Showing 27001 words to 30000 words out of 74305 words
Chapter 10 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
hankali yace menene? Aisha cikin murna tace yafara magana.
Da sauri Abba ya iso gareshi yace Yusuf? Yusuf yace na'am. Alhamdulillah Abba ya soma furtawa. Nan suke cike da murna. Aisha tarasa mezatai dan farin ciki. Yayarta takira salma ta gaya maya.
Nan da nan suka hade a asibiti, kowa ya zagayeshi yana tambayar ya jikinsa. Ganin yadda kowa ke farin ciki hakan yasa hawayen farin ciki zubowa a idanunsa. Sannan tunaninsa yaje gun ina ma zaiga Haneefah! Aisha da ta lura da hakan tasa hannuwa ta share masa hawaye tace yaya komai yazo karshe mudai mu dage da addu'a.
Allah cikin ikonsa Yusuf na samun sauki, hannunsa ma yayi sauki sai dai karatun nasane sai a hankali. Yana samun kulawa gurin iyayensa da kannensa. Likitoci na aikinsu yadda ya dace. Rahma ko babu ruwanta da shiga tsabgarsa, jiran mum dinta take tazo ta yanke mata wannan zama da take.
Aisha kadai ta lura da takunta, tana tausayawa yayanta domin tasan raba shi akai da Haneefah. Kullum tunaninta ta yaya zata shawo kan wannan al'amarin?
Watan su uku aka sallame shi suka dawo gida, amma har yanzu yusuf bai samu kafa ba, da keke yake amfani. Ganin haka yasa Rahma hankalinta ya tashi kan bazata iya rainon gurguba.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼29
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Hankalin Rahma baki daya ya tashi domin ganin wahalar zatai mata yawa. Nan ta fara neman mum dinta a waya. Mum tace kada ki damu zanzo asan yadda za'ai.
Abba da Momy sun yanke shawarar fitar da Yusuf kasan waje domin duba lafiyar kafafunsa. Cikin wata daya aka kammala shiri zuwa india, Abba da Yusuf kadai zasu. Hakan yayiwa rahma dadi sosai domin yanzu batason shiga al'amaransu.
Suna sauka motar asibiti tazo ta dauke su. Bayan sun sami ganin likita suka masa bayanin komai. Dogon bincike sukai game da lafiyar Yusuf baki daya. Likita ya samu guri ya zauna ya fuskanci Yusuf da Abba.
Likita yace kunzo mana da cewar kafafunsane suka samu rauni al'alin akwai babbar abu bayan wannan. Abba yace ka fahimtar damu likita.
Likita yace ya samu shock sosai a hatsarin da yayi domin dakyar in zai sake haihuwa. Cikin rashin fahimta Abba yace kamar yaya likita? Wannan case din muna samunshi amma ba sosai ba, domin jijiyoyin da suke hanyar da maniyyinsa zai samu fita sun kumbura, in akace za'ai aiki hakan zai zamo hatsari domin zasu iya tsinkewa garin taba su, sai dai zamu bashi magunguna da zasu sa jijiyoyin su sabe, in ya taki sa'an maganin zai mishi aiki inko bai dace ba sai dai kuyi hakuri shi da haihuwa. Duk asibitin da zaije a duniyar nan abinda zaiji kenan.
Abba ya share gumin da ya feso mishi yace toh yanzu likita maganin yaushe zai fara amfani? Likita yace zamu daurashi kai muddin kuka bamu hadin kai, sannan ko wani bayan wata hudu zaizo medical checkup, batun kafafunsa kuma ba abin tada hankali bane zamusan yadda zamuyi amma shima sai an masa aiki.
Abba yace ba komai likita mun gode, a shirye muke da duk abinda kuka umarcemu. Abba ya juya kallonsa gun Yusuf daya jingina a jikin pillow yana jin dukkanin abinda suke tattaunawa.
Abba yace Yusuf kai hakuri sannan ka jure wannan jarabawar da ta sauko maka, hakika inka jure zaka kasance mai kyakykyawar rabu duniya da lahira.
Yusuf ya murmusa yace babu komai Abba , fatana a duniya nakasance mai tsoron Allah da tawakkali dashi a duk halin da na tsinci kaina. Wannan abin bazai tada min hankali ba sai kara nutsar dani da yayi, domin shekararun baya da kafafuna da hannaye na lafiyayya, yau dan nawayi gari nasamu canjin rayuwa bazan yi fishi ba, Alhamdulillah! Da ya bani ikon kasancewa cikin musulunci, fatana na koma garesa yana mai alfahari dani.
Abba yace tabbas zaka kasance cikin bayin Allah salihai, Allah yayi maka albarka. Cikin sati daya akayiwa Yusuf aiki kuma ansamu nasara sai dai bai soma tafiya dai dai ba. Watan su daya suka dawo gida Nigeria.
Abba ya sanar da Momy halin da danta yake ciki, kwarai tayi matukar tausaya masa. Tasan duk ita taja masa, amma tayi alkawarin bazata sake saka ido akan abinda yayanta suka so ba muddin bai kaucewa shari'a ba.
Rahma ko jin haka yasa taji sanyi a ranta domin ta samu hujjar rabuwa dashi taje ta auri wadda taga dama. Takira mum ta samar da ita, ba karamin bakin ciki umma nusaiba tayi ba amma ta soma lallashin yarta kan zata zo kada ta kuskura ta dago wata magana. Rahma ko tace inanan ina jiranki amma kizo da wuri domin ko wacce kwana na daya a gidannan sai naji sun fice min arai.
Da dare bayan ya huta ya nufi dakin Momy domin tunda yayi wannan jinyar bai samu ya sanar da ita abinda ke ransa ba. Zaune ya tadda ta kan sallaya ta idar da sallah tana shirin tashiwa. Yayi sallama ya shigo ya zauna kasan carfet yana qara gaishe ta, cike da fara'a take amsawa tare da yi masa ya jiki? Ya amsa da sauki.
Ya dago ido cike da hawaye yace Momy sirrin cigaban zaman lafiyane ga dukkanin wani ďa da yake faranta ran iyayensa musamman mahaifiyarsa, ina alfahari dake samun ki uwa domin kin bani cikekken abinda duk wani dan Adam zai bukata ta bangaren uwa, hakika bani da abinda zan biyaki sai dai in miki addu'a tare da faranta ranki..... amma Momy yunkurin nuna bacin ranki gareni yasa na gamu da wannan hatsari, Momy zan miki komai amma ina mai rokon ki kada sake fishi dani.. na yarda da fushin
Rayuwa ta dawo Yusuf sabuwa domin ko wani wayewar gari sai yaji tsananin son Haneefah, ya rasa ya zayyi kowa da rabuwa da kowa amma bazan hira fushin kina, in maganar Haneefah ne na rabu da ita wlh bazan kuma zuwa ko da kofar gidan sune ba nidai Momy dan Allah ki yafeni bazan qara ba... ya karashe maganar yana hawaye.
Momy dauriya tayi ta hadiye hawayenta tace babu komai ya wuce, nidai ka rike Rahma amana domin ina da tabbacin ta isheka komai na matar da kake so, nasan zata rufamin asiri ta zauna dakai lafiya domin ýar uwar kace. Na yafe maka Allah albarkaci rayuwarka ya baka lafiya.
Yusuf baiso jin wannan amsar ba ya amsa da ameen. Yace Momy kitayani addu'a Allah bani ikon daina son Haneefah.
Momy tace zaka daina nan da wani lokaci. Ya tashi ya fita jiki a sanyaye. Bayan fitarsa umma nusaiba takira Momy take sanar da ita tana nan tafe gobe idan Allah ya kaimu.
Yusuf yana fita ya nufi dakin Aisha. Tana zaune tana karatun qur'ani, jin shigowarsa yasa ta dakata ta fuskance shi. Ta gaishe shi sannan ta mishi ya jiki yace da sauki. Aisha tace yadai yaya kamar fuskar ka na cikin damuwa? Babu komai Aisha ina laptop na? Ta tashi ta dauko mishi tace yaya Allah ya rufawa laptop naka asiri da shima ya kone!
Murmushi kawai yayi yace ina ga nan da sati daya zan koma abuja. Aisha tace haba yaya kabari ka dada samun kwarin jiki saika tafi. Yace inna zauna anan babu abinda nake gomma inje can zan rika mosa jiki da ayyu kan office.
Aisha tace Allah qara lafiya. Kallon kanwarsa yake sosai yace inason sanar dake wani secret but kimin alkawarin bazaki fadawa kowa ba sannan dalilin sanar da ke so nake ki sani a addu'a na musamman domin nasan zaki yi.
Aisha tace insha Allah zan tayaka ko menene
*Dr HANEEFAH* 30
Dedicated to Batul Mamman (Mrs) 💖
Idonsa cike da hawaye yace sis, wallahi har yau ina har gobe inajin son Haneefah amma Momy takasa gane Haneefah wata bangarece na farin ciki a rayuwata, ina sonta tana da hankali she have all qualities da nake bukata agun mace, Momy ta rasa lokacin da zata rabamu sai saura wata biyu auren mu? Kuma ta sani nayi nesa da ita, tabbas nasan Haneefah zata jure amma nasan tana can tana fama da zuciyarta, nasan irin son da take min mun kwallafa rai zamu mallaki juna muyi zama na amana but it's over! Ina tunanin wani irin hali Haneefah take ciki na gamu da hatsarinnan, dubi yadda na koma.
Murmushi yayi yace nagode wa Allah daya tasheni har ya bani ikon dada neman afuwar Momy, amma dan ta rabamu zuciyar mu a hade da Haneefah nasan addu'ar mu bazai fadi kasa ba, sannan agun Allah nake tsammanin mallakar Haneefah. Sis inaso ki tayani addu'a Allah bani ikon jure rashin ta na dan lokaci kadan domin nasan zata dawo gareni.
Aisha as duk tausayin dan uwanta ya cika ta tace na maka alkawarin tayaka addu'a, kuma inada tabbacin Momy zata fahimce ka wata rana! Just keep praying. Aisha tazo kusa dashi tana ci gaba da kwantar masa da hankali. Murmushin jin dadi yayi ganin yadda kanwarsa take kokarin kwantar masa hankali. Yanuna farin cikin sa ya tashi ya nufi sashin sa.
Kwance ya sameta kan doguwar kujera tana waya... jin abinda take cewa ne ya dakatar dashi! Sweetheart wallahi ba haka bane amma na maka alkawarin ka bani nan da 1wk kacal kasan ina sonka.... Yusuf dake tsaye yana jinta ya girgiza kai ya shiga cikin daki ya kulle kanshi da key.
Zama yayi bakin gado ya kunnan laptop nashi. Gurin hotuna ya shiga yana kallon hotunan Haneefah har yazo inda suka dauka su biyu acikin motarsa! Hawayene ya soma sauka idanunsa yace a wannan rana muka rabu gashi yau kusan wata biyar bamu ji muryar juna ba. Nan ya tuno da maganarta lokacin da yayi kwana bai kirata ba tace _na maka uzuri kana aiki amma inaso ka kasance dani a tunanin ka, ni ko da bacci ya sace ni kana cikin mafarkina, kaine tunanin domin na damka maka duniyar soyayyata_
A hankali yace Haneefah duk inda kike pls don't give up on me, muci gaba da addu'a, nasan rabuwarmu nadan lokacine inada tabbacin sake rayuwa dake.
Tuno Rahma yayi, nan take ransa ya baci wadda a dalilinta aka hana auran mosoyiyarsa gata da igiyar auren ta tana waya da wani. Tsaki ya ja ya share hawayen sa... zan zauna da ke dan Momy amma bazan lamunci wannan wulakancin ba.
Ya tashi da nufin shiga ban daki ya koma da sauri ya zauna jin wani irin azaba da mahadin(joint) cinyoyinsa sukayi. Lumshe ido yayi yana ambaton Allah. Ya kai kusan minti goma kafin ya samu tashiwa a hankali yana dingishi ya shiga ban daki, bayan ya fito ya dauki qur'ani ya soma karatu.
Washe gari misalin karfe takwas ya fito domin gaida iyayensa ya tarar Rahma na kwance inda ya barta tana bacci, da alama ko sallah bata yi ba. Tashin ta yayi yace gari yayi haske. Tsaki taja ta qara kwanciyarta. Bai kara cewa komai ba ya fice.
A falo ya tarar da Abba yana shirin fita, da sauri ya gaishe shi. Abba ya amsa tare da yi masa ya jiki yace da sauki. Abba yace nizan fita saina dawo.
Yusuf ya wuce bangaren Momy. A falo ya same su Aisha na shirin fita. Ya gaida Momy ta amsa ta masa ya jiki. Anan take sanar dashi zuwan umma nusaiba yau, yace Allah kawo ta. Suna cikin magana suka ji sallamar salma.
Bayan sun gaisa tace nazo duba jikin yaya Yusuf ne kafin in wuce office. Yusuf yayi murmushi ganin yadda yan uwansa suke kula da shi hakan na mishi dadi.
**** ****
Dr Mubarak ya dubi Haneefah yace inaso ki maida hankalinki kiyi karatu, ni yanzu a matsayin qanwata na daukeki shiyasa na zabi kiyi karatu a wannan jami'ar domin nayi karatu cikin sa nasan mutane da dama cikin sa, kamar yadda nasanki da kwazo ina so ki ninka kwazonki kiyi karatu, ban lamunci kiyi soyayya ba sannan bazan hana ki hulda da jama'a ba amma kisan wadda zakiyi da su nidai fatana ki maida hankalinki akan abinda ya kawo ki.
Haneefah tace nayi maka alkawarin bazan baka kunya ba, zan maida hankalina akan karatu. Dr Mubarak ya kalli wayar dake hannun ta yace naga wayarki babbace abinda zaki bukata shine laptop da iPad, zan dawo miki dasu anjima sannan ki bani account number ki, abu na karshe shine inaso kimin alkawarin duk abinda ya shafi abin bukata na makaranta ki nemeni kada ki fada a gida sannan duk wata zan tura miki kudi shi na al'amuran yau da kullum ne ina fata zaki kiyaye?
Insha Allahu nagode sosai Allah qara arziki. Cikin kwanaki goma Dr Mubarak ya nuna mata ko ina game da department nasu, tare yake rakata suke attending lectures, kullum in sun fita da safe sai yamma suke zuwa sai dare yake samun tafiya gurin bukatunsa, ya nuna mata muhimman gurare da zata bukata misali kasuwa, gurin ciyan abinci da sauran su. Ta tabbatar wa kanta cewa Dr yayi mata abinda qanwarsa ma sai taje.
A washe gari zai koma gida suka zauna ya dada sanar da ita komai kan makarantar nasu. Washe gari har airport ta rako shi sannan ta koma. Haneefah abinda ta fahimta game da wannan balarabiyar shine, farkawa take tana ganinta ido biyu akan sallaya tana addu'a bayan tagama zata idar da sallah asuba saita zauna karatun qurani amma a hankali take ta yadda bazata dami kowa da daga murya ba har rana ta fito, bayan karfe bakwai yayi zata shiga wanka ta fito tashirya saita fita, da dare zata bude takardun makarantar ta tayi karatu in dare saita dauki takardu manya na addini ta soma karantawa zuwa awa daya sannan ta kwanta. Wannan tsarin yayi matukar bala'in burge Haneefah, babu abinda yake hada su sai gaisuwa. Nan Haneefah tayi sha'awar yi mata magana sai kuma tayi shakka ta kyaleta.
Hakarayuwar Haneefah takasance a birnin London, dabi'ar su ya zamo daya da wannan balarabiyar amma sai dai basu san koda sunan junansu bane da department nasu. Sai gaisuwa.
**** **** ****
Haneefah ta maida hankalinta sosai gun karatu, bata kula kowa daga ta gama abinda takeyi zata koma hostel, wani lokacin zata wuce library ko wani guri wadda aka warewa dalibai ta zauna shiru tana nazarin mutane da yadda suke rayuwa. Sau tari in taga guri shiru zata zauna tayi ta kukanta inta tuno da Yusuf, wani lokaci kuma ta zauna tayi shiru tana tunanin ko wani irin hali yake sannan ta godewa Allah daya bata ikon daukan al'amarin a saukake amma bata fasa addu'ar Allah daidaita tsakanin su ba.
Tana waya da mutanen gida sannan tana tabbatar musu komai na tafiya mata yadda ya kamata. Haka ga barrister suna gaisawa bayan kwanaki kadan.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼31
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Zaune take tayi shiru tana kallon fararen fata yaruka daban-daban wadda suke aji daya. Kowa na harkan gabansa... tunanin tashiwa take ta fita taji an zauna kusa kusa da ita
Juyowar da zata yi suka hada ido cikin harshen turanci tace kema kinanan ajinne? Haneefah ta daga mata kai alamar eh! Balarabiyar tace in bazaki damu ba inaso mudanyi wata magana.
Haneefah tayi murmushi tace zan so sauraron ki amma bana tunanin zan tsawai ta ina magana cikin harshen da ba nawa ba saboda ban iya sosai ba.
Balarabiyar tace kada ki damu zan fahimce ki. Suka tashi suka nufi bangaren da aka ware saboda hutawar dalibai. Haneefah tayi mamakin gurin domin bata taba zuwa ba kuma gurin ya bata sha'awa, babu hayaniya kowa a zaune yake wasu suna tattaunawa wasu suna karatu.
Balarabiyar ta dubi Haneefah tace ni sunana Raihana Aaqil, haifaffiyar garin Saudi Arabia ce, nazo nan makaranta ne, ina da burin yin karatu sosai a rayuwata a kasashe daban-daban hakan yasa na zabi zuwa London. Tun da nasi admisson nake rokon Allah ya bani abokiyar karatu mai hankali da nutsuwa wadda tarbiyyarmu zata daidaita sai kuma cikin ikonsa ya hadani da ke, tunda na ganki naji kin kwanta min arai amma sai na kasa tunkaran ki domin bansan wani irin tarba zan samu agun ki ba. Ba karamin5 farin ciki nayi ba da na ganki kullum cikin ajinmu domin na tabba inba gurin karatun ki bane bazaki zo ba. Kina burgeni sosai yadda kike tafiyar da rayuwar ki babu ruwanki da kowa kuma inason mutum haka pls Allah ne ya hadamu mukasance masu kulla zumunci cikin yarda da amana.
Haneefah tayi murmushi tana kallon Raihana, kyakyawace fara tas, kallo daya zaka mata kaga nutsuwa tattare da ita. Babu komai ina maraba dake Allah bamu ikon gudanar da zumunci domin shi.
Cikin murna Raihana tace nagode yanzu tashi mu tafi aji kada lectures nagaba ya wuce mu amma baki sanar dani sunan ki ba? Haneefah ta bata amsa tana mikewa. Tare suka jera har suka tadda an soma lectures.
Bayan sun koma hostel misalin karfe hudu sunci abinci sun huta Raihana tace yanzu time table zamuyi na karatu da sauran al'amuran amma in bai miki ba zaki iya canza wa. Haneefah tace yi in gani.
Raihana ta dauko paper da biro ta soma zanawa, da safe misalin karfe bakwai zasu shiga wanka suyi shirin makaranta zuwa karfe bakwai da rabi, kafin takwas sun iso makaranta kuma zasu samu zaman gaba. Bayan sun gama lectures ko akwai interval kafin karfe biyar zasuje library library mu tattauna kan abinda mukayi a aji sannan in muka fahimta zamu wuce next course line mu rage karatu domin zamu fahimci abubuwa, sannan in muka koma gida zuwa magriba lokacin hutu ne in muka zamu it's fita zai mu fita mudan zaga gari, bayan mun dawo mukai sallah zamu kasance masu addu'a har akira sallah isha'i daganan sai mu rinka karatu zuwa goma ko sha daya saimu dauki littafin addininmu mu karanta daganan sai mu kwanta, zuwa asibahi saura awa daya zamu tashi muyi rako o'i muroki gafarar mahaliccin mu, in aka kira har lokacin asuba bayan mun idar sai mu dauki alqurani har zuwa karfe bakwai. In muna weekend zamu ware awa uku na karatu saimu fita zaga gari. Ina fata wannan tsarin yayi miki?
Cike da mamaki haneefah ke kallonta tace yanzu na dada tabbatar da zanyi dacen kasancewa dake, tsarin yayi wallahi amma fa ban sauke alqurani ba.
Raihana tace kada ki damu zan rinka