Showing 48001 words to 51000 words out of 74305 words

Chapter 17 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5181

kyautata ma Allah zato, da sun kyautata biyayya gare shi.


Mutanenmu da kike gani yawancinsu yaran masu kudi ne, niba yar kowa bace bazan cusa kaina inda rayuwata da nasu da banbanci ba. Inason kasancewata haka domin yar Adam nake kada in zamo mai dogon buri, kema ai bansan kin fito daga gidan masu kudi bane saboda ke rayuwarki daidai kike yinsa.


Raihana tace hakane. Allah bamu ikon tsare kawunan mu ameen


****


Kwance yake rigingime yana tunanin irin matsayin da ya taka yanzu, yana da kudi, motoci, da dukkanin abin bukatar rayuwa sai dai haryanzu bai cika ba domin bayi da mata kuma ba cikekken lafiyane dashi ba. Jawo wayarsa yayi kirar GALAXY S7 yana so yakira likitanshi amma ya fasa domin yagaji da tafiya India. Browsing yafara asibitoci amma idanunsa yakai kan wani asibiti dake London. Nan yashiga yaga yanayin asibitin zuciyarsa ta raya masa da ya tafi can.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼49


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Cikin sati biyu ya kammala shirin tafiya London. Yaje gida yi musu sallama suka masa addu'an samun nasara. Cikin sati na uku ya daga jirgi zuwa London.


**** ****


Zaune take ta zubawa hotunan gabanta ido tana nazarin gano wasu matsaloli... ajesu tayi agefe ta dauki takardanta na makaranta ta soma karantawa domin suna gama wannan semester wadda zasu shiga gaba shine zasu gama makaranta.


Aje takardun tayi ta dafe kanta a hankali tace ya Allah gani gare ka, ka bani ikon rabuwa da wadannan bayinka lafiya.


Nan ta fara tunanin da ta saba a duk sanda taji abubuwa sun fice mata akai, wayarta ta jawo ta kunna karatun qur'ani mai girma tana sauraro. Shafa cikin ta tayi da taji murdan da ke mata.


A hankali tayi murmushi tace ko yaushe zan ganni da ciki? Tunani take yadda take sha'awar itama ta mallaki da ko ya.


Tana cikin tunani taji anturo mata kofa an shigo. Tana ganinshi ta hada rai. Murmushi Rohan yayi yace murmushi dabi'ar kwarai, duk da rasuwar dukkanin 'ya'yanshi illa nana Fadima r.a


Duk da rasuwar matar shi ta kwarai kuma mahaifiyar 'ya'yanshi


Duk da kasancewarshi maraya gaba da baya tun daga yarintarshi


Duk da rasuwar makusanta kuma masoya a gare shi Hamza r.a, Ja'afar r.a ga baffanshi Abu Dalib


Duk da irin 'dumbin nauye-nauyen da suke kan shi na al'umma wajen ya'da kalmar Allah da kawo gyara a cikin al'umma da kuma fama da mushrikai da kaidinsu.


Amma bai kasance ba illa mai yawan murmushi da fara'a!!
Wannan shine Manzon rahma sallallahu alaihi wasallam.


kayi murmushi domin koyi da abinda yake yi, sannan kuma ka dace da samun lada na sadaka, kamar yadda Manzon Allah s.a.w yace: (( murmushin ka ga fuskar 'dan uwanka sadaqa ne)).

Kimin murmushi domin bakisan ko rabiwarmu dake bane domin sallama nazo miki anjima zan wuce India.


Jikinta ne yayi sanyi dajin kalamunsa, a hankali tace kayi hakuri da dukkanin abinda nake maka ina maka nunene abinda kake kokarinyi bazayyu bane.


Rohan yace bakiyi niyya ba shikenan na hakura, ina miki fatan alkhairi a rayuwarki Allah sa gaba inmun hadu kimin magana kada kice baki sanni ba.


Da fara'arta tace na'isa! Kada ka damu indai wannan ne insha Allah ba rabuwarmu kenan ba zamu hadu nan bada jimawa ba.


Hira sosai sukai da Rohan tace inya tashi yafiya ita zata kaishi airport.


Saitaji babu dadi domin ta saba dasu, dan ma Kevin na kusa da sune. Da wuri ta tashi a asibiti taje gida tayi musu girki ta gayyaci Rohan da abokinsa suka zo. Ko Raihana da tazo tayi mamaki, sanda taji labarin tafiyar Rohan tayi dariya tace nasan da biyu kikai haka Haneefah.


Hira sosai sukai tare da basu wasu sirrika da bazasu wahalaba in sunzo jarabawar gamawa.


Har airport suka rakoshi saida sukaga tashinsu sannan suka koma cike da kewar shi


****


Kwance yake cikin hotel da yayi masauki yana hutawa. Saida ya huta sosai sannan ya fito nemar waya.


Kiran layin asibitin yayi sannan ya musu bayani atakaice. Cikin mintuna da bazasu wuce goma sha biyar ba aka zo aka dauke shi zuwa wannan asibiti.


Yayi duk abinda ya dace akace gobe yazo ganin likota tunda yasamu ya bude file. Komawa yayi hotel din dai baisan inda kuma zaije ba.

Can kuma ya tuno yakamata ace ya kira mutanen gida domin sanar dasu ya iso lafiya, ya yanke shawarar idan yayi sallar magriba zai fita yakirasu.


Su Haneefah an dawo daga rakiyan Rohan. Dai-dai zasu shiga gida tace na manta iPad dina a office bari in biya in dauka.


Kevin yace bani makullin office din in dauko miki in bazaki damu ba? Mika masa tayi domin ta gaji bacci take so tayi.


Bayan ya dauko ne yayi mantuwa yana da abinyi. Yaje yayi bukatarsa kenan yabi hanyar makarantar su domin zaifi saukin sadashi da gidan Haneefah. Tafiya yake yaji yayi karo da mutum har iPad dake hannunsa ya fadi. Hakuri Kevin yafara bashi tare da sunkuyo ya dauki iPad nasu, tsayawa kallo yayi domin iri daya ne. Yusuf yayi murmushi ya karbi dayan yace babu komai yayi wucewarsa. Shima ya wuce. Ya kaiwa Haneefah ya musu sallama ya fice.


Washe gari Haneefah taje makaranta suka tarar an fara test dan haka bata samu shigowa asibiti ba.


Shiko Yusuf daya je asibiti akace dashi saiya jira wadda take duty domin ta tafi makaranta saita dawo. Ganin ba zuwa zatai ba ya kama hanya ya shiga gari.


Bayan ya dawo ne yaja iPad nashi domin amfani dashi. Mamakine yakamashi daya kunna yaganta babu passward alhalin nashi akwai passward.


Gabansa ne yayi mugun faduwa ganin Haneefah agaban screen din iPad. Mussuka idon shi yayi amma ya tabbatar itace. Shiga hotuna yayi yaga hotunan dukka na Haneefah ne . Ya fita yashiga e-mail nan yaga e-mail din ba nashi bane.


Kallon iPad din yake nan ya tabba ba nashi bane, ya tuno da mutumin da sukai hasari jiya acan sukai musayya. Amma mamakinsa shine aina wannan baturen zai hadu da Haneefah? Shiga hotuna yayi yana kallon ta. Ganin tunaninsa na neman rikicewa yarufe iPad din ya kwanta.


Washe gari misalin karfe goma ya tafi asibiti wannan karon office din Dr Michael aka nufa dashi, yayi masa bincike ya gano matsalar. Dr Michael yayi murmushi yace damar sake goda kwakwalwar Haneefah yazo, ya dubi nurse data kawo shi yace kikai shi office din Dr HANEEFAH .


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼50


Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖




Gaban Yusuf ne yafadi jin an ambaci Haneefah. Tashiwa yayi zai fice yaga Kevin. Kevin ne ya mika masa hannu suka gaisa yace kaine wadda muka hadu jiya ko?


Ajiyar zuciya Yusuf yayi sannan yace eh nine iPad din ba nawa bane inaga munyi musanya ne.


Kevin yace kai hakuri na Haneefah ne amma yanzu tare muke inhar bata fita zuwa makaranta ba zamu iya samunta in mukai sauri. Nurse din tace dama office nata zan kaishi kace da ita Dr Michael ne yaturo shi.


Kevin yace banyi tsammanin zata duba patient ba amma bari muje.


Shiko Yusuf gabansa ne yake faduwa domin Haneefah da ake ambata. Da sallama Kevin ya shigo ganin kofar a bude take. Haneefah ta sunkuya tana neman littafinta daya makale kasan durowa jin muryar Kevin ne yasa bata dago ba taci gaba da abinda take.


Kevin yace patient kika samu... tun kafin ya karasa tace ina da test a makaranta babu wadda zan iya dubawa yanzu. Kevin yace Dr Michael ne yace in kawoshi fa.


Dagowa tayi tana duba takardan ta tace kaga abinda nake nema yanzu zan karanta kafin na tafi ma..... dago ido tayi domin ganin wadda ke tsaye, takardun hannuwan tane suka zube ganin Yusuf a tsaye gaban ta ya kura mata ido.


Shiko tsaye yake ya zuba mata idanu tamkar baitaba ganinta ba. Lokaci guda hawaye ya taru idanunsu.


Karfin hali tayi ta kauda idanunta tace bani da lokaci yanzu zan tafi makaranta. Zata fita taga Dr Michael yashigo yace Haneefah kin dubasa?


Tace sir inada test nanda mintuna kalilan inason tafiya makaranta. Yace wannan ba abin damuwa bane zan kira lecturer da kuke da course nashi sai musan yadda za'a amma inaso ki dubamin wannan patient din domin complicated case ne kuma inaga akwai aiki da za'a masa.


Saitaji hankalinta ya tashi dason jin abinda ke damunshi amma bata nuna ba tace toh shikenan zan same ku a dakin na'ura kafin zan dauki history.


Bayan sun fita ta koma ta zauna a mazauninta har lokacin Yusuf ya kasa motsawa daga inda yake. Cikin sarkewar murya tace ga guri zauna.


A hankali ya zauna amma ya kauda idanunsa a kanta. Haneefah ta kallesa tace meke damun ka?


Batare da yakalleta ba yace shekaru uku da suka wuce ne nayi hatsari nan ya kwashe dukka nin abinda likitoci suka sanar dashi. Shiru tayi ta lumshe idanunta tana jinjina abinda ya faru dashi. Mikewa tayi tace ka biyoni.


Sun tarar da Kevin ya kunna komai suna jirarsu. Kevin ya mika masa rika na marasa lafiya yanuna masa daki yace shiga ka canza. Bayan ya canza ya fito Haneefah ta masa nuni daya kwanta kan wani na'ura. Yana kwanciya ta danna wani madanni yashiga dashi.


Tsayawa tayi gaban screen din tana ganin sassan cikinsa. Nazarin wuraren da ta gani take har na'urar ya kammala ya fito dashi. Hoton ya fito Haneefah tasa hannu ta karba ta wuce office.


Tausayinsa ne yake ratsa illahirin jikinta, tabbas yasha wahala domin alamu sun nuna. Bangare daya kuma wani irin sabon soyayyar shine take ji. Wannan ba lokacin tunani bane ta bafa azuciyarta. Kurawa hoton ido tayi tana nunanin yadda za'ai, turo kofar da akayine ta dago ido tana kallon me shigowa, hada ido suka yi taji wani irin fadiwar gaba shima haka.


Ya salam! Ya fada azuciuarsa, daidai inda Dr Michael yashigo ya nufo inda Haneefah take yace kin gano matsalar? Ba tare da bata lokaci ba tace eh, har yanzu akwai glass biyu dake jikinsa wadda suke dada nitsewa kowani wayewar gari cikin jikinsa


Hannu tasa ta nuna masa tace kaga nan? Za'a gani jijiyoyine suka kumbura amma akwai glass daya sannan cikin cinyarsa akwai shima glass daya makale wadda wani sa'in in yana tafiya yana sashi dingishi. Anan ta masa karin bayani yadda za'abi ayi masa aikin cikin sauki.


Dr Michael yace great! Bayaninki haka ne sannan treatment dinma haka ne. Ya juya gun Yusuf daya wangale baki da hanci yana kallon Haneefah.


Yanzu dai mungano matsalarka, zamu maka aiki in har ka amince kaje ka biya sai gobe mu fara domin ba abin daga lokaci bane, kwayoyin maganin da kake sha babu abinda zai maka sai tarin illah...


Sallamar Raihana suka yi, ganin Dr Michael yana ciki zata koma Haneefah tace shigo yanzu nima zan tafi. Ta kalli Dr Michael tace patient nane zaku iya cirewa a salary na.


Dr Michael yace cike da mamaki aida kin fadamin tun farko, yanzu shikenan za'a iya masa gobe sai kizo ayi dake.


Haneefah tace inada abinyi zaku iya masa sannan nurses su kula dashi. Raihana tunda ta shigo take kallon Yusuf da mamaki? Tambayar Haneefah takesonyi amma sai sun fita waje.


Zata fita Dr yakirata tace pls sir banasonyin jayayya dakai tana kaiwa nan tasa kai ta fice. Shiko Yusuf mamaki ya hanasa cewa komai, saida da Dr Michael yace dashi zai iya tafiya gobe da dare za'a masa aiki misalin karfe bakwai yazo. Ya tashi jiki ba kwari ya fito yana tafiya ya tsaya ya siya Sim ya koma hotel.


Kasa tafiya makaranta tayi suka wuce gida. Zama tayi kan kujera tana hawaye, Raihana dake kallonta tace hawayenki zayyi nasaba da kallon masoyin ki ko nace ki dakata bazaki daka ta ba amma zanso jin ya akai kuka hadu.


Tana kuka ta labartar mata yadda suka hadu. Murmushi Raihana tayi tace Allah mayyin yadda yaso, kun rabu kunyi nesa da juna tsawon shekara uku amma yau kuka sake haduwa amma me dalilin biya masa kudin aiki?


Haneefah tace taimako ne kawai nayi. Raihana ta fashe da dariya tace taimako manya, naji kinyi taimako amma kada ki manta alkawarin da kikaiwa mahaifiyarsa inko kina son gamawarsa da duniya lafiya kada ki yarda maganar SO tashiga tsakanin su infact ki nemi hutun sati biyu a asibiti sayya gama abinda yake saiki koma dan ba patient naki bane shawarar dazan baki kenan.


Haneefah ta share hawayenta tace lallai ne nayi nesa dashi domin alkawarin da nayiwa mahaifiyarsa.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼52


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Yusuf ji yayi gabansa ya fadi, ina shi ina kallon Haneefah da wani? Yayi murmushi yace nagode aboki amma inani ina sauka a gidan matar aure.


Dr Abdullahi yace kada ka damu bata da aure, karatu take aka dauketa a asibitin shine suka hada mata da gida.


Kallon Abokin nasa yake tamkar baisan abinda yake furtawa ba. Yusuf yace ba Haneefah dake rike da yarinyarta ranar dinner party kuba? Naganta akace da ni matar aure ce.


Dr Abdullahi yace ba yarta bane, bansan inda ta samo ba, matata tace ansa ranar aurenta saura wata biyu aka fasa, shine ta samu scholarship ta tafi karatu can London, yanzu haka saura watanni yarage ta gama amma naji suna cewa in tazo zatai aure, kada ka damu Yusuf na yarda dakai bazaka cutar da ita ba.


Yusuf yakasa yadda zai fassara yanayin da ya tsinci kanshi domin kwata kwata tsaye yake amma ya kasa mosi.


Dr Abdullahi ne yace kada ka damu engineer na yarda dakai, yanzu Inna je gida zan sanar da matata sai ta hada ni da ita inyaso taban address din sai in tura maka inyaso taje ta dauke ka a airport.


Yusuf yace dagaske batai aure ba? Dr Abdullahi ya tsare sa da ido yanason gano wani abu.


Ganin haka Yusuf yace nifa in tana da aure ka fadamin saboda bana sauka gidan ma'aurata. Dr yace wallahi bata da aure in har bazaka sauka gidan taba shikenan. Sukai sallama akan saiya jishi a waya


Zaune yake cikin mota yana nazarin maganan abokinsa, da gaske Haneefah bata da aure? Toh ya aunty Muhibbat tace tana da aure? Abin ya daure masa kai sosai. Sai kuma ya tuno in dagaske ne bata da aure fa?


Wani irin farin ciki ya lullubeshi. Da sauri ya tada mota ya dauki hanya zuwa gidan Aisha. Mai gadi na bude masa ko fa ya fito cikin hanzari ko rufe motar bayyi ba.


Cikin sauri ya shiga gidan ya tarar tana zaune kan kujera tana yiwa Ra'ima wasa. Cike da tsananin farin ciki yayi sallama tare da karban Ra'ima yace my little princess takwaranki ta kusa zuwa gare ni.


Aisha tashiwa tayi ta tsaya karewa yayan nata kallo ganin farin cikin da ke fuskarshi da abinda yake fada tace Yaya irin wannan farin ciki haka? Kuma kake cewa Haneefah ta kusa zuwa gareka?


Yusuf yace zauna in baki labari, zama sukai ya sanar da ita abinda sukai da Dr Abdullahi. Shiru Aisha tayi tana kallonsa tace har Momy taje gidan akace da ita Haneefah tayi aure.


Turus yayi yana kallon ta. Tunani yake wannan lamarin yana da daure kai... Aisha ce tace yanzu Yaya kasan mafita? Girgiza kai yayi alamar aa domin jikinsa ya gama yin sanyi kada muyi gaggawa a wannan lamarin, in kaje London ka sauka gidan nata saika tabbatar inma tana da aure ko bata dashi nima anan zansan yadda zan gano lamarin amma kada ka nunawa kowa abinda ke faruwa tatta ita da kanta amma kafin nan zan so ka sanar da abokin naka lamarin.


Gyada kai yayi alamar ya fahimceta yayi mata sallama ya wuce gida. Tunda ya kwanta tunani barkatai suke masa yawo a kwakwalwa, wani bangare na zuciyarsa kuma tsananin farin ciki yake ji amma bai bada damar wannan farin cikin ya samu zama a zuciyar shiba.


Tagumi yayi yana kallon kasan tiles. Momy ta turo kofa tashigo da sallama. Da sauri ta iso tace lafiya ? Meyasaka wannan ta gumin?


Murmushi yayi yace Momy a kullum fatana rabuwa dake lafiya, bana son kusan toh abinda zai bata miki rai. Durkusawa yayi gabanta yace Momy yafiyarki nake nema dan Allah bana bukatar tsinuwar ki, albarkanki nake nema wadda jikokina zasu kasance cikin albarka.


Momy da duk jikinta yayi sanyi ta zaunar dashi tace kada ka damu, zaka kasance cikin albarkata har karshen rayuwata, nayi kuskure abayi da na ambata maka wannan furuci yanzu da kaina nake nadama. Da inada damar aura maka Haneefah da na aura maka nasan tunanin ta ne yasa kake irin wadannan maganganu, amma ka sani kada son zuciyarka ta kaiga ga halaka, kabar tunaninta tayi maka nesa ka nemi wata ka aura.


Yusuf yace wata qila nakusa aure Momy! Cike da murna Momy tace Allah nuna mana ya sanya alkhairi, aina take da zama? Yusuf yace in na zo daga London zamuyi magana. Dadi ya cika Momy dakyar sukai sallama sai hira suke. Daren ranar Yusuf bayyi barci ba.


Washe gari misalin karfe sha daya ya musu sallama ya fita. Waya yayiwa abokinsa yaci sa'a yana wajen aiki.


A office ya same shi suka gaisa. Batare da bata lokaci ba ya sanar da shi abinda ke tafe dashi, bai boye masa komai ba ya sanar dashi haduwar su da Haneefah da yadda rashin auren ya kasance, yadda sukai da aunty Muhibbat da yadda suka hadu da Haneefah a London ya qara da cewa tabbas akwai boyeyyen al'amari tsakanin mu, pls ka fahimce ni sannan ina bukatar taimakon ka, nasan kafin in sameta zan sha kuma family suna fishi da ni amma nasan in kayiwa Nana bayani zata fahimtar da su.


Dr Abdullahi yace bansan haka abin yake ba aboki, amma insha Allah komai ya zo karshe tunda mum naka ta sauko, mafita daya ne muddin tana son ka har yanzu, kuma babu wadda ya nemi auren ta abin zaizo da sauki, yanzu zan baka address din in kaje kawai kaje gidan direct.


Yusuf yace amma inason maganan ya zamo sirri, zanje mu daidaita kafin nan. Abdullahi yace babu matsala Allah tabbatar muku abinda yafi alkhairi.


****


Dr Mubarak ya kasa aiki, juyi yake akan kujera yana tunanin yadda zai bullowa Haneefah, gashi ta kusa gama makaranta, shi tsoron shi kada ta zo gida manema su fito ta amsa musu tunda ya fahimci bata son auren nasa, domin hujjarta baikai taki auren sa ba.


Tunanin tafiya London ya fara. Ya yanke shawarar tafiya neman soyayyarta, domin yanzu *_Dr HANEEFAH_* ce babban burin shi.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼51


Dedicated to Batul

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login