Showing 3001 words to 6000 words out of 74305 words
Chapter 2 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
yara su taso da Qur'an a bakinsu ba sanin story books ba Allah sa mugane ameen, nana tace kina da gaskiya na dogara ga Allah kuma insha Allah inna samu admission ko apart 1 me zanyi aure haneefah tace karma kiyi mana.
Suna taba karatu ahmad ya leko yace kuzo umma nakiranku. Zaune suka taddata haneefah tace sannu da hutawa ta amsa mata tace yauwa, ta kalli haneefah cike da murmushi tace dama lokaci yayi dama batun zaki bude account ne, lokaci yayi da kema zaki fara adani kamar yan uwanki nana da ahmad, ajiyannan da zakiyi zai amfanar dake damu watarana, dubu goma ne a ko wacce wata, nasan yanzu ba wani sutura kika damu dashi ba tunda kullum cikin uniform kike, gabama in zaki saya kisiya daidai karfin ki sannan ki rage tambayar abbanki kudin makaranta sai wadda ya dace ki tambaya ina fata kuna jina? A sanyaye tace eh sannan ko lokacin auran ku yazo bazamu sha wahala sosai ba ammafa sai kuna tattali, Allah ya muku albarka tashi ku tafi.
Haneefah tana matukar son mahaifiyarsu, duk kudin da take samuwa akansu yake karewa tasan tanayin hakanne domin su kauda idanunsu akan abin hannun jama'a, duk da basu da kodayi amma ummansu tana wadatar dasu da komai. Gaskiya iyaye abin tausayawa ne musamman uwa, zata salwantar da dukkanin farin cikin ta domin ta faranta ran yaranta, babu abinda ya'ya yadace suyiwa iyayensu kamar su faranta musu sannan su bisu da addu'a.
Washe gari ta tashi da tsananin tsinkar zuciya, ta idarda sallah tayi dukkanin abinda ya dace kuma ta saba na ibada amma stil zuciyar bata daina ba. Kokarin shirin fita take amma takasa shiryawa cike da mamaki tace yau kuma mezai faru. Dauko Qur'ani tayi ta zauna karatu, a hankali taji zuciyar ta lafa, ta dauko carbi ta soma addu'a. Takai kimanin minti ishirin sai ta tashi ta shirya taje yiwa umma sallama, umma ta bata kudin da zata bude account tayi musu sallama ta fita.
Zaune take a ward (pediatric) dinsu amma takasa tabuka komai sai addu'a take a zuciyarta, zaman ya gagareta ta tashi ta nufi gun aminiyarta dake labour ward. Kasa shiga tayi domin jirine ke daukanta intaga jini. Tana cikin tsaye sai ga hadiza ta fito tace ah yar'uwa kece kika tsaya anan, haneefah tace so kike abani gado kenan domin nikam fadiwa zanyi, dariya hadiza ta soma yi domin sarai zata iya tace meya fito dake lokacin lunch bayyi ba? Haneefah tace wlh yau nakasa gane kaina tun dazu wani iri nakeji. Hadiza cike da damuwa tace kodai wani abu yafaru ne? Aa babu komai tace kiranka anbato _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musi bati wakhlifni khairan minna_, haneefah tace inshaa Allah zanyi nagode, zan tafi bank yanzu innatashi zan wuce gida tace toh Allah kiyaye hanya ki gaida gida.
Saukowa tayi cikin adaidaita sahun da ya kawota ta sallameshi ta shiga bank zuciyarta na dada tsananta wajen bugu. Zaune take tana jiran a sallami wadda suke gabanta tana karewa cikin kallo tana kara sha'awar zama accounter. Daidai wani bakin ko fa da yayi lungu ta tsugunna take cika forms da aka bata, zata mike takai takardun tana kara dubawa batare da ganin gaban taba.
Gaisawa yayi da abokinsa zai wuce office din manager hanakalinsa nakan abokin nasa, tafiya yake baya duba gabansa ya juya yana yiwa abokin sallama cikin sauri. Dab zai karyo kwanan yaji yayi karo da wani abu, tarwatsewar takardune ya tabbata mishi mutum ne. Cike da tsiwa ta dago zata fara magana hada idanun da sukai me yasa fasa abinda take shirinyi.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼5
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Kallo cikin ido suke, a take taji wani irin nishadi ya lullubi zuciyarta, kimanin dakika goma suka dauka, tayi saurin kawar da kanta ta sunkuya ta fara daukan form da suka tarwatse. Baice da ita komai ba saida ta kammala ta dago yace am sorry, najuya ina maganane batare da kula da abinda yake gama naba.
jin muryar tasa take tamkar kada ya daina magana tsaban dadi, bata tabajin murya irin tashi ba. Batare cewa komai ba zata wuce yace kinji? Ta daga ido cikin wani salo da itama batasan tayi ba ta murmusa tayi gaba abinta batare da tace dashi komai ba. Ta kammala komai ta nufi gida.
Misalin karfe goma da rabi ta kammala shirin baccinta ta kwanta, idanunta a lumshe ta soma karanto suratul mulk (yana tsare dan adam da azabar kabari) sannan ta soma neman gafarar mahaliccinta tana ambaton _ASTAGFIRULLAH WA'ATUBU ILAIK_(yana dakyau mu koyawa kanmu wannan dabi'ar, yin istigfari har bacci ya daukemu. Allah sa mudace) bayan ta kammala tanemi bacci ta rasa, kalaman wannan mutumin suke mata yawo a kunne, ta tsinci kanta da son sake jin maganarsa koda sau dayane.... tunani takeyi sosai taga ba mafita bane ta dauro alwala ta fara jera nafiloli saida bacci ya dameta sosai ta kwanta kan sallayar bacci ya dauketa.
*** **** **** ****
Dr Hassan ke zageye da daliban da suke zangon karshe, duk cikin su an angagara wadda zai dauki jinin yaro, duk yabi ya tada musu hankali shi baza'a dauki jininsa ba, mum kice su tafi allura a hannunsu kuka yake yana maganar..... tazo wucewa Dr Hassan ya daka mata tsawa tare da kiranta, cikin hade rai yace inason ki debamin jinin yaronnan cikin harshen turanci, zuciyarta ke bugu domin tsoron kada ya dameta da yaren da bazata iya tsawaita magana ba.
Ta dauki allura ta nufi gefen gadon ganin yana kuka yasa ta ajiye alluran, bayan sun gaisa da mamar tasa da dubi yaron tace sannu ya amsa da yauwa. Tashiga share mishi hawaye tace ya sunanka? Habib masha Allah suna mai dadi saitaga yayi murmushi, tace ina fata jiki da sauki yace eh, tace kana son zaman asibitinne? Yace aa inason tafiya gida. Dr dake tseye yana kallonta yace shine aikin da nasaki? Bata kulasaba taci gaba da cewa habib in kanaso ka tafi gida toh ya zamto..... tsawan da aka daka matane yasata mikewa cikin bacin rai, tafara magana cikin harshen hausa kai ka sani amma ai ina kanyi ne ko haka zanzo gun yaro in riko hannun shi yana fizgewa allaura ta karye ace ban iya aiki ba? In bazaka zubamin ido ba ga alluran wadda kasasu agaba su dauka. Ta mika masa allura, cikin fusata zayyi magana Dr Mubarak dake bayanshi yariko shi ya kalli haneefah yace kici gaba. Ta juyo kan habib tace tunda kanason komawa gida in anzo yi maka allura kada kayi kuka, kuma nasan kana da dauri ko ? Yace eh I'm strong like ninja, tace yauwa kuma zan sayo maka choculate muddin kamin alkawarin bazaka sake kuka ba cike da jin dadi yace toh, tace ka rufe idonka saika mikomin hannun ka bazaka ji zafi ba... haka ko yayi ta rinka lallashinsa baisan sanda aka dauka jinin ba, ji yayi tace bude idonka, yana budewa yace aunty babu zafi gobe kizo ki kara daukawa. Tayi masa murmushi tace toh.
Dukkansu suka zuba mata ido, ta mikawa Dr ta juya gun mum din habib ta mika mata dari biyar tace kisiya masa choculate. Zata wuce Dr Hassan yace kina wani level? 200 cike da mamaki ke kallon sauran daliban nan ya soma surutu kan su aje hankali suyi karatu. Dr Mubarak yace kisame ni a office tace toh.
Tun wuce warta ya zuba mata ido tabbas itace wacce jiya suka hadu a bank, yadda tashawa kan yaron cikin kankanin lokaci yafi birgeshi atake zuciyarsa ke raya masa wani abu da bazai iya fassarawa ba. Haka kawai yaji yana son yi mata magana. Sallama yayi gun mara lfiyr da yazo dubawa amma kash ya dubata ko ina bai ganta ba gashi gobe yake son komawa gurin aikinsa.
Zaune kan kujerar shi ta same shi, ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a tare da bata izinin zama. Yafara magana cike da damuwa zakiyi mamakin kirana sbd nasan baki taba ganina ba tace hakane, yace taimako zakimin a sannan ta dago ido tana kallonshi Allah sa zan iya ta amsa mishi, wato inada mata da yara biyu mace da namiji, ina matukar son matata domin auren soyayya mukai. Ina matukar son yara dayawa amma ta kafe biyu sun ishemu nayi nayi amma taki karshe tace cire mahaifa zatayi, inaso in rufa mana asirine bana son maganan yaje kunnen manya domin za'a iyace in qara aure ni kuma bana tsammanin zanso wata daban kamar yadda nakesonta yakarashe maganar kamar zayyi kuka.
Cike da tausayi haneefah ke kallonsa, tace yanzu me kake so ayi? Gobe misalin karfe 9:30 kizo da ciwon ciki zamu karasa sauran insha Allah.
*Dr HANEEFAH*👩🏼 6
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Tare suke shigowa asibiti da hadiza daga restaurant karaf idanunta suka sauka kanshi, jingine yake jikin wata CRV 2015. Yayi bala'in kyau cikin manyan kaya, sannan ta kare mishi kallo, fari ne amma ba sosai ba, shiba dogo ba, ba gajere ba ba amma yadan fita tsayo. Idanunta suka dada hango kwantacciyar gashin kanshi kamar balarabe sannan sajenshi da ya matukar karbeshi. Kallo daya zaka mishi ka fahimci nutsuwa da kamala tattare dashi.
Kallo shi take sai dai ta fahimci kamar wani yake nema domin idanun sa nakan mai fita da shigowa. Karaf suka hada ido ya sakar mata murmushi daya kara mishi kyau, gani tayi ya nufo inda suke ta kawar da idanunta akanshi.
Sallama ya musu suka amsa, ya gaishe su hadiza kadai ta amsa. Kallonsa ya koma gun haneefah dake kallon wani guri daban yace sister nazo na dada baki hakuri domin naga baki amsa min ba. A hankali ta juyo suka hada ido tace ba komai, taja hannun hadiza suka soma tafiya yace in bazaki damu ba inason magana dake! Budar bakinta tace matar aure ce. Hadiza cike da mamaki ke kallonta harsuka wuce ward dinsu.
Binsu yayi da kallo tare da tsananin mamaki. Ba matar aure bace take yabawa kansa amsa, amma me dalilinta nasarar dani? Bincike ya soma tunanin farawa sai dai jirgin yamma zai yau ya wuce gurin aikin sa. Murmushi yayi daya tuno inda zai samu information akanta, ya juya ya nufi motarsa.
Dakatar da tafiyan hadiza tayi tare da jan hannunta suka koma kan wani benci suka zauna. Haneefah mesa kikace kina da aure? Banason dogon surutune yasa na katse zancen, aina kuka san juna? Nan ta labatar mata da abinda ya faru. Hadiza tayi murmushi tace in yazo da batun so fa? Haneefah cike da mamaki tace har tunanin haka kika? Hadiza tace babu yadda Allah baya hada bayinsa, mesa zai tako yazo domin amsa hakurinsa? Haneefah tayi murmushi tace da aminiyarta haba yar uwa, kallo daya zaki masa kinsan dan masu kudine, sannan yafini kyau nesa ba kusa ba kuma tabbas mazan yanzu sai wadda tafisu kyau taya tayaya kike tsammanin zai soni? Cike da mamaki hadiza tace ban taba tunanin kemai irin wannan tunanin bace, kinsan so saboda Allah baya duban ilmin mutum ko kudi ko kyawu? Abinda yake bukata shine kikasance mai gaskiya da rikon amana babu cuta babu cutarwa! Haneefah tace tabbas ina sane da hakan amma cike da murmushi, amma ina jiyewa kaina randa za, fada tarkon so sbd ban iya shiba. Hadiza tace in tambayeki mana? Ina mai sauraronki, shin wani irin miji kike burin aura? Lumshe idanunta tayi tare da soma magana ina son namiji wadda yasan darajar dan adam, wadda ya wadatu da ilmin addini wato mai tsananin tsoron Allah, wadda duniya bata gabansa wadda zai soni tsakani da Allah ya nunamin tsantsar kauna da kulawa, wadda annabinmu Muhammad (S.A.W) ya kwadaitar damu mu aura, wadda..... hadiza tayi saurin dakatar da ita tace ai kin gama komai insha Allah kin samu, kijira lokaci amma kada ki manta duk mabukaci baya bacci ki dage da tsayuwar dare, ta murmusa tace insha Allah.
**** **** **** ****
Washe gari misalin karfe 9:30 yasameta a kofar Dr Mubarak, idonta cike da hawaye ta turo kofar yashiga. Zaune suke suna fuskantar juna, hade rai yayi ya dago fuska yace waya baki izinin shiga? A sannan haneefah ta fashe da kuka tana cewa cikina cikin tsawa yace fita? A hankali kyakykyawar matarshi wadda fuskarta alamar tausayi tace haba Dr, ka dubata mana shine zata shigo babu excuse? Ganin bata ce komai ba kuma kar planning nasu ya rushe yace ga guri zauna, wani irin ciwon ciki? Tace nidai tun da dare nake fama amma yanzu ya tsananta, yace in period naki zaizo wani irin alama kike? Yana ciwo amma ba ko wanni lokaci ba, ok. Yace yaushe ne next zuwan shi? Ina kanyi... a matsayinki na student of health bazaki iya banbanta menstrual pain ba? Haneefah ta sunkuyar da kai, ki tashi kibani wuri.
Ta dago tace, Dr ina banbantawa, babban burina shine inyi aure in hayayyafa, shine nake tsoron duk wata ciwon ciki domin kada ya tabamin mahaifa. Cike da mamaki matar Dr ke kallon haneefah, Dr yace shekarunki nawa? 19 tabashi amsa ya juya gun matarsa yace kindai ji abinda take cewa, yarinya karama tun kafin tayi aure take tunanin future ta, amma ke kokarin cire mahaifa kike. Zuro ido tayi ta fuskanci inda take kallo tare da cewa aunt gun Dr kika zo domin a cire miki? Mesa? Tana so tayi magana haneefah ta katseta ta hanyar cewa baki da wata hujja nayin hakan. Ko kinsan cewa babu wadda ya isa yayiwa wani kyautar da ko ya inba mahaliccin muba? Kina da tabbacin za'a maida miki mahaifane? Duk yawan yaranki kinsan zasu dauwama tare dakene? Yau Allah ya baki daman da mutane da dama suka rasa amma zaki nemi rasashi da sanin ki da wayonki? Akwai mata da dama da suke tunanin yawan haihuwa na tsufar da mutum da wuri, abin ba haka bane. Kiyiwa mijinki kwalliya in yaran kikarasa su kiyi meh? Kina takamar mijinki na sonki? Hmm kallesu da ido kawai, yaranki sune rayuwarki, Kisani cewa duk sonda mijinki ke miki muddin kika rasa yara zai iya rage sonki ya auro wadda zata hayayyafa mishi kuma ta mamaye masa zuciya a barki da kunar zuciya, sannan yan uwanshi su gujeki. Wasuma tsabar rashin tausayi jarirai suke hadawa da fida saboda basaso nonuwansu su zube, namijin banza, kinsan sinadarai da suke dauke da nono kuwa? Abincin yaro kuma lafiyar yaro. Nidai shawarata kada ki soma domin dana sani na gab da zuwa miki, mahaifarki itace abin alfaharinki a gidan miji, kada kibiyewa kawaye domin wasun tsantsar muguntane a zukatansu. Ki zauna da mijinki lfy kada aji kanku inma bai sani ba kada ki fada mishi, in kika fita bakisan gidan wa zakiba, kimin afuwa in maganganuna sun bata miki rai.
Dago kanta tayi hawaye na tsiyaya a kuncinta tace, ya sunanki, haneefah. Ta kama hannunta gam ta rike tace hakika nayi nakusa fadawa rami mai zurfi wadda babu wadda ya isa fiddoni, sai gaki bansanki ako inaba kinzo kin haskamin gabana nagane ramine. Dayawa muna cutar da kanmu, yarana biyu, na manta akwai rashi. Sai yanzu kika tunomin, bansan da wani irin baki zan gode miki ba. Murmushi haneefah tayi tace ba komai Allah shige mana gaba a al'amuranmu.
Dr Mubarak bai tabajin cewa akwai yara masu baiwa masu ilmin addini da kaifin hankali irin haneefah ba. Ya kalli matarsa yace kin janye? Tace eh najanye sannan ina neman afuwanka, kai hakuri ka yafemin.
Haneefah tace zan wuce a sanyaye. Matar Dr tace pls inaso in kulla zumunci dake, murmushi haneefah tayi tace toh. Matar tace sunana Barrister Ramlat ga lambata. Haneefah ta karba ta fice ta barsu.
*Dr HANEEFAH*👩🏼 7
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ward nasu ta wuce ta duba abinda zata duba ta wuce ward dinsu hadiza.
Agajiye ta shigo gida domin tasha aiki a labour ward, ta tarar da nana a sakar gida zata shiga falon abbansu. Nana ta nufota tace wadda suka taba aiki da abba yakawo ziyara kije ki canza kayanki ku gaisa.
Cikin ladabi suka gaidashi ya amsa yace masha Allah ya karatu? Haneefah tace Alhamdulillah nana tagama nice da saura haryanzu. Cike da murmushi abokin abban nasu yace toh Allah bada sa'a, tare suka ce amin gaba da mikewa suka shiga ciki.
Alhaji mudassir ya dubi abokinsa Alhaji hamisu bayan fitarsu yace masha Allah, nana tagama makaranta aiki take ko takusa aure? Abba yace babu ko daya jiran admission take amma har yanzu shiru. Cike da mamaki Alhaji mudassir ya dube shi yace irin matsayina a garinnan amma yaranka su nema admission har so biyu? Abba yace ai komai da lokacinsa, bazayyu in rika daurawa wasu nawi ba. Wannan shine zumunci? Nasan abinda kake gudu amma kasani bana daya daga cikin mutanennan. Metake so ta karanta? MBBS. In bazaka damuba ka kawo requirment dinta saura dalibai biyar yarage na wannan fannin wadda zasu kasan Egypt (scholarship)sai insa hannu su tafi. Abba yace har Egypt? Abokin nasa yace tunda tayi niyya kada kahanata tunda ta samu wannan damar, sannan binta zakai da kyakykyawar addu'a. Abba ya numfasa yace to shikenan, nayarda da tarbiyyarta ,nagode kwarai da gaske.
Magana yaje kunnen su haneefah sai murna ake. Umma ko ranta bai so ba, tafison yaran suyi aure amma dai batai shishshigi lamarin ubangiji ba, addu'a tayi maata na samun nasara.
**** **** **** ****
Zaune yake ya kurawa files din gabanshi ido, ya kasa aiwata komai sai tunanin wannan yarinyar yake. Runtsa idanunsa yayi a hankali ya bude. Kwanan sa biyar kenan yana abu daya wadda ya kasa tantance meye.
A hankali ya dauko wayarsa da ke kan table dinsa ya fara dialing no. accounter, ajiyar zuciya yayi jin layin a kunne ana dagawa yace haba accountr tun yaushe nake kiran layinka? Daga daya bangaren aka amsa, am