Showing 72001 words to 74305 words out of 74305 words
Chapter 25 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
anan garin sai muyi shopping ai.
Haneefah ta yarda da hakan amma tace kada kowa ta dame kanta da tsumi saboda irin fruit da nasha ba kadan bane shi kadai ya gama min aiki. Dariya suka kwashe suna cewa lallai Haneefah kinyi baki, duk cikin mu fruits muka rike hannu biyu, sai Zuma.
Tun daga ranar suka soma shiri, ita dai Haneefah har yanzu tana jin ciwon marar daurewa take aka soma shiri da ita.
Cikin kwana uku suka kammala siyayya aka yiwa Yusuf magana domin tafiya da kayayyakin abuja. Aunty Muhibbat, zuwaira da Hadiza aka hada suka tafi jeren amarya.
Ana gobe walima aka kawo kayan lefe, mamaki ya cika su, auren ma ya wuce amma sai sun hado lefe. _Ko ban fada ba masu karatu kunsan lefen Dr HANEEFAH bazai misaltuba_ .
Haneefah zaune take gidan Inna tana jiran isowar mai kunshi taji ana sallama, kafin ta tashi ta shiga ciki taga Aisha rike da Ra'ima sun shigo. Da sauri suka rungume juna suna murna.
Gaisuwa sosai suka da nuna farin cikin sake haduwa da juna. Aunty Haneefah Allah ya dubi zuciyarku yanzu gashi har kunyi aure.
Murmushi Haneefah take. Mika mata Ra'ima tayi ta sanar da ita takwarar tace ana kiranta da Ra'ima. Haneefah ta karbeta cike da tsananin son yarinyar. Mamakin irin son da Yusuf da family shi suke mata takeyi. Rungumeta tayi tace nagode Aisha Allah bani ikon zama daku bisa amana da lafiya.
Aisha tace ko shakka babu kemai amana ce, muna farin cikin zamanki matar Yusuf. Haka suka kasance masu yiwa junansu kyakykyawar zato.
Washe gari akai walima gidan amarya da ango. Yan uwa sai fatan zaman lafiya suke musu. Da dare aka Abba da Umma suka sa Haneefah agaba sukai mata nasiha sosai kan zaman hakuri.
Washe gari aka turo mota domin tafiya da sauran kaya. Duk shagalinnan banda Nana akai domin mai jego ce. Sannan aka sake turo mota inda wadda zai tafi amma amarya zirgin safe zata bi. Abba ya hana kowa tafiya yace dasu Amal insun sami hutun makaranta suje.
Washe gari aka zo tafiya da Haneefah, kuka kama tayi shi na rabuwa da iyaye ba shiri. Gidansu Yusuf aka wuce da ita, Momy da Abba ma sukai musu nasiha sannan akai mata rakiya airport. Cikin jirgi babu aikin da take sai kuka, lallashin duniyar nan Yusuf yayi amma batayu shiru ba haka suka iso.
***
Tsararren gida ne, wadda kaya da aka jerasu sun amshi gidan. Haneefah komai na cikin ya burgeta. Bayan kwana biyu su aunty Muhibbat suka koma gida. Haneefah abin babu yadda ta iya sai hakuri. Amma a duk sanda ta bude ido taganta cikin gidan Yusuf ba karamin jin dadi take jiba
Da dare bayan ta idar da sallah tana zaune bakin gado yashigo yace tashi suyi sallah domin godewa mahaliccinsu daya kawo su wannan rana.
Bayan sunyi dukkanin abinda aka koyar bisa sunnah yace zo muje dakina. Kamo hannunta yayi har suka iso. Tsarerren dakine babba. Gurin wardrobe ya nufeta ya bude side daya yace wannan dukkaninsu English wears ne. Daga yau su nake bukata ki rika sakamin. Ya bude daya side yace wannan kuma nighty ne.
Daya bayan daya ya nuna mata ko ina, Haneefah gidan ya mata kyau. Sai dai cike take da tsoro domin yau zata kasance da Yusuf a makwanci daya. Tsaf ya ganota da tsoro dan haka ya kwantar mata da hankali yana cewa baki da lafiya yakamata ki kwanta da wuri ko... ganin haka yasa ta rage tsoron nata.
_Bayan sati biyu_
Tsantsar so da kauna, kula da juna, kyautatawa da aminci ke dada yawaita tsakanin masoya biyu. A kullum yana godewa Allah daya hada sa da mata kamar Haneefah, domin ta gama hada komai wadda namiji ke bukata agun mace.
Sau tari zai kura mata ido yana kallonta, shi kawai kullum cikin tsananin sonta yake ga tsananin sha'awarta da yake amma yana tsoron tabata domin gani yake kamar zata suma kamar yadda tayi kwanaki.
Itama anata bangaren haka abin yake gunta, ta fahimci mijinta na bukatar ta saboda haka yau zata bashi mamaki domin ta gane nufinsa.
Zaune take kamar kullum tana jiran isowarsa. Sanye take da wani English wear wadda yayi masifar mata kyau, ya fito da dukkanin surar jikinta tasha kwalliya. Jiransa take amma shiru baizo ba har karfe tara da rabi.
Gabanta ne ya soma faduwa ganin har goma ta wuce bai zoba. Ta kasa zaune ta kasa tsaye ta soma zagaye falo.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼70
Dedicated to Batul Mamman Mrs💖
Da sauri Yusuf ya taro ta. Haneefah na kokarin tureshi amma ya rungumeta yana tambayar are u alright? Bai gama rufe bakinsa ba ta gama wanke shi da amai.
Baibari ta tashi ba saida ya tabbatar ta gama sannan ya taimaka mata suka nufi toilet. Shiya gyara ta sannan ya gyara inda ta bata yana mata sannu. Yana kokarin canza kayansa tace pls kada fesa turare shi ya sani amai.
Yana gama shiri yace tashi mu tafi asibiti. Juyarda kanta tayi tace ni zan samu sauki a gida. Zama yayi kusa da ita yana cewa meke damunki? Cikin kuka ta matso ta fada jikinsa tace babyn mu na wahalar dani.
Cikin rashin fahimta yace baby? Gyada masa kai tayi tace eh ciki ne dani wata uku. Dagota yayi cikin tsananin farin ciki yace what! Ciki gare ki? Rungumeta yayi cike da murna yana cewa Alhamdulillah. Allah kaine abin godiya, yace tashi muje asibiti a dada dubaki
Cikin shagwaba tace ni bana so su hada ni da magani. Yusuf ya shiga lallashin ta dakyar ta amince suka tafi aka dubata. Tun daga wannan lokaci tattalin ciki ake, Yusuf baida hira sai na baby. Har Haneefah ta samu sauki a wannan lokaci ne Yusuf yace dama yana son biya musu kujerar hajji amma su saita haihu zata tafi shima ya fasa tafiyar.
Labari dayazo kunnen Haneefah tayi tsananin murna domin Yusuf ya biyawa iyayenta kujera... zamansu gonin ban sha'awa.
****
Watanta takwas amma kamar yau zata haihu domin cikin yayi nawi kuma yayi babba. Wannan lokacine take so ta tafi kano amma Yusuf bai amince da tafiyar ba gashi ba aiki take ba sai zaman gida.
Zaune take tana waya da Raihana, basu manta da juna ba, Haneefah a kullum bazata taba mancewa da barrister ramlat da Dr Mubarak ba, sai Kevin, Rohan da Raihana wadannan mutane sun taimaketa arayuwa bazata manta da su ba.
Yusuf zaune kusa da ita yana kallonta, shi tausayi yake bata yadda take fama da cikinnan amma ya lura kamar fishi take dashi. Bayan ta kammala wayarta ya dubeta yace dearie nifa banki tafiyarmu kano ba, wasu abubuwa nake kokarin yi saina kammala nake so mu tafi.
Haneefah tace babu komai Allah kaimu. Ganin har yanzu bata huce ba yace toh shikenan dama so nake na maido da aikina kano sannan na kammala ginin da zamu zauna ciki shine... da sauri Haneefah ta juyo tace da gaske dearie? Gyada mata kai yayi
Kokarin tashiwa take amma Yusuf yayi sauri tashiwa yaje ya rungumeta yace basai kin tashiba. Tsananin murnanta ta nuna mishi tare da tambayar yaushe yake tsammani? Yace duk sanda ya kammala zai sanar da ita.
Anyi haka da sati biyu suka tattara suka koma kano, Haneefah murna dangi murna. Komawarsu da wata daya ta haifi yan biyu mace da namiji. Ranar suna namiji ya samu suna Muhammad ba'a dangana ga kowa ba sai annabinmu Muhammad (al'ameen) tsira da amincin Allah su tabbata gareshi. Macen taci sunan Momy(ummi).
Rayuwa ya koma so wonderful tsakanin family biyu, Haneefah ta soma aiki a TH dake garin kano.
Watannin yaranta biyar Yusuf ya mata albishiri da sabon asibiti daya bude mata. Tsananin farin ciki Haneefah take, tabbas rayuwa duk wadda ya fuskanci matsala toh tabbas zaiji dadin juriyarsa. Fatanta a kullum ya barta da mijinta cikin tsananin farin ciki ya karesu da sharri.
Zaune yake yana aiki da laptop ta shigo rike da ummi a kafada ta kwantar da ita. Zama tayi gefen mijinta ta rungumo shi tace aikinnan ya'isa ka huta. Kashe laptop yayi ya juyo gareta yana cewa dama ke nake jira, kizo in samar wasu al'ameen kani.. zaro ido tayi tace da wuri haka? Yace nidai yanzu nake so......
Tammat bihamdulillah!
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya bani ikon kammala wannan littafi mai suna Dr HANEEFAH. Dalilin rubuta wannan littafin nawa dalililaine da dama amma babban abin shine HAKURI.
Muddin muka kasance masu hakuri tare da barwa lamuranmu a hannun mahaliccinmu to tabbas zamu ribance abin fiye da tsammanin mu, hakuri a lokacin da ka rasa abu, hakuri akan abinda aka maka sannan kana da halin ramawa, hakuri tare da kau dakai akan abinda ya wuce in muka rike haka tabbas zamu ji dadin zaman rayuwa. BIYAYYA GA IYAYE
Musani duk abinda muke a duniyar nan muddin bamu biyayya ga iyaye, bama neman albarkan su to tabbas muna cikin hatsari. Babu wani bawa da al'amarin sa zai gudana yayi daidai face yakasance mai yiwa iyayensa biyayya, iyaye ba abin wasa bane ko da gangan fushinsu na bin yara saboda haka mu guji yankewa yaranmu hukunci saboda wani sa'in mu da kanmu muke jefasu ga hakala. Duk da Yusuf na yiwa tsananin yiwa mahaifiyarsa biyayya amma saida ta hukunta shi da abinda bai kamata ba, wani abin takaicin wasu iyaye har mallake yaransu maza suke, me yayi zafi? Keba gidan miji kike zaune ba? Waya takura miki? Abinda zaki hukunta matar yaronki bakisan Allah zai saka mata ba? Ko ke babu yara mata gabanki? In ma tsoron kada a mallake miki yaro ake mesa bazaki dage masa da addu'a ba? Ko kinsan addu'ar uwa ga danta karbebbene? Mu kula kada mu daurawa yaran mu abinda zai cutar dasu. YAN UBA
Duk abinda kishiya zata miki kada ki kuskura ki koyawa yaranki kishi domin alhaki zaki dauka, kamata yayi ki nuna musu kaunar yan uwansu muddin suka girma suna kuntata musu zaki gani da kansu zasu ja jiki su daina kula su batare da YAN UBANCI BA.
NIYYA. A duniyar nan duk abinda dan adam yayi niyya toh tabbas zayyi/zai zama sai dai yana da karancin NIYYA. In ilmi kake so ko daukaka ko menene mutum zayyi amma muzamto masu kyautata NIYYAR MU, misali ga Haneefah. Bata so karatun likitanci ba amma da tayi NIYYA lokaci daya ta zamo Dr HANEEFAH, ba bangaren daya bama bangarori da dama. Saboda haka mu koyarda yaranmu kyakykyawar NIYYA ba buri ba. Sannan ina rokon iyaye muzamto masu gyara tarbiyya yaran mu da dabi'unsu, yazamto kalmomin addini ya zauna abakinsu ba wadda suke gani a cartoon ba.
YARDA DA ADDU'A. A kullum mu kasance masu ambaton Allah, mukasance Allah shine jin mu, ganin mu, tafiyarmu komanmu. In abu yasame mu kafin mu yanke hukunci mu rika ambaton Allah. Muddin muke rike haka to tabbas zamu kasance masu jin dadin zaman duniya domin duk wadda yace Allah ya gama komai. Yadda Haneefah ta tafiyar da rayuwarta yayin da ta rasa Yusuf, da yadda ta dage da addu'a da yadda ta yarda da addu'an ta shi ya kaita ga wannan matsayi, yarinya ce karama amma tasan yadda ta tafiyar lamuranta wato tabarwa Allah. Shi addu'a amsar shi ya kasu kashi uku;
1. Eh an amsa maka yanzu
2. Eh an amsa maka amma sai zuwa wani lokaci
3. Aa abinda ka roka ba shine mafi alkhairi agare kaba amma zamu baka abinda yafi alkhairi.
Yan uwa me muke bukata daya wuce zabin Allah? Me zamu gani dahar zai rudemu a a wannan duniyar? Duniyar da zamu barta.
Shin kina son jin dadin zaman aure? Kiyi niyya zakiyi aure badon jin dadin zama ba zakiyi aure saboda ita ibada ce. Mu koyawa yaranmu da kannen mu wannan dabi'a sannan muyi musu nuni ba'a gaggawa a al'amarin aure.
Mu tuna lokacin da Momy tayi calling off aurensu, biyayya Yusuf ya mata, itama ma Haneefah hakuri tayi amma bayan shekaru suka zo suka sake haduwa shin ko kunsan tarayyarsu a wannan lokaci babu alkhairi? Lokaci da dama muna ganin abu tamkar alkhairi ne amma sharri ne, sharrin kuma zamu ga alkhairine.
Idan ka zamanto Mutumin kirki,mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya hadaka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka.
Koda ka samu matsala da wani daga cikin Jama'arka, kar ka fidda tsammanin alkhairi daga gareshi. Watakil idan kayi masa uzuri ka kyautata zato gareshi, ka yafe masa, sai alkhairi ya biyo bayan hakan.
Mutanen kirki anan duniya, sune ma'abotan alkhairi a lahira. Kuma mutum ba ya zama mutumin kirki har sai tunaninsa da ayyukansa duk sun zama na kirki.
Kayi kokari ka chanza rayuwar wani bawan Allah daga mummuna zuwa kyakkyawa. Ko ta hanyar shawarwari, ko taimako, ko agaji, ko kuma ta dalilin afuwarka.
Allah shi bamu dacewa aduniya da lahira. Ameen.
Gaisuwa ta musamman gare ki BATUL, nagode da gudun mawarki, nagode kwarai Allah kara lafiya ya albarkaci zuria ameen.
Gaisuwa gareku makaranta littafin Dr HANEEFAH. Ina ganin sakonni. Nagode da addu'ar ku sosai Allah sadamu da alkhairi. Sannan ina bukatar addu'ar ku aduk inda kuke.
Dr HANEEFAH is my first novel and last.
_Bintu Ramadan take muku fatan alkhairi_