Showing 9001 words to 12000 words out of 74305 words

Chapter 4 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt

25 Jan 2025

5168

shirin shiga in kiraki, kin gama zaku wuce ko? Rasa abin fada tayi.


Shiko ganin idonta a kumbure alamun tayi kuka sosai sai hankalinsa yadan tashi. Cikin sauri ya tashi ya mikawa auwal hannu yace kada mu makara zamu wuce. Sukai sallama.


Tuki yake amma hankalinsa baki daya na kanta. Ita ko tunda ta shiga ko kallon inda yake batayi ba. Ina kwana yace da ita tace lfy atakaice. Tabbas akwai wani abu domin tunda yake da ita bata taba amsar gaisuwan shiba sai dai ta kara gaishe shi. A sanyaye yace jiya nakira amma baki samu daga waba. Tace eh wani abin nake. Tambayanki nakeson yi. Kina da ra'ayin auren mai mata? Lumshe ido tayi sannan tadan kishin gidu tace meye aibunsa in har yana tattare da abubuwan da annabi ya kwadaitar mu auren irinsu? Wasu matan suna wahalar da kawunansu wajen zaban miji, suna ganin aure shine jin dadin rayuwa. Duk macen da fassara aure haka ko shakka babu cikin wahala zata kasance... mika al'amura ga Allah yafi komai. Murmushin jin dadi yayi yace zaki aure ni? Dariya tambayar ta bata tace auren irinku sai mata masu ilmi da class kyawawa irinku ta karashe maganan da zolaya. Yace bakisan irinku kunfi tsada ba? Ga namiji wadda yasan me yakeyi baya bukatar komai gun mace sai kyawun tarbiyyarta.


Murmushi tayi ta rufe idanunta sannan tace aikai ka samu. Mu kabari a baya. Dadin hira take ji dashi, haka shima. Cikin yar tafiyannan sun dada fahimtar juna, kusan ra'ayinsu daya.


Sun shigo garin kano tace ya sauketa ta karasa gida yace kiyi hkr in kaiki. Ba yadda ta iya haka ta hakura tafada mishi anguwan nasu. Dab zasu shigo layinsu tace saukeni anan. Ya dubeta inane gidan? Tace nidai bazan qarasa dakai kofar gida ba. Parking ya gyara sannan ya dubeta yace haneefah kalleni. Dagowanta suka hada ido yace ina sonki haneefah, so na hakika. Batace komai ba sai hawayen da ta soma zubarta. Motan ta bude ta fito ta dauki kayanta sannan tayi wucewarta. Kwala mata kira yayi amma kamar bada ita yake ba. Jan motarsa yayi yadau hanyar gidansu.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼12


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


A hankali ya bude motar ya fito. Ganin motar abban nasa yasa ya nufi bangaren shi. Zaune suke suna tattaunawa ganin dansu yasa suka dakata tare dayin murmushi. Sallama yayi suka amsa. Cike da nutsuwa yake gaida iyayen nasa. Abban nasa yace ko sanarwa babu. Murmushi yayi ya sunkuyiyar da kansa sbd. Momy tace tashi kaje ka huta zansa aisha ta kawo maka abinci, yace toh ya mike ya fice.


Sallama tayi ta tura kofar, kwance ta taddashi sanye da jallabiya. A hankali ya bude idanunsa yace sannu aisha. A ajiye tiren hannun nata ta fara zuba masa abinci ta soma gaidashi, cike da kulawa yake amsawa. Ta mika masa ya fara ci suna hira irinta wa da qanwa. Bayan ya kammala ta kalleshi sosai ta fara magana, yaya yanzu bazakai wani abu game da auren ka da Rahma ba? Wlh bata dace da kaiba. Yarinya an sangartata bata da nutsuwa ba tarbiyyar kirki ba? Murmushin takaici yayi yana kallon kanwarsa dake matukar tausaya masa yaace toh ya zanyi? Babban sirrin zaman rayuwa da jin dadin gobe kiyama ya tabbata ga mutumin da shine wadda yake yiwa mahaifiyarsa biyayya, nabi ko wace irin hanya domin in kawar da zancen auren amma maganar har yanzu tananan. Allah na mikawa lamurana ya dubamin yabani ikon rabuwa da ita lfy. Na danne zuciyata zan auri zabinta tunda itama zata barni in auri zabina. Cike da tausayawa aisha tace Allah tabbatar da abinda yafi alkhairi agaremu yace ameen.


Bayan fitar ta ya kawo waya domin kiran haneefah domin muryarta kadai yake sonji amma yaji wayar a kashe take.


Tafe take tana sharar hawaye. A hanya suka hadu da ahmad tayi saurin goge hawaye yace kukanne har yanzu baki daina ba? Girma yazo miki gomma kin hakura. Murmushi tayi domin ita kadai tasan abinda ke damunta.


Tarar da umma da kannenta tayi suna kallo, suka mata sannu da zuwa. Tadan taba hira sannan ta wuce dakinsu.


Kwance take tana tunanin kalmar yusuf. Ya cancanci a soshi amma yaushe ne auren sa da zabin mahaifiyarsa? Mafita dayane matakin da na dauka yayi.


Hira suke amma hankalinta nakan yusuf. Shi take gani tunaninsa ya hanata sakat. Mikewa tayi ta musu saida safe ta nufi dakinsu. Tagama shirinta tsaf ta hau kan gado a sannan taji kewar yayarta sosai tace Allah sarki nana da kinanan hiran kafin mu kwantama daban. A hankali ta bude wayarta. Babu wani tunani takirashi.


A hankali yake magana cike da ladabi momy baqin maganarki nake ba. Kimin uzuri ayyukane suka shigemin gaba. Tace yusuf hakurin mu yakare shekaru biyar ba wasa bane, yarinya kowa ya fito tace kai take jira to wannan karan ya zamo maka dole ka aureta ko in hanaka auren zabin taka tunda yan matanne ke naka wasa da hankali. Cikin sauri ya dago kai yace aa momy baza ai haka ba, na miki alkawari zuwana nagaba sai afara shirin bikin. Badan taso ba tace Allah kaimu.


Yana shiga dakinsa yaji wayansa na ringing, daga wanda zayyi yaga sunanta cikin sauri ya daga tare da yin sallama. Amsa sallamar tayi daganan bata karace komai ba, katse wayar yayi ya sake kiranta. Tace ya gajiya, Alhamdulillah ya amsa. Shiru kamar dakiku biyar tafara magana yusuf nagode da kasancewar cikin rayuwata sannan nagode kwarai da gudunmawarka kan cigaban addinina amma kasani bazan iyaci gaba da zama dakai ba... shakuwar inta yawaita zan kasance cikin tsananin damuwa, kai kuma aure zakayi kaga ko gonda na hakura kaje ka auri zabin mahaifiyarka.


Ajiyar ziciya yayi yace haneefah pls kece zabina, kada kisa wannan ya zamo hujjar rabuwarmu, ina sonki so na hakika, ina kwadaitar wa zuri'ata samunki a matsayin uwa, sannan suruka wajen iyayena. Nasanki na yarda da tarbiyyarki.


Jin yayi shiru tace hakane amma ina gudun bacin raine, iyayena da yan uwana suna sona nima ina sonsu, bakin cikinsu nawane musamman mahaifiyata, ina tsoron kada wani abu yaje ya dawo. Murmushi yayi yace haba haneefah? Duk wanda ya ji tsoro zai samu damuwa a zuciyarsa, amma ban da wanda ya ji tsoron Allah. Shi kam wanda ya ji tsoron Allah zai samu aminci da kwanciyar hankali a zuciyarsa... addu'a makamin mumini ce ... Don haka muyi riqo da addu'a kuma mu dogara da Allah ko yaushe komai zaizo mana da sauki, nidai pls amincewar ki nake bukata.


Gaba ki daya ya gama daureta. Itadai tana son shi amma kamar tana hango akwai matsala.... sannan yayi gaskiya duk zuciyar da tayi riko da Allah to tabbas babu wani sauran damuwa da zai dameshi.


Jin tayi shiru yace momy ta bani daman auran wadda nake so, ko bakya tunanin zanyi adalci tsakanin? Murmushi tayi tace kai mutum ne da zaka zaunar da wasu ka musu nasiha kan suyi adalci tsakaninsu, ina da tabbacin kai adaline.


Murmushin jin dadi yayi yace godiya nake. Taci gaba da cewa zan kasance tare dakai, sannan na baka amanar rayuwata baki daya, yadda ka tarbiyyantar da ni matsayin masoyiyarka haka zan kasance. Cike dajin dadi yace kin amince kina so na kuma zaki aure ni?? Tace eh na amince Allah tabbatar mana abinda yafi alkhairi kuma in hakan ta faru pls I
banason zama gida daya tare da ita in zayyu. Cike dajin dadi yace ameen, nayi alkawarin rikeki amana sannan zanyi haka da yardan Allah. Nan suka soma hira tamkar sun jima suna tare.


***** ****** ****** ******


Cike da takaici tayi wulli da wayar dai-dai inda mum tata tashigo. Cike da damuwa ta qaraso ganin yartata kamar wani abu na damunta. Baby rahma waya tabamin ki cikin kuka tace mum tun dazu nake nemanshi amma number busy ko da wa yake waya, wlh mum kiyi wani abu hakurina ya kare kibarni kawai in auri wani. Haba rahma saida aski yazo gaban goshi? Mum baya so na, masu kudi da dama sun nuna suna so na do ki bari ince wani ya fito ni wlh nadai na sonshi, cikin cigar lallashi tacewa yar tata aurenma ai kowanne ba iri daya bane, dan uwan naki na da kudi kuma harkanshi bunqasa yake.. zaki fi jin dadi zamanki acan, in kukai aure kika haifo na miji saiki fito ki auri wadda kike so in kinyi hakan kin gama min komai. Cike da kauna ta riko hannun mahaifiyar tata tace mum na miki alkawari aikata abinda zai saki farin ciki, amma ki gaggauta aikata hakan. Mum tace to shikenan in watannan ya kare da kaina zanje kano sai ansa ranar aurenku zan dawo.
*Dr HANEEFAH* 👩🏼13


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Zaune suke ita da hadiza cikin makaranta kasancewar zasu fara zana zarabawar sati mai zuwa, sunzo duba time table. Hadiza tayi murna jin maganar kawartata sosai tayi mata fatan alkhairi. Suna cikin magana taji wayarta na ringing, cike da murmushi ta daga tare da yin sallama, shima murmushi ya saki suka gaisa yace ina cikin asibiti. Haneefah tace mun koma makaranta yace ok ina zuwa.


Kawarsu suka hango ta inda suke zaune mai suna sadiya. Tayi sallama ta zauna ta ciro powder ta fara. Haneefah data kasa hakuri tace sadiya ina zaki haka da safe kina kwalliya? Wlh wani saurayinane zaizo shine nake dan shafe shafe domin nayi haske a idonsa, kinsan mazan yanzu in baka kwalliya ko na soyayya bazaka samu ba bale na aure.


Sama har kasa haneefah ta ke kallonta hadiza dake mintsininta alamar tayi shiru haneefah tace wlh saina fada, sadiya mesa matan yanzu kuke wahalar da kanku? Dubeki kina da kyau kina da haske amma saida kika kara da bleaching, kinsan hakan zai taba lafiyarki ko? Wato baza'ai so Dan dan Allah ba. Na kasa gane meke yawo a kawunan mu, kowa ya damu daya kasance yana da saurayi ko aure wannan abinfa nufi ne na Allah, misali matan yanzu sun damu da sai sunyi aure dan sunga kawayensu duk sunyi, sun manta cewa kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwar, tun kafin muzo duniya Allah yarubuta mana duk abinda zamuyi kuma da lokacinsa. Muyi la'akari da auran yanzu kowa zaman hakuri yake, babu wadda yake zaman kwanciyar hankali 100% sai kinyi shi domin Allah zakiji dadin hakan.... lokaci bai kure mana ba mu dage da addu'a Allah kawosu lokaci mafi alkhairi kuma wadda zamu kasance domin Allah.


Hadiza ta nunfasa tace tabbas maganarki gaskiyane, gaggawa aikin shaidan musamman a lamari irinta aure. Matan yanzu sun fison a musu karya, wani namijin dan yana sonki zakiga ya fada wannan harka. Abin takaici akwai matanda basa biye kodayinsu, wani namijin zaita kashe miki kudi da zarar ya aureki shikenan, wani bazai kashe ba sai kinshi go gidanshi, shiyasa ake cewa mu dage da addu'a sannan mubarwa Allah sabinmu. Allah bamu mazaje nagari dukkaninsu suka amsa da ameen.


A sanyaye sadiya ta tashi tabar gurin, suka ci gaba da tattaunawa kan matsaloli irin ta rayuwa. Suna zaune taji wayarta na ringing tana dagawa ta masa kwatancen inda zai sameta.


Sanye yake da fararen kaya fari tas, komansa fari da glass da ya matukar karbeshi. Sai daya kusa hadiza ta lura da irin kallon da haneefah take mishi hadiza tace malama aja aji irin wannan kallon, harara ta daka mata.


Ya karaso tare da sallama suka amsa, hadiza ta basa guri ya zauna tace Alhamdulillah kawata ta sanar min komai, naji dadi kwarai, sannan ina tayaka farin cikin samun haneefah, badan ita kawata ba, haneefah ta kasance diya tagari wadda kowani irin namiji zayyi alfahari kasancewa da ita matsayin mata. Allah ya tabbatar mana abinda yafi alkhairi. Dukkansu suka amsa da ameen banda haneefah data amsa azuciya domin tun isowarshi kanta sunkuye, kunyarshi sosai takeji. Hadiza ta musu sallama ta tafi.


Kallon ta yake yanajin wani irin jin dadin. Yafara magana a hankali bazaki dago ki kalleni ba? Shiru tayi. Murmushi yayi yace nagode wa Allah daya nunamin wannan rana gani gake a matsayin masoya. Allah bamu ikon cimma burin mu. A hankali tace ameen. Yace yaushe zaki gama makaranta? Shekara mai zuwa insha Allah warhaka mun gama, yace Allah nuna mana ameen ta amsa. Ya qara jefo mata tambaya kina da ra'ayin muyi aurene ko sai kin kammala? Bani da raayi nafiso inna kammala sai ayi bikin amma anan zamu zauna ko? Yace aikin nawa fa cike da zolaya tace saika ajeni anan, inda nake aiki zamu zauna nima zanso ki kammala amma kafin inaso inje gida su abba susan da ni. Tace ba komai yaushe zaka je? Ko yanzuma a shirye nake domin nayi sallama da mutanen gida inna tashi zan wuce. Tace yanzu dai babu kowa gida sai dai in kazo wani lokacin. Toh shikenan duk yadda kikace. Suka dan taba hira sannan ta damesa da ya tashi ya tafi kada ya makara.


Taku suke a tare har suka iso inda yayi parking. Tace next month insha Allah auren hadiza zaka zo? Yace mezai hana in aka gayyo to ni, Allah kaimu. Yace inga wayar da kike amfani ta nuna masa gionie p4 yace shikenan. Allah baku sa'a a exams naku, nasan kina maida hankali sosai a karatu, ni mutum ne mai son karatu sosai dan haka ki dage kinji ? Ta amsa tare da murmushi. Sallama sukai kamar kada ya rabu da ita.


Nana takirata take sanar da ita sun iso lfy har sun gaisa da umma da abba. Cike da farin ciki haneefah ta sanar da ita batun yusuf, fatan alkhairi tayi mata sukai sallama.


Bayan sun kammala abinda zasuyi haneefah ta wuce gidan auntin ta muhibbat. Taci sa'ar samun humaira, anan take sanar dasu batun yusuf sannan take sonjin ra'ayinsu game da lamarin.


Humaira tace yanzu wazai fara aura? Ke ko ita? Kuma har kinsawa ranki zama da kishiya, dukkanin mu bamu da kishiyoyi haka muke fatan kuma ku soma shiga as first wife, sbd ko yaushe mune kan gaba, don me kike gaggawa? Haneefah tayi murmushi tace tabbas naji mata da dama suna fadin haka, amma nawa ganin ba dukkanin mata suke rike matsayin first wife, sbd duk sanin da kikai masa danya qaro aure in kika daina, wadda yazo tazo ta fiki kwazo ta karbeshi kenan. Mata mudaina gadara da hakan... lokacine da zamu ninka kyautatawarmu ga mazajenmu. Kinga wlh banajin tsoron tazo ta sameni ko in sameta abin bukata shine ki tsaftace zuciyarki sannan ki dage da dukkan abinda zai dauke masa hankali.... muhibbat ta buge kafadunta tace shisa muke ji dake haneefah, Allah tabbatar muku da alkhari dukka suka amsa da ameen.
*Dr HANEEFAH*👩🏼 14


Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖


Soyayya ake na gaskiya, tsaftatacciya wadda babu yaudara ciki. Suna mutunta juna tare da kokarin kawar da duk wata hanya da zasu samu sabani tsakaninsu. Hakan yasa dukkaninsu sunyi dace sosai. Bangaren haneefah ko banda kulawa da soyayya da take samu, ta samu qaruwa sosai game da addininta domin abubuwa da dama tasani da qarin haske akai, hakan yasa ta dada rikeshi.


Kwanci tashi ba wuya gurin Allah. Yau su haneefah suka gama jarabawarsu tare da hutun sati biyu. A daren ne take sanar da yusuf ta kammala exams. Yayi mata fatan alkhari tare da tambayarta inta gama wani course takesonyin specializing akai? Tace nidai har yanzu ban yanke shawaraba, hasalima ba so nake yiba.


Cike da mamaki yace mesa? Accoutr nake son zama tukun aka turoni nan, Allah akwai wuya. Yace haba dearie nasan zaki iya, a matsayinki na mace bai kamata ki karanta wannan fannin ba, kinsan aikin dan jama'a zakiyi, Allah kadai yasan irin ladan da zaki samu. In zaki bi shawarata inason ki zamo gynecology.


Zaro idanu tayi jin abinda ya ambata tace ina ni ina waccan gurin! Nida yaren kuma ban gama koya ba.


Cikin rashin fahimta yace wani yare? Turanci mana ta bashi amsa. Duk da dakewar da yayi saida abin yasashi dariya sosai. Jin yadda yake dariyar hakan yasa taji dadi, da sauri ta danna record. Yace amma kin sani dariyar da na dade banyi ba. Aishi karatu fahimta yake bukata, in wannan matsalarne zaki koya da yardan Allah.


Haka suka kasance kullum cikin kyautatawa juna. Sun matukar kara shakuwa.


***** *****


Auren hadiza sai matsowa yake yi domin saura wata daya. Haneefah sai faman shiri ake. Ana saura sati uku suka fara rabon anko. Ga karatu sai kara zafi yake.


Sunje gidan wata qawarsu da sukai makaranta tare tsokanar haneefah saura ke. Nima insha Allah bazan jima ba cewar haneefah.


Kawar tasu tace inada matsala, tun dana sami cikinnan na tsani mijina banson ganinshi. Ko zaki bani shawara. Haneefah ta fara bayi;


Idan mace ta Sami ciki me ya kamata tayi game da muamalar ta da mijinta???


A: gudunsa zatayi su fara wasan buya da hantara??


Ko


B: Naniqeshi zatayi tare yin wasu abubuwa na yarinta da shagwaba??




Lokuta da dama idan mace ta Sami ciki babu abinda ke fara zuwar Mata Sai tsanar mijin ta...bawai ko wace mace ke Hakan ba...Amman 80% haka muke.


To anan abinda ya kamata mace tayi a irin wannan period din shine.


Dolene ta daure bawai Sai tana soba..A'ah saidan rikewa kanta wata dama da take da ita domin Har idan ta bari ta kubce Mata to dawowarta Sai a slow.
Ki kasance ko yaushe kina tare da megidanki Kamar yarda kika saba koma fiye da hakan...tunda a wannan lokacin shi namiji yake jinki fiye da ko yaushe a baya...saiki dage wajen jikawa....surfawa...dakawa...da Kuma tukawa...hakan zai Kara Miki martaba sosai domin kin bashi damar yaso abinda yake da bukata darajar Ki zata Kara karuwa can kololuwa


Amman rashin samun hakan zai iya jawo Miki matsaloli Kamar haka zai fara Zaman waje...maana majalisa a tunaninshi daya dawo gida yaga ba daidai ba maana baki jika mashi kayan wankin shiba...bare yasa ran Zaki wanke mashi wata kilama harda guga...gara ya zauna a waje idan kinyi bacci saiya lallavo ya kwanta.
Wata matsalar idan ya hadu da mugun aboki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login