Showing 18001 words to 21000 words out of 74305 words
Chapter 7 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
ta fita ta nufi sashin su... a daki ta tarar tana waya kan ta gama rusa maganar auren yusuf.
Ba shiri aisha ta koma daki ta zauna bakin gado. Wannan wani irin son kai momy take son aiwatar wa?? In aka rusa maganar auren yayanta shinya zai kasance? Tabbas tasan yadda yake son haneefah ! Tunani ta tsaya yi ta yadda zata nemi mafita. Inta sanar da yusuf hankalinsa zai dada tashi, bata isa ta tunkari momy ba domin yadda itama ta dau zafi, mafita shine Addua. Ta daga hannu sama tana rokon Allah ya duba musu wannan lamari.
Yadda aka tarbesu sunji dadi sannan abba yabada haneefah ga yusuf, an bada sadaki ranar aure kuma wata biyar aka sa, dai-dai da gama maarantar ta da wata biyu kenan.
Labari yaje kunnen masoya. Babu wadda yakai yusuf murna a wannan rana . Tun daga wannan rana ya fara irga ranar auren shi.
Su inna bakin ciki sun rasa inda zasu shiga ganin yaron daga gidan masu hali yake. Abba da umma an fara shiri ba kamar umma ba, yadda take ji da haneefah.
Haka sauran yan uwa dukkaninsu suna murna tare da Allah nuna musu wannan rana.
***** ****** *****
_BAYAN WATA BIYU_
Haneefah jinta take complete. Komai yazo mata dai-dai. Babban burinta takasance ta kammala karatu tana tare da abar kaunarta.
Haka abin yake ga yusuf. Yana bawa rahma kulawa.
Zaune take ta baje takardu tana hira. Taji wayarta na ringing taga matar Dr Mubarak na kiranta tace nashiga uku nidai bani da kirki. Ta daga cike da kunya tace dan Allah kiyi hakuri kullum inason kiranki Allah bai bani iko ba. Barrister ramlat tace ba komai haneefah kina lafiya? Lafiya lau, ya Dr da yara? Duk suna lafiya.
Barrister tace dama nakira in sanar dake na haihu gobe suna amma dan Allah wannan karon kizo gidana.
Haneefah tace Allah raya bisa tsarin addinin musulunci, zanyi kokori insha Allah inzo, yauwa haneefah nagode yanzu zan tura miki address din gidan nawa. Haneefah taje ta gayawa umma tace Allah kaimu goben sai kije .
Washe gari haneefah ta tashi da matsanancin faduwar gaba, so biyu wannan abin ke faruwa mata. Na farko haduwarta da yusuf sai yanzu na biyu. Ko wanni abu zai faru Allahu a'alam.
Suna waya da yusuf amma kwata-kwata jinta yake wani iri yace dearie lafiya? Haneefah ta bashi labarin abinda ke damunta. Shima yace abinda yake fama dashi. Cike da mamaki tace Allah sa da mu da alkhairi.
Yanzu kina ina? Yusuf ya tambaya. Zanje anguwane. Ya dubi agogon hannun sa yace turomin address din gidan da zaki.
Haneefah tace meza kai? Yace kedai turomin. Ta katse wayar ta tura masa. Yusuf dake aiki ya tattara kayan shi ya nufi gida. Bayan yagama shiri ya dauki mukullin mota ya dauki hanyar kano.
Misalin karfe daya da rabi haneefah ta sauka bakin gate da ta tabbata shine gidan. Ta sallami mai a daidaita sahu ta tsaya tun daga bakin gate tana karewa gidan kallo tace mashaa Allah . Ta kira barrister tace ta iso. Duk da jama'an dake gidan hakan baisa ta fito ta dauki haneefah ba. A tare suka shigo ta zaunar da haneefah ta mika mata baby. Barister ta shigo da wata mata ta nuna mata haneefah. Suka karaso wannan mahaifiyata ce cewar barrister . Cike da ladabi haneefah ta gaisheta. Bayan sun gaisa tagabatar mata da sauran yan uwanta. Matuka haneefah taji dadin karrawa da sukai mata.
Bayan awa biyu haneefah ta tashi tace zata tafi. Godiya suka mata har bakin gate suka rakata. Tana fita zata tari abin hawa taga motar yusuf. Cike da mamaki ta qarasa ta bude tashiga tace dama kana garine?
Tun fitowarta ya kafa mata, tayi kyau sosai. Yace yanzu zuwana. Ya tada mota suka soma tafiya. Ganin ya dau hanyar gida tace zan biya gidan hadiza in amshi sako, ya nufi inda ta fada masa.
Tuki yake ko magana bai mata ba har suka iso gidan yayi parking. Ta lura da fuskarsa a daure shiyasa ko magana batayi masa ba. Zata fita ya kulle motar. Ta juyo suka hada ido ganin idanunsa sun kada sunyi ja ga hawaye da ke kokarin taruwa a idonsa.
Yace dearie bana jin dadin zuciya ta bansan meyake son faruwa dani ba. Kwarai ya bata tausayi yadda yake magana. Ta danne nata abinda take ji a zuciya tace babu abinda zai faru sai alkhairi, ka kwantar da hankalin ka. Babu abinda zai faru.
Ciro wayarsa yayi yace kiyi hakuri abinda zan miki. Bata ce komai ba ya jawota kusa dashi kansu a hade ya dauke su a hoto kusan kala uku sannan ya dauketa ita daya. Karban wayan ta yayi ya tura mata hotunan da sukai da nashi shi daya.
Abubuwan da yakene yasa ta fara zubar da hawaye. Ganin haka yasa yace pls dear kidaina haka kawai yau najini wani irine. Mika mata wayar yayi yace next year war haka kina dauke da babyn mu.... wayar ta amsa zata fita tace ni kabudemin kofa cikin shagwaba. Ya koikoyeta tasa dariya tace baka iya bama. Haka har suka mantar da junansu abinda suke ji yayi mata sallama kan anjima da dare zai dawo.
Tana shiga gate din harta iso bakin falo zata shiga taji an bude ko fa. Wadda taganine yasa bugun zuciyarta ya tsananta wato mahaifiyar yusuf.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼21
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Tsananin fargaba da tsoro ya hana haneefah ko da taku daya. Ganin ta tabbatar momy ce ta sunkuyar da kanta kasa.
Har kasa haneefah ta durkusa gaida momy, da fara'a ta amsa tare da cewa inason magana dake.
Nan da nan zuciyar haneefah ke bugawa da sauri. Ta musu jagora zuwa ciki. Babu kowa a falon kuma tayi mamakin ganin falo a bude.
Guri momy ta samu ta zauna, sannan ta karewa haneefah kallo. Yarinya qarama amma tana son birkita rayuwar familinta. Momy ta fara magana da cewa nasan kin sanni, ko da a hoto ne yusuf zai nuna ma ki ni amma niko bansan ki ba saida kika so raba kan dana sannan na nemi sanin wanene ke. Yanzu zuwan shi amma ko matarsa baije ya gani ba yazo inda kike. Toh inaso ki bude kunnen ki kiji abinda zance miki. Ina so kimin alkawarin abubuwa biyu: na farko ki janye aurenki da yusuf, na biyu ki fita arayuwarsa ma'ana ki yi nesa dashi inko ba haka ba zan tsine mishi, kinga ko bazai amfane ni ba nima bazai amfane niba... amma in kikamin alkawarorinnan biyu to tabbas masoyinki zai kasance cikin albarkana har tsawon rayuwarshi.
Hadiza dake bacci taji alamun mutane ta tashi ta nufi falo. Abinda kunnuwanta suka jiye mata ne yasa ta qaraso da sauri ta durkusa gaban momy tace Dan Allah mama kiyi hakuri, wlh suna son juna. Haneefah tana da kirki bazata cutar miki zuria ba. Kada kira ba soyayyar da Allah ya hada.
Momy ta miki tace nidai nagama magana, muddin tana so masoyinta ya gama da duniya lafiya toh tayi abinda nace tana kaiwa nan tayi ficewarta.
Haneefah tunanin tane ya tsaya, ta nemi koda yawu abakinta ta rasa. Ta rasa tunanin me zata yi. Murya a dashe ta cewa hadiza ki tasheni a mafarkin da nake. Hadiza dake kuka ta qaraso gurinta ta rungumeta tace haneefah dan Allah na rokeki da girman Allah kada ki tada hankalin ki, ki dauka a matsayin kaddara ne ... bata qarasa ba taji wayar haneefah na ringing.
Haneefah ce ta daga wayar tana kallon mai kiran. Tace yusuf ne hadiza a sannan ta tuno da kalamun momy. A tayi rejecting kiran, ya qara kira. A sannan haneefah ta fashe da matsanancin kuka.
Kuka take kamar ranta zai fita. Hadiza na tayata. Kimanin mintuna arba'in suka dauka haka. Nan take haneefah ta tuno da nasihar yusuf:
A matsayinka na musulmi, a koda yaushe, ka shiryawa zuwan kaddara da zata iya samunka, mai kyau ko marar kyau, ta alkhairi ko ta sharri. Idan ta alkhairi ta same ka, sai kayi godiya ga Allah, idan kuma ta sharri ce ta same ka, to sai kayi hakuri. wannan shi ne mataki, kuma matsayi na zama cikakken mumini.
Sannan godiyarka da hakurinka akan nau'ikan kaddarori biyu da suka same ka, suke nuna cewa dukkanin al'amuranka alkhairi ne. Babu wanda ke samun wannan matsayin a cikin Musulmai sai Mumini.
Wannan shi ne ma'anar fadin Annabi s.a.w.
"Abin mamaki, abin sha'awa ga al'amarin mumini, hakika dukkanin al'amarin sa alkhairi ne, babu wanda ke samun haka sai mumini; idan abin farin ciki (alkhairi) ya same shi, sai yayi godiya (ga Allah), sai hakan ya zama alkhairi a gare shi, idan kuma abin bakin ciki (sharri) ya same shi, sai yayi hakuri, sai hakan ya zama alkhairi a gare shi ". Imamu muslim ne ya rawaito.
Ya Allah kasa mu sifantu da wadannan sifofi na mumini. Allah kasa mu zama muminai.
Haneefah ta qara fashewa da kuka tana mai ambaton Allah.
Momy ko tana isowa gida ta nufi sashin su yusuf. Kwance ta same shi a falo yana tunanin meye dalilin rashin daga wayarsa da haneefah tayi. Ganin momy yasa ya tashi ya zauna.
Bata amsa gaisuwar shiba tace inaso kaban aron hankalin ka. Da farko inaso ka janye maganar auren ka. Ba shiri yusuf ya dago kai
Momy taci gaba inaso ka fidda yarinyar nan a rayuwar ka da duk wata mace domin rahma har abada itace taka. Abu na karshe inaso ka samu mahaifin ka adarannan kace gobe ya sanar dasu ka fasa. Umarni na baka in ko kaki, Allah ya isa tsakanina dakai ka nemi wata uwar ba ni ba.
Yusuf idon shi ya kada yayi ja. Kallo daya zaka mishi kaga tsananin tashin hankali a tare dashi. Maganar ummansa ya tuno. Inbai rabu da haneefah ba zata tsine mishi? Inta tayi hakan meye amfanina a duniya? babu ya bawa kanshi amsa. Tashi yayi ya shige daki ya kulle da makulli sannan ya kwanta kan gado. Tashi ya kuma yi ya dafe kansa dake mugun sarawa. Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuun ya soma furtawa a hankali ya soma hawaye.
Yana bude baki yace Alhamdulillah! Tashi tsaye yafara kai koma. Ya sake zama bakin gado ya dauki wayarsa yashiga hotuna yafara kallonta. Take tun haduwarsu har zuwa rabuwansu abin yake zuwa mishi.
Zuciyarsa yaji yana tafasa daganan zuciyarsa ta kare ya fashe da matsanancin kuka. Kuka yake yana ambato Allah har aka kira sallah la'asar. Tashi yayi yashiga yayi wanka sannan yayi alwala ya fito. A daki yayi sallah. Sujjadarsa yake sanar da mahaliccinsa halin da yake. Bayan ya idar ya dauki qur'ani yafara karantawa. Har aka kira sallah magriba. Sallah ne ya tada shi. Bayan ya idar ya sake ci gaba da karatunsa domin baisan abinda zayyi da yafi haka ba.
Ita ko haneefah tunanin mahaifanta dayan uwanta take, muddin suka ganta cikin wannan hali hankalinsu zai tashi, ita ko batason hakan ta faru.
Bayan ta idarda da sallah tana zaune tana sharar hawaye hadiza tazo kusa da ita tace haneefah kiyi hakuri, babu abinda zamuyi da yafi haka.
Murmushin karfin hali tayi tace bani da mafita daya wuce haka. Amma inason kisan ina matukar bukatar addu'a. A hankali tace momy zanbi umarnin ki, nayi alkawarin barin rayuwar yaronki har abada.
Ta mike ta tattara kayanta tayiwa hadiza sallama kan sai sun hadu gobe.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼23
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ganin haka yasa matafiya suka tsaya ganin hatsarin da ya auku. Ganin yadda motar yusuf ya zamto babu kyan gani babu wadda yayi
tsammanin akwai mai rai ciki. Dakyar suka samu suka ciro shi. Suna cireshi motar ta kama da wuta.
Ganin jini kota ina zuba yake yasa wani bawan Allah yace ataimaka asashi motarshi zuwa asibiti domin tabbatar da yana da rai ko ya mace.
Gari mafi kusa suka nufeshi wato kaduna. Emergency akashigar dashi. Bayan anyi bincike aka gano yana da rai amma yana bukatar jini sosai, ko neman wadda yakawo shi basuyi ba suka sa masa jini domin ceto ransa. Bayan likita ya fito ya nufi gun mutumin da ya kawo sa yace yabisa office.
Likita ya kalleshi yace wadda ka kawo yana cikin hadari sosai domin mun kasa binciken meya same shi sai mun qara masa jini. Yanzu dai ga kudin jinin ka biya nanda awa daya zamu soma binciken inda yaji ciwo sosai.
Mutumin ya numfasa yace Alhamdulillah yana da rai, amma likita accident ne, niba kowansa bane. Likita yace baku samu wayarsa ko wasu abubuwan da za'a samu cikekken bayani akan saba? Aa likita motar ma kamawa tayi da wuta, zan biya dukkanin abinda kuke bukata har Allah sa ya farfado ya sanar da mu daga inda yake.
Likita ya numfasa yace zamuyi iya kokarin mu, kaima Allah biyaka abinda kayi. Sukayi sallama ya fice domin biyan kudin jini.
****
Haneefah ta samu guri ta zauna can nesa da inda za'a ganta. Tana zama taji gabanta yayi mugun faduwa, nan take yusuf yafado mata arai. Tunani take ta fitar dashi aranta kwata-kwata ta daina tunaninsa, a hankali tace bazan iyaba. Nan da nan taji wani irin daci a zuciyarta, yanayine wadda bazata iya fassara yadda ta tsinci kanta ba. Ta dago ido tana kallon inda take, nan take taji garin kano ya fice mata arai. Tsintar kanta tayi tana cewa ya Allah kabani ikon barin garinna, nayi nesa da shi. Hawaye take sosai
Hadiza ne ta tsaya nesa da ita tana kallon aminiyarta, kwarai ta matukar tausaya mata domin tasan yadda take son yusuf amma babu abinda zatai daya huce hakuri. Hawayen da ke zubo mata ta share tare da nufo inda haneefah take.
A hankali ta dafe kafadarta tace inata nemanki ashe kinanan. Haneefah waigo a hankali suka hada ido da aminiyarta. Murmushi ta sakar mata tace inanan ina zaune, nasan zaki zo. Hadiza ta share hawayen haneefah tace nasan dole abin yadame ki amma haneefah ki kwantar da hankalin ki kiyi addu'a, addu'a ba ta faduwa kasa. Ko a baka yau, ko a baka gobe, ko kuma a baka abin da ya fi wanda ka roka, addu'a makamin mumini ce 'yar-uwa... Don haka muyi riqo da Addu'a kuma mu dogara da Allah ko yaushe.
Haneefah tace insha Allahu zanyi amma ba lallaine in manta abin cikin sauki ba. Hadiza tace nasani, exam namu fa sati mai zuwa ki kwantar da hankalin ki kiyi karatu. Allah zai kawo miki wadda ya fishi.
Haneefah ta tsaya kallon kawarta tace wadda ya fishi?? Zamanin yanzu kina tunanin zan samu kamar yusuf, mai hankali da nutsuwa, wadda zai so ni tsakani da Allah sannan ya kula dani? Wadda zai kasance kullum zai sakani farin ciki haba hadiza ya kike tunanin zan samu wadda zai maye gurbin yusuf, nidai nasan nayi rashi, bansan mesa momy bata so na ba, bansan mesa ta rabani da danta ba... bana jin zan ji sha'awar tarayya da wani matsayin miji.
Hadiza dake yi mata kallo tausayi tace nasan radaine yasa kike fadin haka, amma duk da haka kada kibari yazamo wannan tunani ya dauwama cikin zuciyarki. Shin kinyi tunanin haduwa da yusuf ne? Ba shirin ki bane sannan ba shirin yusuf bane, momy ba itace ta rabaku ba Allah daya hadaku shi ya rabaku , hakan na nufin akwai boyeyyen sirri cikin lamarin, ki dage da addu'a insha Allah komai zaizo ya wuce. Kuma ai agun Allah kike tsammanin abu ba gurin dan adam ba.
Haneefah tayi tana nazarin maganganun kawarta tace hakane, amma wlh inason barin gari. Hadiza tace ina zaki? Duk inda Allah ya kaini amma nidai banason ci gaba da zama anan. Hadiza tace to ko zakiyi applying scholarship?
Haneefah ta kalleta tace agarinnan wa nasani dazai shigemin gaba duk yaran manya ne. Duk da haka haneefah ki jarraba in Allah yayi da rabonki sai ki ga an dace. Haneefah tayi shiru tana jin kawarta. Daga ido tayi taga hadiza tana hawaye haneefah tashiga share mata tace yi hakuri mana, kukan ya isa aini na hakura.
Hadiza tace toh dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Murmushi ta mata suka tashi suka nufi inda ake tutorial. Yinin wannan rana haneefah babu abinda take fahimta, bata ci komai ba haka ta koma gida.
Abba kasa yiwa haneefah magana yayi lokacin da taje gaida shi. Domin yarinyar ta soma bashi tausayi.
Umma ce ta sanar da ita zuwan abban yusuf, anan ta tabbatar cewa ta rabu da yusuf. Tunanin inda zata je ta fara domin batajin zata rayu a inda zata rika jin motsin yusuf, gashi babu wadda tasani a garuruwan Nigeria sai auwal dake abuja, bazata soma tafiya ba saboda inda yusuf ke zama ne. Nan ta tuno da shawarar hadiza kan tayi applying scholarship.
Haneefah ta canza, ba kamar itama ba, ta rage yawan dariya, batacin abinci sosai, bata iya karatu kullum tana daki, ko asameta tana karatu kota lumshe ido tana addu'a. Duk wadda yaji labarin abinda ya faru saiya tausaya mata.
Itadai jarabawa tayi amma batajin zata wuce. Cikin sati biyu ta rame, maganar tama ya canza. Ya zamto babu ruwanta da kowa da komai.
Zaune take gaban abbanta tana sauraronshi. Yace haneefah meke damunki? Mesa bazaki sake ranki ba? Fadamin duk abinda kikeso muddin baifi karfina ba zan miki.
Kanta sunkuye tace abba inason inyi applying scholarship ne, ina neman izininka, nayi maka alkawarin tsare mutuncina ka yarda dani abba.
Cike da tausayi abba yace na yarda dake haneefah sai dai banyi tsammanin zaki samu ba amma duk da haka kije bazan hanaki ba. Allah sa hakan shi yafi alkhairi.
Tace toh abba nagode. Taje ta sanar da umma yadda sukai da abba. Fatan alkhairi tayi mata sannan ta hada mata qualifications nata ta shirya ta tafi ministry of health. Inda ta tabbata nan ake karban takardun.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼22
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Haneefah tana shiga gida bata tsaya ko inaba sai gun ummanta. Zaune ta sameta kan sallaya tana lazimi. Ganin haneefah cikin irin yanayinnan yasata yin fatiha. Umma cike da kulawa tace meya faru haneefah?
Haneefah tayi murmushi tace umma ki kwantar da hankalinki, kamar yadda nazo da karfin gwiwa ki saurareni. Sanin kankine cewa banason abinda zai tabamin ke harta kaiga yana damunki,