Showing 21001 words to 24000 words out of 74305 words
Chapter 8 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
nasan damuwata na daya daga cikin abinda zai saka ki cikin damuwa, amma da yaddar ubangiji bazan bar nawa damuwar ya gusar da farin cikin mu ba.
Nan haneefah takwashe duk abinda sukai da momy ta sanar da ita. Haneefah taci gaba umma narasa tunanin mezanyi inji dadi, umma nasan rayuwata zata canza na lokaci kadan amma kuyi hakuri da hakan. Na tabbata wannan jarabawane Allah ya aikomin, ki tayi da addu'a Allah bani ikon riketa hannu biyu. Umma ina bukatar addu'a. .. Nan ta fashe da matsanancin kuka.
Umma karfin hali tayi ta soma rarrashinta, tabbas sai yau nasan kina aiki da ilmin ki. Allah baki miji nagari. Kuka take kan cinyar mahaifiyarta har aka kira sallah magriba.
Daganan haneefah tashiga daki ta kulle. Umma tace su amal kada kowa ya sameta su kyaleta. Bayan abba yadawo daga sallah umma taje ta sanar da shi abinda sukai da haneefah. Abba baice komai ba illa Allah sa hakan shi yafi alkhairi.
Zaune take kan sallaya tana tuno yusuf, abin kamar a mafarki yau saura wata biyu aure aka fasa. Murmushi tayi tace Allah na nasan kana min shiri abinda yafi alkhairi agare nine. Insha Allah zan kasance mai addu'a domin wannan alkhairin ya iso gareni. Kallon wayarta tayi ta dauka tace nasan kaima momy taje tasameka, muyi hakuri wata qila hakan shi yafi alkhairi agaremu. Tadauki wayar ta kashe tasa a drawer sannan ta dauki qur'ani ta fara karantawa.
***** *****
Mahaifinsane yace yusuf kana da hankali kuwa? Wata biyu ya rage kace ka fasa aure? Yusuf yace abba ban taba neman wani alfarma ba, amma ina rokonka wannan karon kamin abba.
Abba cikin bacin rai yace zanje in sanar dasu amma ka sani alhakin wannan yarinya bazai barka ba. Tashi ka bani wuri.
Yana tashiwa ya nufi gun mahaifiyarsa ya sanar da ita yadda sukai da abba sannan yace momy ki yafemin, inban kasance da albarkan kiba babu amfanina a duniya, zanyi duk abinda kika sani amma banason jin wannan kalamai ya karasa maganar yana hawaye
Cike da tausayin danta tace ba komai tunda kayi yadda nace. Allah yi maka albarka. Yace ameen, gobe zan fita da safe zuwa abuja, zuwana nagaba zan tafi da rahma. Ya tashi ya fita.
Tunanine fal cikin zuciyar momy, shi namiji kenan ya macen zata kasance?
Yana fita ya nufi dakin aisha. Kusa da ita ya zauna yace aisha kitayani addu'a. Tace yaya lafiya? Bai bari taga idanunsa ba yace ba komai ya fice.
Lap top nasa ya jawo yayi uploading dukkanin hotunan haneefah. A hankali yace Allah ne ya hadamu kuma shizai rabamu. Umma zanyi miki biyayya amma nasan haneefah alkhairi ce agareni, zanci gaba da addu'a har Allah ya kawo min ranar da zan mallaketa. Murmushi yayi ya tashi yayo alwala ya shiga gayawa Allah halin da yake ciki.
Haka haneefah takasance, tana karatun qur'ani tana kuka, daga baya ta tashi ta fara jero nafiloli.
Yadda suka ga dare haka sukaga rana, babu alamun bacci cikin idanunsu. Basu biyewa tunaniba domin babu mafita, Allah suke gayawa lamuran su.
Haneefah ko karatu takasa sai addu'a. Da asuba ta tashi ta idar da sallah sannan ta fara karatun qur'ani har gari yawaye. Misalin karfe bakwai ta shirya ta fito. Ta samu umma da sauran kannenta suna breakfast. Ta gaida umma sannan ta dauki kofin shayi ta hada tana sha.
Shan shayi take amma bajin dadinsa take ba, kada umma ta damu kan bataci komai bane take sha. Amal ta dubeta tace yaya haneefah kada ki damu, kici gaba da addu'a Allah zai sauya miki abinda yafi alkhairi. Bintu ta amsa tace zamu taya ki addu'a babu komai insha Allah.
Murmushi tayi tace ko saboda ku bazan damu ba, nagode da kulawar ku kannena. Umma dake kallon su ta hadiye hawayen da suka ciko mata tace Allah yi muku albarka, ya dada hade kanku.
Dukkansu suka amsa da ameen. Haneefah ta musu sallama ta fito ta fita makaranta. Bata je gaida abba ba saboda ba gidan su ya kwana ba.
Tana isowa bakin titi ta tare adaidaita sahu ta shiga. Tunda suka soma tafiya babu abinda take banda zubar da hawaye. Jin gine jikin karfe, sun tsaya traffic.
Adai dai inda suke tsaye shima yazo ya shiga. Rungume sitiyarin motan sa yayi yana hira abasu hannu, ya juya inda take. Jajayen idanunsa suka sauka a kanta. Kallon ta yake tana zubar da hawaye shima ya soma taro su idanunsa.
Kada ta jawa kanta kallo yasa ta dago domin goge hawaye suka hada ido. A sannan hawayen idanunsa suka sauko, ya goge hawayensa sannan ya mata nuni da tayi yadda yace. Ba musu tayi sannan ya girgiza mata kai yana murmushi, itama murmushin ta soma. Anan aka basu hannu sunaji suna gani ko magana sun kasa yiwa juna suka rabu.
Haneefah ne tunaninta ya karkata ina zaije da safennan? Abuja ta bawa kanta amsa. Take tashiga yin addu'a Allah kaishi lfy
Tunda yaganta ya kasa nutsuwa. Mesa momy zata mishi haka? Wani hali haneefah take? Wani matsayi haneefah zata dauke ni? Na yaudareta? Aa nasan bazata fassarani da hakan ba. Tausayinta yaji ya lullubeshi.
Yayi nisa cikin tunani, tuki yake amma baya fahimtar abinda ke gabansa. Saida yazo dab yaga babbar motar da ke gaban sa, kokarin kaucewa mai motar yake wajen canza hanya shima mai motar ganin yusuf bai bashi hanyan ba yake kokarin bin gefensa domin kauce mishi. Guuuufffff!! Kake jin haduwan mota, ganin haka driver babbar motar ya rikice tukin ya kubce a hannunsa ya tura yusuf kan motar dake bayansa. Mummunan hatsarine ya auku domin manyan motoci biyu suka sa motar yusuf a tsakiya. Kallon motar zakayi ka tabbata wadda ke cikin baya raya.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼24
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Kusan mutum goma ta tambaya kafin aka nuna mata ofishin. Knocking tayi aka bata izinin shigowa. A sanyaye ta shiga ta zauna. Bayan ya gama rubuce rubucensa ya dago ya kalleta yace ko akwai taimakon da zai mata.
Haneefah ta sanar dashi yace ai lokaci ya wuce sai dai shekara mai zuwa. Ta tashi tafita jiki ba kwari. Can nesa inda ake parking motoci ta jingina jikin wata bishi domin jirine ke debanta dalilin yunwarda ta addabeta. Jira take tadanji sauki saita qarasa gida.
Dr waccan ba haneefah bace, Dr Mubarak ya juyo inda aka nuna masa. Itace ko amma ko me takeyi anan? Barrister tace muqarasa mugaisa da ita sai mu wuce.
Haneefah tadan fara jin sassauci tashi tayi ta soma tafiya sai kuma ta kasa, ganin zata fadi yasa ta koma ta zauna. A hankali take zubar da hawaye tace sai shekara mai zuwa, bana kaunar qara koda wata dayane agarinnan .... bata qarasa ba taji ana mata sallama.
Saurin goge hawayenta tayi ta juyo domin amsa sallama amma tuni sun gano. Murmushin karfin hali tayi ta gaishe su. Cikin damuwa barrister tace haneefah meya sameki? Me kikeyi anan? Haneefah ta qara murmushi tace wlh yanzu nake son komawa gida.
Ganin tana kame kame yasa barrister tace dan Allah haneefah fadamin gaskiya meya sameki? Ganin zasu takurata ne yasa tace nazo summition ne na tarar anyi closing sai next year, shine na tsaya anan domin jirin da nake ji inya lafa zan kama tafi gida.
Dr yace inga takardun naki? Ta mika masa ya kalla. Barrister tace kiyi hakuri, in wannan ne matsalan bari in shiga in kara confirming kinsan wasu lokutan basa sauraron mutane. Zo mushi ga.
Barrister ta rikota suka shiga. Bayan sun gaisa da mutumin ya nuna cewa ya taimaka mata inda guri. Mutumin yace Dr sanin ka danai yasa bazan maka jayayya ba, wlh sai dai tajira next year.
Barrister tace ka fadi ko nawa zan baka indai sunanta zai fita, nasan bakuyi placing sunayen su ba. Mutumin yace haba madam, Dr ya wuce haka agurina. Ranta ne ya baci ta juya ta kalli haneefah tace kijiramu a waje. Nan haneefah ta juya ta fice.
Bayan fitarta tace Dr mezai hana ka biya mata tunda Allah muke roko ya nuna mana randa muma zamu faranta mata rai. Dr yace kin rigani fadane nima abinda nakeson.
Ya dubi mutumin yace alfarma muke nema, ya za'ai mu samu visa nanda sati biyu, domin inason tafiya london nan da sati uku acan zan nema mata university. Mutumin yace wannan ba damuwa bane, indai student ne zamusan yadda za'ai domin suma wadda muka turasu sun fara lectures saiku hanzarta. Suka masa godiya.
Haneefah dake zaune a bakin office tana jiransu ta tashi suka tafi. Tana musu kwatancen gida har suka iso. Dr yace saikimin magana da abba in yana ciki ta amsa da toh.
Tare da barrister suka shiga cikin gida. Umma na kitchen tashi sallama haneefah, da sauri ta fito taganta tare da bakuwa. Da fara'arta ta musu sannu da zuwa tare da yiwa mata isowa zuwa falo, haneefah ta nufi kitchen dauko ruwa. Bayan anyi gaisuwa haneefah take sanar da ita matar Dr ce Barrister ramlat, tare muke da Dr in abba na nan yace zai shigo su gaisa.
Umma tace Allah sarki mun gode da zumunci, haneefah kirawo shi ya shigo abban naku yananan. Haneefah ta fice sanar da Dr. Falon umma ta kaishi sannan taje ta sanar da abba yana da baki a falon umma.
Bayan anyi gaisuwa Dr yafara magana wato dazune muka tarar da haneefah a minstry of health ta kai takardun ta neman karatu a kasar waje amma akai rashin sa'a sun rufe sai shekara mai zuwa, nazarin da nayi ba lallaine ko shekara mai zuwan yayi ta samu domin suna cike sunayen wadda suka sani ne, ma'ana suna da candidates nasu, shine ni da mata ta mukai shawaran biya mata karatun ta.
Ba abba da umma ba, haneefa ce ta dago ido cike da mamaki tana kallon shi. Dr yaci gaba haneefah badan kin taimakamin ba zan miki, aa ina da niyyar Allah nuna min randa ni da matata zamu faranta miki domin kin cancanta fiye da haka, sannan nazarin da nayi wajen fitar dake kiyi karatu tamkar sadakace garemu. Domin nasan mutane da dama zasu amfana da abinda kika karanta.
Dr ya dubi abba yace kada kayi mamakin jin haka,
Ba haneefah ba. nan ya kwashe abinda ya faru tsananin su yafadawa abba, dan haka ku bani dama Allah yana gani bazamu cutar ta ba, zan kaita london domin nafi zuwa can ziyarar wasu asibitoci kuma bazan samu wahalar samarmata makaranta ba domin nayi zaman can nasan mutane da dama.
Abba da duk mamaki ya cika shi yace Alhamdulillah, hakika nagode da shaidar da kukai mata sannan nagode da abinda kazo dashi, bani da abin cewa sai Allah ya saka da alkhairi sannan na amince da tafiyarta sai dai ku nemi amincewar ummanta.
Umma ta numfasa tace babu komai Allah sanya alkhairi. Haneefah ta dago ido cike da hawaye tace nagode Dr Allah biya ka, Allah azurta ka da zuria nagari. Dukka suka amsa da ameen.
Bayan tafiyar su haneefah tana kwance kan gado momy tayi shiru tana ambaton Allah kamar yadda ta saba, umma tashigo ta sameshi a haka. Zama tayi kusa da ita tace haneefah.
Haneefah ta amsa tare da matsowa ta kwanta kan cinyarta umma. Umma tace nasan kin zabi barin garin nan akan rabuwa da yusuf, amma zanyi farin ciki da tafiyarki bisa sharadi daya.
Haneefah tace umma zanyi shi, nayi miki alkawari ko menene. Umma tace inaso kimin alkawarin abinda ya kaiki zakiyi wato karatu. Haneefah tace indai wannan ne umma namiki alkawari.
Sannan ta qara dubarta tace haneefah ki rage yawan tunani da damuwa, domin hakan zai dagamin hankalin sosai. Haneefah ta tashi zaune tace umma bazan miki karya ba, tunani kam sai a hankali zan rage, kadai ki tayani da addu'a. Tace insha Allah.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼25
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Wayar umma ne tab soma ringing, tana dagawa taga nana. Bayan umma tayi sallama ta daga sun gaisa nana tace haba umma, yau sati uku baku nemeni ba duk shirye-shirye bikin yarki ya hanaku tunoni ? Itama inata kiran layinta bana samu domin inyi congratulating nata ta gama makaranta... tunda ta fara magana umma tayi shiru tana kallon ta. A hankali ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar da nana, nana kuka take sosai tace umma mesa bazaku sanar dani da wuri ba
Umma tace karatunki yayi nisa, bama so mu daga miki hankali amma yanzun ma yazama dole tunda barin garin zatayi. Haneefah dake zaune tana jinsu tace da umma ta bata wayar.
Jin muryar haneefah yasa ta qara fashewa da kuka. Haneefah tace haba nana, ni da kaina banyi irin kukan da kike ba ko so kike nagaza juriya nima nasoma kuka? Cikin sauri nana ta tsayar da kukanta tace aa shikenan dan Allah kada kiyi, kuma namatukar jin dadin jin haka. Allah zaba miki mafi alkhairi arayuwarki.
Haneefah tace ameen. Ta goge hawayen da ke sauko mata tace cikin zolaya ainima nakusa keta hazo cikin turai, nana dan fadamin abinda ake cikin jirgi kar inyi kauyanci.
Nana tayi dariya tace wannan kam dole sai kinyi gaki da shegen karambani da zumudi! Haneefah tayi dariya.... nan suke ta hira har ta tabbar ma nana ita komai ya wuce gun nata. Umma dake zaune tana jinsu ta goge kwallar data zubo mota, tana addu'ar Allah qara hade kawunan su.
Shirye shirye haneefah take sosai domin Allah-Allah take su tafi, kullum babu abinda take sai taje cikin yan uwanta ana hira dole ta mantar dasu cewa ita ba damuwa take ba, wadda bata boye damuwar ta itace hadiza domin tana kwantar mata da hankali sosai. Sau tari sai aganta tayi shiru, wani lokaci tunani take wani lokaci addu'a take. In dare yayi saita kasance cikin addu'a tare da karatun qur'ani. HANEEFAH baiwar Allah.
Visa ta yafito sai dai tafiyar ta matso sosai domin sallamar Dr suka ji, bayan an gaisa yace tafiyar gobene sannan zamu biya Egypt, an wakiltar dani inje inga karatun yaranda aka tura shekaru hudu da suka wuce, bayan kwana biyu sannan mu wuce london domin na kin samu admission ma.
Cikin murna haneefah tace Dr akwai yayata da take Egypt bansan ko university su bane, ta sanar dashi.
Yace can zamu, saiki shirya gobe da safe zanzo mu tafi domin jirgin safe zamu hau zuwa abuja daganan sai mu wuce. Hakikanin murna haneefah ta bayyana. Gidan dukka murna suke. Ahmad dai yace kuje kuyi karatu nima ku fitar dani.
Cikin murmushi haneefah tace inda rabonka harsai ka gaji dashi. Da daddare Ahmad ya dauki motar abba suka je gidan mama, tayi mata nasiha sosai tare cewa komai kaddara ne amma ta sani wani kaddaran addu'a na canza shi, ki dage sosai da addu'a Allah maji rokon bayin sane. Nan suka wuce gidan aunty muhibbat da humaira. Suma nasihar suka mata dajan kunnen tayi karatu tace tana neman alfarma gurinsu su mata alkawari, tace duk sanda yusuf yajo nemana kuce nayi aure. Aunty humaira tace aidama basu sameki da arhaba bale azo ace a qara bada ke. A gidan hadiza ne tadan jima sannan ta wuce sannan ita ta bukaci tayi mata alkawarin sanar da yusuf tayi aure inya zo nemanta.
Bayan sun koma gida, ta shiga gidan inna domin yin sallama babu yabo babu fallasa sunyi sallama.
Kwance take kamar yadda ta saba dakin umman tare da kannenta da Ahmad sai umma. Haneefah tace inaso kumin alkawarin in yusuf ko daya daga cikin dangin yusuf yazo kuce nayi aure banaso susan banida aure. Dukka suka amsa da toh. A wannan daren haneefah ta saki ranta sunyi hira sosai da yan uwanta musamman umma sannan ta nuna musu tafiyarta na daga cikin kwanciyar hankalinta domin zata danyi nesa da garin ko zata manta abinda ya faru cikin sauki.
Washe gari da safe ta nufi gun abba domin gaishe shi. Yace haneefah cikin turai zaki duk da bana shakkar komai amma kada ki zamto mai son mu'amala dasu, ki kawar da kanki akan komai kije ga abinda ya kaiki, yarda da sukai dake ne yasa suka biya miki wannan makaranta kada ki zuba musu kasa a ido, muma kin nuna can kike so yasa muka amince amma bamusan hukuncin Allah ba, Allah yayi miki albarka yasa kifara a sa'a ki gama a sa'a. Ta amsa da ameen. Taje ta dauko jakarta da wayarta amma ta kasa kunnawa. Karfe takwas da rabi Barrister da Dr suka zo. Dr yace na gode abba kuma na maka alkawarin sa ido kanta da karatunta.
Har airport ramla takaisu sannan ta mikawa haneefah wani dan karamin jaka, ta karba tayi godiya. Tara jirginsu ya tashi zuwa abuja, da rabi suka daga zuwa kasar Egypt. Da dare suka sauka, motar makarantan yazo daukan su. Tunda suka shiga haneefah ta baje ido tana kallon duniya, bata san anzo makarantar ba sai da Dr yace bani number yar uwar taki. Dr yakira nana yasanar da ita inda zata zo ta sameshi.
Cikin minti goma sha biyar saiga nana, da sauri suka tashi suka rungume junansu. Nana kuka take sosai na tausayin yar'uwarta ganin yadda ta rame. Dr yace jibi zamu wuce saita zauna gurinki nizan wuce masauki na. Nana ta dauki jakar haneefah suka wuce hostel nasu.
Su biyune a dakin, ita da wata yar sudan. Tayiwa haneefah sannu da zuwa cikin harshen turanci ta amsa duk da ba wani gane yaren take sosai ba. A wannan daren yan uwa biyu basu runtsa ba. Washe gari bayan sun karya karfe bakwai da rabi suka fito aji harda haneefah. Mamakin yar uwarta take yadda tajita take yaruka daban daban ,in anzo gun haneefah shiru. Nana tace nasan zaki fini domin inda zaki je kunfimu da komai. Takaitattun guri nana ta zaga da ita. Ta dada kwantar ran haneefah tace komai zaizo ya wuce. Karewa nana tayi da kallo tace inba munafurci ba gurin da babu iyayenki da yan uwanki jibi yadda hankalin ki ya kwanta har kika qara kyau! Nana tayi dariya tace haneefah bansan sanda zaki canza ba. Haneefah cikin zuciyarta tace karfin haline nana.
Dr ya gama abinda ya kawo shi dan haka ya tattara suka wuce london. Tunda suka sauka haneefah ke karewa garin kallo. Hotel suka wuce domin hutawa, kowa dakinsa daban daban. Saida suka huta sosai tukun suka fita, Dr yasiwa haneefah sim. Tasa wayarta ta kira umma