Showing 54001 words to 57000 words out of 74305 words
Chapter 19 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
sonka ina da wadda nake so.
Damm!! Yaji gabansa ya fadi.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFA* 👩🏼55
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Dr Mubarak durkushe yake gaban Abba yana jiran amsar da zai fito daga bakinsa.
Abba yace Alhamdulillah gaskiya naji dadi kwarai da gaske wannan maganar taka domin kai yarone mai tarbiyya, amma zan so naji ra'ayin ita Haneefah kafin ka turo magabatan naka domin bazan aurar da yarana ga wadda basu aminta ba.
Dr yace dama izini nazo nema, in ka amince min zuwa gobe zan wuce can London mu daidai ta.
Abba yace toh yayi kyau, Allah kiyaye hanya. Sukai sallama. Bayan fitarsa ya wuce gida ya sanar da barrister yadda sukai, ta nuna masa farin cikinta tare da masa fatan alkhairi amma kishin na nan, babbar dutse ta ajiye a zuciyarta daya danne mata shi wato _AMBATON ALLAH_. Shiri tsaf yayi yana jiran wayewar gari.
*
Umma da jin zancen tayi farin ciki amma ba can cikin zuciyarta ba amma bazatayi shishshigi lamarin ubangiji ba zata ci gaba da addu'a Allah tabbatar da alkhairi rayuwar auren su
**** ****
Da sauri Raihana tazo ta riketa tace haba Haneefah kin manta baki da lafiya ne? Fizge rikon da Raihana tayi mata tayi tace kice dashi ya fita banason ya qara ko da awa dayane, tana kaiwa nan ta dauki wayarta ta fice tabar musu gidan gaba daya.
Raihana ta bita da kallo cike da mamaki, yau ita take tsawata Yusuf dinta haka? Ita da ko a hoto a nutse take masa magana. Fita tayi domin bin ta Yusuf yace dan Allah ki saurareni kada dan ita taki saurarata kema kice bazaki saurare ni ba. Raihana tace mu koma falo sai inji meke tafe dakai.
Jikinsa a sanyaye yace dagaske Haneefah tana da wadda ta ke so? Raihana tayi murmushi tace iya zamana da ita yau kusan shekaru hudu babu wadda take so tamkar ka, bata da zancen kowa sai naka, dukkanin burin ta da farin cikin ta a tattare dakai take hangowa.
Yusuf yace Alhamdulillah, tabbas nasan muna son juna tunda duk tsawon lokacinnan bamu daina dawai niyar soyayyar muba, amma bansan dalilinta naqin sairarona ba.
Raihana tace akwai dalili, mahaifiyarka ta nemi alfarman inaga wannanne dalili.
Yusuf yashiga mamaki, wato Momy har Haneefah bata bari ba? Cike da damuwa ya sanar da ita duk abinda ya faru dalilin rabuwansu da bayan rabuwarsu ya qara da cewa dan Allah ki sanar da ta saurareni na sake dawowa rayuwarta.
Raihana kam taga abu, sun rabu kuma suka sake zuwa suka hadu lallai mahakurci mawadaci tace kada ka damu zan mata magana, insha Allah zaku daidaita nayi farin ciki sosai.
***
Nana na katse wayar ta juya tana kallon mijinta tace wanene bakon da ya sauka gidan Haneefah? Kai tsaye ya bata amsa abokina Yusuf, nabaki labarin sa ai.
Nana tace ko kana da hoton sa? Yace menene na bukatar son ganin hoton sa? Tace nidai inason ganin pls ka nunamin.
Dauko wayarsa yayi ya lalumo hoton Yusuf ya nuna mata. Nan take ta hade rai tace ai dana san shine ban bari ka hada sa da ita ba. Yace dalili? Nana ta sanar dashi komai tace sun rabu, yanzu ta ganshi hankalinta ya tashi,nasan yanzu haka tana ta kuka domin har yanzu bata daina son sa ba, ni abinda nake gudu kada damuwar ya taba karatun ta.
Abdullahi yace ki kwantar da hankalin ki, inshaa Allah bazai taba karatun ta ba yanzu ki kirata ki kwantar mata hankali. Nana ta samo kiran Haneefah yana ringing bata dagawa. Nan hankalinta ya tashi tace dan Allah ka kira abokin naka kace kada maganar komai ya hada su nasan yadda take sonshi ganin sa ma tada mata da hankali yake.
Ganin yadda hankalinta ya tashi yace to zan kirashi, dakyar ya lallabata tayi bacci.
*****
Zaune take tana kuka mai cikin sauti mai tsuma zuciya, gata bata da lafiya duk ta rame na lokaci gida abar tausayi. Babu abinda takeji kamar ta cire zuciyarta, tunani take duniya gidan wahala.
Wannan wace irin so ne? Mahaifana suna so na amma duk nabi na tada hankalina?? Anya Haneefah abin naki bayyi yawa ba? Tu no da abinda taiwa Yusuf ne yasa ta kara fashewa da kuka tace ina sonka amma bani da mafita bayan wannan, mahaifiyar ka tamin iyaka da kai, zanbi ko wacce irin hanya domin ganin zamanka lafiya da mahaifanka. Ganin tunani da kuka ba shine mafita ba, shiru tayi tana kallon yadda kowa ke harkan gabansa babu ruwansu da kowa. Jin tsananin yunwa yasa ta tashi da nufin komawa gida amma ta kasa domin jiri ke dibarta, ganin lokacin sallah yayi ta tashi ta lallaba ta kamo hanyar gida. Dakyarta iso domin yunwa ya galabaitar da ita.
Tana bude kofa ta ganshi abude, alamar babu wadda ya fita bayanta. Dakyar take tafiya har ta iso kitchen, neman ruwan zafi tayi ta zuba a kofi ta zauna tukun ta soma sha domin hada shayi ma tana ganin wahalane.
Bayan ta sha ta kifa kanta tana fitar da numfashi a hankali. Takai kimanin mintuna takwas tukun ta tashi ta nufi hanyar daki.
Sam bata kula da mutum a falo ba domin duk tagalabaitu. Shiko Yusuf shiru yayi ko motsi ya kasa ya zuba mata ido. Duk yabi ya damu, domin ganinta bata da lafiya amma tsoron mata magana yake mata...
Tana shiga daki ta tarar da Raihana kan sallaya ta idar da sallah. Itama ban daki ta nufa domin dauro alwala tayi sallah.
Dakyar tayo alwalan jin kasan mararta na mata wani iri. Bayan ta idar ta tashi ta nemi magani tasha ta kwanta kan gado.
Raihana ta mata sannu tace ko zata kawo mata abinci? Aa ta amsa.
Shiru sukai na dan lokaci sannan Raihana tace pls Haneefah ki sauko daga fushin da kike, Allah ya amshi addu'ar ki Momy ta amince dake, hakurin ki da juriyarki ne yakai ki cimma wannan nasara, hakika duk wadda yakasance yana tare da hakuri to nasara na biye dashi dan haka saiki tashi kije ki gana da angon naki ku daidaita.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼56
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ganin Haneefah tayi shiru yasa ta kira sunanta, nan ma shiru. Tashiwa tayi taje domin ganin lafiya? Bacci ta tarar ya dauketa, murmushi Raihana tayi ta lullubeta da bargo.
Raihana taji wayarta na ringing, tana daukawa taga course mate nasu yace lafiya yau baku shigo ba? Raihana tace Haneefah fa ce bata ji dadi ba amma yanzu da sauki.
Yace dama yanzu akai kiran gaggawa na dalibai bangaren karatun mu, amma kada ki damu kizo innaji komai zan kiraki in sanar dake ta amsa da toh sukai sallama.
Shiko Yusuf kallon kofa yake ko zaiga Haneefah ta fito amma shiru bata fito ba, jin tsananin yunwa yasa yaje ya soma cin abinci da aka tanadar masa.
Dab da magriba Haneefah ta bude ido. Tashiwa tayi ta nufi bandaki ta wasa ruwa ajikinta sannan ta dauro alwala. Bayan ta idar da sallah ta zauna kan sallaya tana jiran magriba tareyin lazimi.
Bayan sun idar da sallah Raihana taje ta kawo musu abinci, ta tarar Haneefah tana karatun qur'ani a sirrince har lokacin isha'i yayi domin babu nisa, tashiwa tayi ta idar ta soma cin abinci domin yunwa take ji sosai. Raihana kallon tausayawa take mata domin yadda takecin abincin sai maijin yunwa sosai.
Haneeah tace ban hanaki cin abincin ba in zaki zo kici, Raihana tayi murmushi tace aa, ki gama ci saiki ragemin. Tana gama cin abinci wayar Dr Michael yashigo wayarta.
Da sauri ta daga tare da gaishe shi tace yanzu nake kan hanya sir. Yace takardar hutun ki da nace zamu baki zaki zo ki karba domin daren yau zanyi tafiya. Haneefah tace toh sir ganinan zuwa.
Tana gama wayar tayi tsallen murna tace Alhamdulillah, sis zanje karban takardan hutu na saina dawo.
Raihana tace bari in kaiki baki da lafiya. Zan iya tafiya kafin nazo kice da wannan bakon ya tattara yabar gidannan, tana kaiwa nan ta sauki makullin mota ta juya ta fice.
Zaune yake yayi shiru idanunsa nakan Tv amma hankalinsa baya kai tunani yake yadda zai bullowa wannan al'amarin. Yana tunani ya ganta ta fito cikin sauri.
Har taje kofa zata fice ta juya suka hada ido. Dam!! taji gabanta ya fadi da sauri ta kawar da idanun nata ta bude kofa ta fice.
Raihana ta fito taga harta fice Yusuf yace ina zata je bata da lafiya? Kiran gaggawa aka mata yanzu zata zo ba dadewa zatai ba, kafin tazo ka koma daki domin haryanzu bata sauko ba cewar Raihana.
Yace meke damunta? Shiru tayi, ya sake tambayar tace ciwon kai ta juya ta shiga ciki
Ji yake kamar ya bita, tashiwa yayi ya shiga daki jin kanshi na sarawa, kwanciya yayi amma ya kasa runsawa. Tabbas tana sonsa amma mesa take masa haka? Ko Raihana bata sanar mata komai bane? Ya Allah daga gareka muke kuma gareka zamu koma ya furta a hankali yana mai runtsa idanu jin tsananin sonta da yake fuzgarsa.
Tuki take amma hankalinta yana tare dashi, wani irin so nake maka? Maimakon son naka ya ragu kullum ninkuwa yake shin yaushe zan daina sonka? Duk sanda na ganka ina rasa mekemin dadi musamman inna tuno ammin iyaka dakai, ya Allah ka dubamin lamarina tsakanina da wannan bawan naka. Daidai tayi parking ta share hawayenta ta sauko.
Direct office din Dr Michael ta wuce. Turo kofar tayi tashiga, shi kadaine yake zaune waya makale a kunnen sa, zata juya ta fita ya mata nuni da hannu ta shigo sannan ya katse wayar yana mai cewa zai kira anjima.
Bayan ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a yace dama zanyi tafiyane shine nace bari in baki takardan domin rashin sanin ranar zuwana wata kila inzo kun fara exams. Ya mika mata farar takarda yana mai cewa in kuka gama exams da hutun wata biyu saiki koma bakin aikin ki, bayan kin komo kin zama senior staff sannan asibiti zata dauki nawin ki karatunki wato masters amma in kina da ra'ayin karatun a wannan shekarar in ko baki da ra'ayi sai zuwa next year.
Karbar takardan tayi tana murmushi tace nagode sir. Zata tashi yace kamar baki da lafiya? Tace eh amma da sauki.
Shiyasa baki samu fitowa aiki bako, meke damunki? Ciwon mara ta amsa a takaice.
Yace Haneefah yakamata kiyi aure, kamar yadda na sanar miki watannin baya, kada kikai stage dinda allurar dana baki bazai rike ciwon ba, muddin kikakai wannan stage zaki samu matsala a mahaifarki.
Kanta a sunkuye tace sir zanyi. A sanyaye ta mishi sallama zata fice yace ammm! Ina Yusuf ne? Yakamata ace yazo checkup saboda duba aikin da muka mishi.
Kamar bazatai magana ba saita tuna lafiyar sane za'a duba gomma Dr Michael yananan ayi komai. Komawa tayi ta zauna tace ya dawo in bazaka damu ba in kirashi yanzu ka duba shi? Yace babu matsala kirashi.
Karban wayansa tayi domin tabar nata a gida ta kira Raihana, tana dagawa tace kizo da bakon ki nanda mintuna kadan Dr Michael nason ganinshi dan zayyi tafiya tana kaiwa nan ta katse wayar.
Cikin minti ashirin suka iso. Ko kallon su bata yiba Dr ya mike yace bari muje dakin na'ura. A takaice kusan ita ta duba lafiyarsa. Duk motsin junansu akan idanunsu, ita Haneefah satar kallon shi take shiko baya boye kulawarsa gareta.
A haka suka bincike tas Dr yace yaranka nawa? Nan wani abu ya taso ya tokare wuyan Haneefah, amma da mamakin ta taji yace babu ko daya. Nan Dr Michael yace kada ka damu aikin mu yayi kyau. Daganan sukai sallama suka fice.
Raihana ce ke tuki gefenta Haneefah, bayan kuwa Yusuf ne ke zaune yayi shiru. Duk sai taji babu dadi abubuwan da take mishi amma ya ta iya, jugum suka iso.
Ta riga kowa shiga gida, gurin karatun su suka wuce shi kuma ya koma daki. Sun soma karatu kenan sukaji kira daga makaranta gobe su fito da shirin su karfe uku na rana zasu tafi Chicago sati daya zasuyi.
A wannan dare dukkaninsu sun kasa bacci, kowa tunani yake ga su a ruf daya amma ko gaisawa sun gagara, Haneefah zuciyarta ta kasa daurewa. Ta raya wannan daren tana mai ambaton Allah dakai kukanta gare shi.
Shima Yusuf ya mika lamarunsa ga mahaliccin sa yana mai nemar mafita agareshi. Raihana kam tana ganin ikon Allah amma tayi alkawarin zuwa gobe saita sanar da ita komai.
Bayan asuba Haneefah ta kwanta bacci. Sai kusan karfe goma ta tashi. Yau kam tajita jikin da sauki, tana tashiwa ta nufi banda ki tayi wanka ta fito. Bayan ta shirya tsaf ta fito neman abinci.
A falo ta tarar da Yusuf da Raihana suna hira, jin bell yasa ta nufi ko fa taga wayene. Tana budewa taga Dr Mubarak tsaye.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼59
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Take Dr ya gano cewa jininsa yayi mugun hawa, cikin kayansa ya dauki allaurar bacci yasa mishi domin ya samu hutu. Nan take Yusuf ya soma bacci.
Dr Abdullahi ya dubi Abba yace yana bukatar hutu, ku biyoni falo in muku bayani komai. Suna fitowa falo Nana taga Aisha.
Aisha ma taganta da sauri ta karaso tana kuka tace dan Allah aunty Nana kiyiwa Haneefah magana, kice ta amincewa Yaya Yusuf kingan shi wallahi yana cikin wani hali.
Kallo daya Nana ta musu taga damuwa tattare dasu, ta qara dubar Aisha cike da lallashi tace calm down sister! irin wannan damuwar da kuka shiga shi zai yadda sashi cikin wani matsalan, babu abinda zai same shi.
Dr Abdullahi yace ina so ku kwantar da hankalin ku, insha Allahu komai zai dawo mana da sauki game da abinda zan fada. Wato Yusuf jininsa yayi mugun hawa ta yadda zai samu illah amma kafin ma zamusan yadda zamuyi, nasan damuwarsa bazai wuce Haneefah bane yanzu hanyar nemo ta takasance dashi zamuyi domin muddin yaci gaba da damuwa a lokaci daya zuciyarsa zata iya bugawa domin tana tara damuwan ne.
Abba kasa magana yayi ya tashi ya fita, Aisha da Muhammad kam sai kuka babu bakin magana. Momy ce tayi karfin hali tace Abdullahi tayi aure fa! Yanzu ya zanyi da raina in Yusuf wani abin yasame shi, yau sabo dani gashi yana neman rasa ransa.
Nana tausayin wannan bayin Allah ya cika mata zuciya tace Haneefah batai aure ba, hasalima haryanzu tana son danki tamkar yadda yake sonta.
Momy tace ni da kaina naje har gidan yar uwarta tace dani tayi aure, shima ya tabbata da auren da tayi.
Nana tace ni yayarta ne uwa daya uba daya, yar'uwata batai aure ba, hasalima tana jiran izinin kine tsawon shekaru hudu.
Cike da mamaki Momy ta taso daga inda take tazo kusa da Nana tace Nimai laifice, nasan ban kyauta ba, saura wata biyu aure na janye maganar nasan family ku suna jin haushin abinda na aikata amma ina neman afuwa *YAR ADAM*, bansan soyayyar nasu mai karfi bace sannan bansan da ku nake tare ba, ZURI'A wadda annabinmu ya kwadaitar mana mu hada wadda zamu gina ingantaccen ZURI'A, dan Allah ina mai baki hakuri, kada ku hukunta Yusuf ni yakamata ku hukunta.
Nana ta dago idanunta da suka cika da hawaye tace idan kowa zai rama laifin da aka yi masa yaushe ne za a daina yin
laifi? Laifi kowa ana yi ma shi. Amma masu rauni su ke daukar fansa.
Masu karfi su suke yafewa. Masu
wayo sukan manta ne da an yi masu.
Bamu da irin wannan hali kuma bamu zamu koyo ba, ki kaddara Allah bai nufi auren su a wannan lokaci ba ko kuma in sukai akwai hadari cikinta, sannan shi aure lokaci ne, in Allah ya kaddara ko kina so ko bakya so dole ayi auren. Umman da Abba basa bamu he wadda bama so, dan haka babu abinda zai sami Yusuf zan kirata da kaina inji abinda ya faru da suka hadu a London.
Dr Abdullahi dake zaune yana murmushin jin dadi samu Nana matsayin mata domin ji yake kaf duniya babu wadda yakaishi dace, a zuciyarshi yace abokina dole ka damu domin gidan su Nana akwai tarbiyya, mace mai tarbiyya kuma duk namijin da yasameta tabbas yayi dace
Momy tace itama can take? Eh Abdullahi ya amsa, labatar musu abinda ya faru tsakaninsa da Yusuf yayi, Nana tasha mamaki haka ga Momy. Amma suna jiran farkawarsa domin suji abinda yafaru.
A wannan rana gidan yazamo tamkar zaman makoki ake, salmace kadai take gidanta batasan wainar da ake toyawa ba, Abba ko yayi fishi bayayiwa kowa magana. Sai dab da sallah isha'i yafarka domin harsu Nana sun shiga mota zasu tafi suka ga Muhammad na tsayar dasu yana cewa ya bude ido.
Dukkansu suka dunguma zuwa dakin shi. Tashiwa yayi ya dafe kansa da hannuwan sa yana tuno abinda ya faru dashi.
Da sauri Abdullahi yazo ya rike shi yana mai cewa relax kada kuma ka tuno komai ya wuce.
Dago dakai yayi yana kallon abokin nasa da mamaki yana tambayar kansa yaushe yazo? Kallon daya bayan daya yakewa jama'ar dake dakin karaf idanunsa yakai kan Nana.
Ganin yadda yake kallon tane yaji hawaye na neman zubo masa yace Nana Haneefah taki saurarona ta amince da DOCTOR! Ya qarashi maganan cikin sarkewar murya.
Da mamaki take kallonsa tace Dr Mubarak? Yace eh shi, ya share hawayensa yaci gaba da magana nasan nayi rashin Haneefah domin bazan aikata haramci ba wato neman aure kan neman aure, xan kasance mai hakuri tare da fidda rai akanta.
Shiru kowa yayi tamkar ruwa ya cinyesu. Dr Abdullahi yace ba komai, yanzu dai rashin damuwarka muke bukata bacci sosai yakamata kayi kafin mu nemi mafita.
Momy da Aisha sun kasa magana sai ido. Sai da suka tabbatar da hankalinsa yadan kwanta tukun sukai musu sallama akan gobe zasu zo. Bayan fitarsu ya tashi yayi sallah yana mai addu'ar Allah tabbatar masa da alkhairi rayuwarsa. Abba ma ya shigo yayi masa nasihan bai kamata ya rika sa abu a ranshi harya dame shi sosai ba. Nuna musu yayi insha Allahu zai rage.
Kusan goma suka fice Momy tamkar kada ta barshi shi daya. Shiru yayi yana kallon sallaya dake zaune akai, tabbas saboda damuwarshi bai kamata ya daga musu hankaliba amma shi baisan