin wannan aure, banasonta, na jure amma ko ganinta banason yi. Narasa me zanyi, tun 6years back nace bana so amma sai da akamin, gashi yana son halakani.
Duk zafin kishinta amma ta tausaya mishi. Tasowa tayi yazo kujeran da ke fuskantar shi tace haba yusuf bansan ka da haka ba. Da ilmin ka kada ka soma daukan halayen jahilai. Saboda soyayya bazaka sauke nawin da ya rataya a wuyar kaba? Haba ka dadayin hakuri insha Allah wata rana sai labari, yaushe akayi auren ? Kuna tare?
Aa ya bata amsa, tana gidanmu, anyi auren watanni biyu da suka wuce. Zaro ido tayi sosai tace ai zaka bata lamarin mu. Cikin rashin fahimta yace wani lamari? Taya kake tunanin momy zata amince da auren mu in kana yiwa diyarta haka? Rufamin asiri ban shirya rabuwa da kaiba.
Dariya ya soma jin yadda take maganan. Murmushi tayi tace inaso ka kasance fiye da daa, ka kwantar da hankalin ka. Allah sa hakan shine mafi alkhairi agare ka. Maza kaje gida ka gaishesu pls, ran momy da amarya zai baci, shiru yayi. Kaji ango ya bata rai. Ta soma dariya tana cewa jama'a kuzo kutayi shari'a amarya batayi fishin kishi ba ango yana fishi.
Dariya ya soma. Nan haneefah ta fara zolayarshi yanata dariya har ya manta bacin rai dake tattare dashi. A hankali take kallonsa yadda yake dariya cikin nutsuwa tace zanso ka kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarka koda bana tare dakai. Shiru shima yana kallonta yace kece farin cikina... zatai magana taga agogon dake manne jikin bango tace ai lokacin tashin naka yayi, ya mike itama ta mike domin yi masa rakiya.
A hankali take binsu a baya har suka iso bakin titi, haneefah ta tsayar da mai adaidaita sahu yusuf ya shiga sannan ta koma. Ganin haka yasa momy tabi bayan a dai daita sahun daya shiga har taga inda ya tsaya wato airport. Juyawa tayi ranta abace tana kissima hukuncin da zata yankewa yusuf da wadda tagansu karo na biyu dashi
*Dr HANEEFAH* 👩🏼19
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Tafiya take amma tunanin yusuf take da auran shi har ta iso gida. Aunty muhibbat ta iske a falo take tambayarta har ya tafi? Haneefah ta amsa da eh. Shiru tayi ta samu guri ta zauna tana tunani, aunty muhibbat ta kura mata ido tace meya faru? Haneefah ta dago ido cike da hawaye tace yayi aure!
Ta bata labarin yadda abin yake da yadda suka rabu, ta qara da cewa wallahi ni yanzu shi nafi tausayawa baki ga yadda ya canza ba duk yabi ya dami kanshi.
Aunty muhibbat tace Allah sa haka shine mafi alkhairi agare ku, sannan yanzu lokacine da zaki dada janshi a jiki kibasa kulawa ta musamman, duk da kuna son juna wasu mazan in suka dandani zumar amaryansu zasu manta da wata a waje, ki kwantar da hankalin ki sannan lokacine da zaki dage da addu'a kan wannan lamari.
Haneefah da tuni ta fara hawaye tace wlh yusuf bazai iya rabuwa dani ba, ni matar shi ce, shi mijinane, we belong to each other..... cike da dariya aunty muhibbat ta katseta da cewa mai da wukar hajiya, an daura muku aure shaidu muke jira.
Haneefah tace kullum haka yake cewa, makaranta muke jira na kammala. Ta tashi ta qarasa ayyukanta na cikin gida, tayi girki ta koma daki ta dauko qur'ani tana karantawa har aka kira sallah azahar.
Bayan ta idar aunty muhibbat tace yaushe kikai alwala da har zaki tashi kiyi sallah? Aini da alwala nake zama.
Aunty muhibbat tace duk surutun da kikai dazu alwalan ki bai karye ba? Haneefah tace wayace surutu yana karya alwala? Abubuwan da suke karya alwala shine; yin iska, yin bayi, fisari, suma, nauyayyan bacci, kiss da sauran su... amma banji yadda surutu ke karya alwala ba, sai dai in mutum baya iya rike najasar da zata fito masa daga jiki misali in mutum baya iya rike iska, sannan in yana hira baisan sanda zayyi ba to wannan rike alwala bazayyu masa ba saboda lalurarsa.
*SAKAMAKO (LADAN) ZAMA DA ALWALA*
Daga Abdullahi Ibn Buraidah daga Babansa Allah shi kara masu yarda yace: Watarana da safe Manzon Allah SAW ya kira Bilal RA da me ka rigayeni a Aljannah, na shiga Aljannah sai naji karar takalminka a gaba na, sai Bilal yace Ya Manzon Allah SAW da dai ban sanni da wani abu ba sama da yin Sallah rakao'i biyu kuma dazarar alwala ta warware nike sabuntawa, sai Manzon Allah SAW yace itace. [ Ibn Khuzaima ]
Ko shakka babu zama da alwala na kare bawa daga sihiri in sha Allah.
Ya Allah ka azurtamu da kasancewa cikin alwala a tsawon rayuwarmu ameen.
Suna cikin tattaunawa yusuf yakirata ya sanar mata sun sauka lafiya amma ta dadana nuna mishi rashin jin dadin baije gida ba. Ko sauraron ta bayyi ba ya katse wayar.
****
Kwance take tana fuskantar kofar shigowa daki, gidan da wadda suke ciki baki daya sun fice mata arai. Tunanin barin gidan take. Tasan a baya tana son yusuf amma yanzu gaba ki daya ya fice mata arai tun kafin auren su, inba dan mum ba ai wannan wulakanci ne. Ace yau watanta kusan uku bata sashi a ido ba... zan bar gidannan amma nayi alkawari bazaka auri zabin ka ba ko wacece ita.
Wayarta taji yana ringing ta daga hello mum ina kwana. Daga daya bangaren tace ya kike baby? Lafiya lau mum, mum nagaji da gidannan wlh nifa banyi tsammanin burin ki zai cika ba.
Mum tace wai har yanzu ba ciki ne ko kinje scan suka ce macece? Takaicine ya kama rahma tace mum tun da nazo gidannan ban sashi a ido ba bale maganar ciki ni gaskiya nagaji. Cikin rarrashi tace kada ki damu namiki alkawarin zuwa gobe zai dawo, yanzu zan kira yaya in sanar da ita. Bata kira amsar taba ta katse wayar.
Momy na office tana ayyuka kiran yar uwarta ya shiga. Bayan sun gaisa mum tace haba yaya, ni nayi tunanin rahma zata fi samun kwanciyar hankali yasa na baku ita amma gashi har yau wata uku bata sa mijinta a ido ba? Nidai nayi mamaki, tunda abin yazama haka gobe zanzo in tafi da ita. Tana kaiwa nan ta katse wayar.
Momy ta rasa mezatayi, wato rahma har ta sanar da mamarta. Kiran umma nusaiba tayi tace haba nusaiba, kinsan ni maison kwanciyar hankalin zuri'ar ki ne. Ki zauna kada ki dawo, nasan yadda zan bullowa al'amarin.
Bayan sunyi sallama takira yusuf tace lallai yabiyo jirgin yamma yazo kada ya kuskura ya kwana a abuja. Ya amsa mata da insha Allah zaizo.
Cike da faduwar gaba ya iso ya sameta zaune a falo. Ko gaisuwarsa bata amsa ba zata fara magana yayi saurin cewa momy dan Allah kiyi hakuri, nasan na bata miki rai amma na miki alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba. Shiru tayi tana kallonsa bata ce komai ba tace shikenan tashi ka tafi.
Duk da yasan ba cira yayi ba amma yana addu'an Allah sa ta sassauta masa.
Rahma tana kwance a falo tana kallo ya shigo da sallama. Ko kallonsa bata yi ba bale ta amsa. Jin shiru bai fito ba yasa ta bishi. Waya yake da haneefah idanunsa a lumshe da alama yana jin dadin wayar. Kare masa kallo tayi tsaf sannan taja dogon saki ta fice.
Haneefah tace next month fa zamu shiga last semester. Tsaban dadin jin maganarta baisan sanda ya mike ba yace Allah dear? Wayyo mun kusa kasancewa tare. Murmushi tayi tace Allah kaimu rai da lfy. Nan suka soma hiran yadda zasu tsara auren. Bayan sun kammala wayar yake tunanin yadda zai bullowa momy da maganar.
*** *** ***
Tun daga wannan lokaci kowani weekend yusuf zaizo kano amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsa da rahma. Ita ko kallonsa bata kaunar yi bale ta kaiga su tsaya suyi hira. Haka shima baya shiga tsabgarta har tsawon wata biyu. Daga nan hankalinsa ya karkata kan auren sa da haneefah, yadda zai dauko da maganar.
Yau lahadi dukkanin su suna gida. Ya shiga bangaren mahaifinsa domin gaishe shi ya tarar da momy. Bayan sun gaisa mahaifin nasa ya fahimci kamar da magana a bakin dan nasa yace yusuf kamar kana da abin cewa. Yace eh abba dama wadda muke tare ne tana shirin gama makaranta nan da watanni biyar shine nake son aje neman mun auren ta...
Momy ce ta daka masa tsawan da yasashi yin shiru. Har kana da bakin cewa zaka kara aure? Yaushe kayi auren wlh yusuf ka kiyayeni kada kaga ina daga maka kafa.
Abba yace tunda ke zaki daura masa auren saiki hana in gani. Tun da farko yana da wadda yake so amma kika dage sai ya aureta, saiki bari shima ya auri wadda yake so yusuf Allah tabbatar mana da abinda yafi alkhairi, anjima zan sami abokaina da sauran yan uwa insha Allah gobe zamu je nema maka aure, saika sanar da ita zasuyi baki. Cike da farin ciki ya amsa da toh ya tashi ya fice.
Momy ma ficewa tayi ranta a bace ta nufi sashenta. Zama tayi bakin gado tana tunanin maganan mijinta. Alhaji sai dai kai hakuri amma wlh ko bayan raina yusuf bazayyi zaman aure da kowa ba sai rahma
*Dr HANEEFAH* 👩🏼20
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Yusuf yana fita ya nufi sashin sa cikin sauri ya kira haneefah yana sanar da ita yadda sukai da abba, itama ta nuna farin cikinta.
Da yamma ya dauki hanyar gurin aikinsa. Yasan momy na fishi dashi amma yasan yadda zai shawo kanta.
Haneefah ta sanar da umma, umma ma taje ta sanar da abba. Kwarai sunyi farin ciki, a sannan abba ya sanar da dangi su biyu da makocinsa akan zuwan bakinsa.
**** **** ***
Su aunty muhibbat da humaira sune kan gaba wajen shirye shiryen taran baki. Inna ko lekowa bata yiba ita a yaranta sai tura jabir tayi ya kalle musu wani irin mutane zasu zo.
Haneefah ko tana gidan aminiyarta hadiza anata ta hiran yadda auren zai kasance.
Zaune momy take tana tunanin yadda zata bullowa lamarin. Rahma ta shigo ko sallama babu ido cike da hawayen munafurshi tace momy da gaskene yau yusuf za'akai kudin auren shi? Cike da tausayi momy tace zo diyata. Tazo ta zauna kusa da ita. Kada ma ki tada hankalinki namiki alkawarin ba'ai aurannan ba koda bana raye.
Toh momy ki hana tafiyar mana! Murmushi momy tayi tace abbanku ya dage yanzu, zan kyale suje amma wallahi aure dai bazai aurota ba. Murmushin jin dadi rahma tayi ta tashi ta fice. Aisha dake sauraronsu tayi maza taja da baya ta koma inda ta fito. Sai data tabbatar rahma ta tafi itama