Showing 66001 words to 69000 words out of 74305 words
Chapter 23 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
kasance tare matsayin ma'aurata, burina ya cika arayuwa, bayan mun fidda rai a mallakan juna sai gashi yau mune abu daya, gaskiya bazan so nesa da ke ba amma zan baki daman karasa karatun ki in yaso nizan koma in soma shirin tarewar mu amma zan rika kawo miki ziyara immediately kina gama mkaranta sai mu kasance tare.
Babu shiri Haneefah ta soma hawaye. Ganin haka Yusuf ya rikice yace menene? Bakya son na koma? Zan zauna it's ok stop crying. Haneefah tace ni dan Allah ka fahimce ni nasaba karatu ni daya, zanzo na kammala ni daya kuma inna koma gida ina son hutu kamin na tare gidan ka.
Tsaf ya gano ta yace hutu kamar zuwa yaushe. Haneefah tace inna koma gida kamar 5-6months.
Mikewa Yusuf yayi ya taso yazo kusa da ita yace in kyaleki ki gama makarnta ke kadai kuma in barki a gida wata biyar kina matsayin matata? Fashewa tayi da kuka tana gyada kai alamar eh. Yusuf yace ya salam! Shikenan naji hkan kika fi so hankalin ki zaifi kwanciya tace eh. Yace shikenan tare da mikewa yaje ya zauna wani bankare daban.
Ganin haka yasa ta tashi ta fice a dakin, binta yayi da kallo azuciyarshi yana mai cewa nidai ba iyawa zanyi ba.
Bayan ta koma daki ta tarar Raihana na bacci. Tajo plate na abinci ta soma ci tana murmushi. A zuciyarta tace ya Allah nagode maka, amma bansan mesa nake kunyarsa da yawa ba? Kwata-kwata na kasa sakin jiki dashi. Murmushi tayi data hango rashin amincewa a fuskarshi. A haka ta kara shi cin abinci ta zauna zuwa minti goma sha biyar tukun muke ta maida plate kitchen itama ta zo ta kwanta ta soma bacci.
Sai bayan la'asar suka tashi. Saida sukai wanka domin samun karfin jiki sannan sukai sallah. Bayan sun idar suka zauna shiru domin kowa gajiya tattare dashi.
Raihana ta dubi Haneefah tace ke bazaki je gun mijinki bane? Ko kallonta batai ba bale ta bata amsa. Raihana ta kuma cewa innine fa zan bar muku gidan. Nan ma bata ce komai ba ganin haka yasa itama tayi shiru da bakinta. Sai kuma suka dauko hiran karatu.
*8:30pm*
Dauke take da try, knocking daya aka bata izinin shigowa. Zaune ta samesa kan sallaya yana waya. Tana ajewa zata fita ya mata nuni da ta tsaya. Nesa dashi ta zauna ta sunkuyar da kai.
Bayan ya kammala cike da nutsuwa ta gaishe shi. Amsawa yayi yana murmushi, baice komai ba ya zuba mata ido kamar mai nazarin wani abu.
Ganin yayi shiru ta dago idanunta karaf suka hada tayi saurin sunkuyar da kanta. Allah-Allah take tayi sallama dashi batare da yayi mata komai ba.... tana cikin tunani taga ya ta so a inda yake ya nufo ta...
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼65
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Ganin yazo dab da ita ta nannadu guri daya kamar taga wani abin, shi abin dariya ma ya bashi anan ya fahimci tsananin tsoro tattare da ita.
A hankali yace Dr HANEEFAH! Duk da cike take da tsoro hakan bai hanata tsananin jin dadi yayin kiran sunanta ba, ji take tamkar shi kadai ya iya kira. A hankali ta dago kai amma ta kasa hada ido dashi.
Yace shikenan ina tare da matata amma sai in tafi in barta, kimin adalci ki bari na ci gaba da zama dake hankalina zaifi kwanciya.
A hankali tace ni fa banqi zaman ka ba, ayyu kan ka kuma ni karatuna.... ta karashe maganan cike da soma kukan shagwaba.
Yace shikenan naji but nikam zan rika zuwa kuma tare zamu rika kwana da matata a daki daya.... tun kafin ya qarasa ta turo baki ta soma hawaye. Shiru yayi yana kallonta.
Mikewa tayi ta soma zuba masa abinci, har gabansa ta kawo ta ajiye zata tashi ya jawota ta fada jikinsa.
Riko sosai ya mata ya soma mata rada a kunne ina zakije? Nagaji da kwana ni daya yau da ke zan kwana. Lamo tayi jikinsa tace kamin afuwa mubar kasarnan kafin mukasance tare dakai daki daya, kada ka manta mu biyu ne a cikin gidannan, kuma karatuna yazo karshe kullum nake cikin karatu yanzu haka karatu Raihana take na barota, amma in kana son in kara maimaita shekara daya ne zanyi yadda kace amma bawai nima inason nesa dakai bane, inka sabarmin bazan iya ci gaba da karatu ba.
Da gota yayi yana kallonta, tana dago idanunta yace mai wayo, na fahimce ki. Zan koma gida in soma mana shirin inda zamu zauna kema saiki karasa karatun ki amma kina gamawa a gidana zaki sauka...
Zatayi magana ya rufe mata baki da nashi, dakyar ta kwaci kanta ta gudu tana cewa cikin zuciyarta saika kara ganina ai. Kamar yasan abinda take fadi ya fashe da dariya yace zanga yadda zakiyi in muka koma gida.
Kwanan sa uku ya soma shirin tafiya domin gurin aikin sama na bukatar sa sosai sannan yana son yaje ya soma shirin inda zai saukar da amaryarsa, babu yadda zayyi domin Haneefah ta dage saiya koma gida.
Har airport ta rako shi a motar ta, zata fita yayi saurin riko hannunta ta juyo suka hada ido, tayi saurin kawar da kanta domin duk sanda suka hada ido sai taji wani irin abu mara misaltuwa.
A hankali yace ina sonki sosai Haneefah, pls take care of ur self. Murmushi tayi ganin yana matsowa tayi saurin fitowa ta zagaya ta zo ta bude mishi kofa. Qin fitowa yayi, ko kallon inda take bayyi ba.
Zuwa tayi gabansa ta durkusa tare da kamo hannuwan sa tace nima inason ka sosai... da sauri yace naaqi ai ban karasa ba kika fito.
Murmushi tayi tace kada kayi missing flight naka! Yace in baki komo mazaunin ki ba sai dai inta zama anan. Bata son musu domin zai aikata yasa ta tashi ta zagayo tashiga ta zauna tare da sunkuyo da kanta.
A hankali yasa hannu ya dago fuskarta ya manna mata kiss a goshi sannan ya bude mota ya fito ya zagayo ya bude mata. Da murmushin jin dadi ta fito. A hankali suke taku har suka shiga sai taji kamar kada ya tafi, shima Yusuf daurewa yayi.
Saida taga tashiwarsa sannan ta koma gida. Yinin ranar bataji dadi ba sai da taga kiransa ya koma gida lfy kafin ta runtsa ta samuyin bacci.
Cikin taimakon Allah ya soma shirin sa, Abba ya dauki nawin duk wani irin gini yake bukata a birnin tarayya. Can gida kano ma aka fasa sashin Yusuf aka masa gyara sosai.
Kowa na murna da bikin Engineer Yusuf da Dr Haneefah.
**** ****
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, a yau ake yaye daliban kiwon lafiya dake jami'ar Oxford university London. Kowa cike yake da farin cikin wannan rana musamman dalibai.
Raihana tare take da mahaifanta sai yayanta, hannunta na cikin Haneefah domin kada ta ji wani irin yanayi amma duk dauriyar Haneefah sai da taji tana sha'awar ganin mahaifanta a wannan rana.
Makaranta ta soma nuna farin cikinta a game da dalibai da suka nuna kwazo da sukai karatu kan gaskiya... sannan ta bukaci dalibai guda uku da suka cancanta yabo agun illahirin malamai da maarantar baki daya.... Haneefah da Raihana aka kira abinda basu taba tsammani ba duk da sunsan ana ji dasu a bangaren su amma basu dauka dukkanin makaranta na Alfahari dasu ba.
A hankali suka taso suna tafiya har suka iso gaban taro, sai wani bature mai suna Felix. Sun samu kyaututtuka da dama har Haneefah ta kasa hakura ta soma kuka. Raihana na lallashin ta, aka bukaci kowa yazo dan uwanshi.
Nan Haneefah tayi shiru, Felix matar shi ce ta fito, Raihana kuma yayanta har akazo kan Haneefah. Sun kuyar da kai tayi kamar daga sama taji muryar Ahmad.
Da sauri ta dago kai tana kallon sa da mamaki. Bayan ya gama yazo gurinta da sauri tana farin ciki ta kama hannuwan sa tace Ahmad kaine? Yana dariya yace eh nine.
Zata kuma magana taga Dr Mubarak shi da Bar. Ramlat. Daga bayansa kuma Umma da Abba sai Yusuf dake biye dasu. Tana hawaye tana murna, da gudu taje ta rungumi Umma tana kuka. Dakyar Umma ta dagota tana ya'isa haka
Ahmad dake gefen Umma yace in bakiyi shiru ba zamu koma inda muka fito, dagowa tayi da sauri tana share hawayenta tace ashe zaku zo? Abba yace Umma da Ahmad kika sani ko?
Haneefah tayi murmushi tace Abba banyi tsammanin zuwan ku ba, nan ta soma gaishe su. Suna gaisawa kafin tazo gun Yusuf Raihana ta iso itada mahaifanta suna gaida su Umma, Haneefah ta gabatar da iyayen Raihana ga su Umma.
Bayan sun sami guri sun zauna da mintuna kalilan aka yaye su Haneefah daga makaranta. Bayan an kammala aka soma dauka hoto anan Haneefah tazo gaban Dr Mubarak da Bar. Tana cewa nagode sosai da gudunmuwarku a rayuwata, bani da bakin gode muku sai dai in tayaku da addu'a, nagode sosai...
Bar. Tace babu komai Haneefah, Allah qara mana zumunci. Shiko Dr Mubarak bai iya cewa komai ba sai murmushi domin farin ciki sosai yake da karatun Haneefah.
Suna gama dauka hotuna saura Yusuf, tsaye yake daga gefe yana kallon ta. A kunyace take kallonsa har ta karaso inda yake. Shiru tayi yana kallonta ya cije lebe yace zaki gamu dani ai.
Yayi gaba ta bisa a baya tana dariya kasa-kasa. Bayan sun gama komai suka kamo hanyar zuwa gidan Haneefah tare da Raihana da yan uwanta.
Suna shiga suka ga Kevin da Rohan suna shirya abinci. Haneefah ta tsaya da mamaki tana kallon Rohan tace yaushe kazo? Yace tambayi Raihana.
Raihana tana dariya tace nasan da zuwan dukkanin su kawai sunce nayi shiru kada na sanar dake ne.
Wannan ranar yana daga cikin ranaku da Haneefah da bazata taba mancewa ba, musamman inta tuno da yau ta kammala karatun ta, ta kasance matar YUSUF abin ba qaramin dadi yake mata ba.
Yusuf duk yadda ya so su hada ido da Haneefah hakan baya yiwuwa, harya gaji ya zuba mata ido. Sun zauna cin abinci Yusuf ganinsu Umma yasa yaji bazai iya ciba, Dr Mubarak ya fahimce shi dan haka ya kalli Haneefah yace nida Yusuf, Kevin da Rohan da yayan Raihana ku kai mana daki acan zamu ci.
Abba baice komai ba dan yasan dalili. Kamar yadda akace dasu haka akai, mazan suka tashi suka shiga ciki inda aka shigar musu da abinci.
Haneefah tana kokarin shiga falo taga anja hannunta zuwa dakin dake dab da shigowa................
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼67
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Tsaban rudewa ya kasa magana, babu abinda bai mata amma ko motsawa bata yi. Cike da tashin hankali ya bude motar yazo mazaunin driver yaja ya soma tafiya. Yana tafiya yana waigawa yana kallonta. Ikon Allah kadai ya kawo shi asibiti, ko gyara parking bayyi ba ya fito ya.
Dr Mubarak dake kokarin fita a asibiti yaga babu hanyar wucewa, fitowa zayyi yayi magana a gyara parking yaga Yusuf na ciro Haneefah cikin mota ko motsawa bata yi. DA sauri shima ya fito ya nufo gunsu yana tambayar lafiya?
A sannan Yusuf ya bude baki yace Mubarak Haneefah ce... sai kuma yakasa cewa komai. Cikin sauri Dr Mubarak ya bashi izinin biyoshi.
Tsananta bincike yayi sosai akanta, kusan awa daya yayi kafin ya gano abinda ke damunta. Tsananin mamaki ne ya cika Dr Mubarak yana kallon Haneefah da bata san inda take ba. Yana kokarin fita Haneefah ta bude ido dakyar tace na rokeka da girman Allah ya zamto lalurata sirrine tsakanina dakai, sannan ta sanar masa allurar da take amfani dashi.
Shiru yayi yana kallonta baice komai ba ya fice nemo allurar. Yusuf da tunani fal yacika masa zuciya ya rasa mezayyi, yana kai komo yaga Dr Mubarak ya fiti. Da sauri ya nufi gunshi... tun kafin yace komai yace ka kwantar da hankalin ka zata samu sauki yanzu zanje siyan allurane.
A hankali ya turo kofar ya shigo, hangota yayi ta dafe kasan mararta tana hawaye. Da sauri ya nufota yana mata sannu, ta kasa bude ido taganshi tsabar azaban da take ji. Yusuf ji yake tamkar ya cire ciwon ya mayar jikinsa. A hankali ya zauna gefenta yana mata sannu. Ganin ta kankame hannunsa ta fashe da kuka yayi, rungumeta yayi yace shikenan yi hakuri pls..
Dr yashigo dauke da allura yana sauri, Yusuf yace an kawo allura bari asaka miki kinji zaki samu saunki. Haneefah ko jinsu bata yi domin wannan karon har wani irin abu take ji, kuka sosai take. Yusuf ya soma gyara ta domin asa mata allurar amma gani sukai ta sake faduwa sumammiya.
Saida Dr Mubarak yayi kokarin cire Yusuf kafin ya soma bata taimako. Alhamdulillah ta samu bacci, dan haka ya fito domin sanar dashi halin da take ciki. Bayan ya sanar da Yusuf yace yana zuwa ya fice.
Zaune yake ya zuba mata ido, tsoro ne kodai bata da lafiya? Yana cikin tunani kiran Dr Abdullahi ya shigo wayarsa. Ganin agogo yayi karfe goma sha daya da rabi, yana dagawa yace kumin afuwa wlh ina asibiti ne bata da lafiya.
Daga daya bangaren kuma Dr Abdullahi yace rashin lafiya kuma? Kuna wani asibiti? Ya sanar dashi. Cikin mintuna kalilan ya iso, ya tarar da Haneefah sai birgima da ambaton Allah take. Yusuf ya gama rudewa yana ganin kamar shine silar komai.
Dr Abdullahi bayason sa hannun akan patient da bashi ya fara dubawa ba dan haka yaja da baya ya tsaya. Dukkanin wani taimako Dr Mubarak ya bawa Haneefah. Samun bacci tayi sosai domin.
Dukkanin su sunyi shiru, Dr Abdullahi ya duba agogo yace nizan wuce gida, sai zuwa gobe da safe zan shigo. Yusuf baima san me suke cewa ba sai da Dr Mubarak ya tabashi sannan ya dawo hayyacinsa. Dr Mubarak yace zan tafi office inta tashi saika kirani, suka karbi number juna sukai sallama.
Dab da sallar asubahi ta bude ido, a hankali zata mike taji an rikota, da sauri ta juyo tana kallonsa. Ganin rikon da yamata ne yasa yayi saurin saketa a tunaninsa wata kila tsorone yake sata sumewa. A hankali ta mike ta zauna. Ciro waya yayi ya kira Dr Mubarak yace tafarka.
Ko minti biyu basuyi ba yayi sallama yashigo. Tambayoyi yake mata... ganin yayi yawa yasa ta dago idanunta ta kalli Dr Mubarak tace babu abinda nake ji gida nake son komawa yanzu.
Babu yadda basuyi da ita ba amma tace ita gida zata koma. Duk yadda Dr Mubarak yaso kebewa da ita taki amincewa illacewa ta warke batajin komai.
A mota babu wadda ya iya cewa junan shi komai illa Yusuf daya lura tana cije labe. Bai iya cewa komai ba ya nufe gidan Nana da ita. Suna zuwa aka soma kirayen sallar asubahi.
Nana idonta biyu da babynta taji shigowar mota, ta tashi mijinta yaje ya duba kosu Haneefah ne suka zo domin hankalinta na kanta duk da mijinta ne yazo ya dauke su?
Da sauri ya bude mata kofa, ta fito. A hankali take tafiya harta iso dakinta. Dakyar ta zauna bakin gado tana rera kuka. Nana da' mijinta sai Yusuf dake biye dasu har cikin dakin suka tarar ta a wannan hali.
Jin shigowarsu yasa ta share hawayenta tana kokarin mikewa amma sai taji bazata iya ba. Nana tazo ta dafata tana tambayarta dama baki da lafiya? Haneefah ta gyada mata kai alamar eh, sannu suka mata. Ta gyara kwanciyarta. Yusuf da Abdullahi suka fice sallah.
Tunda ta kwanta bacci sai karfe goma ta tashi, shima dakyar. Kamar kullum yau ma rama tayi sai kukan da take duk dauriyar Haneefah wannan karon ciwon daban yake.
Zaune take bakin gado ya shigo cikin kananan kaya. Kallo daya ta masa ta dauke kai tare da fadin _sarki ya tabbata ga wadda yayi wannan kyakykyawar halitta_.
Zama yayi kusa da ita yana kallonta, tausayinta ne ke ratsa shi. A hankali yace ya jikin naki? Ta amsa da sauki. Yace meke damunki yanzu? Tace babu komai.
Mamakin raman da tayi yake. A haka Dr Mubarak yazo, yana kokarin dubata ne tace ta samu sauki. Dr Mubarak yace kinsan abinda ke damunki kike cutar da kanki? Matsayinki na wadda ya dace ki lura lafiyar kanki, mesa kikai haka Haneefah?
Ganin ba magana zatayi masa ba ya tashi ya fice ranshi a bace. Yana fita ya samu Yusuf zaune a falo yayi shiru. Dr Mubarak ya zauna kan kujeran da ke kallon Yusuf yace yaushe Haneefah zata tare?
Yusuf na kallon shi yace a gaskiya zuwa yanzu bamu sa lokaci ba amma inta samu sauki zamuyi magana.
Dr Mubarak yace samun saukin ta na la'aka da komawarta saboda zatafi samun kulawa a hannun ka, yanzu abinda nake so kaje ka soma shiri amma kada ya dauki sati daya ko kwana biyar.
Yusuf yace zanfi so nayi magana da ita domin jin ra'ayinta..... bai karasa ba Dr Mubarak yace kada ka bi ta Haneefah, kayi abinda na ce muddin baka so ta kuka samun kanta a irin wannan yana yi
Cikin rashin fahimta Yusuf yace ban fahimci abinda kake nufi ba.
Dr Mubarak yace baka ga yadda ta rame ba? Babu abinda take bukata kamar kasancewa tare da ita u have to do something. Ya mike tare da yi masa sallama.
Yusuf yayi shiru yana tunani, tashiwa yayi ya nufi gidansu Haneefah. Kamar kullum yauma da Ahmad suka hadu. Har falo ya kaishi sannan ya shiga ciki yayiwa Abba magana.
Cike da fara'a suka gaisa yana masa ya gajiya? Ya amsa da alhamdulilah. Shirun da Yusuf yayi ya tabbata akwai magana abakinsa kuma bazai wuce na tarewar sa da Haneefah ba.
Kamar daga sama yaji Abba yace Alhamdulillah Haneefah dai ta komo gida lafiya, kuma kimanin wata hudu da daurin auren ku, inason ka nan da sati daya ka zo ka tafi da ita, bazan hanaka komai ba amma bana son ta wuce sati daya. Farin ciki ne ya lullubi zuciyar Yusuf ya shiga godewa Abba.
Yana fita ya nufi gidan Aisha ya sanar mata, farin ciki take tayasa tace yanzu bazamuyi shagalin biki ba? Yace zaku batamin lokaci domin nafi bukatar matata. Aisha tayi dariya tace in abban Ra'ima yazo zan tambayesa sai mu je gida mu soma shirin tarban amarya amma zan sanar da salma.
Yana fita ya nufi gidan su yana murnar sanar dasu abinda ya faru. Yana shiga yaga motar salma, murmushi yayi yace kinzo a daidai