Showing 36001 words to 39000 words out of 74305 words
Chapter 13 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
tunani meya kawo ta? Tuna ranar da ta durkusa gabanta tana bata hakuri tayi, share hawayenta tayi ta dauko ruwa da cup ta aje akan plate ta fito.
Momy duk kunya ta cika ta dakyar ta bude baki tace dama address dinsu Haneefah nazo nema.
Hadiza ta dago tace ko lafiya? Momy tace gaskiya gane kuskurena nayi nake son bata hakuri.
Murmushin takaici hadiza tayi tace kuskure? Kin manta lokacin da na durkusa gabanki ina baki hakuri? Ko da Haneefah bata kasance matar aure ba bazaki sameta da sauki ba balle yanzu da aurenta haihuwa yau ko gobe.
Momy cike da dana sani tace tayi aure? Hadiza tace eh lokacin da kika hana auren cikin manemanta suka fito a wata biyu aka daura auren yanzu haka tana kasar waje da aure batama Nigeria.
Cikin sanyin jiki ta tashi tace nizan wuce. Har bakin gate hadiza tayiwa Momy rakiya tace ta gaida gida.
Bayan tafiyarta Hadiza tace am sorry na miki karya amma Haneefah ce ta nemi wannan alfarma agurina, kuma bazan iya katse mata karatu a wannan lokaci ba Allah zaba musu abinda yafi alkhairi.
***** ***** *****
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Zaune take cikin office tana tunanin sabon salon Dr Mubarak, in ma sonta yake ya sani bazayyu ba domin bazata sakawa da barrister da haka ba. Bangare daya kuma ga Rohan daya fitineta da nashi salon, da tayi magana yace kawai missing nata zayyi inya koma India.
Juyo da kujeranta tayi tana fuskantar hoton yusuf dake gaban table nata. Raihana ce ta shigo da sallamarta tace Haneefah a gyne ward kina da patient ana neman ki. Dago ido tayi tace Raihana zo nan, tazo kamar yadda tace ta nuna mata hoton Yusuf tace dubi shi kullum cikin tunaninsa nake bansan ko shi yana tunani na ba, nayi escaping daga Nigeria ko zan daina tunaninsa amma gashi sauramin shekara na koma ban dain.....
Bata qarasa ba taji wani irin murdan mara daya hanata motsi, shirun da tayine yasa Raihana tace ina jinki. Amma sai ganin Haneefah tayi tana salati tare da rike mararta kafin tace meye ta fadi su mammiya.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼37
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Raihana ta matukara rudewa, ta rasa wani irin taimako zata fara bata, da sauri ta saki Haneefah ta fito domin kiran taimako ta ga Kevin da Rohan. Ganin rudewarda tayi yasa suke tambayarta, ganin ba bata amsa zasuyi ba yasa suka shigo office din.
Dukka sukayo kanta suna jijjigata amma ko motsi batayi, Kevin ya bude fridge ya dauko ruwa aka yayyafa mata amma shiru. Ganin haka yasa Rohan daukarta suka fita.
Emergency suka kaita, Kevin ne yayi kokarin kawo musu rigar shiga threater ganin haka yasa Raihana yasa fashewa da kuka tana cewa meya sameta ne zaku shiga da ita? Rohan a rude yace kisa mana! Dai dai nan Dr Michael yazo yake tambayar Raihana lafiya take kuka?
Cikin kuka tace sir Haneefah ne unconscious, cike da mamaki yace Haneefah? Bai jira amsarta ba ya wuce inda aka shigarda ita.
Likitoci kusan goma akanta. Sanda suka tsananta binciken awa biyu suka gano matsalar dake damunta. Raihana nesa da su tayi tana kallon irin binciken da sukeyiwa Haneefah, babu abinda take sai addu'a Allah bata lafiya. Hawaye take da ta tuno dazu tare suka ta ho asibiti amma gashi yanzu itace kwance bata san ma inda take ba.
Duniya kenan babu abinda zamu nema muji dadi kamar mu kasance masu kyakykyawar zuciya. Sharar hawayenta tayi lokacin da ake kokarin daga Haneefah acireta a daki zuwa daki na musamman.
Bayan an kwantar ta ne Dr Michael ya kalli Raihana yace nan da awa daya zata iya tashi, komai zai daidaita amma ki kirani ina office, ta amsa da toh.
Dukkanin su zubawa Haneefah ido sukai ganin yadda ta koma cikin awa uku! Duk dauriyar Rohan saida ya zub da hawaye lallai dan Adam bamu da tabbas, rayuwa muke da buri amma bamusan yaushe zamu koma ga Allah ba, yanzu ne anjima aa Allah shiya barma kansa sani, ji yake kamar ya ciro cutar ya dasa a jikinsa. A hankali ya tako har ya iso dab da ita yace Haneefah ki bude ido dan Allah, kitashi kiga yadda muka damu da ganin kin bude idanunki, in wannan ne matsalar na miki alkawarin maganance miki ita zan kasance da ke har abada....
Raihana ta katseshi da cewa Rohan na rokeka da Allah kayi shiru ka kyaleta, irin wannan yanayin zaka danko mata maganar zaka rayu da ita inta tashi lokacin hayaniya sannan in ciwon bai ragu kuma fa? Ko kallon Raihana bayyi ba yaci gaba da surutan shi.
A hankali ta bude ido tana kallon inda take, lumshe ido tayi jin abinda take ji ajikinta. Sake bude idonta tayi ta juya kenan suka hada ido da Rohan.
Rohan yace sannu Haneefah, da sauri Raihana tazo kusa da ita tana cewa Haneefah meya sameki? Kina iya magana? A hankali Haneefah ta tashi ta zauna tace am fine but.... kuma sai kuma ta kasa karasawa. Raihana tace bari inje in kira Dr yace inkin tashi in kirashi.
Dr Michael ya dubi Kevin da Rohan yace su basu guri. Ya dubi Raihana yace dalilin da yasa bance ki bamu guriba shine duk lokacin da irin wannan matsala ta taso mata zaki iya taking action domin na tabbata tare kuke. Dr yace Haneefah kina da aure? A sanyaye tace babu.
Ya fara bayani yace abinda ya sameki ba abin tada hankali bane amma sai kinyi saurin daukan mataki wato aure, inba haka ba abin zai samo miki babbar matsala. Yaci gaba da bayani wato kina da tsananin sha'awa right? Ya jefo mata tambaya
Nan Haneefah tayi shiru tare da sunkuyar da kanta katsa. Dr yace wato kwayayen haihuwan kine da basu samu mazauni suke son fitowa ta hanyar baki wahala amma mun gano kuma kina da tsananin sha'awa, ciwon marar da kikai yana nufin muddin baki samu haihuwa ba ko sau daya ne hakan zaici gaba da faruwa dake, kuma zai iya haifar miki da matsala a mahaifa, shawarar da zan baki shine kiyi gaggawar yin aure. Ke kuma Raihana nan gaba taimakon da zaki bata shine allurai zaki mata ki kwantar da ita, da zarar ta farfado zata koma daidai.
Ya kalli Haneefah yace Allah baki lafiya yanzu zan aiko miki da alluran naki, zaku iya tafiya. Bayan fitar Dr Raihana ta taso tazo kusa da Haneefah, zatayi magana taga su Rohan sun shigo.
Sannu sukai mata ta amsa, ta tashi a hankali ta lullube jikinta tace da Raihana zata je tattaro kayanta a office ita tajira akawo mata alluran sai su wuce gida. Rohan yayi saurin shan gabanta yace Haneefah baki da lafiya zanje in dauko miki duk abinda kike bukata ki kwanta ki huta tukun sai mu wuce. Wani kallo Haneefah ta watsa mishi, ba shiri ya bata hanya ta wuce.
Tana shiga office ta maida kofar ta rufe da makulli. A hankali taje kan kujerarta ta zauna, hannu tasa ta dauki wayarta dake katsa ta kunna. Idanunta suka sauka kan hoton Yusuf. Kamar kullum ta shafa hoton a hankali tace har yaushe zan jira ka? Zuciyata da dukkanin gangar jikina takace yaushe zaka zo mukasance cikin farin ciki? Banajin zan iya kasancewa da wani da namiji inba kaiba Yusif.
Runtse idanunta tayi da jin murdan marar har yanzu bai dakata ba. Ya Allah ina rokonka da kyawawan sunayenka, dan soyayyar da kamawa annabinmu fiyeyyen halitta, annabi Muhammad (S. A. W) Ka bani ikon tsare kaina da aikata zina, ka bani ikon killace budurcina har izuwa gidan mijina, ka bani ikon cire son bawanka Yusuf a zuciyata inba alkhairi bane shi gareni, inko shi mafi alkhairine gare ni kabani ikon hakuri da har izuwa randa zaizo gareni, ya Allah ni baiwar kace mai yawan zunubai ina neman tuba gare ka... Nan ta durkusa ta soma kuka kamar ranta zai fita.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼38
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Saida taji bugun kofar tamkar za'a balle kofar sannan ta tashi taje ta bude kofar. Rohan tagani biye da Raihana, basu hanya tayi suka wuce. Da taimakon Raihana suka tattara dukkanin abinda take bukata suka fita.
Cikin mota babu wadda yayiwa wani magana. Raihana ke tuki gefenta haneefah, kevin da Rohan suna baya. Har suka iso gida babu wadda yayiwa wani magana. Haneefah ce ta fara shiga gidan, bata tsaya ko ina ba sai bedroom. Rage kayan jikinta tayi tashiga bandaki domin wanka.
Da ruwan dumi tayi wanka ta fito daure da towel. Gaban mirro ta tsaya tana karewa kanta kallo ganin lokaci daya harta fada, ikon Allah tace cikin zuciyarta, yanzu nice cikin qanqanin lokaci na koma haka? Kuma nake buri da son haduwa da Yusuf, dan Adam kullum cikin buri muke yanzu in fadi na rasu a wannan lokaci babu abinda zan tsira dashi illa abinda nake sakawa a zuciyata, in sharri ne yaragemin. Allah sa mucika da imani. Ko shafamai bataiba tasa doguwar riga da himar ta tsaya sallah. Bayan ta idar ta kwanta ba'ajima ba bacci ya saceta.
Jin shiru yasa Raihana lekowa taganta tana bacci, ta koma falo tace dasu tayi bacci. Sallama sukai mata akan anjima zasu zo su ganta.
Gab da magriba ta bude ido. Raihana tagani gabanta tayi tagumi ta zuba mata ido. Janye mata tagumin tayi tace nasamu sauki fa, banajin... kallon agogon da tayine yasata tashi da sauri ta nufi banda ki yin alwala. Bayan ta idarne ta zauna lamizi domin mintina kalilan suka rage lokacin sallah.
Zaune suke suna cin abinci kan dining table, duk motsin Haneefah idon Raihana na kai, data lura da hakan tace na samu sauki, abaya yanamin irin wannan ciwon amma na yaune ya tsananta kuma nasan insha Allah shima daga yau na daina.
Raihana tace tausaya miki nake, lokaci daya yadda kika rame, kenan kowanni wata haka zaki kasance, pls Haneefah kiyi auren kada wani ciwon ya tashi.
Haneefah tace in rashin lafiya ta sameka kafin ka tuna da likita, kafin ka tuna da komai ka tuna da Allah. Ko wanni bawa ya kamata ya kiyasta a zuciyarshi Allah shi ya kawo wannan cutar sannan Allah shi zai warkar dani, ban karyata abinda suka ce ba domin nima nakarance shi amma kada zawa ranmu cewa lallai hanyar da suka fada mana itace kadai mafita, addu'a ma maganine, sbd haka zanyi kokarin yin auren amma saina kammala karatuna tunda na kusa sannan bani da miji sai Yusuf.
Raihana wani sa'in tana mamakin rayuwar HANEEFAH, tabbas komai na rayuwarta baki daya bisa tsarin Allah ne amma taki yadda zata manta da wannan saurayin nata, duk da batasan abinda ke zuciyarta ba domin wani sa'in zasu kai wata biyu bata ambaceshima amma lokaci daya wataran ta hoton shi gaba tayi ta kuka.
Raihana tace Haneefah kina bani mamaki sosai, kina cewa kin mika lamuranki ga Allah amma haryanzu kin kasa rungumar kaddarar rabuwa da Yusuf, yakamata ace yanzu kin manta da shi.
Haneefah tace mantuwa? Kenan ba kaunarsa nake ba, inkinga na manta da Yusuf bana numfashi, inna daina addu'a samunsa matsayin miji saina ganni cikin gidan wani aure, auren ma bana tunanin zanyi shi dan ina so, nan da shekara daya zan koma gaban iyayena kinga bazasu so ganina ina zaune gaban su ba dole inyi aure, a sannan zanyi yunkurin mace yin rayuwa da Yusuf.
Haneefah ta share hawaye yanta tace family na suna so na, basa kaunar bakin cikina musamman ummata, ko aiki bazan soma a kasar muba sai da aure akaina.
Raihana tace Allah zaba miki miji nagari, ya zakiyi da Rohan da dukkan alamu yana sonki.
Tsaki taja tace rabu da shirmen shi, shida saura wata uku mu rabu, insha Allah zamu rabu lafiya. Haka suka ci gaba da tattaunawa har lokacin sallah isha'i. Bayan sun idar ta dauki waya domin kiran umma su gaisa, ba lallaine ta sameta ba a irin wannan lokaci ba takira Nana.
Bayan sun gaisa take mata albishirin ansa ranar auren ta nan da wata daya. Ihun murna har yasa Nana katse wayar. Raihana dake kusa da ita duk hankalinta ya tashi tace lafiya? Bata saurareta ba ta kara kiran Nana.
Nana tace so kike ki toshemin kunnuwa da wannan ihun? Haneefah tace sis yi hakuri duk cikin murna ne, amma nayi murna sosai wallahi ya sunan shi? Abdullahi Nana ta bata amsa, naje interview ne muka hadu dashi, saurayine bayyi da mata sannan na yarda da tarbiyyarsa da ilmin addininsa atakaice mun yarda da junan mu cikin kankanin lokaci shine yace da gaske yake kuma baya son a dauki lokaci, watan mu uku da haduwa.
Haneefah tace wallahi nayi matukar murna amma ai wata daya yayi kadan wani irin shiri kuka tana da?
Nana tace nima so nake na kiraki mu fara shirin kika rigani kira, yanzu abinda nake so da ke nan da sati uku zanzo amma kada ki fadawa kowa a gida nasan zasuce zasu hanani.
Nana tace ai in babu ke auren ma bazai dauru ba. Dariya Haneefah tayi tace yanzu me yarage dan nasan kun gama siyayyar kayan kitchen?
Sai kinzo kedai... cike da doki suke hirar yadda bikin zai kasance, sunyi sallama akan anjima zata kirata.
Sanar da Raihana abinda ya faru tayi, ta tayasu murna itama tare da yi musu fatan samun zaman lafiya.
Sauki ya samu gurin Haneefah domin tana fita aiki kuma tana samun yin karatun ta. Rohan yayi duk wata hanyar da zaibi ya samu hadin kan Haneefah abin ya gagara, ganin tana son watsar dashine yadan hakura da takura mata.
Kamar kullum bayan ta samu nutsuwa da aikin ta ta nufi wani bangaren asibiti domin tayasu aiki. Daga nesa ta hango bakaken fata cikin asibiti, tazo dab dasu taji suna hausa. Farin ciki ne ya kamata, a hankali tayi musu sallama suka amsa...
Daidai inda dayar take cewa umma kiga Yusuf da dansa, ta mikawa mamar wayar kenan idanun Haneefah suka sauka kan hoton Yusuf rike da jariri yana dariya. Kallon wayar take harta soma ganin duhu....
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼40
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Zaune suke cikin jirgi tana kissima farin cikin da yan uwanta zasu kasance in sun ganta, zata ga Umma, Abba, Ahmad, Bintu da Amal? Bude ido tayi tana murmushi.
Bayan an sanar dasu zuwa mintuna kadan zasu sauka cike da takaici tana kallon Raihana tace na manta sim card na a London, yanzu nayi loosing cantact na. Tsaki taja najin haushi.
Raihana tace saiki sake sabo, ai ba wani abin bacin rai bane. Bayan sun sauka a airport suka ci sa'an samun zirgi zuwa kano. Basu sami wahala wajen samun ticket ba.
Misalin karfe tara na dare suka sauka a airport. Ga kaya ta rasa yadda zatai, kiran Nana tayi ta sanar da ita isowarsu. A nanne Nana ta sanar da zuwan Haneefah a gida. Motar Abba Ahmad da Nana suka shiga zuwa airport.
Zaune suke tana shakar iskan kano, marmari take wajen ganin iyayenta musamman Umma. Suna hira jefi-jefi da Raihana domin ta gaji, banda Haneefah da tsaban farin ciki taji babu gajiyarma tattare da ita. Tunanin Yusuf ya tsaya mata a kasan zuciya amma farin cikinta ya rinjeye tunanin wannan karon. Karaf idonta ya fada kan Nana, duk girmanta bai hanata tashiwa da gudu taje rungumar yar'uwarta ba.
Murna sosai suke da ganin juna. Ahmad tsaye yayi yana kallon kanwar shi da dukka ta canza, farin cikine fal azuciyarshi na ganin ta canza hankalinta kwance duk ta canza. Sai a sannan ta iso gare shi ta kama hannun shi.
Dariya ya soma yace keda zan ganki da jean ko mini skert saina ganki da katon hijabi. Dariya itama tayi tace ai tunda nazo sai kun gaji da gani. Raihana ta iso suka gaisa cikin harshen turanci, daganan suka soma tattara kayansu zuwa gida akan gobe zasu zo su karasa kwasan sauran kayan.
Bintu ce ta bude gate suka shigo. Umma da Amal tsaye a haraba gida, murna bayyene a fuskokinsu na jiran Haneefah.
Motar bai gama tsayawa ba Haneefah ta fito da gudu taje ta rungumi Umma tana hawayen farin ciki tace Umma nayi kewar ki. Umma ta dagota tace muma haka zomu shiga daga ciki sannun ku da zuwa. Bintu da Amal suka kamo hannuwanta cike da farin ciki suka shiga.
Basu tsaya ko ina ba sai dakinsu. Haneefah ce ta fara shiga wanka sai Raihana. Bayan sun kammala komai gurin abinci Raihana ya gagareta ci. Saida Ahmad ya fita ya nemo mata gasassan kaji ya kawo ta samu ci, daganan ta musu sallama ta kwanta bacci domin gajiya take ji.
Zaune take gaban Abba tana gaishe shi, dukkaninsu sun zagayeta tana musu karin bayani yadda take tafiyar da rayuwarta da yadda ta hadu da Raihana. Dukkanin su farin ciki suke ganin hankalinta a kwance, fatarta ta canza, ga kyau da ta kara. Sai karfe kusan sha biyu Abba yace toh kowa yaje ya kwanta abarta ta gaji.
Su biyu aka barwa dakin. Haneefah tsananin farin ciki duk da ta kwanta dakyar baccin ya saceta.
Washe gari da asuba dakyar Nana ta tashe su sukai sallah. Bayan sun idar suka koma bacci. Lafiyeyyen breakfast Nana ta hada musu.
Umma ne ta shigo tana yiwa Nana sannu da aiki. Nana ta turo baki tace rabu da yarki, maimakon tazo daya da yan uwanta yan Nigeria saita dauko balarabiya Allah kadai yasan wahalan da zata bamu kafin ta koma.
Umma tace bakon ka annabinka kada ki bata ladan ki, mukasance masu karrama baki a duk sanda suka zo mana, sannan ciyar da mutum ba karamin abu bane dan haka mu kwadaitawa kanmu ciyarwa komi kankantar sa. Nan da sati biyu kina gidan ki, in kikai baki kada kibarsu su tafi batare da sunsa abinci a bakin su ba, bayan kauna da kimar da zaki samu gun jama'a akwai kyakykyawar saka mako gurin Allah.
Sannan batun dangin miji, ki toshe kunnuwan ki da dukkanin huduban da zakiji, ki zauna dasu tsakani da Allah, ki kauda da kai ga dukkanin abinda zaki ji game dasu. Ki kyautata musu, tabbas dan Adam ba'a iya musu amma duk musguna miki da zasuyi muddin zuciyarki daya ne wata rana zasu sauko su fara binki, wasu matan basa la'akari da suma dangin mijine sannan kada mu manta, duniyarmu ta yau duk abinda kayiwa mutum kaima za'a maka saboda komi qanqantar alhaki zai bika. Allah sa mudace
Nana tayi