Showing 42001 words to 45000 words out of 74305 words
Chapter 15 - DR. HANEEFAH BOOK COMPLETE HAUSA NOVELS BY Batul-Mamman 1-end-1.txt
Kayi HAKURI wajen yin da'a, kayi HAKURI wajen barin haramtattun abubuwa, kayi HAKURI da qaddara. Kayi HAKURI kayi HAKURI.... sabida gobe qiyama ka zamo cikin wadanda mala'iku za su ce ma.
Nidai tunda nake arayuwata ban taba ganin irin Son Haneefah da takewa Yusuf.....
Aunty Muhibbat ce amshe da cewa maganarki hakane amma ki sani, soyayyar da aka gina shi domin Allah haka take, sai dai ke Haneefah ki dada hakuri domin an miki iyaka da soyayyar shi kuma mahaifiyarsa ce, bai kamata har yanzu kina tambayar zuwanshi ba kuma baizo ba, tun bayan tafiyanki ko akan hanya ban taba haduwa dashi ba.
Aunty Humaira tace Haneefah lokaci yayi dazaki mance shi, mun fahimci soyayyarku amma babu abinda zakiyi kamar kiyi hakuri, ki fito da wani mu aura miki shi.
Haneefah tayi murmushi tace indai akan Yusuf ne na daina ambaton shi agaban ku. Tana kaiwa nan ta tashi ta fice.
Nana tace maganarku bazai tasiri akan taba sai addu'a. Suna kan tattaunawa Hadiza tashigo da sallama, Nana tace wayyo yau Haneefah murna Hadiza tazo kwanan biki. Aiko tana jin muryar Hadiza ta fito ta dauki ummulkhairi suka fice.
***** *****
A hankali yayi parking ya fito. Kamar kullum ya nufo falon Abba. Da sallama ya shigo suka amsa, Momy tace yau da yamma ka dauko hanya? Abba yace ai auren yaron abokina ake, shi yaron tare sukai karatu sai dai likita ne.
Yusuf yace yau suke da dinner party shine yace lallai sai nazo afara komai dani, kuma inason zuwa in duba lafiyar Aisha ma.
Momy tace Allah bada zaman lafiya, Aisha tana lafiya. Suka dan taba hira ya tashi ya fice.
Da dare misalin karfe takwas ya shiga yiwa Momy sallama, ya tarar suna hira da kaninsa. Muhammad yace yaya kayi kyau sosai, murmushi yayi yace nagode auta. Yayiwa Momy sallama ya fice.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼45
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Haneefah kallon Yusuf take tamkar bata taba ganinsa ba. Niyyar yi masa magana tayi saita tuno alkawarin da ta daukarwa Momy. Ta hade rai zata wuce yasha gabanta yace dan Allah ki saurareni kiji abinda zance dake dan Allah Haneefah.
Jin ya ambaci Allah ta tsaya duk da zuciyarta bai amince da tsayuwar nan ba. Yusuf cike da wani irin yanayi yace Haneefah hakika na miki laifi duk da bani da niyyar aikata hakan amma yazama dole innemi afuwarki, nasan bazaki kullaceni da zalunyar kiba amma ya kama dole na nemi afuwarki domin manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce:
_"Mutane uku (3) Allah Ta'ala Ya na karban addu'ansu ko shakka babu: Addu'ar wanda aka zalunce shi, Addu'ar matafiyi da Addu'ar Mahaifi ga abun da ya haifa"_. Tirmizi ya fitar da hadisin, Sheikh Muhammad Nasiriddeen Albani ya inganta shi.
Ina nemar afuwan ki dan Allah Haneefah ki yafemin.
Ganin hawayen idanunta na neman zubowa ta rabe ta gefensa ta shiga mota ta tayar tayi wucewarta.
Ganin haka yasa shima ya koma motarsa ya juya domin barin gurin domin kwanciya yake bukata baya jin zaici gaba da tsayiwa.
Tsayiwa tayi agefen hanyarsu ta rushe da kuka. Bakamin komai ba Yusuf na yafe maka duniya da lahira, wlh ina matukar sonka amma bansan ko kai har yanzu kana so na ba! Ganin anfara tafiya sallan juma'a yasa ta share hawayenta ta qarasa gida.
Shiga dakinsu tayi ta tarar babu kowa sai Raihana, tana shiga tasa mukulli ta kulle dakin tazo bakin gado ta zauna tana share hawaye.
Raihana ta taso da sauri tace meya faru Haneefah? Ke da waye? Haneefah tace nida Yusuf ne, mun hadu yanzun nan yace yana neman afuwa na.
Raihana tace kinga irinta ko? Yanzu aida yana sonki binki zayyi!
Ya isa haka Raihana, kina nufin baya so na? Ban damu da sonshi gareni ba abinda ya dame ni yaushe zanji na daina sonshi? Yaushe zuciyata zata daina tunani ta daina wahala akanshi?
Raihana tace kamar yadda kika fara sonshi haka zaki daina, dan haka kidaina wahalar da kanki kawai kiyi aure amma duk wadda zaki aura ki tabbata yana sonki kuma wadda zayyi hakuri dake da soyayyar dake cikin zuciyarki.
Maganarta gaskiyane. Jin an fara kwankwasa kofa yasa ta tashi taje ta bude kofa taga kannenta ne, komawa tayi ta kwanta jin kanta ya fara ciwo nan take bacci ya dauketa.
Har aka fara gabatar da walima tana bacci domin bata sallah shiyasa ba'a damu antashe daga bacci ba. A hankali ta bude ido taji loudspeaker wadda ake gabatar da walima dake harabar gidansu tana cewa;
Suna daga cikin siffofina ce saliha:
*TANA TARAYYA DA MIJINTA* :A cikin domin taimaka masa wajen kafa gida mai tarbiyya da kuma iyali mai taimakon addini matukar dai ra'ayinsa bai sabama Allah ba.
*TANA KARFAFA MIJINTA* :Domin cin nasara wajen abunda yasa gaba.Saboda mace tana da tasiri kan mijinta in ta karfafashi zayyi aiki,in ta karya masa gwuiwa ba zai ci nasaraba .
*TANA TAIMAKONSA KAN BIN ALLAH* :Domin Manzo ( ) Yace *MUMINI BAI TABA SAMUN FA'IDA BA BAYAN TSORON ALLAH KAMAR MATA SALIHA MAI TAIMAKAWA MIJINTA AKAN ADDINI* (Sahih Muslim).
*MAI DAI-DAITA 'YA'YANTA*: Mai tarbiyyantar dasu,mai karfafasu wajen ibada,mai tausayi, da Rahma, mai koyamusu ilimin dake dashi domin su amfana.
*MAI NUNA KAUNA GARESU* :Da tausayi da basu hakkin da yakamata.
*MAI NASIHA GA MIJINTA DA 'YA'YANSU*: Domin addini nasiha ne gaba d'ayansu,kamar kowa yasani domin gina gidan da mijinta,da 'ya'yanta da 'kasa da al'umma gaba d'aya.
*MATA WATA HALITTACE*: Mai mahimmacin tane Allah yasa kowane mutum sai ya shiga ta hannunta zuwa wannan duniya da muke ciki ko malami,ko sarki,ko mai kud'i, ko gwamna,ko shugaban 'kasa kai koma waye sai yakoyi halin mace shiyasa insunyi kyawu to duniya zatayi kyau,misali inda matan duniya kowanne zata kame farjinta bazatayi zinaba to da zinan ma ta mutu a duniya don haka manzanci Manzo ya basu muhimmanci ya kuma girmamasu,matar da zata bada gudumawa ta zama mai ilimi mai hakuri ,mai hali nagari, mai tarbiyya, mai kamun kai kamar yadda muka gani abaya da kuma nan gaba.
*TAZAMA MAI KYAKKYAWAR 'DABI'A*: Manzo ( ) Yace *Babu wani abu da zai kai mutum aljannah kamar kyakkyawan d'abi'a* Sannan kuma Yace *Babu wani abunda yafi kyakkyawan dabi'a nauyi akan mizani kamar kyakkyawar dabi'a* Ya kuma ce *Wanda Yafi kowa cikar imani shine mafi kyakkyawan dabi'a* (IMAM TIRMIDHI)
*MAI GASKIYA*: Kamar yadda Allah Yace *YAKU MASU IMANI,KUJI TSORON ALLAH KU KASANCE TARE DA MASU GASKIYA*(Suratut-tauba) Manzo Yace *Gaskiya tana shiryarwa zuwaga bin Allah,bin Allah Yana shiryarwa zuwaga Aljannah* (Bukhari da Muslim)
54, *BATA SHAIDAR ZUR*: Wato bata ji bata ganiba kiran karya kawai saboda Manzo ( ) Yace *Shaidar Zur yana cikin manyan zunubai* (Bukhari da Muslim)
*MAI NASIHA DA MUTANE*: Kan ayyukan alheri saboda Manzo Yace *Wanda ya shiryar zuwa ga aikin alheri,kamar wanda ya aikata*(Sahih Muslim).Haka kuma wanda ya kafa mummunar hanya ko kyakkyawa yana da lada ko zunubi batare da anrage na kowayeba.
*Allah Yasa muna daga cikin wad'annan mata salihan*.(Amin)
Jin yasa ta tashi zaune taci gaba da sauraron nasihohi:
Ka gode ma Allah a duk yanayin da ka samu kanka.
Wata rana wani mutum suna tare da abokin shi sai ya ga wasu gidaje masu kyau, sai ya ce ma abokin:
_"Wai ina muke lokacin da aka raba wadannan dukiya haka? "_
Sai abokin ya kama hannun shi ya tafi da shi asibiti ya nuna masa marasa lafiya a kwance, sannan ya ce mishi:
_"Su kuma wadannan muna ina aka raba musu wadannan ciwo dake damun su?"_.
Don haka ka mu zama masu godiya ga Allah 'yan uwa.
Raihana ce tashigo tace nazo duba kine ko kin tashi, amma yanzu kika tashi ko? Haneefah ta daga mata kai tace eh, kinzo da allurar da Dr Michael ya baki na ciwon marata?
Cike da damuwa Raihana tace na manta ban dauko ba. Haneefah tace zama bai kama muba nanda kwana biyar zamu wuce london nafasa karasa sati biyun dan haka saimu fara shiri.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼43
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Momy tabi bayansa da kallo hawaye na taruwa a idanunta. Sau tari tana jin bakin cikin raba shida tayi da Haneefah domin bai manta da ita ba, tana kallon hoton ta a dakinshi.
Batasan da wani ido zata ganshi tace Haneefah tayi aure ba, ban maka adalci ba Yusuf amma ina maka addu'a samun mace tagari.
Jin motocin daukan amarya yazo yasa aka fita da Nana da tasha ado harta gaji da kyau. Haneefah zirga-zirga ya hanata zama guri daya domin fitan ta daga wanka kenan zama'a suka soma fita.
Aunty Muhibbat ce ta bata mukullin motar ta tace su tafi inta gama. Tsaye take gaban madubi tana kwalliya, cikin nutsuwa take kwalliya harta gama, ta dauki lace nata gown ta saka. Ta nannade gashinta yadda bazai fito waje ba ta tusa cikin cap.
Tsayawa tayi tana kallon kanta, dankunne da tsarka da abin hannu da agogo, cap da style na jikin kayanta duk silver, duk da wannan kwalliyar saida ta dauki gyale. Raihana ne ta dauki waya ta soma daukarta a hoto tace dama haka kike kullum bakya kwalliya.
Haneefah tayi dariya tace ai karatu naje yi. Itama sanye take da habaya irin ankonsu tayi rolling. Suna fitowa suka hadu da Umma.
Umma ta tsaya tace maasha Allah, ki zamto mai ambaton Allah irin wannan kyau haka. Cikin mota suke amma Raihana sai daukar Haneefah take a hoto.
Duk saurin su sunje sun tarar ba'a gama shiga hall din ba. Tana sauka kallon jama'a suka koma kanta. A hankali take tafiya harta iso gurin rike da hannun Raihana. Aunty Muhibbat tace duk irin wannan kwalliyar saida kika dauki gyale? Hadiza tace ai gonda da kika dauka saboda yadda ake kallonta da gyale ma.
Anan Haneefah idonta ya fara kallon jama'a saboda a tunanin ta kallon Raihana ake. Sai taji kunya duk ya lullubeta.
Bayan sun shiga sun zauna aka bude taro da addu'a tare da kiran kanin anko ya gabatar da yayansa tare da fadin takaitattcen tarihi akanshi. Bata Ankara ba taji ankira sunanta. Kamar bazata tashi ba sai kuma ta tuna Nana ce fa, ta tashi rike da hannun ummulkhairi.
Bayan ta gaisar da kowa tagabatar musu da takaitaccen tarihin Nana, sannan ta kara da cewa Allah basu zaman lafiya, babu wadda bata birge ba yadda ta tsara maganar tamkar tana kallo ne.
Zamanta keda wuya aka kunna waqa, khalifa yazo ya zauna kusa da ita yace kin birge fa, bani wannan yartaki in rike ta. Ya karbi ummulkhairi yace tashi kice ki watsa musu naira kin wani zauna anan, ya matso kusa da kannenta yace muna so mu aurar dake tashi ko zakiyi kasuwa.
Haneefah tace ai banyi kwantai ba haka ba, kuma ni banga..... shiru tayi ganin su Aunty na shiga filin rawa. Babu yadda ba'ayi da itaba amma taki shiga, a hankali ta tashi ta fara gaisawa da yan uwa, kowa yana mata fatan alkhairi a karatun ta.
Tazo zata wuce gurin zamanta khalifa ya ja hannunta suka shiga, bata ankara ba taji an soma yi mata ruwan kudi, duk yadda taso fita sunki hanata haka ta hakura tana dan takawa.
Yadda sukaga ana rubibi akan Haneefah yasa suka kyaleta ta fita taje ta zauna. Zaune take rungume da ummulkhairi suna kallon yadda party yake gudana. Haneefah tace lallai anayinta, kusan yan matan gurin kaf babu lullubi ajikinsu saika rasa banbanta wanene matan aure cikinsu. Tananan zaune har lokacin da Hadiza tace da ita za'a fara rabon abubuwa ta tashi su fara.
Duk inda tayi ummulkhairi na makale da ita hakan yasa wadannan da basusanta ba suke zatan ko diyartane. Tazo kan wata kawar Nana na hannunta ya qare dan haka ta fita domin dauko wasu cikin mota.
Tafiya take cikin rashin sani tsantsin tiles da ruwa yazube ya dauketa, da hanzari Ahmad yazo ya riketa yana mata sannu. Hannunta ya rike har suka zo inda aunty Muhibbat take. Aunty Muhibbat tace ai duk sa idon abokannan nakune yasa taso faduwa.
Ahmad yayi dariya yasa hannu yana gyara mata cap nata daya kusa faduwa, garin gyara ya fadi gashinta suka kwance. Haneefah takaici yacika tace sakeni na gyara kayana. Yasa hannu ya karbi ummulkhairi ta soma gyara cap dinta.
Tun saukarta cikin mota ya kura mata ido, shin itace ko mai kamarta? Saida ya shiga yaga Nana ce amarya ya tabbata Haneefah ce toh amma aina ta samu yarinya? Gabansa ne ya fadi daya tuno kardai aure tayi? Take ya nemi hankalinsa ya rasa. Dakyar yake iya gaisawa da abokanan sa, babu abinda yake sai kallonta.
Yadda take magana cikin kwarewa da nutsuwa cikin harshen turanci ne abin ya dada basa mamaki, tuna kalamanta yayi inda take cewa_aini yaren naku ne ban iya ba. Yusuf yace wanne? Haneefah tace turanci_ tabbas yasan Haneefah bata kware ba amma aina ta koyo?
Sanda ya ganta cikin filin rawa jama'a na mata kari sai yaji wani abu ya tokare masa makoshi. Sai yaji tamkar ya tashi ya fizgota ya fitar da ita cikin filin. Amma shi kam bai yarda da wannan yarinyar da ke makale da ita. Yana son yi mata magana amma yana tuno da Momy, amma wannan karon saiya mata magana kodaa gaisuwane. Ganin ta fita ne shima ya tashi ya bita a baya.
~Bintu Ramadan~
*Dr HANEEFAH* 👩🏼44
Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖
Aunty Muhibbat ce tagansa tsaye ya kura mata ido, neman abinda zai kawar da hankalinta Haneefah take, sai ko ga kawar Nana ta fito zata tafi ta nufo inda suke tace Haneefah dama kinyi aure harkin haihu baki gaya mana ba, aiko Nana bata gari a lokacin yakamata ki sanar damu?
Haneefah tayi dariya zatai magana Aunty Muhibbat ta amshe da cewa kinsan auren yazo a kurarren lokacine kuma yanzu bata kasarnan da zama ba anan ta haihu.
Haneefah ko sai murmushi take. Allah raya, Nana ma Allah basu zaman lafiya, dukkaninsu suka amsa da ameen.
Neman tsayawa yake amma yagagara, a hankali ya soma tafiya har yaje ya zamu bakin fulawowi ya zauna duk da duhun gurin. Idanunsa sun kada sunyi ja zuciyarsa na masa kuna _Allahumma ajirni fii musibati wakhlifni khairan minna_ ya samo ambata, tunaninsa sun tsaya cak!
Aunty Muhibbat ta samu abinda take so, tace da Haneefah ina zuwa. Tarar dashi tayi a zaune ya dafe kansa da hannuwansa, kwarai ta tausaya masa domin tasan tunanin yar uwarta yake amma inba haka tayi ba hankalin Haneefah zai tashi.
Ko agaba ina gargadinka daka fita harkan Haneefah domin yanzu matar aurece hankalinta ya kwanta. Haneefah tayi maka afuwan dukkanin abinda ka aikata agareka amma kasani wannan karon yarda ka mata magana har mijinta yaganta, muddin ka bata mata aure toh wallahi bazamu yafe maka ba cewar aunty muhibbat, bata jira cewarsa ba tajuya ta fice.
Gurin haneefah ta nufo, taja hannun Haneefah suka koma ciki. Suka tarar ana dauka hotuna, Haneefah ja da baya tayi ta zauna. Azuciyarta tace kana ina Yusuf? Rungume kake da danka niko gani inata tunanin ka. Hawaye take kokarin zubar wa amma ta maidasu.
Raihana ce ta dafa kafadarta yace a duk sanda na ganki kina tunaninsa nakan gane ki, mesa bazaki bawa yayarki daman tayata farin ciki ba, wannan taron duk saboda ita akai amma saiki ware kanki kinzo kina tunanin wani? Kina tsammanin zata ji dadi?
Batace da ita komai ba ta kamo hannun Raihana suka nufo inda amarya take suka soma dauka hoto. Raihana cikin zuciyarta tace ur so special Haneefah, kinajin magana koda bakiso shisa duk yayunki suke sonki.
Tashiwa yayi yashiga mota. Ikon Allah kadai ya kaishi gida. Bangarensa ya wuce kai tsaye cikin kunar rai. Kan gado ya kwanta ya soma zuba da hawaye. Wannan karon ya kasa controlling kanshi, ya tashi zaune, ji yake kamar ya cire zuciyar ya jefar ya huta.
Momy jin yadda Yusuf yashigo yasan babu lafiya, dan haka da sauri ta tashi ta nufi bangaren sa. Kuka tarar yake, cike da tashin hankali ta iso gare sa tana lafiya Yusuf? Meke faruwa? Tazo ta zauna kusa dashi
Ganin Momy ya sake fashewa da kuka yana cewa Momy tayi aure harda yarta, nashiga uku Momy kullum sonta yana qaruwa cikin zuciyata bansan mezanyi na manta da ita ba. Ba bakin cikin auren ta nake ba hasalima ina taya mijinta murnan samun mace kamar ta amma bansan ya zanyi da sonta ba. Ya qara fashewa da kuka
Momy dauriya tayi tace nasan da auranta domin nima naje sasanta sakaninku naji tayi aure, ban maka adalci arayuwarka dana rabaka da ita ba, ban kyauta ba. Nayi dama ka yafemin Yusuf, nakasance uwa maisa ido kan rayuwar yaransu bansan me kamin dazan saka maka da haka ba.... jin yayi shiru yasa ta kira sunan shi amma kafin ma ta taba shi ya fadi sumamme.
Momy tace nashiga uku Yusuf!! Amma ko motsawa bayayi, cikin sauri Abba dake tsaye a kofar ya shigo yace Yusuf? Amma ko motsi bayayi Abba ya juya yana kallon Momy yace duk abinda yasamu dana saina dauki mataki.
Kwantar dashi sukai kan gado Abba ya dauki ruwa a fridge ya yayyafa mishi. Ajiyar zuciya Yusuf yayi ya bude ido. Momy cikin kuka tace dan Allah ka daina damin kanka kada ka jawowa kanka ciwo kaga plss.
Murmushi Yusuf yayi yace Momy komai ya wuce ki tayani da addu'a. Abba ya soma fada Yusuf yace Abba yariga ya wuce, nabarwa Allah komai, nasan yana jina kuma yana ganina, shi maijin qaine, mai tausaya wa inada tabbacin hakan alkhairi ne agareni.
Momy kusan sha biyu tabar dakin nasa. Kukan zuciya ya zauna, ganin abin ba na dinawa bane ya tashi ya fara nafilfilu.
Haka abin yakasance wa Haneefah, kowa yayi bacci amma banda ita, shikenan yanzu babu ita babu Yusuf! A wannan dare ta soma addu'ar Allah bata miji nagari ya azurta rayuwar Yusuf da farin ciki mai dorewa.
Washe gari walima. Misalin karfe tara Amal ta shigo tace da Haneefah Dr Mubarak yazo yana falon Abba. Tsaki tayi tace ina zuwa.
Zaune ta tadda shi, bayan sun gaisa bai bari yace komai ba tace dan Allah Dr kayi hakuri, kabari Inna qarasa karatuna sai mu dakko maganar domin kasan yanzu ina final year.
Dr Mubarak ya gama nazarinta yace toh shikenan Allah kaimu, amma zaki rika surarata ko?
Haneefah tace aa. Ganin zai takura mata tace ni Dr kawai kayi hakuri ta tashi ta fice.
Dr yace bazanyi hakuri ba, sai nasan yadda zan bullo miki, ko