Showing 12001 words to 15000 words out of 74305 words

Chapter 5 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5166

daganan za a saka mijinki cikin mugun hali...idan akai rashin saA shikenan ya kama wata tashar Kenan inda zai rinkq samun signal...tunda ke kin zama baki da network.


Saimu kiyaye ALLAH yayi mana jagora ya kare mana mazan mu a duk inda suke. Duk suka amsa da ameen.


Biki ya matso, saura kwana uku haneefah taje gidansu hadiza domin qarasa shirye shirye.


Shiko yusuf yana son zuwa ya halicci daurin auren sannan yana matukar son kallon abar kaunarsa. Zuwa gidan nasu ne baiso, kada momy ta dago masa maganar aure, duk da ba auren bane baya so, yafison auren haneefah kafin waccan. Babu irin hakurin da bai bada ba amma anqi hakura. Yanke hukuncin zuwa garin kano yayi amma gidan abokinsa zai sauka bazai wuce gidan su ba.


Bangaren momy kuwa jiran dan nata take yazo domin a tsaida ranar aure. A sannan yar uwar tata tazo. Ta dubi momy tace inata jira naji shiru shine nace bari inzo inji me ake ciki domin yarinyar nan tayi kokari, tana son dan uwanta biye da shekara biyar take jiransa, in wani abinne sai a sanar in san meya kamata, domin anawa ganin inaso in hada kawunan yarannan.


Momy ta dubi tilon kanwarta tace magana nanan, aini namiki alkawari. Jiran dawowarsa nake domin asa ranar aure.


Cike da jin dadi umma nusaiba tace Allah dawo dashi lfy sannan a zuba mishi kinsan yaran zamani, wata qila wata ce ke masa wasa da hankali, yan mata basu kai ko inaba amma sunsan hanyar gidan Malawi da boka ye, su mallake maka da baka jiba baka gani ba.


Momy tace bazan bar haka ta faru ba, domin nasa ido akanshi sosai. Rahma ta ishe shi har abada.


Murmushi umma nusaiba tayi suka canza hira.

An daura auren hadiza da usman. Ganin fuskar haneefah kadai ya isheka tabbacin ita qawace ta hakika domin cike take da farin ciki. Duk wata zirga zirga da ita ake.


Yusuf ma yasamu halartar auren. Kamar yadda ya yanke shawara gidan abokinsa ya sauka.


An kawo amarya gidanta angwaye sunzo siyan baki. An kammala komai bisa al'ada kowa ta fice domin komawa gida. Haneefah ta fito ta nufi motar da ta kawo ta, taga wata mota na mata flashing, bata qula ba sai da yaleko yace ni ne.
*Dr HANEEFAH*👩🏼15


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Juya warda zatayi ta ga yusuf. Mamakin ganinsa tayi ta karaso ya bude mata gaban mota. Ta shiga da sallamarta ya amsa ya kura mata, ganin haka yasa ta sunkuriyar da kanta ta gaishe shi. Ya amsa tare da cewa dearie kinyi kyau sosai pls bari in dauke ki a pic.


Tace aa gele ne a jikini fa, bai jira cewarta ba ya dauke ta duk da ba kallonsa ta ke ba. Ya tada motar suka wuce gida. Wannan karon har kofar gida ya kawo ta yace insha Allah gobe zanzo in gaida umma da abba. Allah kaimu ta amsa masa. Zata fita ya locking door ta juya zata kalleshi karaf ya dauke ta da hoto.


Ta turo baki nidai... nanma yadauketa.. dakyar sukai sallama kan gobe zaizo ya gabatar da kanshi gurin abba.


**** **** ****


Washe gari misalin karfe goma ya dauki hanyar gidan su haneefah. Ya samu kyakykyawar tarba gurin abba kasancewar haneefah ta sanar da umma. Abba ya fahimci yusuf mutumin kirki ne, duk da haka abba sai da ya masa wasu yan tambayoyi da son zurfafa bincike kamar yadda yazo a tsarin addini. Shima yusuf yaji dadi domin yagama gane gidan manya ne. Abba ya amince nasa da haneefah sai fatan alkhairi da yayi musu.


Haka abin yakasance gun umma, ta matukar jin dadin zuwan yusuf. Ita ko haneefah tayiwa umma sallah kan zata je gidan aunty muhibbat. Murmushi tayi domin ta dago ta, Allah kiyaye hanya kice ina gaisheta.

Labewa tayi inda ta tabbata hanyar zaibi ya wuce. Ba'a dade ba ta hango motarsa ta fito. Yana ganinta ya tsaya ta zaga ta shiga. Amaryata! Ta dago ido suka hada ya sakar mata murmushi har an daura auren ta bashi amsa. Yace insha Allah ai mun kusa tunda makarantarki nake jira, haneefah tace nidai gidan aunty muhibbat dani, yace fadi gaskiya kin fito ganina dai. Yanata tsokanarta tana sashi dariya.


Driving take cikin nutsuwa cikin moyarta kirar matris. Traffic ya tsada su kamar ance ta juya idonta ya sauka kan yusuf. Dariya yake cike da nishadi. Mamakine ya kamata yaushe yazo? Kuma wacece take gefensa yana mata irin wannan dariyar? Iya saninta tasan dan nata nada kamun kai baya kula yan mata bale ya sakar musu fuska. Ta dauki waya ta kira shi tana kallonsa.


Jin wayarsa na ringing ya tsaida dariyar zaisa hannu ya dauka aka basu hannu. Yaci gaba da tukin. Momy taso binsu amma bangarensu ba'a basu hannu ba.


Aunty tayi matukar jin dadin ganinsu tare, itama fatan alkhairi ta musu. Ya mata sallama kan zai wuce abuja kada ya makara.


Shigarsa mota ya tarar wayarsa na ringing, da sauri ya daga ganin sunan momy cike da lada bi ya gaidata ta amsa. Ina ka shiga inata kiranka cewar momy? Am sorry momy ayyuka ne sukamin yawa. Naji, kana ina ne? Ina gun aiki amma nakusa komawa gida. Ta rasa me zata ce ma dan nata tsabar mamaki kawai ta katse kiran.


Shiko waji wani iri domin yau yayi abin da bai taba yiba. A hankali ya furta am sorry momy, ina kano amma nakasa kara sowa gida... Inason ganin farin cikin nayi alkawarin auren zabinki domin samun farin cikin ki, da fe kansa yayi ya kifa kansa kan sitiyarin mota... a hankali ya soma furta innalillahi wa'inna ilaihi rajiuun. Saida ya samu nutsuwa tukun ya tada mota ya nufi hanyar abuja.


Kai komo take a dakinta... wai yau dan cikinta yake mata karya? Bayan tagansa da idanunta! Tabbas akwai abu. Tuna fuskar yarinyar tayi yana mata gizo. Tace saina sanki sannan inji alaqarki da dana.


Bayan haneefah ta koma gida umma ke mata gargadinta kan ta aje hankali kan maza, duk da yusuf yazo amma har yanzu bata aureshi ba. Sannan ta aje hankali kan karatun ta sosai tunda tazo shekarar gamawa.


Suna cikin tattaunawa nana takirata, ta labatar mata zuwan yusuf. Ta nuna farin cikinta sosai amma daga baya taji babu dadi data tuno batanan za'ai bikin. Bayan sunyi sallama kiran barrister ramlat ya shigo.


Bayan sun gaisa tace nakira domin inji lafiyarkine tunda ke bakya neman mutane kullum sai annemeki. Dariya is haneefah tayi tace wlh ba haka bane inason kira Allah bai bani iko bane. Tace Allah sarki ba komai ga Dr ku gaisa.


Suka gaisa da Dr Mubarak yake ce mata kiyi karatu sosai fa kune kuke shirin zama graduate. Tace insha Allah sukai sallama. Umma ke tambayarta waye? Nan ta bata labarin abinda yashiga tsakaninsu. Umma tace ina alfahari dake *_Dr HANEEFAH_*.


**** **** ****


Momy ta dubi mijinta tace auren yarannan nakeso ayishi nan da wata daya. Mijin nata ya maida dubansa gareta yace wani yara kenan? Yusuf da rahma ta bashi amsa.


Kallonta sosai yake yana nazarinta. Can ya numfasa yafara magana, na fahimci kimason ta kurawa yaronnan, tuntuni ya nuna bayason auren nan yakamata ki jenye, yaran zamaninnan ba'a musu haka! Ya aka kare ga wadda suke kaunar juna ma bale basa so? Nidai kada ki takura mishi ki barshi ya kawo zabinshi.


Momy tace haba alhaji, ina son dada karfafa zumuncin mune da kanwata sannan ai ita rahma tana sonshi... wannan shine hujjar ki? Nidai bada yawuna ba. Ban yarda da auren da yusuf bazaiyi farin ciki dashi ba. Yana kaiwa nan ya juya yayi shigewarsa ciki. Dauko wayarta tayi ta kira yusuf taji number busy... kusan sau goma take amma amsar daya ce.


Cike da mamaki take dubar wayan nata. Ta tura masa message in ya gama yakirata.


Shiko yusuf waya suke da abar kaunarsa. Haneefah tace ai tunda karatune burinku zan cika muku shi kada ku damu, ku tayani addu'a.


Insha Allah muna kai kuma munsan bazaki bamu kunya ba. Murmushi tayi tamkar yana gabanta tace pls kada ka rabu dani, ina sonka sosai... bana kwadayin rayuwa a inuwar kowa matsayin matar aure inba kaiba... ka sanar dani momy tana da nata zabin, ko su ukune indai zan kasance dakai na yarda na zama ta hudu.


Jawo pillow dake gefensa yayi ya runguma yace dearie bazan rabu dake ba, ke kadai ce kike gabana. Insha Allah zamu kasance duniya da lahira matsayin ma'aurata, muci gaba da addu'a domin neman zabin Allah. Kinsan wani abin muna ganinshi alkhairine amma sharrine, wadda muke ganin sharrine alkhairi ne agaremu. Addua itace mafita. Haka sukasance masu kwantar da hankalin junansu har suka sallama.


Ganin message din momy yayi, lokacin kuma dare yayi domin kusan karfe shadaya da rabine. Yayanke shawaran sai gobe zai kira. Yana aje wayar yaji kira na shigowa, da sauri ya dauka ganin mum.


Ko sallama bata yiba tace dawa kake waya? Nan ya soma kame-kame tsaf ta dago shi. Inason ganin ka gobe duk aikinka, ka aje shi dif ta katse wayar. Zuciyarsa ne ke bugawa uku-uku ganin ba mafita ya tashi domin gayawa mahaliccinsa ya zamto wannan kiran alkhairine.
*Dr HANEEFAH*👩🏼 16


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Karfe goma yayi p arking cikin gidansu. Bai nufi ko inaba sai sashin momy, kannen sa ya tarar a parlour suna kallo. Cike da kulawa ya amsa gaisuwarsu ya tambayi momy, tana ciki aisha ta amsa. Zai wuce tace pls yaya ina son kabani aron wayarka, ya mika mata ya wuce.


Zaune ya taddata tana amsa waya. Bayan ta gama yake gaisheta. Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar. Ta dubeshi dakyau tace badon komai nakira kaba, so nake kaje ka sanar da mahaifinka ka amince da maganar auren rahma, nan da wata daya masu zuwa a daura aure ina nufin kace dashi cikin satinnan a kai kudin sadaki da komai nanda wata daya asa ranar aure.....


Cike da rashin nin dadin maganan yace, umma ban ki zabin kiba, kince nima in auri zabina.... sai nace kada ka auri rahma? Yusuf kwana kinnan nakasa gane kanka, toh wlh in bakai yadda nace ba sai na hana ka aurenta ko wacece ita.


Cikin sauri yace momy na amince ko yauwa a daura, zanje in sanar da abba yanzu. Murmushi tayi tace yauwa ko kaifa.


Yaje ya sanar da mahaifinsa. Mahaifinnasa yace yusuf kada kaje kayi abinda zai dame ka. Yace ba komai insha Allah. Allah tabbatar muku abinda yafi alkhairi ya amsa da ameen ya fice a folansa ya nufi nashi bangaren.


Bayan ta kammala dukkanin ayyukanta ta nufi dakinsu ta kwanta, duk da gajiyan dake tattare da ita tana son kiran yusuf domin yau tun safe basuji muryar junansu ba. Tunanin ko ayyukane suka dan masa yawa.


Sanda kiran ya shigo wayar na hannun aisha, mamakine ya bayya a fuskarta ganin *Dearie* arubuce. Aiko da sauri ta daga wayar taji ance amincin Allah su tabbata gareka abin alfahari.... ni shikenan ma tun dazu jiran kiranka nake amma shiru ka manta dani yau kana ta aiki. Jin anyi shiru ta qara cewa hello!


Aisha tace wayar bata tare dashi. Ras taji gabanta ya fadi, kamar zata katse wayar taji ance aishace kanwar shi amma yanzu zan kai mishi. Ajiyar zuciya haneefah tayi tace ba komai nagode.


Kishin gide ta sameshi kan gadonshi. Tashiga da sallama tana dariya yace yau kuma me ya fadu irin wannan nishadi aisha? Yaya kiranka akai nadaga cikin sauri yace bani wayata, ya karba yana duba mai kiran nasa. Ganin haneefah yayi murmushi yace meye na dariya?


Yaya shine ko kasanar dani munyi sabuwar aunty? Wlh a muryarta naji nutsuwarta. Yusuf yace kardai kin cika ta da surutu irin naki. Aa yaya, dan Allah meye sunanta? Haneefah ya bata amsa. Very cute!!! Yaya dan Allah muga hoton ta? Inta tura zan tura miki...


Suna cikin magana haneefah ta kara kira, suga gaisa cikin shaukin so. Tana shagobe masa tace tazu nakira aisha ta dauka baka ji yadda gabana yafadi ba.. ayya sorry dear. Ban dade da shiga kano ba. Cike da mamaki haneefah tace lfy? Lafiya lau.


Ajiyar zuciya ta saki tare da cewa Allah qara mana lafiya mai albarka. Yace ameen. Yana son sanar da ita amma yakasa. Haneefah tace inada tambaya, Allah sa nasani ya amsa.


*IDAN MUTUM YA SAMU RAKA'A DAYA A SALLAR DA AKE RAKA'A HUDU YAZAI KAWO SAURAN UKUN?*


Wato ina nufin inaso akarayimani bayani akan sallah tare da liman idan mutum yasami raka'a daya wurinda ake raka'a hudu yaza ya kawo sauran ukun, sbd a makaranta hakan na yawan faruwa ga dalibai mata.


Idan mutum yasamu raka'a daya a cikin sallah me raka'a hudu. Idan ya tashi ramuko zeyi raka'a daya da karatun surah, sannan ya zauna tahiya ya kawo biyu a sirran ce. Idan har sallan isha ne, idan la,asar ne ko azahar shima haka zeyi babban cin da zai nuna a gurin shie, rashin bayya nawa. Amma idan mutum ya rasa raka'a daya a sallan magriba, to ze kowa raka'a daya da karatun sura a bayyane, sanna yayi tahiya, ya sake kawo daya a sirran ce batare bayyanawa ba. Domin manzon ALLAH sallahu alaihi wasallam yanuna cewa ''ka ciko abinda ya kubuce ma"
Shiya sa idan Kazo kabi liman sallah, da wannan raka'ar da ka samu kai a wajen ka itace na daya, Daga ya idar se ka cika tazama ma, cikon da kayi shine na Qarshe. kamar yadda ka saba a sauran salloli cikakku, sannan idan ka rasa raka'a daya daga cikin raka'o'in da ake raka'a biyu. Shine zaka kawo ta a sirran ce, batare da karatun sura ba. Allah sa mudace ameen. Haneefah tace nagode sosai. Yace anjima zanzo kamar bayan sallah isha'i. Allah karaso dakai lfy.


Bayan sallar isha'i kamar yadda ya sanar da ita tsaf ya shirya. Yana tafiya can ya hango kanti saida waya nan ya tuno yanason siyawa haneefah. Ya tsaya ya cire kudi a ATM sannan ya nufi wani babban shago. Ya rasa wani irin waya zai siya mata gashi yanason suprising natane. Daga karshe yasiya mata Samsung note3. Ya fito ya tsaya wani shopping mall yasiya mata dogayen riguna masu kyau kala biyu da chocolates ya fito ya kama hanya.


A kofar gida yayi parking ya shigo. Ya turo kafar kenan ya hadu da Ahmad suka gaisa. Yace ka shigo da motarka mana aikazama dan gida, yace barshi kawai ko a wajen. Dole Ahmad yasashi shiga da motar shi. Yace yayi mishi sallama da haneefah. Sanda yayi mishi jagora har zuwa falon abba, kasancewar yau ba girkin umma bane tukun ya fito ya je kiran haneefah.


Light make up tayi, tasa dogon hijabinta. Tasame shi zaune yana aikin danna waya. Sanye yake da manyan kaya.


Dago kansa yayi tare da amsa sallamarta. Bayan tasami guri nesa dashi kadan ta zauna dukkaninsu sukai shiru tsawon minti biyar. Yusuf ya fara magana ya kuma kikai shiru kamar ba mai surutu a waya ba. Ita dai qara shiru tayi domin kunyarsa take ji.


Murmushi yayi ganin ta qara shiru. Yace umma ce takirani shiyasa kika jini yau gani a kano amma gobe da safe zan koma. Ya dago ido ya kalleta yace ina fata zaki bani goyon baya wajen yiwa mahaifiyata biyayya.


Gabanta taji ya fadi amma ta dake bata nuna ba tace insha Allah. Yaci gaba nanda wata daya aure na da rahma shine dalilin kiran.


Numfashinta ta nema ta rasa jin aure daya ambata. Dakyarta daidaita numfashin tace Allah sanya alkhairi, ina tayaka murna
*Dr HANEEFAH* 👩🏼17


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Ji take kamar ta cire zuciyar tayar ta huta saban wani irin kunar dake mata. Ji tayi wani irin abu ya tokare mata makoshi. Duk halin da tashiga kanta sunkuye yake, Allah-Allah take yayi mata sallama yatafi kada yaga hawayen dake makale idonta.


Yagama nazarinta tsaf yace bayan anyi bikin zan dauko da maganarki tunda makarantan yakusa, kina gamawa sai ayi biki. Ganin shirun nata yayi yawa yace ni zan wuce inna koma zamuyi waya.


Batace dashi komai ba suka fito, har gurin motarsa suka iso a sannan ta dago kai tace Allah kiyaye hanya. Zata juya yace haba dear hankalina bazai kwanta ba in mukai irin wannan sallamar.


Karfin hali tayi ta murmusa masa tace yi hakuri, inaso kaje ka kwanta ne domin ka tashi da wuri bana so ka makarane. Yace ba komai kafin ki wuce ga wannan ya bude mota ya dauko leda ya mika mata. Qin karba tayi zata wuce ya dakatar da ita yace kiyi hakuri na canza miki mood naki, amma wannan itace first gift na pls ki karba ba danni ba dan Allah. Ta karba tace nagode cikin sarkewar muryar kuka.


Tuni ya hango hawayenta cikin dacin rai ya shiga motarsa ya fice zuciyarsa na masa kuna. Ya tsani ganin bacin ranta ko kadanne.


Itako haneefah tana zuwa bakin kofar falonsu ta share hawayenta. Tana shiga ta tarar da kannenta da umma suna kallo. Ta mikawa umma ledan tace shine yakawo, kannen nata sukayi gurin ledan suka soma ihun murna tare da cire kwalin wayar suka nunawa umma. Itama mamakin irin wannan kyautar tayi.


Itako ko kallon inda abin yake batayi domin jira take tashiga ciki. Umma ta katse tunaninta da cewa zoki gani haneefah. Tana gani tana yabawa kawai dan karsu gane halin da take ciki. Umma ne tace sai abari in abba yazo yagani saiki fara amfani dashi amma ga chocolates din. Haneefah ta dauki biyu ta musu saida safe.


Shigarta dakin ta kulle da key ta nufi bandaki. Tsayawa tayi ta rasa ne zatayi, ta qara fitowa ta zauna bakin gado. Tabbas kishi nake amma mesa zan damu kaina? Tunda zai aure ni ai shikenan. Yanzu in mahaifiyarsa tace bazayyi mata kishiya bafa? Nan hawaye ya fara zubo mata tace aa hakanma bazai faru ba. Nan ta rushe da kuka tana tausaya kanta


Kwance yake kan 3seater falon shi, yanayin da yabarota shike sosa masa rai, ya dauki waya ya shiga kiranta. Kusan 5missed call bata daga ba, ya kyaleta yasan ba lallaine tayi magana a irin wannan yanayi. Bayan awanni ya qara kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login