Showing 57001 words to 60000 words out of 74305 words

Chapter 20 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5184

sanda damuwarma take damunsa ba, amma yaci damarar mancewa da komai insha Allahu.


Tsawon kwana uku ya dauka baya fita ko ina, Dr Abdullahi yana zuwa yana dubashi haka ga kannensa ma suna tare dashi. Momy ajiye aikinta tayi tace zata kula da danta. Kyakykyawar kulawar da yake samuwa ne yasa yadan warware. Abba ganin dan nasa ya warware yasa ya sauko daga fushin da yake hakan yayi wa yaran dadi domin tun tasowarsu basu taba ganin rashin jituwa tsakanin iyayen nasu ba.


Bangaren Nana kuma mamakin abinda Haneefah ta aikata take. Kullum cikin kiranta take amma bata dagawa, tayi mata text amma shiru ba replay. Kamar kullum takira yau taci sa'a ta daga wayar ko sallama bata gama yiba Nana tace yayi miki kyau yau kwana uku tukun kika daga wayata.


Haneefah tace lectures muke fa bana samu dama, lokaci da nake free kuma inna kira kina bacci shiyasa bana kira. Nana tace nayi mamakinki Haneefah dama duk cika baki kike? Da kanki kaka amincewa Mubarak? Suna cikin magana batery Haneefah ya mace, Nana ta dauka katse wayar tayi baki daya, a hankali tace zaki gamu dani.


Da dare Abba da Yusuf suna zaune suna tattaunawa tare da kallon Yusuf mai gadi ya shigo yace ana sallama da Abba, Abba yace ya shigo Yusuf ya tashi zai fice a bakin kofar shigowa falo suka ci karo da Dr Mubarak.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼57


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Murmushi tashigayi ta bashi hanya ya wuce. Da sallama ya shigo Haneefah na biye da shi har falo. Ganin Yusuf yasa yadan tsaya ya waigo yana kallon Haneefah alamar tambaya.


Batare da cewa komai ba ta wuce kitchen kawo masa ruwa. Bayan ta dawo ta tarar babu Raihana ta shiga ciki shida Yusuf suke gaisawa.


Ta dire try dake hannunta ta zauna kan kujera tana gaishe da Dr Mubarak, ya amsa da fara'a. Haneefah tace saukan yaushe? Yace ban jima da sauka ba nace babu hutu zuwan naki ne bari na biyo tanan kafin na wuce masauki.


Haneefah tace kayi sa'a domin zamuyi tafiya nan da awa biyu masu zuwa insha Allah. Dr yace zuwa ina? Sanar dashi inda zasu da kwanakin da zasuyi ta sanar masa.


Yace babu damuwa nazo na tarar dake da bako. Tace eh, abokin mijin Nana ne yazo checkup asibitin mune yayi masauki anan.


Dr Mubarak yace Allah kara lafiya. Ya kalli Haneefah sosai yace dama bazan wuce kwana uku ba sannan inason magana dake.


Tun kafin suce dashi komai Yusuf ya mike ya basu guri. Dr yace nagaji sosai jin zakiyi tafiyane zan sanar dake, naje gun Abba yabani izinin auren ki amma yace sai na nemi izinin ki, pls Haneefah kin kusa gama makaranta ki bani dama in mallake ki pls! Wadda kike ganin baki kyauta mata ba tana farin cikin kasancewa da ke matsayin kishiya, bansan mesa kike kin aure na ba. Na miki alkawarin rikon ki da amana tsakani da Allah ki bani dama.


Shiru tayi tana sauraronsa. Wanna karon dole ta amince masa, dago ido tayi tace na amince, Allah tabbatar mana abinda yafi akhairi amma bana bukatar zama gida daya da barrister.


Cike da farin ciki Dr yace indai wannan ne bani da matsala, in akwai wani abinma ki fada inajinki.


Tace bana so auren ya dauki lokacin da saina gama makaranta daz ol, inaso inje in fara tara kaya lokaci yana tafiya.


Cike da farin ciki ya mike yace indai wannan ne babu matsala na gode sosai, sai munyi waya pls take care of ur self. Murmushi tayi har bakin kofa ta rakasa.


Rufe kofa tayi tana share hawayen da ya makale mata. Tana cikin yanayin nan ta ganshi ya fito dauke da jakarshi idanunsa sun kada sunyi sha yace nagode da abinda kika min amma ki sani har yau har gobe ina kaunar ki, ina miki fatan samun zaman lafiya gidansa, zan bar miki gida... kasa cigaba yayi ganin hawaye na neman sauko masa ya bude kofa ya fice.


Gudu tayi ta nufi daki ta kwanta kan gado tana kuka. Raihana dake hada musu kaya tace subhanallah! Meya faru? Haneefah tace baisan hukuncin dana yanke shine daidai ba, i love him wit ol my heart, nima bazan daina son ka ba sai dai lokaci yayi dazan hakura dakai ko naki ko na so.


Raihana da kanta ya daure tace ban gane abinda kike nufi ba. Haneefah ta sanar mata komai tace inaga ya saurari duk abinda muke tattaunawa da Dr Mubarak ne.


Raihana ta tashi tana mai ambaton innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun! Haneefah kinsan abinda kika aikata? Momy ta amince da auren ku yazo domin sanar dake zaki bawa wani damar auren ki?


Cikin sauri Haneefah ta taso ta dawo kusa da Raihana tace kina nufin Momy ta amince da auren mu ta janye kudirinta?? Nashiga uku me na aikata haka Raihana? Naga rashi naga samu, jin jiri yana neman daukarta yasa ta zauna bakin gado tana rera kuka.


Daukar waya tayi zata kira Nana taga wayarta ya shigo, da sauri ta daga tace Nana nashiga uku, ki tabbatar min maganannan in gaskiyane? Nana tace it's ok nasan bazai wuce akan Yusuf bane yanzu haka ina tare da Sister shi Aisha wadda ta sa miki takwara, Haneefah ki godewa Allah soyayyarku ta dawo.


Katse wayar tayi ta fashe da kuka tana cewa nashiga uku MEKE FARUWA dani ne? Dashi nake kwana dashi nake tashi tsawan shekaru da dama ina addu'ar daidaitawa tsakanin mu amma gashi yau ka zo gareni rashin sauraron ka ya jamin, nashiga uku. Raihana ki taimakeni ji nake kamar zan mutu, bana kaunar zaman duniyar nan.


Da sauri Raihana tace shiru Haneefah babu kyau irin wadannan kalamai, kada ki manta hakan kaddarar kine,imani da qaddara, yana cikin ruku nan Imani guda shida, wanda imanin bawa baya cika ya inganta har sai ya samu karbuwa a wajan Allah har sai ya yarda da Qaddara mai kyau ko marar kyau.


Ibn Umar R.A yana cewa:
"......Na rantse da Allah da dayansu zai ciyar da misalin dutsen Uhudu na Zinare Allah bazai karba ba har sai sunyi imani da qaddara mai kyau ko marar kyau...."
@Muslim


Imani da Qaddara yana nufin:
"Yarda da amincewa lallai dukkan abubuwa da suke gudana tun daga farkon duniya har zuwa karshenta, Allah ya sani kuma shine ya tsara faruwarsu, sannan ya rubuta hakan acikin LAUHUL MAHFUZ, sannan suna faruwane da ganin damar Allah kuma yadda ya tsara, sannan shine wanda ya halicci dukkan aiyukan bayi mai kyau da marar kyau.


Yarda da wadan nan abubuwa da sallamawa da gaskata su shine Imani da Qaddara.


Imani da Qaddara ya kunshi Martabobi guda Hudu-(4):-
i-Ilimi
ii-Rubutawa
iii-Mashi'ah
iv-Halitta.


1-Martaba Ta farko
"MARTABAR ILIMI"
Shine mutum yayi imani Lallai tabbas Allah yasan dukkan komai, a dunkule da dayday kunsu, ya san abinda ya faru tun farkon duniya, kuma yasan abubuwa da zasu wakana nan gaba har zuwa ranar alqiyama dama abubuwa da zasu biyo bayanta,da abinda yake faruwa yanzu da abinda ma bazai faruba da zai faru Allah yasan yadda zai faru.


Allah yana fada:


"(Wanda Ya saukar da Alƙur'ani) Shi ne Allah, wanda bãbu wani abin bautãwa fãce Shi Masanin fake da bayyane, Shĩ ne Mai rahama, Mai jin ƙai.


(Allah, wanda Ya halitta bakwai ɗin sammai kuma daga ƙasã kwatankwacinsu, umuruinSa yanã ta sauka a tsakaninsu dõmin ku san lalle Allah Mai ĩkon yi ne akan dukan kõme, kuma lalle Allah, haƙĩƙa Ya kẽwaye ga dukan kõme da)


(Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra ba ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma ba ta nisanta a cikin ƙasa, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin masu imani)"


Sannan duk mai son ya samu imani, to ya rinka la'akari tare da tunani game da ayoyin Allah da HalittunSa.


Duk mai son ya rayuwa cikin nagarta da mutunci, to ya rinka fadin gaskiya da aiki da ita.


Ke alkawari kika rike na mahaifiyarsa amma yana dakyau arika sauraron uzuri, sannan amincewa da auren Dr Mubarak nemawa kanki lafiyane domin lalurar da kike tattare dashi, kada mu biyewa so a komai na rayuwa mubarwa Allah zabi.


Haneefah ta share hawayenta tace yanzu shikenan zanci gaba da danne zuciyata na tabbata barin kaina da zuciyata a hannun Allah babban sadaukarwa ne domin na tabbata saiya jarabce ni amma na tabbata alkhairi yake nufi gareni.


~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼60


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Yusuf ya tsaya da mamaki yana kallon sa. Dr Mubarak ya mika masa hannu suka gaisa yace mu shiga daga ciki. Jiki a sanyaye Yusuf yayi gaba Dr na biye dashi.


Bayan sun gaisa da Abba yace nasan bazaka ganeni ba amma shi Yusuf ya ganeni, nine wadda nake neman auren Haneefah wadda shekarun baya aure tsakanin su bayyu ba.


Abba yace Na'am ina sauraron ka. Dr yaci gaba yace lastweek na hadu da Yusuf a gidan Haneefah, wadda a wannan lokacin bansan shiba sai kwanaki dana zurfafa bincike a kanshi.


Ya dubi Yusuf yace lokacin da na karashi maganata da Haneefah game da aure a London na fita, na komo da sake tattaunawa wani abin da ita na ganka ka fita a gidan ranka a bace da alamar kana hawaye, ni kuma bin yaban mamaki ban tsaya na tambaye kaba sannan baka kula da komai dake gaban ka.


Bayan nashiga gidan na wuce dakinsu, maganar da naji ke fita abakinta yasa na dakata nake sauraron su. Tabbas halin da tashiga taban tausayi haka kaima. Anan na fahimci kuna tsananin son juna. Bayan na koma masaukina nake nazarin kalamun Haneefah game dakai.


Bayan na dawo gida batare da bata lokaci ba na wuce gidansu, ina shiga layinsu na hango yayanta Ahmad nan na tsayar dashi nake tambayar tarihin rayuwar soyayyarta, nan ya sanar da ni komai ba tare da ya boyemin komai ba saboda nazamo family member su. Na tausaya Haneefah sosai sannan shi Yusuf na tausaya mishi domin suna son juna raba su akai.


Haneefah tamin abinda bazan manta da itaba, kuma naji dadin zama da ita hakan yasa naji inason kasancewa da ita da kula da ita. Ta taimakeni lokacin da muke bukata, taimakon da duk dukiyata bazatai minba, wasu suna ganin kudi shine jin dadin rayuwa, wasu suna ganin rashin sa ke hanawa . Rashin kudi bai hana jin dadin rayuwa. Abinda ke hana jin dadinta shi ne rashin hakuri da rashin wayewa da rashin sanin ya kamata Allah yasa mu dace.


Ya basu labarin yadda suka hadu da Haneefah, ni da matata muna sonta sosai, a kullum muna neman abinda zamu kyautata mata. Yusuf nasan inason Haneefah amma kafini sonta, ka fini bukatar ta sannan ina da tabbacin zaka kula da ita, na bar maka Haneefah ka aure ta.


Tunda ya fara magana kan Yusuf sunkuye yake yana jinjina lamarin masoyiyarsa sai da yaji an bar masa Haneefah ya dago kai da sauri yana kallon doctor, ya dubi Abba yace dagaske ya barmin ita?


Abba ya dubi dan nasa ya gyada kai sannan kallonsa ya koma kan doctor yace lallai wannan al'amarin akwai ban mamaki ciki, kaganshi akanta yake fama da rashin lafiya gaskiya nagode da wannan sadaukarwa Allah saka da alkhairi.


Yusuf ya taso yazo gaban Dr ya tsuguna yana kallonsa, hawaye yaji yana kwaranya a idanunsa a hankali ya tashi ya rungumi doctor yana cewa mun gode doctor, hakika imanin ka cikekkene domin ka so min abinda ka sowa kanka, Allah shi kadai zai saka maka na gode.


Doctor ya dago shi yace babu komai dan uwa, Allah baku zaman lafiya ku kasance tare anan duniya da can lahira.


Yusuf ya rasa abinda zayyi don farin ciki kawai ya yashi ya fita ya nufi asashen sa. Yana shiga ya kwanta akan gado yana addu'ar Allah mallaka mishi abin kaunar sa, inya runtse ido ita yake kallo. Tashiwa yayi ya dauki sallaya yayi sujjada yana godewa mahaliccin sa.


Bayan fitar Yusuf Abba ya dubi doctor yace yanzu bansan da wani ido zan dubi mahaifin yarinyar nan ba, irin wannan abin haka...


Doctor yace kada ka damu, za su fahimce ka sannan bazasuyi jayayya da lamarin ubangiji ba, in har ka shirya gobe zan shiga muku gaba wajen neman auren Haneefah. Abba godiya sosai yayiwa doctor sukai sallama.


Washe gari misalin karfe uku na rana Abba da abokinsa da yan uwa biyu sukaje neman auren Haneefah. Kamar yadda doctor ya fada dashi akaje neman aure.


Abban Haneefah yana zaune yanajin labaru a radio yaji sallama, kasancewar babu kowa gidan sai su Amal da kanshi ya tashi ya fito yaga Dr Mubarak. Da fara'a yace ya shigo daga ciki.


Dr ya mase bayani da ba ki yake, Abba yace ya shigo dasu. Abba na kimtsawa sukai sallama suka shigo.


Bayan an gaggaisa Abba ya fito yace da Amal yayi baki ta kawo musu abin sha. Cike da kunya abban Yusuf yace ina fatan ka ganeni? Murmushi abban Haneefah yayi yace ai bazan mance ka ba, nagane ka.


Cike da kunya yace yauma bara muka so ina fatan sa'a taimaka mana, mu mance da abinda ya faru domin haka Allah ya kaddara amma yanzu komai ya wuce.


Dr Mubarak yace Abba kada kayi mamaki da ikon Allah, na barwa Haneefah Yusuf domin zuciyarsu a hade take tun fil azal, muddin sun kasa mantawa da juna tsawon shekaru bana tsammanin zasu mance da juna, in zamu musu adalci mu barsu su kasance da juna.


Abba yayi murmushi yace hakika ban rike kai ko Yusuf ba domin na dauka cewa hakan shine mafi alkhairi agaremu amma mesa zaku nemi aure kan aure? Dr Mubarak yace ko daya babu laifinsu anan ni da kaina na yanke wannan hukunci.


Abba yace toh shikenan amma indai neman aure kuka zo dagaske yanzu a daura domin bazan jinkirta ba wannan karon.


Batare da bata lokaci ba suka amince, Abba ya kira yan uwansa da mijin mama da Ahmad. Bayan an fito daga sallar la'asar a masallaci aka daura aure abokin Abba ya biya sadaki. Sunyi godiya sosai sannan sun nuna farin ciki.


Abba yana zuwa gida ya sanar da Umma, taji farin cikin wannan aure. Nan takira aunties nata take sanar da su, sunyi mamaki sosai musamman Nana cewa tayi hakurin su ne ya ja musu auren ba zata amma zamu so ta tare bayan tagama karatu.


Da sallama ya shigo ya tarar da family shi sunsa Yusuf agaba suna ta faman hira, shiko ogan rike yake da Ra'ima yana mata wasa amma hankalinsa yafi karkata da zuwan abban nasa. Abba nashigowa da sauri Yusuf ya tashi yana mishi sannu da zuwa har dariya yabawa Abba, cike dajin kunya ya koma ya zauna.


Bayan sun zauna Abba ya dubi Momy yace toh Alhamdulillah yanzu aka daura auren Yusuf da Haneefah. Ba Momy ba har Yusuf saida ya dago tsabar mamaki.


Momy tace wanne Yusuf? Abba yace Yusuf wadda ke gaban ki da Haneefah da kika ki amincewa da auren su toh yau Allh yakawo lokaci naga kokarin mahaifinta domin ko jayya bayyi da mu ba nan ya kwashe abinda sukai ya sanar da su dan haka sai a soma shiri sannan bana bukatar jin wani magana daban.


Kowa idanunsa nakan Yusuf, tsantsar hawayen farin ciki suka hango cikin idon nasa. Rarrafawa yayi ya taho kusa da Abba yace Abba an auramin Haneefah? Abba ya gyada mishi kai.


Zama yayi ya rungume kafan Abba yana cewa nagode Abba, Allah saka da alkhairi Allah albarki zuri'armu ya sadamu gidan aljanna baki daya... Abba bansanme zance ba Abba.. Momy ta taho a hankali tace babu abinda ya cancanceka kamar ka godewa mahaliccin ka, kayi hakuri iya hakuri amma gashi hakurin ka ya amfane ka, ina tayaka farin ciki samun mata kamar Haneefah.


Haka kowa daya bayan daya yake zuwa tayashi murna amma shi ko murnar ne ta mishi yawa ya kasa cewa komai? Haka Momy da yaranta suka kasance cike da farin ciki a wannan yammaci tare da shirye shiryen yadda amarya zata tare.


**** ****


Zaune take kan doguwar kujerar da ke falon su, dayar kujerar kuwa Raihana ke zaune tana duba littafi. Kwanakin da sukai a Chicago babu abinda ta tsinana duk tayi abinda ya kaita amma yadda jikinta yayi sanyi batabi abin yadda yake ba. Ko da yake babu ta korance a fannin karatun ta,domin in sun shiga meeting da sauran likitocin asibitin Dr Michael tana koyan abubuwan da dama har wadda suka dara level nata. Haka yakasance a Chicago yawancin abubuwan ta sansu.


Ta rasa tunanin me zatai daya, mukewa tayi taje daukar littafinta domin ta soma karatu. Daidai zata zauna taji faduwar gaban da sai da ta sake takardun hannunta suka fadi taje mai ambaton innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun tana mai dafe zuciyarta da hannu.




~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼58


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Raihana tashiga rarrashinta tace ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru kinji? Allah yana tare dake kinga yanzu jarabawa mukasa agaba dan haka saiki kwantar da hankalin ki mu soma karatu.


Haneefah babu abinda take sai hawaye, a haka suka fita zuwa makaranta dan lokaci yayi.


****


Aisha cikin nasara ta soma bincike, gidan Nana ta fara zuwa. Bayan sun gaisa ne take cewa sister Yusuf ne.


Babu yabo babu fallasa Aisha ta amsheta. Cikin nutsuwa Aisha ta shawo kan Nana sannan tana neman alfarman dawo da Yusuf da Haneefah tunda har yanzu suna son juna.


Nana batai mamaki da lamarin ubangiji ba domin ko da zasuyi fishi dasu hakan zai zamo aibu domin abin yariga ya wuce sannan Haneefah bata daina son Yusuf ba. Fatan alkhairi ta musu sannan takira Haneefah.


Aisha taji dadin yadda ta samu karbuwa ba tare da bata lokaci ba, nan ta sanar da ita ai diyarta takwaran Haneefah ce. Cike da farin ciki Nana ta karbi Ra'ima tana sa mata albarka.


Ta nuna farin cikinta kwarai,sukai exchanging number, zasu tafine Nana tace ki sanar da Momy kada halin da ake ciki domin Haneefah fa ce ta nemi alfarman in yazo ace tayi aure amma ni da kaina zanje in same su ko zuwa gobe. Aisha taji dadin hakan, basu so suka bar gidan ma.


Washe gari Nana da kanta taje ta sanar da Umma, Umma tace Alhamdulillah nasan har yanzu suna son tunda mahaifiyarsa ta amince ai shikenan akan ta auri wannan Dr Mubarak domin har wajen Abban ku yazo neman aure.


Nana ta zaro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login