Showing 30001 words to 33000 words out of 74305 words

Chapter 11 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5188

gaya miki har ki haddace tare da tilawa in harma kina so da sauran littataifai da baki karanta ba. Cike dajin dadi Haneefah tace na amince.


Tun daga wannan rana Haneefah ta fara sabon rayuwa da Raihana, rayuwace bisa tsarin addini, dan suna cikin turai basa barin lokacin sallah da mutane, kullum cikin lullubi suke ita Raihana kullum tana cikin habaya. Haneefah har mamakin sauran bakaken fata suke yadda suka watsar da komai kamar ba musulumai ba.

Duk sanda suka samu lokaci suna fita suna yawo da haka suka fara gane gurare. Hankalinta Haneefah ya kwanta amma duk dare sai ta saka Yusuf addu'a, inda alkhairi tsakaninsu Allah basu ikon sake haduwa in ko babu alkhairi Allah albarkaci rayuwarshi ya basa ikon gamawa da iyayensa lafiya. Bata taba nunawa Raihana tana da damuwa, itama Raihana ta dangata ga wadda basason yawan surutu, Haneefah tana jin dadin yadda Raihana ta ke fahimtarta sai kuma ta tuno da aminiyarta hadiza.


Kwance tashi ba wuya gurin Allah, yau su Haneefah suka gama jarabawarsu ta first semester tare da samun hutu na sati biyu. Zaune take tayi tagumi tana kallon Raihana dake hada kayanta zata tafi gida hutu, tabbas kwanakin da tayi da Raihana tana matukar debe mata kewa gashi suna komai tare. Har mamakin Raihana take in tana mata bayanin abinda ya shige mata duhu domin yarinyar tana da baiwar ilmin addini, zaman da tayi da ita ta qara samun nutsuwa domin addini ya dada shigarta, har sunyi nisa a qur'ani, yanzu inta ta tafi dawa zata rika karatu.....


Firgigit Haneefah tayi daga tunanin da takeyi jin an tabata. Raihana ta sakar mata murmushi tace kamar yadda kike tunani haka nima nake tunani, nasaba dake domin kin cancanta domin ke mai riko da addinine, mun hadu domin Allah, zamu kasance domin Allah kuma mu rabu dominsa, in bazaki damu ba ki bini muje gidanmu.


Haneefah tace nagode da shaidar da nasamu agunki kema hakanne yasa na kwadaitu in kasance dake, amma bani da halin binki bayanzu ba, insha Allah wata rana zamu tafi tare, zanyi kewar karatun da muke ne kuma zan kasance ni daya ce shiyasa kika ga na damu.


Raihana ta tashi ta zauna kusa da ita, ta dubeta tace in wannan ne ba damuwa zamu rika yi tru video call nidai kada ki kula kowa bazan ma kai sati biyu ba just a day's.


Haneefah tace toh naji. Ta tashi ta taimaka mata suka hada kayanta domin ba l dogon magana take ba, azuciyarta tace ni da biyamin kudin zuwa akayi aina zan samu kudi da zamu rika video call? Zan dai daure har kizo , sunata hira jefi-jefi domin yanzu Haneefah turanci ta fara zama a harshenta wani sa'in da larabci Raihana take mata magana dan haka har larabci ta soma ji amma kadan-kadan.


Har airport ta mata rakiya Raihana ta bukaci lambarta, garin cirewa ta bata Haneefah ta yar da ID card nata. Saida jirginsu ya tashi sannan Haneefah ta kamo hanyar komawa makaranta. Sun kusa isowa motarsu ta baci, saita sauka tadan fara takawa. Dab ta iso makarantar taga wani hanya da kullum anabi amma basu taba bi ba... ganin mutane nabi itama ta dauki hanyar tana tunanin karambani irin nata. Saida tayi tafiya kimanin mintuna goma sha biyar taga tazo bakin ruwa. Duwatsune manya ga korayen ganye gwanin sha'awa.... ruwane blue wadda ba'a ganin karshen sa, gurin babu hayaniya shiru ga kallon gurin take cike da sha'awar gurin taji an katse mata tunani tare da kiran sunanta HANEEFAH! Ras taji gabanta ya fadi jin muryar namiji a irin wannan guri.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼32


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Farine sol kyakykyawa, kallo daya ta mishi tasan ba dan qasarsu bane wato Nigeria, cike da tsoro karara bayyane a fuskarta tafara ja dabaya ganin yana zuwa kusa da ita.


Mirmishi taga yayi ya mika mata ID card nata tare da yi mata magana cikin harshen turanci yace na tsinta ID card naki ne a airport, kina fitowa na ganki shine nabiyo ki.


A jiyar zuciya tayi tare da mika hannu ta karba tace nagode ta juya ta soma tafiya, shima yayi tafiyarsa.


Hango wasu kujeru tayi, tana leke- leke harta iso ta zauna tana mai ambaton Allah. Kallon ruwan tayi cike da sha'awa, juye juye take taga wasu suna zaune fararen fata sun mannu da junansu tace da'alama soyayya suke. Kusan mintuna goma tana zaune ta kurawa ruwan ido, hakika gurin yayi mata dadi can ta hango wani qaramin gada wadda yana da iyaka ba sallake ruwan yayi ba.


A hankali take tafiya harta iso ta soma tafiya akai, tana takawa taga wasu suna fitowa ta ciki ta basu hanya suna wuce taji macen na tambayar namijin mesa kake son nan dayawa? Ya bata amsa saboda inajin dadin kasancewa anan, inason irin wadannan gurare.


Ras taji gabanta ya fadi da ta tuno da kalaman Yusuf, take ta ciro wayarta ta shiga gurin hotuna, WhatsApp images ta shiga har taje gun hotunan da take so, tsaye yake gaban ruwa ya dauki kanshi a hoto ya tura mata sannan ya dauki inda yake ya tura mata, gurine babu kowa babu komai sai ruwan da ke kwance da korayen ganye.


_Haneefah tace Masha Allah gurin yayi kyau dear! Yusuf yace saboda inajin dadin kasancewa anan, inason irin wadannan gurare_.


Ji tayi hawaye na neman zubo mata, duk yadda tayi domin kada su zubo amma sai da suka soma zubowa a hankali ta maida kallonta cikin ruwa sai taga ya canza kala alamar rana na dab da faduwa (sunset), ya hasko ruwan.


Yusuf mesa bazan daina son ka ba? Mesa bazan iya hakuri dakai ba? Mesa nakejin bazan samu tamkar ka ba? Momy mesa kika rabani da danki? Kinsan yadda muke son juna? A lokaci daya Haneefah ke jerowa kanta wadannan tambayoyi. Sai ta fashe da tsananin kuka wadda har muryarta ya bayyana.


A hankali ta tsaida kukan tana share hawaye tace bazan daina addu'ar Allah mallaka min shiba, agurin Allah nake tsammani ba ke ba Momy, sannan na miki alkawarin zama dashi amana. Sai kuma murmushi ya bayyana a fuskarta da ta tuno da kalaman Yusuf


_Ana hakuri da kishin ruwa a nan duniya domin neman ruwa da inuwa a ranar alkiyama_.


_Don haka, kasance mai yawan azumin nafila a nan gidan duniya domin neman dacewa da inuwa da ruwa mai sanyi a lokacin tsananin ranar alkiyama_


Nagode daka kasance a rayuwata, mai tunamin kyawawan rabo duk da bama tare, zan kasance mai juriyar kishin ruwan duniya insha Allah domin ko wacce jaraba ga dan Adam, tamkar ishine agareshi don haka zan tashi domin neman na lahira ta.


Ta juya ta soma tafiya taji wayarta na ringing, tana dagawa taga Nana. Da sallama ta amsa suka gaisa tace ya karatu da sabon wuri? Ina fata bakya samun matsala? Haneefah tace babu komai wallahi sai alkhairi.


Nana tace haka ake so, muma sai nextweek zamu gama exams, amma next year muke da shirin gamawa insha Allah. Allah taimaka Haneefah ta bata amsa. Suka dan taba hira Sukai sallama.


Bayan ta iso hostel ta nufi banda ki tayi alwala ta fito ta zauna kan sallaya tana jiran lokacin sallah. Wayar ta taji yana ringing, ganin sunan hadiza yasa ta dauka da sauri tana mai cewa amin afuwa yar uwa wlh yau muka gama exams dama so nake na kiraki ko gobe.


Hadiza tace ai kya bari mu gaisa tukun, bayan sun gaisa tace na tura miki hiton diyarki amma shiru baki hau online ba shine nace bari in kiraki. Wani irin farin cikine ya lullube Haneefah tace dan Allah yaushe kika haihu? Hadiza tace few hours ago. Murna gun Haneefah ba'a magana nan ta soma yi mata barka tace yanzu inna idar da sallah zan hau in duba sukai sallama.


Bayan ta idar da sallah ta dauki wayarta domin kallon diyarsu. Kura mata ido tayi tare da tsananin kaunarta da yake shigarta. A hankali ta shafa hoton yarinyar tace Allah sa ki gaji mahaifanki wajen tarbiyya da ilmi. Zaune take ta kurawa yarinyar ido tace ko yaushe nima zan kasance da tawa? Murmushi tayi data tuno Yusuf yana cewa _mu ma next year da babyn mu_ tace ni nasan kaine uban yarana, zan kasance mai jiran lokaci nasan Allah na tare da masu hakuri. Tana cikin surutai Raihana ta kirata tace sun iso lfy amma zuwa anjima zata kirata suyi hira yanzu tana airport, sukai sallama.


Ranar sunan hadiza yarinya taci sunan maryam mahaifyar usman suna kiranta da ummulkhairi. Haneefah sai da tayi hawaye batanan akai suna amma umma da kannenta duk sun tafi suna domin zumuncin Hadiza da Haneefah mai karfine wadda iyayensu ma kansu a hade yake.


Kullum suna waya da Raihana, kamar yadda ta sanar mata ita take kiran Haneefah video call, Haneefah har mamakin Raihana take.


*** ***


Haka rayuwa takasancewa Haneefah a birnin London, kullum cikin karatu take ita da Raihana, babu ruwansu da kowa. Allah cikin ikonsa ta hada qur'anin ta baki daya, da sauran littataifai wadda Raihana ke biya musu, Raihana ta zamo kawa gun Haneefah sannan malamarta. Hakan yasa Haneefah take dada ganin girmanta.


Tunanin Yusuf ya daina damunta sosai, sai randa abin ya taru ya mata yawa sai ta fita ta nemi guri shiru tana mai tunanin shi sannan bata gajiya da yi masa addu'a da dukkanin zuri'arsa. Karatu ya fara tsanani domin ko wani lecture sai sun fita asibiti. Nan suka yanke shawaran ko babu darasi su rika fita asibiti, in sunje zasu nuna ID card nasu. Kasancewa ba wani aiki bane sosai suke a radiography Haneefah takan wucewa gynecology department dake asibiti, nan ta fara sanin abubuwa da sama game da fannin.


Raihana tana lura da yanayin da Haneefah take a sanda ta tuno Yusuf, kyaleta take ra fada mata komai da kanta bazata takura mata ba amma tana sakata addu'a Allah saukaka mata komai.


Kullum waya suke da mutanen gida, tana kiran inna suna gaisawa sai dai inta kira yayun nata ne basa daga waya harta gaji ta daina kira.


Yau asabar babu makaranta, Raihana tana waya da mamarta ita ko Haneefah tsaye gaban madubi take cikin bandaki tana karewa gashinta kallo, yadda yayi tsayi yayi baki tace lallai man gashinnan ya karbeta. Nan ta kurawa kanta ido, ta kara fari tayi kyau, kurajen fuskarta duk sun tafi ga yadda fatarta take sheki. Tace lallai wannan garin ya karbeni babu abinda nake shafawa amma dubi yadda nayi kyau? Menene sirrin? Yayan itatuwa tabawa kanta amsa, kullum cikin shansu take ga ruwa da take sha akai-akai wannan ma wani sirrine ne daya kamata mace ta rike.


Ta fito tana shiri Raihana tace zuwa ina? Asibiti in zaki bini ta amsa atakaice. Itama tashiwan tayi suka fito a tare. Da kafa suke tafiya dan tsakaninsu babu nisa.


Yana kallonta har suka zo suka wuce. Kevin dake kusa dashi yace guy gaskiyan ka yaran suna da kokari yakamata musa su cikin team namu koya kace? Nan ya juya kallon abokinsa yace bakar ta fi burgeni.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼34


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Dr Mubarak yace haba Haneefah bance kada ki nunawa wadannan mutane kwazonki ba? Shine ana meeting da manyan mutane kika sako baki toh gashi yanzu sun rikeki zama ya kama ki a wannan garin, amfani dake zasuyi tayi! Karshema su hanaki karatun Kash!! Mesa kikayi haka Haneefah??


Tunda taga ransa ya baci hawaye ya taru a idanunta, cike da muryar da na sani tace Dr dan Allah kayi hakuri, wlh banqi jin maganar kaba gani nayi ceton rai za'ai shiyasa. Nan Haneefah ta soma hawaye tana mai bashi hakuri.


Ganin yadda take hawaye yasa yaji babu dadi ya soma lallashinta sai da ta tsada hawaye yace kimin alkawarin kada ki sake yin haka sannan kada ki qi karban aiki da dukkanin abinda zasu baki, babu plan nasu ya hau kanki muddin baki karba ba zasu san anason hanaki zama anan daganan zasu nemi mutanen da ke mu'amala dake susan gaskiya, kada kiji tsoro Allah na tare dake in munje anjima ki kula jin dadin ki da aiki kingi?


Tace toh insha Allah bazan sake ba, zanyi yadda kace. Suna tattaunawa suka ga Kevin ,Rohan da Raihana sun nufo su. Bayan sun gaisa da Haneefah ta gabatar masa da kowannen su duk da yana jin labarin kowannen su. Ya nuna farin cikin sa yadda suke tare da qanwarsa, fatan samun nasara ya musu sannan suka nemi guri suka zauna.


Duk motsin Haneefah akan idon Dr Mubarak, mamakine yarinyar take basa, bai taba zaton haka take sharp-brain ba, bangare daya kuma tausayinta yake ko son ta yake? Duba agogo yayi yaga awa dayan yayi, dan haka ya sanar da Haneefah su tafi office din Dr Michael.


Dr Charlie ya dubi Dr Michael yace mesa kayi saurin yanke shawarar bata aiki kuma ita daliba ba yar kasar muba? Dr Michael yayi dariya yace nasan zakayi mamaki amma zan zo ka duba asibitin John akwai wadda ya kaishi tashe da yawan patient?


Charlie yace a'a, Dr Michael yace tara baqaqen fata yayi cikin asibitin domin ana samun gifted cikinsu, mu turawa mun fisu bincike amma su sunfimu saurin fahimta, atakaice tsanarmu garesu yasa suka gane harya kaiga suna zuwa qasarmu domin su kwashe abinda muka bincika, ganin haka yasa John da zarar dalibi ya kammala makaranta zai dauke shi aiki da albashi mai tsoka, da taimakon wadannan ya gina asibitin shi. Nasan asibitina yayi suna amma wannan yarinyar zata tada min asibiti ya zamto duk duniya anaji da asibitina, bakai mamakin yadda cikin qanqanin lokaci ta bani amsa ba dazu a meeting? Kuma tana 200level in takai gaba ya zata kasance?


Cike da fahimta Charlie yace hakane, yanzu sai a bata gida a cotest na qananan likitoci da mota da albashi mai tsoka.


Dr Michael yace ashe ka fahimta, suka kwashe da dariya. Dai dai nan su Dr Mubarak sukai knocking, aka basu izinin shigowa. Suka sami guri suka zauna. Haneefah ce ta nuna farin cikinta game da aikin da suka bata.


Dr Michael yace in bazaki damu ba har masters naki zamu so kici gaba anan kuma asibitine zai dauki nawinki. Haneefah ta kalli idon Dr Mubarak baice da ita komai ba tace ranka ya dade zanso na karasa karatun nawa kafin in dauko da wannan maganar sannan zan nemi shawaran iyayena duk da nasan ba zasu kiba farin cikin sune ace yarsu tana aiki a wannan asibiti.


Sunji dadin furucin Haneefah nan suka mata albishirin da gida, mota da albashinta kimanin dubu dari da hamsin matsayinta na qaramar staff. Ba Haneefah har Dr Mubarak yayi mamaki. Charlie ne ya kaisu har gidan da kyakykyawar motar ta a fake a gaban gidan. Tsarerren gidane wadda ya kunshi komai na bukata a ciki, babban falo da dakuna uku. Komai na cikin yayi amma Charlie ya tambayeta ko akwai abinda take son canza wa ciki? Haneefah tace babu komai. Yace zata iya tarewa ko yanzu ma. Dr Mubarak yace abari ko zuwa gobe sukai sallama ya tafi.


Bayan sun zauna Dr Mubarak ya dubi Haneefah yace kinga da irin wadannan ababe suke zolayar mutane, kuma na tabba ke bazayyi tasiri akanki ba. Haneefah ta dago ido suka hada da Dr tace yaushe kazo ne?


Dab da zaku shiga meeting, shine na biyo ku, dalilin zuwana shine inason tafiya dake Egypt an wakilceni wajen yaye dalibai wato su Nana.


Tsantsar farin ciki ya bayyanu fuskar Haneefah. Dr nagode Allah saka maka da alkhairi, nayi farin ciki kwarai. Yace babu komai saiki soma shiri jibin da safe zamu tashi sannan kada ki sanar da Nana ina son muyi suprising nata.


Haneefah doki take harta iso hostel nan take sanar da Raihana tafiyarsu jibi sannan take shaida mata sabon gidanta. Da dare Haneefah taje ta muna musu domin da Raihana zasu koma gidan da zama, sun yaba da tsarin gidan, ta damka wa Raihana makulli tace kafin suzo tayi abinda ya kamata dan ba zasu wuce kwana biyu ba.


**** ****


An fara gudanar da taro tukun jirginsu ya sauka, da saurin gaske tukun suka iso amma dab ake da kammalawa. Basu wuce minti goma sha biyarba aka gama taron, kowa yana dauka hoto.


Nana saye take tana murmushi farin ciki, bakin cikin ta kuma shine bata ga dan uwanta daya da zasu dauka hoto a wannan rana ba. Ji tayi an rungumeta ta baya, Haneefah ta daga wayarta tace say cheese! Ta dauke su a hoto, hotuna kusan goma sukai kafin Nana tace tsaya tukun ya akai kika zo? Nuna mata Dr Mubarak tayi tace ga wadda ya taho dani je ki mishi godiya. Godiya harda hawaye tayiwa Dr. Shiko ganin Haneefah cikin farin ciki yasa yaji duniyar ta masa dadi domin ya rinyar ta soma birge sa _toh fah_


Nana tayi murnar ganin yar uwarta, sannan tayi mamakin jin aikin da ta samu amma sai da ta gargadeta akan tabisu a hankali. Nana dai baki yaki rufuwa ganin Haneefah ta canza ko dai ta riga ta mance da Yusuf ne? Ta so tambayarta amma tsoron kada ta canza musu mood yasa ba tace komai ba. Washe garin ranar Dr da Nana suka bi jirgi zuwa Nigeria ita ko Haneefah take jiran jirgi zuwa London.




Taxi ta tara har zuwa bakin makarantar su. Bayan ta sauka ta nufi hanyar hostel. Tana zuwa ta tarar a kulle. Waya ta ciro ta kira Raihana tace kina ina nazo fa? Tace ina asibiti amma yanzu zanzo sabon gidan mu, murmushi Haneefah tayi ta katse wayar.


Tafiya take a kafa harta iso bakin Cotest, daidai zata knocking kofa taji horn. Motarta ta gani Raihana tana ciki. Cikin fara'a Raihana ta sauko tace amin afuwa nayi karanbani.


Haneefah tayi dariya tace haba dai gidan ma an baki bale mota. Ta bude mata suka shiga, subhanallah! Haneefah ta fada ganin yadda falon yayi kyau ya tsaru, Raihana taja hannun ta zuwa kitchen nan ma ya hadu domin irin tsarin turawannane masu tsananin kyau, zagaye gidan tayi cikin tana mamaki harta iso sama inda aka yi domin shakatawa, glass ne ya rufe gaban sai gefen wardrop na takardu da kujeru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login