Showing 51001 words to 54000 words out of 74305 words
Chapter 18 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
Mamman (Mrs)💖
Kwance yake akan gado kansa yayi masa za fi tsabar tunani? Allah mai iko mai yadda yaso, wannan itace Haneefah? Itace ta zama DOCTOR? Ta zama consultant? Cikin shekaru kalilan? Tabbas in kayi niyyar abu zaka yishi sai dai kana da karancin niyya.
Murmushi yayi daya tuno ko turancin kirki bata iya ba amma yanzu kwarewarta cikin harshen har mamaki take basa, yarinya karama amma halinta da nutsuwarta yananan.
Tashiwa yayi ya jinginu jikin gado ya lumshe ido. Hango tsantsar soyayyarsa yake cikin idanun sa. Allah sarki dearie har yanzu kina so na? Goge hawayen daya zubo masa yayi yace but it's too late, ur already married.
Babu abinda yakamace kamar HAKURI. Amma meya kawo ta London? Zaman aure yabawa kansa amsa. Mesa ta biya maka kudin aikin da za'a maka? KYAUTATAWA da nuna yafiyarta gareka.
Murmushi ya kuma yi yace ya zama dole in fita rayuwar ki Haneefah, domin in ina kallon ki hankalina sake tashiwa yake nesanta kaina gare ki shine mafita. Tashiwa yayi zai shiga banda idonsa ya hango iPad din ta.
Yasa hannu ya dauka yace kenan abokin karatun tane. Sha'awar budewa yaji yana yi, nan taje ya kunna babu inda yayi niyar shiga sai hotuna.
Duk inda yaganta a waje lullube take da habaya ko dogon hijabi, kuma yawanci hotunan suna makaranta ko wani guri daya tabbata library ne. In yazo inda bata da lullubi da sauri yake wucewa dan ba tsayawa yake ya kare mata kallo ba. Baya ganinta da kowa sai wadda ya sukai musanyar iPad da wani dan India hakan ya tabbata mishi wata kila abokanan kara tunta ne.
Ya dauki tsawon lokaci yana kallo domin ganin mijin nata amma bai gani ba, kuma baiga yarinyar daya ganta a auren Nana ba. Fita yayi yashiga gurin videos nanma ba abinda yake nema bane sai kawai ya kashe ya' aje iPad din.
Murmushi yayi yace ina tayaki murna domin kula da mijinki daya ke yine yasa kika canza. Allah baku zaman lafiya.
Da dare ya kira Abba yana sanar dashi abinda sukai da likitoci amma bai sanar dashi komai game da Haneefah ba, Abba yace kai kadai Yusuf. Yusuf yace babu abin damuwa Abba inaga abin yana da sauki kuma akwai wadda nasani cikin likitocin zasu kula da komai nidai addu'ar ku nake bukata.
Abba yace Allah baka lafiya yasa ayi a sa'a. Ya amsa da ameen sannan sukai sallama ya katse wayar.
Kwanciya yayi amma ya kasa bacci bayananta ne ke yawo cikin kunnensa. Ganin kada ya aikata haramci yasa ya tashi yayi alwala ya soma nafilfilun yana rokon Allah yabashi ikon fin karfin zuciyarsa.
Itama abin haka yakasance agunnata, duk yadda taso daurewa abin yaci tura. Raihana data fuskanceta tace haryanzu lokaci bai kure miki ba, kina da rai da lafiya sannan kina da bukata ba juyi zakirika yi kan gado ba, duk mabukaci baya bacci, naga alama bazaki iya hakura dashi ba, shima haka, saiki tashi ki sanar sa da Allah halin da kike ciki, cikin ikonsa mahaifiyarsa da kanta zata zo neman aurenki wa Yusuf.
Tsaki Haneefah tayi tace kina tunanin shine yake damuna ni jarabawarmu nake bi arai tana magana tana mikewa taje tayo alwala ta soma nafilfilu.
Washe gari hankalin Haneefah ya kasa kwanciya, so take taje ayiwa Yusuf aiki amma tananan amma ta rasa abinda yasa bazata ba, ganin sai tunani take yasa ta yanke shawarar in an masa kafin ya farfado zata tafi.
Cikin nasara akai aikin, Dr Michael da kanshi yayi aikin dan ganin kada a samu kuskure domin Haneefah. Daki na musamman aka kai Yusuf.
A hankali ta turo kofar ta shiga. Har yanzu alluran bai sake shiba. Tafiya tayi gabansa tana kallonsa, bai canza ba domin yadda tasan shi abaya haka yake sai dai fari daya kara. Ji take tamkar ta maida shi ciki, ganin ya fara motsi ta tashi da sauri zata fita amma tuni ya ganta.
Murmushi yayi ya sake rufe ido domin baya son dogon tunani game da ita. Tana fita ta tsaya gefen dakin tana hawaye, ganin kada azo a sameta ne ta wuce da sauri zuwa office din Dr Michael.
Yana fita suka hadu. Ta gaishe shi ya amsa tare da cewa munyi nasarar aikin da mukai sannan aikin da mukai free ne ba sai an cire a salary ki ba sai dai zai rika zuwa checkup wata biyu sau biyu domin qara tabbatar da lafiyarsa.
Tace sir ku sanar dashi domin yau bazan sake zuwa ba sai bayan sati biyu banajin dadin jikina. Yace babu komai duk sanda kika samu sauki zaki zo sannan muna son baki hutu a asibiti domin kije kiyi karatu tunda kun kusa. Tayi godiya ta wuce abinta.
Tun daga wannan rana ta yanke zuwa asibiti. Ta aje hankalinta sosai tana karatu. Addu'a take Allah bata ikon hakuri da juriya inko haduwan sune alkhairi Allah janyo lamarin kusa. Kallon hotunansa kadai yana sa taji sanyi aranta dan haka damuwarta ta ragu domin tanaji ajikinta komai ya wuce.
**** ****
Yau kimanin watansa biyu da zuwa Nigeria. Bai gayawa kowa haduwansa da Haneefah ba. Alhamdulillah ya samu sauki, zafin da yake ji a kafafunsa duk yadaina ji komai ya koma normal.
Lamarin Haneefah fa duk ya tattara ya aje a gefe domin ya hakura da ita tunda takasance tare da wani a matsayin ma'aurata.
Yau juma'a ya dauki excuse gurin aiki domin tafiya London ranar lahadi, ba tare da bata lokaci ba ya dauki hanyar kano domin yiwa iyayensa sallama.
Tun kafin ya isa gida ya ji yana sha'awar biya su gaisa da abokinsa domin tun ranar dinner sa suka rabu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya nufi gurin aikinsa.
Yayi parking kenan Dr Abdullahi ya fito da alama gida zai tafi. Ganin Yusuf yasa ya tsaya yana murmushi harya iso ya mika masa hannu suka gaisa.
Dr Abdullahi yace kaikam shiru Abuja ya boye ka. Yusuf yayi dariya yace amin afuwa wlh abubuwanne sukai yawa yanzu ma nazo gida sallama ne shine nace bari in biyo mu gaisa.
Dr yace ka kyauta ina zaka ne? Medical check up zanje London. Wani asibiti Dr ya tambaya? Yusuf ya sanar dashi. Dr yace ai asibitin da kanwar matata take aiki kenan Haneefah, in bazaka damu ba zan hada ku ka sauka gidanta saiku tafi tare ganin Dr ma zaizo maka da tsauki.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼53
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Kasancewar yau babu aiki da makaranta yasa tun safe ta tashi yin sharar dakin da bakon zai sauka, domin sunyi waya da Nana ta sanar mata da zuwan bako.
Dakin farko wadda ke nesa da nasu kadan ta gyara. Tsaf ta gyara dakin tamkar kullum ana rayuwa ciki, tanakan wanke ban daki Raihana ta leko tana ganin gyara tace Haneefah kekam kin huta arayuwa, komai kin iya, girki, kwalliya, gyara, kula da mutum komai na rayuwa, ki godewa Allah sannan ina taya Dr Mubarak samun ki matsayin mata.
Murmushi take amma jin an ambaci Dr Mubarak saita hada rai tace saiki auramin shi ai.
Raihana tayi dariya dace zan so ganin wadda zaki aura, Allah saiya jure zama da ke domin kina da taurin kai ta fannin aure ace ke kin makalewa wadda baki da tabbas akansa?
Haneefah tace yanzu ke kika nemi tsokanata, aure dai zanyi kuma bauta zai kaini gidan miji dole inyi biyayya. Dr Mubarak dai bazan aura ba sai dai wani daban, Yusuf kuma na mance da shi hotunan sa da kika makala bazan cire ba sai na tashi barin gidannan, yadda na cire zan koma Nigeria haka zan yakice shi in cireshi a zuciyata.
Raihana tace Allah sa da gaskene, me sunan bakon da zamuyi?
Haneefah tace wallahi ban sani ba, ban ma tsaya na tambaya ba amma tace zaizo ba sai munje dauko shi a airport ba. Duk hiran da suke cikin harshen larabci domin yanzu in dai da Raihana suke sai larabci.
Bayan sun gama komai sukayi wanka. Hira suka zauna a daki Raihana tace ni yanzu bana son nagama makarantar nan, nasaba da garin sannan ina tare da amintacciya wadda ta gama sanin halayyata muna zaman lafiya.
Haneefah tace kada kiyi tunanin zumuncin mu zata yanke, har abada muna tare. Hira suke sosai Haneefah ta fara canza fuska. Raihana tace lafiya Haneefah?
Da sauri Haneefah tace cik.... kafin ta karasa ta fadi tana rike da mararta.
Hankalin Raihana ya tashi sosai tana jijjiga Haneefah. Ganin ko motsi batayi ta soma kuka, tashiwa tayi ta nufi inda ta aje allurar tana ciwon mara.
Bayan ta saka mata da minti biyu taji ajiyar zuciyar Haneefah. Raihana tayi hamdala ta gyara mata kwanciyarta ta rufeta da bargo. Zama tayi gabanta tana kallon ta tana tunanin kowa da irin cutarsa a duniyar na, shiyasa a duk halin da mutum yakasance ya godewa Allah.
Tayi sallah la'asar tana kan sallaya taji motsin Haneefah. Da sauri ta iso gareta domin tafi awa biyar tana bacci.
Gani tayi tana dan birgima ta rike cikinta, Raihana ta hayo kan gadon ta riketa tana mata sannu. Addu'a take tana tofa mata, suna cikin wannan yanayin taji bell na kofa yana ringing.
A hankali ta aje kan Haneefah a pillow ta tashi domin ganin waye. Tana bude kofa ta ganshi tsaye da jakar kayan shi. Mamakine ya bayyana fuskar Raihana domin ta gane shi. Cike da mamaki ta bude baki cikin harshen turanci tace wa kake nema?
Yusuf yace nine bakon da akace in zoni nan gidan. Babu musu ta bashi hanya ya wuce. Shigowa yayi da sallama yana ware idanu ina zai ganta.
Gaisawa sukai sannan ta mishi jagora zuwa dakin shi. Mamaki fal a zuciyar Raihana ta fito ta nufi kitchen ta hada masa komai ta nufi dakin shi. Bayan ta aje zata fita ta nuna masa banda ki.
Bayan fitarta ya tashi ya shiga ban daki yayo wanka sannan ya dauro alwala.
Har dare yaji gidan shiru, ji yake babu gajiyar hanya tattare dashi, so yake ya kafa idonsa akan Haneefah.
Wayar Haneefah ce ta soma ringing, ganin sunan Nana yasa ta dauka wayar suka gaisa da Nana ta sanar da Haneefah bata kusa da wayar.
Nana tace bakon ya iso ko? Raihana tace eh amma.... jin motsin Haneefah yasa ta katse wayar kallon ta ya koma kan Haneefah.
Birgima ta soma yi tana salati, kuka Haneefah take, wannan karon ta fita hayyacinta sai kuka, wasa wasa sun kusan raba dare a wannan yanayin, ganin haka yasa Raihana ta tashi ta nemo allurar bacci ta sawa Haneefah. Nan take bacci ya sace ta.
Tsaye tayi tana kallonta, lokaci daya ta rame duk ta fita hayyacinta, ganin tunani ba mafita bane ta fito domin neman drip ta sawa Haneefah.
Duk wucewarta yana kallon ta, gani yayi ta nufi wani guri tazo dauke da drip a hannunta. Ita ko Raihana sam bata lura da shiba domin cikin sauri take.
Yanzu ya tabbata babu lafiya. Tashiwa yayi ya shige daki ya zauna tunani, ina Haneefah take? Ko dai bata da lafiya ne? Kusan karfe biyu tukun ya samu ya runtsa.
Daidai karfe uku ta farka. Ta tashi a hankali ta zauna, ganin drip a hannunta yasa tasan ta dade. Ganin Raihana tayi kan sallaya tana sallah.
A hankali tacire ta tashi dakyar ta nufi ban daki. Ruwan zafi ta hada sannan tayi wanka da alwala ta fito. Bayan ta rama dukkanin sallolinta tayi addu'a ta juya ta fuskanci Raihana.
Ya jiki ta mata? Da sauki ta amsa. Kasa tashi tayi nafilfilu, karatun qur'ani ta zauna. Idonta biyu har aka kira sallar asubahi, bayan ta idar zata tashi ta kwanta domin allurar baccin har yanzu bai saketa ba tace da Raihana bakon yazo?
Raihana tace eh, Nana ta gaya miki wanene bakon? Aa bata fada ba, ita dai tace abokin mijinta ne zaizo checkup asibitin mu, tana kaiwa nan ta kwanta bacci ya soma daukarta.
Raihana kam shiru tayi. Ganin gari na qara haske ta tashi tashiga kitchen ta soya chips, ta dauki try yasa akai da ruwan zafi, bread da kayan shayi ta nufi dakin Yusuf.
Sallama tayi ya amsa ya bude kofa, ta aje tire tare da gaida shi ya amsa tayi saurin ficewa. Shiri tayi ta fita siyo drip domin wadda ta sawa Haneefah ya kare.
Fitowa yayi a hankali ya nufi falo. Kusan mintunansa goma baiji motsi ba, dan haka ya tashi zai koma daki yaga wani glass da alama wajene ya nufi gurin domin ya leka. Daidai yazo wucewa kamar ance ya juya ya hangota kwance lullube da bargo.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼54
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Baisan sanda yakaraso dakin ba, tsayawa yayi yana kallon ta. Lullube take ta rabu guri daya, hannunta dake makale da drip ne kadai ke waje.
Da hijabi ajikinta purple, colour ya dada haskata. Ji yayi tausayinta da tsananin sonta na ratsa illahirin jikinsa.
Ya dauki tsawan lokaci yana kallon ta tare da tambayar kansa me yake damunta? Ya kalle bedside drower da fuskanta ke kallo, dauko hoton yayi yana kallo.
Rufe bakinsa yayi da tafukan hannunsa yana kallon hoton shi, a sannanne ya dago idanun shi zuwa dakin, hotunan sa yake kallo.
Yanzu ya yabbata Haneefah bata mance dashi ba kamar yadda shi ma bai mance da ita ba, tana sonshi kamar yadda shima yana sonta, wani irin so sukewa juna? Sunkuyo yayi yana mai sharar hawaye a hankali yace tun kafin naji komai daga gare ki nasamu abinda nake bukata....
Ji yayi ance me kakeyi cikin harshen turanci? Tashiwa yayi yana kallon Raihana yace meke damun Haneefah?
Haneefah ta soma birgima tana salati, Raihana tazo da sauri ta kama hannun ta dake makale da allura gudun kada ta jima kanta ciwo tana mata sannu...
Raihana ta dago kai tana kallonsa duk yabi ya rude amma ya kasa cewa komai tace ka fita! Ganin kamar bazai fita ba ta daka masa tsawa ka fita!! Yana tafiya yana kallon su har yakai bakin kofa. Ganin ba matsawa zayyi bane yasa ta tashi ta rufe kofar da key.
Haneefah wannan karon tasha wahala sosai, dakyar ta samu ta nutsu. Raihana kam sai kuka inta tuno hira suke amma cikin kankanin lokaci Haneefah ta nemi lafiya ta rasa.
_Kamar haka ne duk wani bawa yana raye batare da ciwon komai ba lokaci daya zai fadi ya rasu babu ciwo, shi yasa ake cewa kullum mukasance da kyakykyawar niyya_.
Kusan karfe 11:00am Haneefah ta farfado. Wasai ta tashi kamar ba ita tayi ciwo ba sai dai rashin karfin jiki. Kallon Raihana tayi taci kuka idanunta sunyi ja tace
Yanzu meye na kuka? Kinsan ciwon nadan lokaci ne zan farfado kike kuka? Raihana tace baki ga yadda kika koma ba? Wallahi duk wadda yake tare da ke sayya tausaya miki.
Haneefah tace na ki tausayin ya wuce misali, domin har ciwon kai zaki iya sawa kanki tana magana ta mike ta shiga banda ki. Tseye take gaban madubi bayan ta fito daga wanka tana kallon kanta yadda ta rame, juyowa.
A hankali ta gama shirin ta cikin dogon kaya kamar yadda ta saba, ta dauko babbar himar tasa zata fita Raihana tace mata ina zaki?
Haneefah tace ba office zan fita ba, bako zanje in gaisa da shi, tun jiya yazo fa. Raihana tace wai basu fada miki bakon bane?
Abokin mijin Nana ne cewar Haneefah. Sannan ta fita Raihana ta bita da kallo cikin zuciyarta tana cewa wannan wani lamarine yake son wakana? Nana da kanta ta bari Yusuf yazo? Shiru tayi tana jiran shigowar Haneefah dan tasan bazata shigo lafiya ba.
Ita ko Haneefah tana fita ta nufi dakin, sanda ta bude baki zatai sallama saida taji gabanta ya fadi. Baki na karkarwa tayi sallama, jin anyi shiru ta kuma yi, nanma shiru zata kwankwasa kofar kenan taji an bude kofa.
Ganinsa a tsaye yasa gabanta yayi mugun faduwa. Ja da baya tayi tana kallonsa, shima kallon nata yake amma sun kasa furta ko da kalma dayane. Da sauri ta jiya ta nufi dakinsu.
Tana shigowa ta rufe kofar da sauri tazo gurin Raihana cikin muryar kuka tace nashiga uku, bayan tunaninsa har kallonsa nayi yau cikin gidannan, dan Allah kije ki kara dubamin nasan bashi bane gizo ne.
Raihana ta kamo hannun ta tace shine Haneefah, pls control urself kada ya gane hankalin ki a tashe yake.
Haneefah ta dafe kanta tana salati. Mikewa tayi zata dauki wayarta ta kira Nana Raihana kamar tasan abinda zatai ta fizge wayar a hannunta tana cewa nasan kiranta zakiyi akan mesa ta bari Yusuf yazo amma inason k isan cewa itama tana da hankalin da bazata aikata miki haka ba.
Haneefah bata tanka mata ba ta karbi wayarta ta shiga kiran Nana. Nana tana daukawa ko karasa sallamarta batai ba Haneefah tace kin kyauta, bakon da kuka turomin keda mijinki, harkin manta abinda ya shiga tsakanina da mahaifiyarsa shine kika barsa yazo?
Nana tace wayene kike magana akanshi? Badai Yusuf ba? Haneefah tace shine yazo, inaso kice da mijinki yace da abokin sa ya tattara kayansa yabarmin gidana bana son ya qara ko da awa dayane tana kaiwa nan ta katse wayar.
Kuka ta zauna yi. Raihana bata ce da ita komai ba zata fita domin hada lunch tace inkin fita kice dashi ya fita yabar gidannan... bata qarasa ba taji yace kibari in kikaji da me nazo sai nabar gidan.
Haneefah tashiwa tayi tace babu abinda nake sonji infact bana bukatar ganinka ka fita! Babu yadda bayyi akan ta sauraresaba amma kememe taki.
Yusuf yace in bakyason ganina me ya kawo hotunana? Pls Haneefah nasan har yanzu muna kaunar junan mu ki tsaya kiji me zance.
Dago ido tayi tana kallon shi, gani yayi ta nufi inda hotunan suke ta soma cirowa, gaba daya ta zo ta zubar gabansa glass din baki daya suka fashe.
Raihana dake kitchen ta taho da sauri jin fashewar glass tazo ta tarar da abinda Haneefah ke aikatawa.
Haneefah ta nuna hotunan da ta zubar gabansa tace indai nine ga hotunan ka kwashe ka tafi dasu har abada bana son kara ganin ka!
Yusuf ya dago manyan idanunsa da suka kada sukai ja yace nine bakison gani? Haneefah tace eh!! Nadaina