Showing 45001 words to 48000 words out of 74305 words
Chapter 16 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
ban aureki yanzu ba inada tabbacin nine mijinki ya tashi ya fice.
Sanye take da habaya baki tana tuki zuwa gidan aunty humaira, zata je ta dauko snacks. Bayan ta sauka ta kulle motar ta fito taga wani mota gaban nata mai bala'in kyau, kallon motar take har tashiga gidan.
Mai gadine ya taimaka ta fito da su ta bude boot suka aje. Aunty humaira tace sai anjima zamu zo saboda akwai sauran ayyuka daban kammalaba.
Ta fito tana takawa a hankali har zuwa bakin mota. Har zata shiga motar ta ta juya zata qara kallon motar domin ta mata kyau, Dammm! Taji gabanta ya fadi ganin sa a tsaye waya makale a kunnensa.
Shima abinda ya faru dashi kenan, yakasa ci gaba da wayar. Kallonta yake tamkar bazai daina ba. A hankali yazo gabanta yana kallonta yace HANEEFAH!
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼47
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Haneefah ta nunata yatsa tace wlh kika kuskura kika qara jefa ta da kalmar rashin kunya sai kinga abinda zan miki, in kina yiwa wasu suna kyaleki amma ni baki isa ba.
Wani likitane ya fito yace meke faruwa? Nan likitar ta fashe da kuka tace marina tayi kuna banyi komai ba.
Likitan ya zaro idanu yace mari? Ya matso kusa da Haneefah yace mesa kika mareta? Kinsan ita wacece?
Haneefah ba wannan yakamata ka tambayeni ba, tambayata zakai menene dalilin marin. Na mareta ne saboda ta kiramin mahaifiya KE, yanzu kai in akaiwa mahaifiyarka haka meza kai?
Shiru yayi yana kallon Haneefah. Haneefah tace bata san aikin ta ba, domin a tsarin kwantar da hankalinsu yakamata tayi ba rashin kunya ko isaba da gadara ba, gadaranki kinyi karatu kin zama likita amma ke ba komai bane tunda baki iya treating mutane ba...
Jin muryar Dr Mubarak tayi yace meke faruwa anan? Likitar cikin kuka tace marina tayi.
Dr Mubarak yace me kikai har aka mareki? Kada ku tara mana jama'a ku sameni a office. Da sauri Haneefah tace ina da patient zan iya shiga in dubata.
Dr Mubarak yace zaki iya shiga. Da sauri ta shiga labour room, ta tarar Aisha na fama. Bazata manta fuskarta ba. Da sauri ta nufota ta kama hannuwan ta tana mata sannu.
Su Momy ikon Allah suka tsaya gani, tabbas wannan Haneefah ne. Ita salma bata taba ganinta ba dan haka bata ganeta ba.
Aisha ta kalli Haneefah tace mutuwa zanyi, dan Allah ki kiramin Momy. Haneefah tace bazaki mutu ba kirika ambaton Allah, zaki sauka lafiya.
A hankali Haneefah ta fara duba matsalarta, nan ta gano kwanciyar yaronne ba daidai ba, a hankali ta gyara kwanciyar sannan ta kara ta, cikin taimakon Allah ta haihu kyakykyawar yarinya fara tas. Mikawa nurses din tayi suka amsa domin gyara ta. Ita ta gyara Aisha ta kaita bed rest sannan ta fice.
Neman kaucewa su Momy take amma saida suka ganota. Salma ce ta tare ta tare da tambayarta ya ake ciki? Haneefah tace ta sauka lafiya, ta haihu mace duk suna lafiya yanzu zanje in karbo allura ne ina sauri.
Ta saci kallon Momy ta lura duk kunya ta lullubeta, wucewa tayi abinda. Hadiza da take jiranta bakin kofa ta jawo hannunta tace Haneefah ina ke ina kaiga marin yar commissioner? Haka fa take da wulaqanci.
Haneefah tace ni nunamin office din Dr Mubarak inje in qara mata marin. Hadiza ta zaro ido tace wato hanyarzu akwai sauran halayyarki da baki daina ba, kina da saurin hannu yakamata ki daina.
Dai-dai suka shigo office din Dr. Zaune ta same su ,itama ta nemi guri ta zauna.
Haneefah ne ta soma magana, labayar mishi abinda ya faru tayi sannan ta qara da cewa babu ta riga ta haihu. Cike da mamaki suke tambayarta ta haihu?
Haneefah tace ai gaggawar kune yasa kuke ganin sai CS, yaron breach yake in kuka gyara kwanciyar kuka dan karata kasancewar primi ce zata haihu, sannan yadda kike tsawatar da relative na patient bai kamata ba, wannan ilmin da kika samu ko kinsan Allah ne ya zabe ki amma kike wulaqanta bayin sa, sam dan Adam bai kamaci wulakanci ba, koki dauka maganar da nagaya miki ko kada ki dauka wallahi kika kuma wulakanta wani har raina ya baci mari kam zaki sha.
Murmushi Dr yayi ya kalli Haneefah yace am proud of u, Allah albarkaci karatun ki, ke kuma suwaiba ki daina ta kama da komai dan cikin qanqanin lokaci zaki rasa komai ki koma ba komai ba, dan haka wulaqanci babu kyau Allah kyauta.
Jikinta yayi sanyi, a hankali ta dubi Haneefah ta bata hakuri. Murmushi tayi tace ba komai. Dukkansu suka mike dan zasu fita taji muryarsa yace ki tsaya inason magana dake.
Kamar bazata juyo ba sai kuma ta koma ta zauna. Azuciyarta tace wannan karon ka daukomin maganan SO ko AURE saina baka mamaki...
Katse mata tunani yayi da cewa yaushe zaki koma? Tace jibi zan koma ta bashi amsa kai tsaye.
Shine bazakije gaida Ramlat ba? Yanzu nake son tafiya inna fita daga asibitinnan. Murmushi yayi ganin yadda take bashi amsa a takaice yace ina fata bakya kula kowa domin nariga kowa duk wadda kika saurarama bata lokacinsu suke domin nizan aure ki.
Murmushi Haneefah tayi sannan tace yanzu kai aurene kake son yi? Baka tunanin rashin dacewar hakan? Duk abinda kukai min da matar ka sakayyar da zan mata kenan? Ka manta irin son da kakewa matar ka, kai da ba kinka kake cewa bazaka iya yi mata kishiya ba! Waiku mesa kuke haka ne, in kunsan bazaku iya rayuwa da mace daya na mesa kuke sawa matayen naku arai, ina so yazamo lokaci na karshe da zaka furtamin wannan kalmar aure domin saboda ni bazan lamunci bacin ran matar ka da ta daukeni tamkar yar'uwarta ba kaima na dauke ka tamkar yayanane...
Bata qarasa ba taji ance kada ki hana aikata alkhairi dan farin cikin wani.. tashiwa tayi tsaye ganin Barrister Ramlat.
A hankali ta shigo ta zauna kujerar da ke fuskantar Haneefah tace zauna ya kika tsaya? Jiki a sanye Haneefah ta zauna tare da sunkuyar da kai.
Barrister tace tabbas nasan mijina yana so na, kuma munyi zama na amana dashi, bai taba nunamin qin abinda nakeso ba don haka dama ne tazomin tazan barsa yayi abinda yake so. Nasan dalilin da yasa yafara sonki har yake sha'awar aurenki, Haneefah ke yarinya ce mai saurin shiga rai, kinsan yadda zaki bi da mutum ku zauna lafiya kuma akwai abinda baki sani ba, kin zabi rayuwa bisa tsarin addini sannan kika samu karbuwa gurin mahaliccin ki
Duk bawa daya kasance mai tsantsar biyayya ga mahaliccin sa babu shakka zai kasance cikin bayin Allah da yake alfahari dasu musamman bayin Allah masu tsananin hakuri da wadadanda rayuwar duniya bata gabansu, lokacin da Allah ya so bawansa zai kira mala'ika jibril yace ka shaida na so bawana WANE, sannan mala'ika jibril zai sauko zuwa sama ta farko yace da sauran mala'iku ku shaida Allah ya so bawan sa WANE haka zai rika sanar da sauran mala'iku har zuwa sama na bakwai, a sannan za'a sauko da soyayyar da wannan bawa zuwa doron kasa, sai kiji jama'a suna son bawan Allah.
Ba komai ke jawo haka ba sai tsantsar ibada, sbd haka bazanyi mamaki son da mijina ke miki ba, amincewarsa amincewata ne.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼46
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Shiru Raihana tayi tana kallonta. Ganin kallon yayi yawane tace ciwon ya kusa tashiwa nafarajin alamu, alluran kadai zai iya controlling yanzu babu shi.
Raihana tace inka zo nan da zama fa? Haneefah tace kafin ma zanyi aure. Bude baki Raihana tayi tana kallon Haneefah tace yau da kanki kike furta hakan?
Haneefah ta daga mata gira alamar eh. Tashiga bayi ta wanke fuskarta ta dan shafa powder suka fito. An watse taro cike da dadin rai. Da dare Haneefah take sanar dasu kiran gaggawa ake musu a makaranta dan haka ko sati bazata kuma anan garin ba.
Kowa baiji dadin hakan ba amma suna mata addu'a Allah sa nanda shekara ta dawo cikinsu lfy.
Washe gari aka daura auran Dr Nana khadija da Dr Abdullah. Yan uwa da abokan arziki sun shaida auren sanna ana taya wadannan ma'aurata murna.
Haneefah ba'a samu zama ba domin tana tare da Nana tana serving kawayenta. Barrister Ramla ma ta dawo, ta samu karbuwa hannu biyu a sannan Haneefah take bata hakuri amma ta mata alkawarin zata je mata kafin ta koma.
Da dare akazo aka dauki amarya zuwa tsararren gidanta da duk wadda yagani koda makiyine bai isa ya kushe ba.
Washe gari akai yini nan akabar amarya ita daya.
Haneefah ta soma yiwa jama'a sallama. Hadiza tana wajen aiki Haneefah takirata a waya take ce mata tana hanyan zuwa gurinta domin zibi zata wuce London.
A harabar asibiti tazo ta dauketa zuwa dakin hutawan nurses, nan ta hadu da wata colleague nasu suka gaisa tace Haneefah kema naji labarin auren ki bayyu ba, am sorry inshaa Allah zaki samu wadda yafishi, ke ai kina karatu ma kada ki damu zaki zamo wani abu da har sayyayi nadamar barin irin ki.
Koni nan kin ganni bana kula kowa sai na zamo wani abu ta fanni likitanci.
Haneefah tayi murmushi tace muna damuwa da yanda za ayi mukai Matsayin da za a kira mu da sunaye masu daraja a duniya... Professor, Engineer, lawyer, likita dss.. Amma me muke yi saboda mallakar sunayen matsayi a lahira? Me azumi, me tsayuwan dare, me taqwa? Wannan tambayan na bukatar tunani.
Idan ya kasance kana rayuwa ba tare da yin sunno ni ba, ba wutiri ba sallar walha, ba karatun Qurani, ba azkar, ba azumin litinin bare na Alhamis, ba ka wani aiki da kake fatan ya amfane ka gobe Qiyama. To kada kayi mamaki idan ka rasa nitsuwa a nan duniya. Kuma kada kayi mamaki idan ka ta shi kaga ba kada komai gobe qiyama. Kana gani ana kiran mutane, wannan ya shiga aljannah ta kofar ma su azumi, wannan ta masallata, zumunci, jihad dss.
Uwaisul Qarni (Rahimahullah) yana cewa :
"Da ace mutun zai kama hanyan haduwa da abokan gaba... Sai rigar yakinsa ta masa nauyi ya cire ta a hanya, takwabinsa ta masa nauyi ya jefar, guzurinsa su masa nauyi ya tafi ya barsu. Kawai sai ya hadu da abokan gaba, ba komi a tare dashi. Yaya za ayi yayi nasara a kansu??? Kamar hakane wanda zikiri ya masa nauyi yabarta, sunnoni suka masa nauyi ya kyale su, yin farillai akan lokaci suka masa nauyi yake jinkirta su... Kuma wai a haka yana kukan halin kunci na rayuwa dayake ciki... Shai'dan ya zama shi ke hukunta zuciyarsa. Miskiynnn! Ya halaka kansa tun kan abokan gaba su halaka shi" Misalin wanda ba ya shirya ma lahira kenan. Abokin gabansa (wuta) na jiransa a lahira, ga kuma maganinta atare dashi anan duniya (ibadu da halin kirki) In suka masa nauyi anan ya watsar... ya san sauran.
Dan uwan Iman...
Ka yawaita tuna fadin Allah (Kaico na! Da na gabatarda aikin kwarai domin rayuwata) Ayar za take tuna maka cewa rayuwar duniya ba rayuwa bace. Rayuwan nan dai da kake mantawa dauwamammiya. Lahira ba...
Abinda nake bance karatu babu kyau ba amma yadda muke fifita muzamo wani abu a duniyarne akwai takaici Allah yasa mu dace.
A sanyaye suka amsa da ameen. Kawar tasu tace gashi shekaru sai qara yawa suke mazan ma ba wani son manya suke soba, da zarar kin wuce shekaru ishirin shikenan an dainayi dake.
Haneefah tace inji wa? Saidai baki killace kanki ba, aure lokacine yan uwa mudaina sa irin wadannan tunani a zukatanmu, yanzu ke nawa muke da zamu damu kanmu shekara ishirin da uku zuwa hudu nefa! Ga yayata satin da ya wuce aka daura aurenta, abin yarda da Allah kawai, wasu basa aure da wuri saboda hakan yafi musu alkhairi, wani auren gomma babu tsabar wahala. Dan haka ki kwantar da hankalin ki komai lokacine.
Nan suka ci gaba da hiran su. Haneefah ta kalli agogon hannunta tace zan wuce domin guraren zuwana dayawa yake.
Hadiza bataji dadin hakan ba amma dolene yasa zasu rabu. Tafiya suke har suka zo daidai labour ward.
Daidai sunzo wucewa idanun Haneefah suka sauka kan Momy, ganin wata mai labcourt ta fito tamikawa Momy tace gashi kusa hannu za'a mata CS domin ceto ran danta.
Momy dake cike da damuwa tace yaushe muka kawo ta? Batai nakuda sosai bama muka kawota yanzu za'a mata CS?
Likitar tace ke mata bazaki gaya mana aikin muba, in zaku sa hannu toh in bazaku saka hannu ba zaku iya daukarta ku koma.
Salma tace a'a zamusa hannu kiyi hakuri mudai Allah sa ayi a sa'a. Haneefah tayi hanzarin karban takardan cike da bacin rai tana kallon likitan tace me kika ta?
A wulakance likitar ke kallon Haneefah tace KE! nace da ita, Haneefah ta matso kusa da ita tace maimaita inji?
Zata qara cewa K... bata qarasa ba Haneefah ta sauke mata kyakykyawar mari. Kallonta tayi cike da mamaki tace kika mare ni? Haneefah ta kuma yi mata marin ji kake Tasss!!
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼48
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Sannan na tabbata baki da son kai tunda har kina gudun bacin raina innaji zancen aure, namiji in ya soma maganar aure ba'a iya dakatar dashi, kuma ba yinsa bane yin Allah ne zanfi jin dadi inya auro ki domin nasan halin ki, pls Haneefah ina taya mijina neman auran ki.
Ba Haneefah ba hatta Dr yayi mamakin matarsa. Dukkan su shiru sukai kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
Tashiwa Haneefah tayi zata fita Ramlat ta kama hannunta tace bakice komai ba? Haneefah tace zanyi tunani.
Hadiza ta samu a bakin kofa tana jiranta. Hadiza tace Haneefah zan kara missing naki, gashi wannan cikin zan kara haifa bakyanan nikam duk na kagu kizo tsorona daya kada ki hadu da mazaunin can kiyi aure.
Haneefah maganar dariya ta bata tace shekara mai zuwa zanzo insha Allah.
Hadiza ta rike hannuwanta tace sis ki manta da Yusuf, lokaci yayi da zaki mance shi, nasan abin da wuya domin haduwarku kunyi soyayya, yadda ra'ayinku da dabi'arku yazo daya ne kikejin kamar bazaki samu kamar saba amma kada ki manta, Allah daya hada ku shizai kara hadaki da wadda yafisa, kiyi la'akari da yadda kowa bayason damuwarki, fatansu ki kasance cikin kwanciyar hankali, da wannan nake rokon ki kicireshi azuciyarki ki daina damuwa kansa, insha Allah komai zai daidaita.
Haneefah tayi murmushi tace sis bazanyi alkawarin daina sonshi ba domin Allah ne ya halicci wannan son azuciyata, zan miki alkawarin aure da zarar nagama duk wadda ya fitomin zai aureni zan amince amma saina dawo gida Nigeria, sannan bazan amince da auren Dr Mubarak ba.
Hadiza ta zaro ido tace yana sonki ne? Haneefah tace eh.
Hadiza tace bazamu miki dole ba duk wadda kike so shi zamu baki.
Sukai sallama tamkar kada su rabu da juna. Haneefah tana tafiya tana tunani "_ Hakika inka hadu da yan uwa da abokai nagari ka godewa Allah domin kullum ganin ka cikin farin ciki shine burinsu, sannan zasu kasance masu maka nasihohi masu ratsa zuciya_"
Me nake nema arayuwar duniya?? Yardar Allah, tsoron Allah da soyayyar annabi aduk inda nake, faranta ran iyaye da rabuwa dasu lafiya! Iyaye da dangi suna alfahari dani, tabbas babu abinda abinda yafi wannan dadi. Sai taimako ga mabukata tare da rayuwar gidan aure ya saura, tabbas zanyi biyayyan aure ko waye na aura bisa tsarin addini insha Allah.
Da irin wadannan tunanen ta iso gida. Tana zuwa ta shiga gidan Inna bayan sun gaisa ta fito ta shiga gidansu. A sannan suka soma shirin tara kaya.
**** ****
Tunda suka zo gida kowa jikinsa yayi sanyi musamman Umma, mijin Aisha rike da sabon baby yana kallonta. Ganin dukkaninsu sunyi shiru yasa ya ajiyeta ya tashi ya fita.
Salma tace aini da nasan itace bazan bari ta tafi ba, hakuri zan bata. Momy tace kibata hakuri akan tazo ta auri yayanki? Lokaci ya kure domin tana sa aure tuntuni.
Aisha ta mike tace what? Nashiga uku ina yaya yake bansan yazai dauki al'amarin ba.
Momy tace aiya sani, nan ta kwashe labarin daya auku daren da yake dinner party Dr Abdullahi ta kara da cewa ban san wace halin ya shiga ba kafin wannan abin ya faru.
Salma da Aisha dukkanin su kika suke, Aisha tace yanzu meye amfanin rabasu? Wadda kikai dominta tanar gidan, irin halin da yaya Yusuf ya shiga Allah kadai yasani kullum nice abokiyar shawarar shi ina bashi hakuri akan ki sauko, gashi kin sauko amma tayi aure dole ya hakura.
Salma tace yanzu in akaiwa Aisha ko ni tabbas bazakiji dadi ba, in zamu aikata abu murinka jin in mukaiwa kanuwan mu ya abin zai kasance, amma dubi ita harta manta domin yadda ta mare nusaiba dan ta miki rashin kunya.
Aisha tace yanzu dai ya'isa sannan kada ku gayawa yaya abinda ya faru gudun kada murinka maida hannun agogo baya. Ta dubi yarinyar da take kwance tace zan roki mijina alfarman yasa takwaran HANEEFAH.
Haka ko akai, ranar suna yarinya taci sunan HANEEFAH amma suka yanke shawarar a tambayi Yusuf ya zabi sunan abinda za'a kirata. Yusuf yayi farin ciki da mamakin wannan takwarar daya samu yace akirata da *RA'IMA* wato farin ciki.
A take ya shiga WhatsApp ya sa hoton ta a dp sannan ya rubuta a status nashi _my little princess RA'IMA_
_Ko ninan ~BINTU RAMADAN~ ina mamakin irin wannan soyayyar ta YUSUF da HANEEFAH_
**** ****
Agajiye suka dawo daga makaranta kasancewar yau ne aka yaye daliba gaba dasu wato su Rohan, su kuma nanda wata takwas za'a yaye su.
Raihana tace gobe walima zakije? Haneefah tace ai dolena saboda kosu Rohan da Kevin dan haka anjima da dare inmun huta zamuje mu siyo kayanda zamu saka.
Raihana tace da kin sanar dani tun wuri sabbin kaya zamu sa da naje Dubai nazo.
Haneefah tace aiko kun koma Dubai da zama bai kamata ki dauki zuwansa tamkar a mota bane don siyayya koda yake kuna dashi takashe maganar a hankali.
Raihana tace inason tambayarki, a cikin class namu akwai bakken fata mesa bakyason mu'amala dasu?
Haneefah tace Kar ka yarda ka shiga cikin mutanen da suke da dogon buri har rayuwarsu ta kare basu aikata wani aiki na alheri mai yawa ba sannan su rinka cewa: ai muna kyautata ma Allah zato. Wannan karya ne, domin inda sun