Showing 60001 words to 63000 words out of 74305 words
Chapter 21 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
ido waje tace lallai dagaske yake, sai dai yayi hakuri domin Haneefah ta samu wadda take so.
*
_2days later_
Momy zaune take tana tunanin halin da Yusuf yake domin basuyi waya ba, sallamar Aisha ce ya katse mata tunani ta tashi ta tarbesu da fara'a.
Bayan ta gaisheta take tambayar Abba na nan tace ya fita amma yakusa zuwa.
Shiru sukai sannan Aisha tace ko kinji labarin Yaya? Momy tace tunanin rashin samun sa a waya da nakeyi nake kika shigo, nayi kiran harna gaji, Allah sa lafiya......
Bata karasaba taga Muhammad rataye da jaka Yusuf na biye dashi. Kallo daya Aisha tayiwa fuskarshi ta fahimci babu nasara amma ta dake ta tashi tana mishi sannu da zuwa.
Shiru yayi ya kasa magana, ganin haka yasa Momy tace ko dai gajiyane Yusuf? Muhammad yace Momy flight yabi fa, yana sauka a taxi muka taho amma bansan ko direct daga London yake ba?
Momy cike da damuwa tace Yusuf ya kayi shiru? Me likitocin suka ce? A sannan ya dago idanunsa da suka kada sukai ja yace komai lafiya, mikewa yayi ya soma tafiya Aisha da taje dauko masa ruwa tace Yaya tsaya kasha ruwa.
Bai saurare taba ya fice daga falon yana sharar hawaye. Yana fita yaga motar Abba yana shigowa, sauri yayi ya shige falonsa amma tuni an hango abinda yake boyewa.
Momy ta tashi cike da damuwa tace Aisha wai meke damun yaronnan? Nashiga uku in wani matsalan aka kuma hangowa.
Muhammad cike da damuwa kamar zayyi kuka yace Momy hawaye yake zubarwa fa? Aisha batasan sanda ta saki kofin hannunta ba ta nufi hanyar falo.
Driver bai gama parking ba Abba ya bude motar ya fito yana kiran Yusuf shikuma tuni ya rufe kofar. Sai gasu Momy sun fito sun nufoshi, Abba ya juya yace meya same shi? Me kuka masa? Babu wadda ya bashi amsa suka fara dukar kofar falon Yusuf.
Yusuf yana shiga ya rufe falon, sauri yake har ya iso baedroom nashi. Zama yayi kasan tiles yana hawaye, yarasa mezayyi yaji sassauci dukkanin tunaninsa sun tsaya, Haneefah taki sauraronsa, lokacin mallakanta yayi amma bayida wannan damar, wazai SO ta maye mashi gurbin ta? Jin numfashinsa sama- sama yasa yayi lamo ya kwanta yana fitar da numfashi a hankali domin jin nawin da kirjinsa yayi.
Babu irin dukan kofar da basuyi ba amma shi ko ji bayayi. Abba ne yayi sauri yaje ya dauki key yazo ya bude, a wannan hali suka zo suka same shi. Muhammad ne da Abba suka taimaka shi suka kwantar dashi akan gado.
Momy ne ta fashe da kuka tace nashiga uku Yusuf me nake gani dan Allah kada ka mutu ka tashi, Aisha da tuni kuka kubce mata ta dauki wayarsa ta kira Dr Abdullahi tace pls kazo, Yusuf babu lafiya it's urgent ka taimaka. Dr dake tuki yace babu damuwa gani nan zuwa ya katse wayar, ya juya ya kalli Nana yace abokina babu lafiya bari mu biya mugansa. Tace babu matsala.
Yusuf ya kawar da kanshi domin baya son ganin halin da suka shiga, magana yake son yi amma yadda yaji zuciyarsa na masa kwata-kwata ya kasa. Hannun Aisha ya riko yana girgiza mata kai yace HANEEFAH
Aisha tace Yaya dan Allah ka kwantar da hankalin ka, zaka aure ta, kada ka shigarda kanka cikin wani hali, hannu tasa tana goge masa hawaye.
Momy tace nidai ban kyauta maka arayuwaba, na rabaka da wadda ta tace ta kasance matar auren ka wadda tasan darajar iyayen ka, ku nemomin ita na nemi afuwarta.
Abba ya daka musu tsawa yace kun isheni da surutu, kin riga kin aikata abinda kike ganin shine daidai, dubi yadda yaronnan ya koma asanadinki! Ko yarinyar nan batai aure ba inna koma neman auren ta me iyayenta zasu dauke mu? Yaro kamar Yusuf ace yau shine ya fito da damuwarsa karara? Dan kawai yana miki biyayya?
Duk sunyi jugum suna hawaye, ran Abba yayi matukar baci yana ta surutu saida wayar Yusuf ya soma ringing tukun yayi shiru. Aisha ta amsa wayar ganin Dr Abdullahi ne.
Muhammad ne yashigo dasu, Nana ta zauna a falo tace zata jira shi anan shi kuma suka wuce bedroom inda Yusuf ke kwance wadda ya soma fita hayyacinsa.
~Bintu Ramadan~
*Dr Haneefah* 👩🏼61
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Da sauri Raihana ta taho tana mata sannu tare da tambayarta ko lafiya? Tace babu komai ta zauna. Kasa samun nutsuwa tayi ta soma ambaton LAHAULA WALAQUWWATA ILLA BILLAHIL AZEEN.
Ganin hankalinta ya karkata gida yasa ta mika hannu ta dauki wayarta ta soma kiran Umma, kusan sau biyar takira no answer, nan ta shiga kiran Ahmad shima baya daga wayar. Haneefah ta tsure gani take akwai abinda ke faruwa.
Tana kiran Abba bugu biyu ya dauka, ko amsa sallama batayi ba tace Abba lafiya inata kiran gida basa daga waya gashi sai faduwar gaba nake ji? Abba yace babu komai sai alkhairi Haneefah amma meya tadaki da tsakar darennan?
Ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah , Abba karatu nakeyi shiyasa na taso kasan mun kusa fara exams. Abba yace Allah bada sa'a ya rabaki da makarantar nan lafiya.
Ta cike da jin dadi ta amsa sannan tace Abba ka gaidamin dasu Umma.
Zataji amma inason sanar dake wani abu, ki daina fargaban komai ki kwantar da hankalinki domin yanzu ke matar aurece, dazu na daura auren ki, saboda haka saiki aje hankali kin zama matar aure.
Murya na rawa tace Abba aure akamin? Yace eh, na aikata hakan ne badan komai ba sai saboda kowa ya huta sannan in tabbatar musu cewa bana rike mutum azuciya ma'ana kada su zaci abinda sukamin yananan arai na domin hakan bai kamacemu yan adam ba, duk kankantar laifi bai kamata murikeshi a ran muba domin Allah S.W.A shi mai yafiyane sannan yana bamu damar kubcewa daga aikata wani abin hani
Saboda haka mu guji rike abu arai da son ramuwa ga abinda aka mana, shin duniyar ma nawa take? Yau mune wata rana bamu ba, mu rika saurin yafiya sannan kada inji in gani kince komai ga mahaifin yaronnan saboda itace sanadi, tunda lokacin yayi komai ya wuce kinji Haneefah.
A sanyaye tace Abba naji, kuma inshaa Allah zan kasance mai kawar dakai ga dukkanin wani laifi da akamin. Abba yace Allah miki albarka sukai sallama ya katse wayar.
Tana dauke wayar daga kunnenta kiran Umma ya shigo, tana dagawa ta fashe da kuka tana cewa Momy shikenan dan anje gaisuwa sai a dauramin aure...
Umma tayi saurin katseta da cewa ai da amincewarki kika turo shi hakan na nufin ur ready to get marriage, komai ma menene anyi auren sai fatan samun zaman lafiya sannan ina miki jan kunne da kada ki kuskura inji kincewa mahaifiyarsa komai domin babu komai ya wuce.
Cikin daurewar kai take tambayar Umma ni babu abinda mahaifiyarsa tamin hasalima ban taba ganinta ba, nidai munyi dashi kada lokacin ya tsawaita shine harda daurin aure
Umma tace nasan kina son Yusuf shima yana son ki, inaga abinda mahaifinki ya aikata yayi daidai.
Haneefah tace Yusuf kuma? Umma tace eh Dr Mubarak yayiwa mahaifan Yusuf jagora aka daura auren dazu, kada ki tada hankalinki kowa na farin ciki da wannan auren, ta wannan hanyar Allah ya kaddara daurin auren ki kada ki damu kinji?
Haneefah dakyar ta bude baki tace kina nufin da Yusuf aka dauramin aure Umma? Tace eh. Katse wayar Haneefah tayi ta sulale ta zauna kasa tana kuka tana dariya.
Raihana dake kallonta tace wai meke faruwa ne? Kallon Raihana tayi tace an dauramin aure da Yusuf dazu
Raihana ta dago hannayenta sama tana Alhamdulillah, Allah mun gode maka Haneefah kinga ni ko? Yarda da kaddara, hakuri akan abinda aka rasa akan lokaci, yawaita addu'a tare da yarda da addu'a gashi yau kin wayi gari kin samu abinda kike so.
Haneefah ta tashi ta shiga daki ta dauro alwala ta zauna kan sallaya tana murmushi tace Allah kaine abin godiya, duk wadda yaji tsoron ka ya so annabinmu ya rabauta daga kuncin duniya da lahira, kamin baiwar da dukkanin dan Adam ke bukata, sannan yau nawayi gari nakasance matar YUSUF, Allah na tuba ka yafemin.
Fashewa tayi da kuka tana cewa ya Allah nagode maka, duk wani musulmi dake tattare da kuncin rayuwa ka azurtashi da zuciya mai tsananin hakuri.... Haka ta kasance tana zantuka har aka soma kirayen sallar asuba.
Bayan ta idar ta dauki waya ta nemo layin Dr Mubarak domin tasan dare bayyi sosai ba a Nigeria. Bugu daya ya dauka suka gaisa, kasa cewa komai tayi kawai ta fashe da kuka.
Murmushi Dr Mubarak yayi yace shikenan Haneefah menene abin kuka? Godewa Allah zakiyi kuma kada ki damu dani domin komai ya wuce agurina, yadda na fahimci kuna son juna inna shiga tsakanin ku ban kyauta muku ba.
Cikin kuka tace amma ai dakai akafa.... katseta yayi yace babu komai Haneefah na fahimce ki, Yusuf yafi cancanta da ke kema kin cancanci kasancewa dashi, Allah baku zaman lafiya kedai pls ki karashi karatun ki kada ki damu.
Katse wayar yayi batare da tace komai ba, jingina yayi jikin seat na motarsa ya lumshe ido, tabbas yana jin son kasancewa da Haneefah amma yana son ganinta cikin farin ciki. Ganin yadda ya faranta mata sai yaji sanyi a ranshi tamkar an mishi bushara da aljanna *_( a kula aduk lokacin da mutum ya aikata aikin alkhairi kuma saboda Allah tabbas sai yaji ni'imtaccen al'amari ya ziyarci zuciyarsa)_*.
Haneefah ta lumshe ido tana matukar jin farin ciki a zuciyarta, ko bacci ta kasa komawa tsabar murna.
****
Kwance yake kan gado ya kurawa hoton ta dake laptop nashi ido. Wai yau shine mijin Haneefah? Allah mai yadda ya so a laokacin da yaga same. Abin kamar mafarki yaji. Tuno da irin soyayyarsu da burin kasancewa tare da sukeyi aka rabasu amma gashi yau lokaci daya sun mallaki juna.
Babu abinda yake bukata kamar yaji muryarta kuma yayi nesa da ita. Tambayar kanshi yake shin ya takeji domin yasan maganar yaje kunnuwarta. Lumshe ido yayi yana hangota tana aiki.
Ganin an kusa kiran sallah ya tashi ya shiga bandaki ya watsa ruwa tare da yin alwala. Shigan alfarma yayi ya dauki makullin mota ya fice. Bayan ya idar da sallah ya nufi gidan abokinsa Dr Abdullahi.
Parking yayi bakin gate ya ciro wayarsa yakira sa yace yana kofar gida, Dr Abdullahi yace kashigo daga ciki. A falo aka masa masauki.
Nana ta fito rike da waya a kunne tana dariya. Ganin Yusuf yasa ta dada fara'a tace ashe kanin nawa yazo dama nayi tsammanin zuwan ka.
Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi suka gaisa. Nana tace yanzu ake sanar da ni kai amma naji dadi Allah baku zaman lafiya. Dr Abdullahi yace ban gane Allah basu zaman lafiya ba.
Tace yanzu aka kirani a gida ake sanar da ni an daura auren Haneefah da Yusuf. Cike da mamaki yace Allah sarki amma nayi murna aboki Allah baku zaman lafiya ya amsa da ameen.
Tun kafin yayi magana Nana tace nasan lambarta kazo nema gashi nan. Yusuf duk kunya ta rufeshi, shi dai a dole kunyar Nana yake. Abdullahi abin ma dariya ya bashi yace kiyi hakuri girma ya hau kanki ki shiga daga ciki nizan bashi lambarta.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼62
Dedicated to Batul Mamman Mrs 💖
Nana tana dariya ta mike tashiga ciki. Tana shiga Yusuf ya tashi da sauri yazo kusa da abokin nashi ya fizge wayar hannun as yana cewa da wani suna kayi saving lambarta?
Abdullahi dake dariya sosai yace Sis Haneefah. Gudun kada yayi mistake ya tura ta WhatsApp yana cewa nagode nizan wuce.
Dr Abdullahi ya tsagaita da dariyar da yakeyi yace aa tsaya mu tattauna kasan yanzu mun zama so close, yanzu dai kabarta ta karasa karatun da kafin ku tare
Wani kallo ya watsawa Dr yace shekaru nawa muna jiran wannan rana? In ma taro ko occasions kuke son yi mun yafe, nasan dangi sun shaida aure ,saiku jira in muka haihu saikuyi komai.
Dr Abdullahi ya kuma kwashewa da dariya yace kada kayi haka, itama bazata ji dadi ba kabari sai tadawo Nigeria saiku tare aganina hakan zayyi amma yanzu da wanne zata ji? Ya qarasa maganar da zolaya.
Shidai Yusuf shiru yayi yana jiran isowar contact. Yana gani ya mike yana cewa nizan wuce mayyuwa bazamu hadu ba domin cikin satinnan zan wuce London. Abdullahi yana ta mishi tsiya akan kada ya soma amma ko kula abokin nashi bayyi ba.
Bayan ya koma gida ya nufi falon Abba ya tarar Momy na can. Murmushin jin dadi tayi da taga dan nata cikin walwala. Bayan ya gaida su sai kuma yayi shiru yana sosa keya.
Abba abu kadan ya fashe da dariya ya kawar da idanun nasa zuwa kallon tv. Momy da ta gano shi tsaf tace yakamata ka soma shirin tafiya can London ko zaka jirata tazo ne?
Karaf ya sako baki yace dama inason fara shiri gobene, shine nace bari inzo in sanar da ku. Momy tace ai hakan yayi kyau sai zuwa gobe ka shirya zuwa Abuja.
Yusuf ya kalli Abba dake kallon tv yace Abba gobe nake son wucewa. Abba yace Allah kiyaye hanya amma inason tarewarta yakasance inta kammala karatun ta, tunda kadan ya rage saika bari ta kammala amma zaka iya zuwa ku gaisa.
Toh shikenan ba komai Abba. Zai tashi Abba yace a gidan da kake zaune yanzu zaku zauna ko akwai wani plan naka? Aa Abba a sabon gidana.
Abba yace babu damuwa, zan karasa maka sauran ginin sauran shirin kuma mahaifiyarka da sauran yan uwanka yazu karasa cikin nutsuwa tunda har yanzu akwai sauran lokaci. Godiya Yusuf yayi ya tashi ya nufi sashin sa cikin sauri. Momy tabisa da kallon tana binsa da addu'a.
Ya gama shirin kwanciyarsa tsaf ya hau kan gado ya kwanta rike da pillow ya kurawa lambar ido. Shiga WhatsApp yayi ya duba lambarta yaga tanayi. Dp ta ya kurawa ido, itada Raihana, Kevin sai Rohan. Sunyi matukar kyau musamman Haneefah domin gani yake tafi mishi kowa kyau.
Wayarta na ringing harya katse bata daga ba domin bacci ya soma daukarta. Ganin an sake kira yasa ta dauki wayar da nufin ta sa a silent taga lambar Nigeria ne. Ganin batasan lambar ba yasa ta daga tare da yin shiru.
Shima shiru yayi. A hankali ta furta wanene? Shiru yayi ya lumshe ido jin muryarta. Ta sake maimaita tambayar tare da cewa banaji fa.. shima a hankali ya furta DEARIE
Idanuwanta ta bude baki daya jin muryar shi, ta nemi bacci ta rasa amma ta dake ta qara tambayar wanene? Murmushi yayi yace in hukunta ni zakiyi kada ki hukunta ni ta wannan fannin bazan iya jurewa ba.
Wani irin farin ciki ke ratsa illahirin gabobin jikinta, kasa magana tayi ta lumshe ido tana sauraronsa. Jin yayi shiru yasa ta fashe da kuka
Hankalinsa ya soma tashiwa yana tambayarta meya faru? Lallashin duniyar nan yayi amma taki shiru, ganin hakan yasa ya soma bata hakuri amma nan ma taki shiru, da kanta ta katse wayar ta kashe baki daya tana murmushin jin dadi.
Shima hankalinsa a tashe tunaninsa baki daya ya karkata gari ya waye ya soma shirin tafiya amma wannan daren bai iya runtsawa ba farin ciki sosai yake tare da godewa Allah.
Da safe dakyar ya kai karfe tara ya nufi gidan su Haneefah. A waje yayi parking yana kokarin fitowa yaga Ahmad da yaya jibril. Sallama ya fito yayi musu suka amsa. Bayan sun gaisa ne Ahmad ya mishi iso zuwa falon Abba shi ko jibril ya nufi gida sanar da Abba yayi bako domin gidansu ya kwana.
Kasancewar su Amal sun fita yasa Ahmad da kanshi ya kawo masa ruwa tare da yiwa Umma magana dake shirin fita aiki.
Har kasa ya sauko gaida Umma, Umma da fara'arta ta amsa tare da tambayar mutanen gida? Duk suna lafiya, ya qara da cewa Umma ina nemawa mahaifiyata afuwa.... bai karasa ba ta katseshi da cewa babu koma ya wuce, ai komai lokacine sai yanzu Allah ya nufa babu komai Allah hada zuciyarku ya baku zaman lafiya. Cike da murna ya amsa da ameen.
Sukai sallama ta fita. Bai jima ba Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya dauko da maganar afuwa Abba ya masa nuni da komai ya wuce fatan zaman lafiya ya musu tare da yi masa nasihar akan rayuwa baki daya.
Yusuf yaji dadin lafuzzan mahaifan Haneefah, hakan ya qara masa qimar Haneefah a idanunsa. Ya sanar da Abba yana son tafiya gurin Haneefah. Fatan tafiya lafiya da zuwa lafiya yayi mishi.
Agurguje yaje gida ya tattara abin bukatarsa ya nufi Abuja daukan excuse gurin aikin shi.
**** ****
Zaune take tayi shiru ta zubawa takar dun gabanta ido, duk da irin karatun dake gabanta hakan bai hanata tunanin sa ba. Meya hanasa kiranta? Sau daya ta gwada kiransa amma bai daga wayarba.
Raihana cikin tsokana tace an zama ma'aurata amma ana yawan tunani. Bata ce da ita komai ba ta dauki wayarta tayi dialing number shi amma bata samun sa. Ji tayi kamar ta jefar da wayar ta tarwa tse.
Suna cikin haka wata balarabiya ta nufo su ta sanar dasu lectures suke dashi yanzu.
Bayan ya sauka a airport batare da bata lokaci ba ya nema taxi domin yana da address dinta. Da murmushi ya nufo kofar ta ya danna qararrawa amma yaji shiru, ya dauki tsawon minti goma yana haka amma ya tabbatar babu kowa domin ba'a bude kofar ba.
Nesa da gidan kadan yayi yanemi guri ya zauna yana kallon mutanen da suke zarya. Kusan karfe tara na dare babu alamarsu gashi gajiya da yunwa ta addabeshi, ruwa ya ciro cikin kayansa ya sha.
Karfe tara da minti arba'in suka yi parking. Sunzo daidai zasu shiga Raihana ta ja ta tsaya ta hangosa yana bacci kasancewar gurin haskene tamkar rana.
Haneefah ma ta tsaya tana kallon inda Raihana ke kallo, da sauri ta mika mata takardun hannunta ta nufo shi da sauri. A zaune yake ya lumshe ido tamkar mai bacci, tausayinsa taji ganin wahala tattare dashi a tunaninsa bacci ya soma.
Tsugunowa tayi tana tunanin yadda zata tashi daga bacci, jin motsi yasa ya bude idanunsa a hankali yana kallonta. Da sauri ta mike zata juya shima ya mike da sauri ya fara binta amma yakasa cewa komai.
Juyowa tayi