Showing 6001 words to 9000 words out of 74305 words

Chapter 3 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5166

sorry, wlh wayanne ya fadi naje nayo welcome back, toh bai fara aiki ba sai yau kuma ban gane mai magana na. yace ba komai, engineer yusuf ne. Allah sarki ina fata kana lfy? Alhamdulillah amma wata alfarma nake so kamin, accountr yace ina jinka. Kwanaki nazo bank naku, sai na hadu da wata yarinya taje bude account domin naga form a hannunta, abinda nake so shine informations nake so akanta like her phone number & address. Accounter yayi dariya yace toh yanzu inba kaiba, ai customominmu suna dayawa, yusuf yace abinda nake nufi shine zaka turomin hotunan duka customomin ta WhatsApp saina zani wadda nake neman pls yanzu aboki, yace badamuwa ya bukaci date, sallama kan zai masa text.


Cikin qanqanin lokaci yaga sako dauke da abinda ya bukata. A hankali har idanunsa suka sauka a kanta. Babu bata lokaci ya qara turawa accountr wadda yake nema. Take ya kuma aiko mishi da abinda yake bukata.


Da daddare misalin karfe 9 suna zaune da nana ana hiran yadda tafiyan zai kasance taji wayanta na qara. Ganin babu suna ta katse ya kuma kira ta dauka tare da yin shiru jin mai maganan. Amincin Allah ya tabbata gareki taji ance, cike da mamaki ta amsa wadda ke magana amma bata nuna ba, yace kin gane wadda ke magana? Aa tabashi amsa. Yace wadda kika hadu dashi a bank last wk, tace ok lfy? Kuma aina ka samo lambata? Murmushi yayi kamar tana gabansa yace hakuri zan dada baki da....... tun kafin ya qarasa ta katseshi tace nagode.


Kiransane ya qara shigowa tadaga yace pls kada ki katse aiko yana fada ta qara kasewa.


Dafe kansa yayi, ya zanyi? Kodai matar aure ce da gaske? Aa yabawa kansa amsa. Jawo wayarsa yayi ya shiga WhatsApp. Farin ciki yayi ganin tanayi, bai dauki lokaci ba yayi mata sallama tare da rokanta kada tayi blocking nashi.


Kamar jira take sai gata online taga sako. Murmushi tayi tace bazanyi ba, amma narokeka karabu dani. Yace ba cutar dake zanyi ba, Allah nasane. Toh me kake so aguna? Nace na hakura! Yace in bazaki damu ba inaso muzama frnds. Tace duk abokanen ka maza basu ishekaba saika hada dani? Kuma ai babu tsari yaza'ai ina matsayin mace zakai abota dani? In matarka ta sanifa, nidai baruwana bazanyi abinda nima banaso amin ba. Banida aure kuma yabata amsa, Allah kawo tagari da zuri'a nagari cike da jin dadin addu'a yace ameen. Nan takashe wayan gaba daya don ji take wani irin abu daban tada kasa fassarashi tunda suka soma magana.


Washe gari ko kunna wayan batayi ba haka ta fita zuwa asibiti. Ward dinsu aminiyarta ta nufa ta jawota gefe hadiza tace yau kuma wani lbr muka samu mai dadi. Nan haneefah ta labartar mata da komai.


Hadiza tace nina sanki nasan halinki tunda muka taso bamu taba abota ko da class mate ba, abinda nake so ki fahimta shine bakisan Allah ya turoshi ya zamto silar wani abu bane. Ki karbeshi da zuciya daya, kada kiyi tunanin mugun nufi sannan ki tuna hadisi na ashirin da takwas
An ruwaito daga Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce:
Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Muminin da ke shiga cikin mutane, ya ke kuma hakuri kan cutarwarsu ya fi girman lada akan muminin da baya hulda da mutane, kuma baya hakuri da cutarwarsu*.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼8


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Haneefah ta numfasa tace maganarki hakane, amma inya wuce gona da iri wlh zanyi maganin shi. Murmushi hadiza tayi tace ji nake ajikina alkhairi ne agareki, ta qara da cewa nextwk usman manyansa zasu zo asa ranar aure. Haneefah dake kokarin kunnan wayarta ta daka tsalle ta rungumeta tare da tsananin farin ciki tace nayata ki murna Allah sanya alkhairi yasa gidan kine har abada tace ameen kema Allah kawo nan bada jimawa ba kafin ta bata amsa wayanta ya soma ringing


Ganin lambar jiya yasa ta dauka tare da sallama amsawa yayi ya gaisheta. Murmushi tayi tace ai kaine babba nice da gaisuwa, farin cikine ya lullubeshi jin yasamu karbuwa. Bayan sun gaisa take tambayarsa yadda yasamu lambarta, bai boye mata komai ba ya sanar da ita. Ita kanta tayi tunanin haka. Tace tana asibiti sukai sallama


Bayan ta koma gida da dare sukai waya tare da sanin junan su atakaice. Ba laifi ta sake jiki dashi domin ta dauki shawarar kawar tata.


Cikin sati biyu suka gama fahimtar junansu baki daya, domin ya tashi daga aboki zuwa yayanta. Sannu a hankali shakuwa ke dada shiga tsakaninsu. Shidai yusuf ya tabbatar son haneefah yake domin irin matar da yake so ne. Yasha alwashin saiya koyawa haneefah soyayyar shi.


A sannan haneefah ta gane wanene yusuf, mutum ne mai hankali wadda yasan darajar dan adam, wadda yake da ilmin addini sosai sannan mai aiki dashi. Zuciyartane ya fara saka mata abubuwa da dama kanshi amma tafi fassarashi da shakuwace.

***** ***** ***** ******


Gab suke da zana jarabawar tsallakewa shekarar gamawa. Ansa ranar bikin hadiza wata biyu masu zuwa. Tun a sannan haneefah ta fara shiri domin tana matukar ji da kawar tata.


Shirye shiryen tafiya haneefah take yiwa yayar tata. Sunje dangi da abokan arziki sunyi musu sallama, kowa na yiwa nana fatan alkhairi domin yarince mai nutsuwa kowa na alfahari da umma da yaranta, domin kyakykyawar zuciyarta da hakurinta.


Zauna suke su biyar ranar alhamis daidai yake da washe garin juma'ar zasu wuce abuja domin can jirginsu nana zai tashi sannan haneefah kadai zata rakata. Nana ta kalli kannenta sosai tace nidai zan tafi kamar yadda na sanku ku dada hada kanku, kunga yadda su inna sukai baqin cikin tafiyana amma Allah ya kaddara saina tafi harda ta kaiga suna yadawa a anguwa abba yaki aurar damu sai boko. Abinda nake so da ku shine ku toshe kunnuwanku akan dukkanin abinda zaije ya dawo. Nasanke haneefah kina da karancin hakuri, kidaina biye musu wata rana sai lbr. Sannan ku maida hankalinku sosai gun karatu domin cimma burin mahaifan mu. Ahmad ka kara hakuri insha Allah zaka samu admission duk da abba yana da hanyar samuwa mutanen duniyar nan sai a hankali, domin shi yana da gaskiya Idan kana so gaskiya ta yi saukin fadi a harshenka, kuma mutane su kiyaye ka, to ka nisanci kwadayi kuma kar ka ji tsoron kowa sai Allah, in lokaci yayi zaka samu. Sannan ke haneefah kema ki dage da karatu kinyi nisa a health babu zancen accounting sannan ki dada hakuri akan hadaki da abba da suke a hankali zai gama sanin komai kudai ku zuba musu ido, babu maida martani. Nasiha sosai yayarsu ta musu sannan ta bukaci shiga suyiwa su inna sallama.


Abban su dake bakin koma yazo shiga yayi saurin barin gurin. Bangarenshi ya nufa yayi alwala tare da godewa Allah daya bashi zuri'a masu albarka.


Suna shiga suka tarar da zuwaira bakin kofar suka gaisheta suka wuce. Gaida inna sukai sannan suka samu guri suka zauna. Nana ce ta fara magana tace dama nazo in muku sallama ne. Inna ta dubesu a wulakance tace naji gobe zaki tafi, Allah kiyaye hanye, haneefah gudun kada wani magana ta taso taja hannun nana zasu fice taji ance sai kiyi abinda ya kaiki domin kada a zo mana da jikan da zamu nema uba mu rasa cewar zuwaira, inna ta karba tace gaskiya kam sbd muna furci suka mallake shi suka kwashe kudin zasu qasan waje su cinye. Jabir da ya salim daya shigo yace munafukai wlh sai Allah ya saka mana ku da matsiyaciyar uwarku.


Saukan mari yaji ras a fuskar sa, cike da mamaki ya bude baki yake kallon ta, suma duk suka taso cike da mamaki ganin wadda yayi mari
*Dr HANEEFAH*👩🏼10


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Kawar da kanda zatayi tagan shi ya nufosu. Yayi matukar kyau cikin kananan kaya. Kallon shi take harya iso cike da murmushi zatayi magana yace waye wannan? Kanin auntynane. Shine kika tsaya akan layi da mutum.


Shigo ganin anzo an tsare ta da tambaya yace mallam lafiya? Yusuf ya juyo cike da bacin rai yace kada ka sake furta mata wata kalma, ya juyo kanta biyoni. Itako cike da mamakin abinda yayi take bin bayansa har suka iso inda motarsa take. Yadan jingine tare da dubata yace yaushe kika shigo shine ko waya bazaki mun ba? Dariya tayi tace yau nazo kuma gobe zan koma, na rako nana ne zata fita karatu, shine bazaki fadamin ba sai dai inji kinzo kin tafi. Tadanyi murmushi ta juya zata koma gun yan uwanta taga suna nufota.


Duk da ya girmesu yadan risina ya gaishesu suka amsa. Yace in bazaku damu ba zan kaiku inda kuke muradi? Aunty tace aa gida zamu koma babu nisa. Duk da haka saida yace zai kaisu. Yayi parking suka sauka yace aunty anjima zan iya zuwa. Tace Allah kaimu. Haneefah zata fita yace minti daya, ta juyo suka hada ido taji wani irin shock take ta sunkuyar da kanta. Yace na katse miki hira da saurayinki shine kike fishi? Allah baki hakuri. Ta juyo tace ba komai ta fice ta barshi.


Karfe takwas ya same shi a gidan yayi sallama ya shiga. Zaune ya tadda auwal a parlour, suka gaisa. Ya mishi bayanin gurin haneefah yazo. Ya shiga yakirata.


Sanye take da himar har kasa ta zauna mesa dashi ta gaishe shi kanta a sunkuye domin tsoron hada ido take dashi yadda nan take takejin wani iri. Nazarinta yayi sosai sannan yace haneefah in tambayeki? Ina mai sauraronka. Shin kin yadda dani? Kai tsaye tace eh. Mesa ya qara jefo mata tambaya? Sbd ka kasance mutum nagari. Shiru yayi yakasa ce komai.


Inaso in sanar dake ko ni wanene. Tace ina sauraron ka;


Kamar yadda na sanar dake sunana yusuf. Haifaffen garin kano ne ni, anan nayi dukkanin karatuna nakaranta computer engineering. Bayan na kammala nayi masters dina sannan nasamu aiki a garin kano. Daga baya ne akamin transfer zuwa nan. Mahaifina Alhaji ismail da da mahaifiyata Hajiya hauwa wadda muke kira momy. Mahaifina dan kasuwa ne babban sannan mahaifiyata lecturer ce a university. Hausa fulani ni ne, mahaifina mutumin kano, mahaifiyata daga adamawa suke. Nine first born gidanmu, sai kanne na salma, aisha da autanmu alkali. Salma tana da aure da yaronta daya sannan ma'aikaciyace a PHC agency dake kano. Ita ko aisha na university 200lvl autanmu kuma yana jss3.


Cike muke da kaunar junanmu, iyayenmu sun wadatamu da kyakykyawar tarbiyya. Amma nafison aisha cikinsu. Ya mika mishi wayarsa dauke da family picture.


Haneefah takurawa hoton ido, suna da matukar kyau. Dukkaninsu fararene sannan kyakykawan jikansu na kwance jikin kakanshi. Idonta ya fada kan aisha taji tana sonta. Batasan sanda ta soma addu'an Allah ya bata ikon shiga cikin suba.


Tace masha Allah, Allah dada kawunanku, ya albarkaci zuri'arku. Cike dajin dadi yace ameen.


Ya saci kallonta yace sannan abu daya. Mahaifiyata naji da kanwarta umma nusaiba. Ita umma nusaiba yarta daya ne. Wadda mahaifiyata ke shirin hadani da ita aure. A sannan haneefah ta dago ido suka hada ido, taji wani irin faduwar gaba da bazata iya fassarashi da menene ba. Ganin yana kallonta ta sakar mishi murmushi ta hadiye hawayen da ke shirin zubomata tace Allah sanya alkhairi yaba ku zaman lfy. A sanyaye yace ameen. Amma haneefah bana son aure, kusan shekara biyar amma sai dauko min da maganar ake.


Cike da mamaki take kallon sa tare da cewa zabin mahaifiyar taka? Nayi nayi in saba da sonta amma nakasa, nayi musu bayani amma sun kasa ganeni aisha ce kadai ke tausayamin, amma tace dani zan auri zabina amma itama in auri zabinta. Kabsha!!! Da yana ganin zuciyar haneefah ko zancen bai dauko mata ba.


Hamman karya ta kirkiro tare da mitstsike ido alamar bacci. Tace in zaka dauki shawarata ka aureta saboda babu wadda takai mahaifiya. Ce mata zayyi ina sonki amma ya gagareshi. Sallama sukai akan gobe zaizo su koma kano tare. Tadai amince amma tayi hakanne domin ya tafi.


Ban daki ta wuce ta ta zauna bakin bafon wanka, hawaye taji yana tsiyaya a kumatun ta. Ji take kamar ta kurma ihu. Toshe bakinta tayi ta soma kuka mai tsuma zuciya. Shin kishi take? Hakan na nufin tanason yusuf? Innalillahi tashiga furtawa a zuciyrta. Abinda nake gudu kenan yanzu ya zanyi? Addu'a ta bawa kanta amsa. Take ta dauro alwala ta fito domin kai kukanta ga mahaliccinta tun kafin abin yayi tsanani. Bayan ta idar da raka'o inta ta zauna yin addu'a.


Bayan ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye. Meyasa baya iya furta mata yana son ta? Yanzu in wani ya rigaka fa? Iya saninta da yayi basu tana hiran wani ba. Dauko wayansa yayi yashiga kiranta. Zaune take tana addu'a taji kiran wayarsa busy ta danna masa. A naga bangaren kuma kodai tana wani abinne?


Jiran kiranta yake amma ya ji shiru. Itako ta kasa rintsawa sai faman tunani take tare tsare kanta da tambayoyi yaushe ta fara sonsa?? Mesa take bata lokacinta? Kusan idanunsu biyu. Ta gama yanke shawarar rabuwa dashi tunda ba sonta yake ba. Shima ya dauki alkawarin zuwa gobe zai sanar da ita zabinsa.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼9


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Haneefah idonta dake cike da hawayen bacin rai ta nuna shi da dan yatsa tace duk zagin da zaka mana zan lamunta amma kada ka kuskura ka sa mahaifiyata ciki, kai har kana da bakin da zaka ce da munata TSIYA? Gaku matsiyata, duk girman da muka baku bakwa gani? Meza mu muku mu burgeku? Muda kake gani ka cire idanu a kanmu domin Allah na tare damu. Gwamma ka fuskanci rayuwa na kwarai kaji dadin duniya da lahira, Idan kana so ka zauna lafiya: Ka bar kallon rayuwar wasu, ka kalli taka kawai
ka bar duba mai wane yake da shi, ka kalli abun da kai kake da shi ka wadata da shi, ka bar kokarin sai ka zama abun da wane ya zama, in ba ka tsaya a in da Allah ya ajiye ka ba to ka hadu da wahala ta har mutuwa sannan duk abun da kake nema, ka nema a wajen Allah, ka bar tunanin Mutum zai maka, ko da a ce ya shigo rayuwarka a matsayin sila, wata rana zai iya goranta maka. Kai namijine ka tsaya ka nemawa yaranka ilmi sannan ka datar da rayuwarka da tsoron Allah. Tana kaiwa nan zata juya ta fita ya fizgota zai wanka mata mari yaji an sake marin nasa. Abba suka gani tsaye cikin bacin rai, ya kalli inna da yaranta yace nagode miki ya juya yafice tare da su haneefah.


Zaune take zuciyarta na mata kuna, jawo wayanta tayi ta kira yusuf. Sallama yayi ta amsa suka gaisa suka somo hira ko zata dan mance bacin rai, yace meke damunki cike da mamaki tace me kagani? Ji nayi a muryarki. Murmushi tayi tace babu komai. Yace bazan matsa miki ki fada min ba amma ki sani in kakasance cikin bacin rai ko farin ciki dole akwai wadda zaka ware ka fada mishi duniyarnan, nayi zaton tuni na tashi matsayin aboki na koma yayanki, amma bansan ko kina shakkata bane. Haneefah tace ko daya kawai dai banajin dadine, zazzabi ke damunki? Aa yace toh tashi masha ki dauro alwala ki fara karatun Qur'ani har bacci ya daukeki. Cike da murmushi ta amsa ta katse wayan. Yusuf na matukar birgeta musamman in suna hira sayya sako mata batun addini, tana matukar jin dadin hakan.


Washe gari misalin karfe goma suka dau hanya kan zasu sauka gidan auwal (yaron mama) domin ya koma can da zama. Nana na ta kuka har suka iso birnin tarayya. Sun sami kyakykyawan tarba. Da misalin karfe 5 na yamma haneefah tace da matar auwal tana son sudan fito su zaga anguwa.


Sanye take da dogiwar riga abaya, tadan shafe bakinta da jan baki, sannan tayi rolling dankwalin abaya da dan takamin ta mai tudu. Tayi matukar kyau sosai. Tafe suke suna hiran manyan gidajen abuja kamar ba Nigeria ba.


Cike da mamaki yake kallonta har suka zo suka wuce. Suko basu lurama da ana kallonsu ba. Tafiya suke sai matar auwal taga kanin kawarta yayi parking ya fito suna gaisawa. Ya dubi haneefah dake kallon wani gida yace kannen kine? Tace aa cousins nashi ne. Yace Allah sarki aunty banyi hanzari ba zaki aramin wannan minti biyu ya nuna haneefah tayi dariya tace bismillah. Suka danyi nesa dasu.


Kafin ya soma magana tace haba mallam ya zaka ce abaka aroma sai kace kaya tana magana tana hade girar sama da kasa. Dariya sosai ta basa yana dariya.


Yusuf dake cikin mota yaji wani irin abu ya tokare masa wuya. Me tace dashi har yake mata irin wannan dariya? Cike da bacin rai ya bude motan ya fito ya nufufi gunsu.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼11


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Washe gari misalin karfe takwas da rabi yasamesu a airport sbd karfe tara dai dai zirginsu nana zai tashi. Nana kuka take na barin gida, ita ko haneefah kukan rabuwa da yar uwarta take da soyayyar da yayi mata ba zata. Sanda akai kiransu kamar sun rabu kenan take kuka. Suna ji suna gani suka rabu.


Tunda tazo gida takasacin komai inbanda shayi. Auwal yayi fadan harya gaji. Zaune take duk tabi ta dami kanta tsakanin jiya da yau. Ta kammala shirinta ta tuno da maganar yusuf inda yake cewa; Duk lokacin da kake so ka zama cikin mutanen da suka rabauta, to ka kiyaye abubuwa kamar haka:


*_Kar ka takurawa kanka akan wani abu da bai iso gare ka ba_*


*_Kar ka damu da me zai faru gobe?, domin idan ka inganta yau dinka, to gobenka ma za ta yi kyau_*


*_Ka tsarkake zuciyarka daga hassada, mugunta da kyeta_*. Goge kwallar da suka zubo mata tayi. Mesa zan dami kaina? Nan take ta fara addu'a Allah bata ikon fin karfin zuciyarta.


Tagama shirinta tsaf ta fito. Ta ganshi zaune a parlour shida auwal. Bude baki zatayi magana auwal yace gata ta fito, yanzu nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login