Showing 39001 words to 42000 words out of 74305 words
Chapter 14 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
murmushin jin dadi tace Ameen, insha Allah zanyi yadda kikace Umma, hakikanin gaskiya inka bude ido aduniyar nan ka fahimci kana tare da uwa tagari toh tabbas kayi dace domin duniyar kama dabanne. Murmushi Umma tayi ta fice a dakin.
Karfe tara suka farka daga bacci. Sunje sun gaida Umma suka wuce gaida Abba. Raihana ta sake jiki suna ta hira da Abba, tana yaba yadda tarbiyyan Haneefah take da yadda suke zaman su lafiya.
Karfe sha daya suka gama breakfast a sannan Nana ta soma kiran aunties na su. Kan kace meye kafin azahar gida ya cike. Mama da yaranta baki daya suka zo, bakin su yaki rufuwa tsaban farin cikin hasken family su, sunji dadin yadda ta kwantar da hankalinta tayi karatu harta canza.
Bayan anyi sallah ne Ahmad yashigo da yaron Mama wadda suke sa'a dashi wato Khalifah, suna shiri sosai nan suka soma tsokanar juna yace zaki tashi ki kawo mana balarabiya dan kinsan bamu da kudin auranta ko? Dariya tayi tace ni da naji labari ka samu aiki shekaran ka daya aika tara kudi, nan suka soma hira tace akwai kayanta a airport in suka samu lokaci sune su dauko mata.
Aunty Muhibbat ce zaune kusa da ita ta kama hannuwan ta suna hira suka ji sallamar Hadiza aiko tsalle Haneefah tayi suka rungumi juna suna murna. Bayan ta sake tane ta ganta da ciki tace shine baki gayamin ba inje in jefar dake? Ina ummulkhairi bata gama rufe baki ba ta ganta a hannun Sadiya.
Da sauri ta karbeta tana dariya. Suka shiga ciki. Farin cikin Haneefah baya misaltuwa domin ji take daban take a yau. Raihana kam zuba mata idanu tayi tana Murmushi azuciyarta tana saka dama haka take? Haneefah ta gabatar da Raihana gun kowa, sunyi farin ciki kuma yadda suka karbeta abin yayiwa Raihana dadi sosai. Suna cikin hira suka ji sallamar Inna a falo ita da sauran yaranta.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼39
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ganin zata fadi ne a hankali ta nemi guri ta zauna ta dafe kai. A wannan hali Dr Michael yazo ya sameta yace Haneefah? Da sauri ta dago kai tana kallon sa idanunta sunyi ja domin zubar da hawayen ma ta kasa.
Ganin yana son saka hannu ya dagota ta tashi da sauri tana gaishe shi. Bai amsa ba yace meke damunki lafiya?
Haneefah tace lafiya kaina kemin ciwo yanzu nake son komawa gida. Yace kije ki huta saikin samu sauki ki fito ki daina wasa da lafiyarki.
Murmushi tayi zata wuce yace nima yanzu zanyi tafiya zuwa Canada sai bayan wata daya zanzo.
Da sauri tace sir inaso in halarci daurin auren yar'uwarta, inason tafiya nan da sati biyu amin izini. Michael yace yaushe zaki zo? Wata daya zanyi ta bashi amsa.
Yace ok ba komai, zan aika miki sako ta account, saiki soma shiri amma kada ki wuce lokacin da kika dauka. Tayi masa godiya zata wuce office ta juya kallon mutanen da tayi niyar musu magana amma bata gansu ba, wucewarta tayi office.
Kuka ta zauna yi, ba komai take gani ba sai Yusuf rike da jariri yana dariya. Lallai ina da kishi! Toh ina ruwana da dansa? Dafe kai tayi tana hawaye. Yusuf yaushe zaka zo ka aureni? Ka manta da ni ne? Yusuf ina sonka? Momy bazan iya hakuri da danki ba ina son shi? Surutai take taji an turo kofa an shigo.
Da sauri suka iso gareta suna tambayarta lafiya? Mesa kike kuka? Rohan da duk yafisu tashin hankali yace kiyi magana Haneefah meya faru?
Cikin kuka tace nashiga uku, bansan wace irin rayuwa bane wannan, a lokaci da dama ina tuhumar kaina bana daya daga cikin bayin Allah wadda suka yarda da kaddara, yaushe zan daina son sa? Nayi tunanin barin kasarmu kozan manta dashi amma banyi ba, yau gashi shekara daya yarage na koma amma ko kadan ban daina ko jin daina son shi ba. Ta tashi ta kamo hannun Raihana tana cewa ki fadamin mezanyi na daina sonshi, wallahi ji nake kamar zan mutu yanzu dana ga shida dan sa, ku bincikeni saboda shi wata kila na kamu da hawan jini... na gaza cire shi a raina, ina tsoron Allah kada yayi fishi akan yarda da kaddaran da banyi ba....
Da sauri Raihana ta toshe mata baki tana girgiza mata kai cike da tausayi. Haneefah taje kusa da Rohan tace nasan kana so na, amma ba zayyu in taba son wani ba. Ta kuma matsowa gun Kevin tace ka fahimtar da abokin ka, banajin wani zai mori dadin zama dani matsayin mata sai dai in mishi biyayya yadda Allah ya umarceni amma bazan iya son shi ba, ya daina damuna kan soyayar shi wallahi bazan iya son Rohan ba Yusuf nake so, shekara hudu ina rainon soyayyar shi auren mu saura wata biyu aka janye amma ina da tabbacin zaizo gareni domin ina son shi....
Cike da tsananin tausayi Raihana taje ta rungumi Haneefah tana tausaya mata yadda take surutu akan so, tace yi shiru sis Yusuf zaizo gare ki, dan kinga yaronsa ba yana nufin ya manta dake bane, kamar yadda kema baki manta dashi ba, biyayya yake kamar yadda kema kike tayasa yi, kada ki manta kullum cewa kike faranta ran iya da yi musu biyayya na daga cikin sirrin zaman jin dadi a rayuwa.
Sannan ki daina ambato da kanki cewa kina da karancin hakuri, yarda da cewa Allah yana jinki kuma yana ganin halin da kike ciki shine ya kaiki ga matakinnan, da baki da hakuri kullum sai kin rinka jituwa da Yusuf amma kin daure ko waya baki taba yi masa ba, dan haka ki kwantar da hankalin ki, kici gaba da addu'a Allah zai kawo mafi alkhairi a rayuwarki.
Sannan Rohan ka daina damun Haneefah da soyayar ka, a irin halin da take ciki bai kamata ka dauko da maganar kaba, karatune ya hadamu toh muyishi, kabar maganan nan da wata uku mun rabu toh dan Allah muyi rabuwar arziki.
Tana kaiwa nan taja hannun Haneefah suka fice daga office. Dakyar Raihana ta shawo kan Haneefah harta dawo normal. A zuciyarta tace ka hadu da mutanen da basason damuwar ka ma ka godewa Allah, musamman mutanen da ke zagaye dakai, Alhamdulillah tace.
Da yamma suka koma gida. Bayan sun huta taga alert a wayarta kimanin miliyan daya, mamaki ne ya bayyana a fuskarta. Da gudu ta shiga daki nunawa Raihana.
Tana karba ta gani tace sunan Michael nagani, Haneefah ta zaro ido tace nashiga uku me mutuminnan yake so ya mayar da ita? Nan ta kwashe komai ta sanarwa Raihana.
Murmushi Raihana tayi tace take-takensa kada ki rabu da asibitinshi, kada ki manta turawa bazasu taba mu'amala da musulunci dan Allah ba suna so su kwadaitar dake kudin sune amma Allah ya fisu, kada ki kuskura cewa zaki bar asibitin da zarar kin gama amma kina gamawa ki gudu garin ku domin sunga kina da kwakwalwa zasu iya amfani dake.
Haneefah tace Allah ya tsare. Raihana tace ina neman wata alfarma in zakimin? Ina jinki zan miki da yardan Allah. Raihana tace zan biki Nigeria amma kafin ina so mu tsaya Dubai kwana hudu zamuyi sai mu wuce.
Haneefah tace na yarda domin ke kin wuce haka a gurina, sai dai zamu bar kasannan dawuri. Raihana tace muje makaranta muyi report sai mu soma shiri. Lokacin da tasan zata samu Nana takirata take sanar da ita tafiyarta amma kada ta sanar gida sannan tana da isheshen kudi kada su saya komai su jira zuwanta.
Haka ko akai cikin satin sukai shiri tsaf da kwana biyar suka daga zuwa Dubai. A gidan kanwar maman Raihana suka sauka, sun samu kyakykyawar tarba. Raihana tace be komai nazo yiba siyayyan Habaya na zo saya, nasan baki taba zuwa Dubai ba zo mufita yawo. Tun adaren suka fito kallon gari, Haneefah taga Dubai sai santin shi take.
Washe garima suka fita. Saida suka koma gida Haneefah take sanar da Raihana tana bukatar funitures da kayan kitchen. A daren suka je suka nemo masu kyau tare da foodflask masu kyau. Haneefah tayi tsaraba ga yan uwanta sannan ta kashe kudi wajen siyan kayan dakin yar uwarta. Itama tayiwa kanta siyayya. Taji dadin zamanta a Dubai sannan tayi sha'awar kara zuwa in Allah ya nufa.
A kwana hudu suka dauki hanyar Nigeria. _Shin ko wace irin al'amari zai wakana a komawar HANEEFAH_?
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼41
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Da sallama suka shigo dakin, dukkanin su murmushi a fuskokinsu amma banda Inna da Zuwaira. Bulkisu, Zainab da ibrahim suka soma gaishe da Haneefah tare da yi musu ya gajiyar da karatu? Haneefah ta amsa da Alhamdulillah.
Dakin yayi shiru, su Aunty Muhibbat anyi shiru ne saboda basason bakaken magana domin yawanci in suka hadu koda da mutunci suka gaisa sai zuwaira da maida musu bakar magana hakan yasa suma suka daina shiga tsabgarsu.
Haneefah ta katse shirun da cewa Ibrahim ya makaranta? Kodai kaima kamar Ahmad zaka bautar kasa ne? Yace Eh amma inaga sai nanda wata biyu. Haneefah tace Allah taimaka.
Hira ake jefi jefi harna tsawon mintuna goma sha biyar daganan suka sallama.
Isarsu gida Zuwaira ta zauna bakin gado tana cije labe. Ibrahim daya lura da ita yace gwamma kin saukar da kanki kun zauna lafiya kamar yadda Zainab da Bilkisu, me kuke nema a duniya da zaku qarar da rayuwarku da hassada? Umma ita tayi hanyar nemamin makaranta kuma take son nayi karatu amma ko dan haka bazaki saukar da kaiba, yaranta daikam sun fiki nesa ba kusa ba, da ilmi da tarbiyya.
Bilkisu ta amsa da cewa hakane maganarka Ibrahim, in bata gyara ba duniya zata gyara domin ko Inna da su yaya Salim sun sauko.
Zuwaira ta numfasa tace tabbas naga asaran kishi domin ya rikidu ya koma hassada, wani kishin ma mugunta ne domin biyewa shaidan ake ya rinka bamu umarninsa da zai kaimu ga halaka, tunda muka taso bamu taba jiyarda kannen mu dadi ba wai mu muna *YAN UBA* da su amma banga laifin muba saina Inna.
Inna dake zaune tana jinsu tace nidai? Zuwaira tace eh, domin da kina tsawatar mana da bamu taso da hakan ba, ku duba Nana itace babba amma duk muzgunawan da muke musu bata taba yunkurin ramawa ba sai Haneefah, itama Umma na dakatar da ita. Kinga ko da kina dakatar damu da duk haka bata faru ba.
Cike da nadama Inna tace shikenan ayya wuce. Nan suka soma tattaunawa yadda zasu fara kyautatawa Umma. Amal da shukra da suke tsaye bakin koma sukai murmushin jin dadi tare da godewa Allah.
Haneefah tace da Hadiza ummulkhairi bata qin jama'a, dubi yadda muke da ita amma batai yunkurin zuwa inda kike ba?Hadiza tace haka take babu ruwanta. Haneefah ta bukaci zata rika kawo ta in zata fita aiki.
Hadiza tace shikenan zamu rika sayawa mu ajeta, inna tashi sai inzo in dauketa.
Da yamma kaya ya iso. Sai da dare ta bude ta'ajewa kowa tsarabar sa. Ahamd da ibarahim tsadadden waya suka samu. Sanda Haneefah ta gabatar da kayan dakin Nana babu wadda bayyi mamaki ba. Umma tace aina kika samo kudinnan?
Haneefah tace asibitin da nake aiki ne na sanar shine suka bani yin tsaya ba, da muka tsaya Dubai shine na sayo domin babu tsada acan. Salary da nake samuwa ne nayo tsaraba dashi.
Nana ta shiga hawayen farin ciki da tsananin kaunar kanwarta, tashiwa tayi ta rungumeta tana cewa bani da bakin yi miki godiya sai dai ince Allah albarkaci zuri'armu ya hada kawunansu.
Haneefah tayi murmushi tace duk abinda na samu naki ne da kannena saboda haka ki daina yimin godiya domin dukkanin abinda na mallaka naki ne.
Umma farin ciki take sosai domin kullum addu'arta Allah hada kawunan yaranta. A hankali tace Haneefah naji dadin furucin ki, Allah yayi muku albarka. Suka amsa da ameen.
Abba shima ya nuna farin cikin sa musamman yadda bata banbanta yaran Inna ba tayo musu tsaraba sannan ya kara da cewa ku dage da addu'an samun aiki mai albarka.
Bayan sun koma daki Nana tace yanzu saura kujeru da sauran decorations na falo, ina da tabbacin komai zai isa da kudin sadaki da sauran kudin Abba domin kinsan yanzu ba aiki yake ba, in kuka huta ko cikin satinnan sai muje kizabamin sannan mu siyo anko.
Washe gari kamar jiya yan uwa suka zo gaida Haneefah. Sun wuni suna hira sannan suka soma tsara yadda bikin zai kasance da ranankun da za'ai shirye shirye. Nana tace ba wani hayaniya za'ai ba. Ranar alhamis da dare dinner, juma'a bayan sallah za'ai walima, sai asabar daurin aure da dare akaita. A lahadi kuma yini.
Da yamma misalin karfe biyar ita da Raihana suka shirya tafiya gidan Dr Mubarak. Ahmad ne yakaisu a motar Abba. Suna isowa bakin gate Haneefah ta tuna da Yusuf, haduwarsu na karshe randa yazo ya dauketa Momy tabiyota, a hankali hawaye suka taru a idonta. Mai gadi ya budi musu gate suka shiga.
Knocking sukai kofan falo, Dr Mubarak ne ya bude. Tsayawa yayi yana kallon ta cike da mamaki.
Ganin baice komai ba kuma sai kallonta yake tace Assalamu alikum. Amsa mata yayi ya bata guri ta wuce. Bayan sun gaisa Dr yace amma nayi mamaki saukan yaushe? Jiya da daddare Haneefah ta bashi amsa.
Cike da kulawa yace amma shine baki sanar dani ba saiki shiko hanya ke kadai? Ganin yadda yayi maganar sai jikinta yayi sanyi domin Ahmad na zaune.
Murmushi tayi tace ko gida ma basu sani ba, nazo auren Nana ne da zarar an daura aure zan tafi bayan sati daya, Dr kai kadaine a gidan? Ina Barrister?
Ta tafi sunan yayarta acan zata kwana sai gobe zata dawo. Haneefah tace toh inta zo kagaisheta zan sake zuwa insha Allah. Haneefah ta tashi suma suka tashi sukai hanyar fita. Dr na cewa su zauna ko ruwane susha amma Haneefah kin tsayawa tayi domin tasan kawai ranta ne zai baci.
Da dare tana zaune Ahmad ya shigo yace Dr Mubarak yazo yana jiranki a waje. Himar tasa ta fito domin batai mamakin ganin saba.
Sallama tayi suka gaisa tace ya shigo ciki. Ba musu ya bita har falon Abba. Kallonta yake yadda ta kara kyau da fari kamar ba itaba. Dago ido tayi suka hada. Yace Haneefah kinsan cewa ina sonki, kuma koda barrister tasan cewa kece bazata hanani auren kiba domin ta yadda dake. Alfarma nazo kimin inaso a hada aure na dake ranar auren Nana.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼42
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ko dagawa batayi ta kalleshi ba domin batai mamakin furucinsa ba sai dai tayi mamakin aure daya ambata. Tunani ta tsayayi, yanzu inta furta batason shi babu dadi domin yana qima a idanunta.
Ta dago ido ta kalle shi shima kallonta yake tace zaka iya bani lokaci nayi tunani? Yace of course, amma bana fatan jin abinda zai dagamin hankali. Ya mike tabi bayansa da kallo tace wallahi ko zan mutu banyi aure ba bazan sakawa barrister da haka ba.
Tana shigowa daki Ahmad yace ina fata ba soyayya yazo ba? Haneefah taja tsaki ta zauna. Nana da suka daurewa kai tace Dr Mubarak din?
Haneefah ta kwashe abinda sukai ta fada musu tare da cewa bacen ce dashi komai ba dan kanshi zai gene ba sonshi nake ba ya kyaleni.
Nana tace aurensa ba aibu amma in kikai haka baki kyautawa matarsa ba, domin ta daukeki tamkar kanwarta da kuka fito ciki daya, ita ta fara bada shawarar a fitar dake waje kiyi karatu kinga ko bazakiyi mata sakayyar da auren mijinta ba domin in akwai abinda mace bata so shine kishiya.
Haneefah tace bazan soma ba, nan gaba in yazo kuce bananan balle ma ai zamu fara fita.
Washe gari Hadiza ta kawo ummulkhairi ta ajeta, yarinyar bata kin mutane gata da saurin sabo. Haneefah gidan kowa takaiwa tsara ba, sunyi murna sosai. Ta fara ziyara amma duk inda ta gifta takan tuno Yusuf, kullum bakinta yana son tambayarsa amma tayi shiru ta kasa. Sun shaku da ummulkhairi sosai, Haneefah tamkar ta hadiyeta take ji.
Aure yazo domin saura kwana daya. Yau ake shirin yin dinner party, Haneefah sunje karban kaya gurin tela sun dawo. Lace ne blue-black da cap silver colour.
Zaune suke cikin daki ita da auties nata, yau kan saita tambaya domin ta kasa jurewa. Tace baku bani labari bayan tafiyata ko Yusuf yadawo ba? Kowa yayi mamakin wannan tambayar
Aunty Muhibbat tace nikam yaushe zanji kin daina ambatan wannan yaro, nikam ya cuce mu, tace da Raihana cikin harshen turanci Haneefah tana ambato sunan wani Yusuf? Raihana tayi murmushi tace sosai domin bana tunanin Haneefah zata mance dashi, bansan wani irin so take mishi ba yanzu haka da naji ta ambace shi nasan tambayarsa tayi duk da banajin yaren naku amma Haneefah inaso ki sani;
ZUCIYA an halicce ta ne saboda soyayyar Allah madaukaki. So, kada ka bata lokacinka wajen neman soyayya, amana da kamala a wajen wanin Allah. Baza ka taba samu ba. Inji Ibn Taimiyyah (Rahimllah)
Sufyan Bin Uyainah (Rahmhullah) yana cewa:
"Ranaku mafi tsanani da bawa yake tsintar kansa acikinsu 3 ne: 1- Ranar da aka haife shi ya fito gidan damuwa (duniya) 2- Daren da zai kwana tare da matattu (kabari) ya hadu da makwaftan da bai taba ganin irin su ba. 3- Ranar da za a tashe shi (qiyama) yaga taron da bai taba ganin irin saba!! Allah ya ce game da Annabi Yahya (A.S) akan wadannan ranaku 3:
(Kuma aminci ya tabbata agare shi a ranar da aka haife shi da ranar mutuwarsa da ranar da za a tayar da shi da rai."
Dan uwan Iman...
Annabinmu (SAW) ya kasance me son ALBISHIR. Ya ce :
Kuyi bushara, kada ku zama masu korewa, kuma ku sassauta kada ku tsananta"
Dan haka, kada ka boye magana me dadi ko na alkhairi a ranka, ka gayama waninka shi ma yaji irin dadin daka ji ko ya karu, ka samu lada. Ka yaba in an yi abin yabo, ka gode, kama wanda kake so addu'a, kuma ka fadi alkhairi ma kowa. Magana me dadi, sadaka ne, ibada ne, shiriya ne. Allah ya ce"
Kuma an shiryar dasu zuwa ga magana me kyau...
Kuma ka sani, jin dadin duniya yana samuwa ne gwargwadon kyautata alaqarka da Allah. Idan kana son rayuwa me kyau to ka rayu yanda Allah yake so ba yanda kai kake so ba.