Showing 27001 words to 30000 words out of 122554 words

Chapter 10 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

Advertisement

26 Jan 2025

24149

Bamu Hada komai Dashi ba.."


Hajiya karima Dake Zaune gefen Zubaida bisa Daya Daga cikin Lumtsuma lumtsuman Royal Chairs din Dake Falon Ta tabe baki tace"Wai Alhaji Tsoron yaron kake ji ne hala..?Kake ta wannan Kumfar bakin..? Yarinyar nan tana iya bakin kokarinta ammh ko yabawa bai Tabayi ba,Hakuri zakayi ku kyaleshi Tunda Bakar Zuciyarsa Haryanzu batajin zata iya yafe muku.."


Abba Kabiru ya mike yana Saba Babban Rigan sa yana Fadin"Lalle baki da Hankali Karima Taya zan kyaleshi ai Mafita Daya na samu Sa"ar da zai zama Suruki na,Shine kadai zai sa ya yafemana laifinmu na baya kamar yadda Dan"uwansa bai Rikemu ba,Kina ganin yanayin Yaron nan Wlh sai ya iya Makamu Kotu nida garba kuma Tsaf za"a Daure mu Tunda Mun Aikata..",


Hajiya karima Ta Mika hannu t Kwantar da Zubaida kan Cinyarta Tana Fadin"Kaima kasan Bazai yi Haka ba,Ai dolensa ne ku nashi ne,Kuma Muktar bazai barshi yayi Haka ba.."Zubaida tayi Saurin Cewa"Umma Toh Shima Daddy Tsoron Uncle Bellon yakeji,Duka gidanan Suna Sonshi bamai Dauremin gindi Sai Daada,Kiga fa Ko Fadama bamai son yi mai Umma gaskiya suna Sonshi Sosai.."


 Abba Kabiru ya Tsaki yana Fadin"Nasani Shi nake gudu ammh ke karima baki ganewa,wannan Tsohuwar Bufullatanan nan Dama Tun Farko ni batamin ba Inama Tunanin Ita ke Zuga Bellon ba Wani ba,ke ko Zyciyarsa kaf bana Zuru"armu bane chan ya kwasoshi Wajen Dangin Fulani,kinsan su da bakar Zuciya da Mugun Abu.."ya karishe Fada yana Rike kugu Cike da Jin Haushi bata samu Zarafin Mgana ba,Abba kabiru ya Cigaba da Fadin


"umh nifa Abun Daya Nake gudu karima,Kada Wannan Shegiyar Zulfa kinsan Ita da Uwarta makirai ne Suje su karkatar da Hankalinshi ya Aure ta Ai ni na Kade Haduwa zasuyi da Garba su yakeni na Shiga Uku.."


Hajiya karima tace"Haba Alhaji yama za"ayi Haka ta Faru Ai Alhaji garba in bai Taimake ka ba, bazai yake ka ba Sai dai Ita Hajiya Sahuran don bata da Kirki kuma indai bai Auri Zubaida ba sai dai kowa ya Rasa.."Jinjina kai yayi yana Fadin",Shine mgana gaskiya..."


Kasim Dake Kofar Falon Tundazu ya Kariso yana Fadin"Abba nifa bana ganin laifin Bello kune masu laifi Tsakani ga Allah baku kyauta ba kuma ko nine irin matakin da zan Dauka kenan ."Yafada yana zama kujeran Datake Kusa data Inda Hajiya karima take zaune ita da Zubaida.


Harara Abba kabiru ya Laftamai kafin yace"Dillah rufemin baki Sakarai kawai,Ai Hashim yafika kirki Yana Kokarin Zuwa Gidan Muktar din yana Tusa kanshi Duk Domin Asirinmu ya Rufu Ammh kai baka ma Zuwa balle ma na saka ka alissafi.."Kasim dake Sanye da Riga da Wando Navy blue Na kamfanin Armani,yace"Ai ina Kiran Ya Muktar ta Waya kuma Abba bana samun lokci ne kaima ka sani.."


Hannu ya Yarfa yana Fadin"Matsa chan ka bani Waje kaima baka da amfani ko Abota sai ku kulla Dashi Bellon mana Tunda Dama da kadan ya Girmeka mu samu Asirinmu ya Rufu kada yaron nan Yace zai yi Shari"a Damu Watarana.."Yamutsa Fuska Kasim yayi kafin yace"Nifa Abba bana son Raini ni,kaga yadda gayen nan yake wani cin mgani da Isa Wani Lokacin fa bai ma kaunar Hada Iska Dakai fa,Ni kuma Zuciya gareni ban Iya Juran Wulakancinsa Tun Kwanaki Dana Taba Kiransa Ya Tambaya ni wanene Inafa cemai nine kasim Dan Wajen Abba kabiru ammh Gayen nan yace bai sanni ba Kuma kada nakara Kiransa ya yanke Kiran.."Yafada Cikin Zafin Zuciya.


Shuru Abba kabiru yayi Kafin yayi Mgana Hajiya karima ta Rigashi da Cewa"Sai fa Hakuri Alhaji Ammh kam kunbi son Ronku,Tsakani ga Allah Ko bakomai Muhammed Dan"uwanku ne Da Kuke
Uba Daya kowa yaji Aikin Da Kuka yi sai yayi Tir daku.."Wata Uwar Harara ya zabga mata kafin yace"Rufemin baki Munafuka Ina ce Lokacin bada Shawarki nake amfani ba.."cikin Daga Hannu tace"A"a Wlh ni Haihuwa nace Ku Hana Hassatu bance ku kashe Rayu ka ba.."


Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Shedan ne,Da kuma Kaddara Kuma duk Garba ne yaja Shi ya kawo Shawaran Gashi mun cika burin mu na Kauda Muhammed Da matarshi,Munkuma yi Nasaran Kwatan Dukiyan Ammh Sai gashi komai ya lalace Karshenta ma Namu ya"yan ne ke Ci karkashin nashi ya"yan da Muka Tozarta Allah kenan.."Yake Fada yana Sauke Numfashi.


Kasim yace"Abba Tunda kun Tuba Shikenan,Shima Ya Muktar din ai ya yafe muku Shima kuma Bellon komai zai Wuce Nan da Lokaci kadan.."Zubaida tace"Allah yaya Daada nan ce ke Bala"in Sonshi Shida Aneesa ko Guda bata kaunar ya Tabasu.."


Cikin Mamaki Hajiya karima tace"Wata Aneesa kuma...? Tafada Tana Wasa da gashin kanta Gyara kwanciya Zubaida Tayi kafin tace"Kanwar Anty Rahila ce Daddy muktar ya Daukota Daga Borno Shegiyar yarinya ce Ta nan sai Zuba iskancinta take Ko Ballon bata Shakka,Mkrantar Dayake koyarwa ma Take ,Tare suke Tafiya kuma in sun samu Hutu su komo Tare.."


Baki Abba kabiru ya Rike kafin yace"Kaji ko... ? Itama Matar nashi So Take ya Auri kanwar nata Kinsan Yan Bornon nan ba Kyau Tuni zasu ja Hankalinsa.."Kasim Dake zaune yayi Dariya kafin yace"Kai Abba Daga mgana sai kace zai Aureta.."zubaida tace",Anya Abba basa ga maciji fa yadda kasan Annabi da kafurai Shi kadai ke iya mata Hukunci agidanan Daada Tayi Shuru ko Anty Rahila bata iyawa da Fitinar Aneesa kamar Mai Bugun Aljanu.."Dariya ta kara Kama Kasim Cikin Nishadi yace"Niko har naji ina Sonta Domin ina son mace mai Tsiwa.."


Hararansa Hajiya karima Tayi kafin tace"Toh mara kunya.."Mikewa yayi yana Sosa keya yace"Umma,Abba ni zan Fita zan Shiga Cikin garin Wajen Abokina Shamo.."Hajiya karima ce Kadai Tace mai adawo lafiya Shiko Abba kabiru komawa yayi ya Zauna yana Wani Nazari Acikin Ranshi.


****


_GRA-Katsina_


*ABBA GARBA HAUSE*


 Â
Suma Duka iyalan gidan Suna Zaune A kayatattacen Falon na Gidan Abba garba,Harda su Hamdiya da Ummu salma da Inna Rukayyah Wacce Suka zo garin Jiya,kuma Sunfi Dasawa da Abba garban Shiyasa Take Sauka agidanshi kuma Matar Shi Sahura Wacce Suke Kira Mama Sahura,Makiran Macece Ta iya Duniyanci Tasan yadda Take Hillatan Mutum Shiyasa Kaf yan"uwan Mijinsu sunfi yabonta Fiye da Karima Umma kenan,Shiyasa basa zama Waje Daya Duk da Abaya sunyi Amintakan Munafunci Tunda Rabuwan Mazajensu yazo kowacce Ta Koma Tsagin Mijinta Shiyasa Inna Rukayyah ke Sauka gidan Abba Garba kuma ko Taje gidan Abba kabirun Umma bata mata Wani karban Mutumci.


Zulfa ce ke Basu lbrin Irin Wulakancin da Bello yayima Zubaida sai Dariya Suke Sha Tun barema Mama Sahura Dake Mirmishi Cikin Kissa Tace"Kash..Banji Dadi ba.."Tafada Tana kallon Inna Rukayyah Wacce Ta kada kai Tana Fadin"Ai ni Wlh naji Dadin Hakan,Duk da Muma bamu Tsira ba Wajen Ja'irin yaron nan ammh gwara yayi mata Haka din,ko ba komai ni Nafison In ma Auren Bellon zaiyi ya Auri Zulfa Saboda Daga Kariman har yarta basu da Kunya sam."


Cikin Kissa Mama Sahura tace"Ah inna ba komai Ai Duk Dayane da Zubaidan da Zulfan Duka Namu ne,Fatanmu Dai Shine ya zabi Daya Cikinsu yadda bazai Auro na Waje Balle har tazo Taji Abunda ya Faru ta Zugashi ya Dauki Mataki bq.."Inna Rukayya ta Girgiza kai Tana Fadin"Hakane...Ammh ni nafi son ya Daidaita da Ita Zulfan,Ai mganar Gaskiya Su kabiru sunyi kuskure Babba,Rudin Shedann Dana Zuciya ya Debesu Kuma Tunkafin Su Fada da bakinsu mutane Su ke Zargi Saboda yadda Suka Hau Dukiyar Marayun,Kinga fa Haryanzu chan Jikamshi Gulmar Dake Tashi kenan.."


Mama Sahura tace"Umh Inna Wlh Alhaji baida Tunanin Kashe Rai,Duk Yaya kabiru ne Yaja Shine mugun Shi ya Dinga Forcing Dinshi har ya amince,Ammh Haryau kukan Nadama yake Yana kuma ganin Laifin Yaya kabirun Daya Dorashi kan Wannan Kuskuran.."


Inna Rukayya tace"Hakane Ai Shi kabiru akwai Hange Hange ne,Allah dai ya kyauta don ma Mun Samu Shi Babban bai Dauki Abun da Zafi ba Shidai Bellon Shine Naga kamar Yana da Wani Shiri ne.."Mama Sahura ta gyara zama Tana Fadin"Shine ai Inna Mukesi mu Jawoshi ajikinmu yadda ko Yana da Niyyar Wani Abu Sanadin Hada Surukanta damu Dole zai Hakura,Ko Zulfan ko Zubaida Duk Wacce ya Aura Insha Allahu Shima zai Manta komai.."


Jinjina kai Inna Rukayyah Tayi kafin tace"Hakane kam..Toh Allah ya bada Sa"a Kafin na Koma zanje Abujan Insha Allahu..."Da Sauri Hamdiya tace"Inna zan biki Banta ba zuwa ba.."Ummu Salma tace"kin ma isa Wlh Dani za"a Je.."Tafada Tana Hararan Hamdiyan Dariya Inna Rukayyah Tayi kafin tace"toh duk naji Gabadayanku Zamu Tafi Ba Dadewa zamuyi ba bai Wuce mu kwana biyu ba Dagachan zamu koma kano Saboda Hutu ya kare.."Jin Haka yasa Suka kama Murna Zulfa na gefe tana latsawa waya cikin Mirmishi tace"Daddy bai da Mtsala Uncle Bello ne Mai Damuwar Inna Shifa bai kaunar ganin Wani Daga Cikinmu Agidanman Saboda mu Har yaji yakema Abuja Mutum kamar Zuciyar kafiran Farko.."


Inna Rukayyah tace"Nagani Zuwana na Farko Diban Albarka da Yaron nan yamin kamar nayi kwallah ,muktar din na mai mgana ya gaisheni Wlh ko Waigowa baiyi ba ya Fice Da Hanzari kamar yaga kashi.."Tafada tana Rike baki Mama Sahura tace"Hmm Haka fa yakema Kowa Ko Su Alhajin basu Tsira ba baya gaishesu..."


Inna Rukayya tace"Gadon Zuciyar Bakaken Fulanin nan ne na Dangin Uwarsu.."Mama Sahura tace"Wlh Haka Alhaji yace.


Daga haka suka Cigaba da Hiransu Sama sama Duk dai Akan Bello ne da Irin Rashin Mutuncin Dayake ma Duk Wanda ya Fito Daga Tsatson Abba kabiru ko Abba garba.


*******


Kwanci Tashi babu Wuya Awajen Allah gashi Har Hutu ya kare,Tuni Daliban GGUSS kwatar-kwashi Sun koma Harda Wasu Daga Cikin yan Jss3 sun Dawo SS1 ciki Harda B.kaita Ita da S.jibiya Tun kwana uku da Yin Resume Suka Dawo Mkrantan Amatsayin Senoirs.


Aneesa ko bata da Masaniyar Komai,Duka gidan ba Wanda Yama Bello Mgnar Aneesa,ganin Tun Satin da Wuce Mallam Inuwa ya maida sa Sch Din sai Kowa ya sakankace kan,Bello ya Bar Aneesa Ta cigaba da Jeka ka Dawo,ko da Su B.kaita suka ga Me bello Jikamshi ya Dawo Shi kadai sai Suka Cire rai kan Aneesa baza ta Dawo ba jidda madaki da Suka Dawo suka Iske Suna Neco sun kusa gamawa Har Dakinsu Tazo Neman Aneesa suka Sanar da Ita Aneesa bazata Dawo ba,Hakika Yan Ajinsu Sun Dawo Da yawa yayinda Wasu kuma Basu Dawo ba,Dalibai dadama in Sukaga B.kaita da S.jibiya Sai sun Tambayesu Aneesa Su kuma Cikin kewa Suce Anee bazata Dawo ba Wasu Dayawa Sunji Dadi wasu kuma basu Ji Dadi Ba Domin Aneesa Ta zama Cele by Force Ackin mktantar Sabida bakinta da Kuma Tana kanwar Da Handsome man Mr.Bello jikamshi.


Aneesa Har party Ta Hada Bayan Komawar Bello Makranta Ita Da Hibba Suka chashe,Ashe Tungunne bata kare ba Duka Duka Satin Bello Daya Da Tafiya yama Ya Muktar Waya kan Ashiryama Aneesa kayan provisin da Abun Bukata Ranar Monday zai zo su koma Tare,Ya Muktar Cikin mamaki yace mai"Na zata zaka barta ta Fara Jeka ka Dawo anan Abuja.."


Cikin Gimtse Fuska Bello yace"No...Nan zata Cigaba Har ta Kamallah.."Daga Haka ya Datse Kiran,Ya Muktar Kuwa kai ya girgiza kafin yace"There is a War In Aneesa Taji Lbri ."Bai gayama Kowa ba sai Anty Rahila Wacce Ta nuna Taji Dadin Haka Ita ke Fadama Daada,Wacce Har Awaya Ta Kira Bellon Yana Jin Mganar Aneesa ne yace"Wlh Tallahi Daada...Mgana Daya bazan Chanza ba Aneesa Bazata bar Kwatar-kwashi ba sai ta kamallah Secondry Duka Tukunnah.."Tunda Daada Taji Haka batama bata ma kanta Lokaci ba Ta Kashe Wayarta.


Anty Rahila da Aneesan Direba ya Daukesu Suka Shiga Mall Suka mata Siyayyah ammh Data Tambayeta sai tace Borno Zata Tura ta ta musu kwana Biyu,Aneesa bata wani soZuwa barno ba Saboda Takuran ya Ali,gashi ita kuma bata wani Shaku da mama Falmata ba Tamafi Shakuwa da Hajiya yana,Ga dai Wanda Tafi Shakuwa Dashi Sosai nan Marigayi Alhaji Bukar Bulama...


Haka dai Suka Dawo Gida Aneesa na Kuncin Zuwa Borno,Daada da Anty Rahila ba Wanda yace mata Kanzil,Ranar Lahadi kuwa sai ga Bello ya Diro Abuja Shida Uncle Aminu Wanda Ita Aneesan bata ma san Zuwansu ba sai Wajen yamma Tana Falon Daada Suka Shigo Tunda Ta gansu sai Jikinta bai Bata ba,Tana gaishesu Aminu ne kadai ya amsa Bello Cikin Tsare gida ya kalleta kafin yace"Ki Tsefe kanki kiyi Kitso ki kuma Shirya Abubuwanki masu amfani gobe zamu Wuce Dake.."


Aneesa Ta zaro Ido Waje kafin tace"Zuwa ina kuma...?


Harara ya sakarmata kafin yace"Zuwa Makranta.."Wani Zabura Aneesa Tayi kafin ta Dora Hannu Akai ta Zumduma Ihu,Wanda Sai da Suka Toshe Kunnuwansu Daada Dake Daki Ta Fito da Sauri Tana Fadin"Lafiya...?


Tasamu Amsan Tambayanta ganin Aneesa malale Akasa Tana Kuka da Birgima Tana Fadin Ita babu Inda Zata Tafi sai dai Akasheta.."Uncle Aminu gefe yaja Aranshi yana Fadin"Yarinyar nan Yar bala'i ce.."Shiko Bello Belt din Kungunshi ya Fara Warwarewa yana Fadin"sai dai ki Mutu ko..? Lalle ko zaki mutu da duka,kinga sai na Dauki gawanki na kai makarantan Bushi girl kawai.."


Zaku ga chanjin kudin Novel Daga sama zuwa kasa hakan ya faru ne bisa Roko da kuma korafin wasu Daga cikin Fans dinmu,na cewa ana cikin wani hali na rashin kudi ne Duba da Kaddaran wannan yanayin Da Allah ya aikomana Shiyasa muka zauna muka ga ya kamata mu Duba ku Domin ko bakomai kun Nuna mana Hallacci da kuma kara wajen Siyan Duka Novels dinmu Muna godiya sosai Allah ya saka da alheri Ameen






*How to pay....â‚?200 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?400...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*




_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �350 ne,VIP �600, Single one �200 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_




*ANITHA..*


 Â
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_


*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_�
   Â
      *🅿�10*


""Daada ce tayi Saurin Rikemai Hannu Tana Fadin"Kul karka Tabata...Ka barta Taji da Abunda ke Damunta yarinyarnan tace batason makrantan nan Bello mezai Hana ku kyaleta Tunda ba Mkarantan Shiga Aljanna bace.


Tafada Cikin Fushi,Bello ya kalleta kafin ya maida Kallonsa kan Aneesa Dake kara Saka Ihu Tana wani Fizge Fizge kafin yace"Dama so take akyaleta ta Dinga zama kara zube ba karatu,Ammh ta iya Rashin kunya ko..?toh Wlh bari kiji In kinga baki Tafi mkranta gobe ba,kin mutu ne kafin gari ya waye Abunda zai Dakatar Dani Kenan.."Yana gama Fadin Haka yayi kwafa bayan yaja Hannun Uncle Aminu Suka Fice Daga Falon Daada Ta bisu da kallon Mamaki da Al"ajabin Zuciya irinta Bello.


Cikin Sigan Lallashi Ta Isa ga Aneesan Tana Fadin"Tashi Anee bar Kukan hakanan,Megidan nawa ne In yayi mgana baya Chanzata sai dai kiyi Hakuri kawai.."Aneesa Tatashi Zaune Tana Share Kwallah Cikin Tura baki Da bata rai Tace"Ni bazan Je ba Daada..Ko za"a kasheni bana so akyaleni..."Tafada tana Shure Shure da kafanta kamar Wata Yarinya.


Shuru Daada Tayi mata Tana Binta da Kallo bata samu Zarafin Mgana ba Anty Rahila ta Shigo Ganin Aneesa Kwance kasa Tana Kuka Harda Majina yasa Tasan Kwanan Zencen Domin Kafin Shigowarta Sun Hadu dasu Bello Tsuke Fuska tayi ta karisa Gaban Aneesa Bayanta Hibba ne Cikin Haushi Tace"Meye Haka Aneesa..? Dallah tashi kibama Mutane Waje karatu fa zaki Tafi ba Wani Waje ba,Ammh kin Zauna kina ma Mutane kukan Banza.."Aneesa bata Saurareta ba sai ma kara saka Kuka Datayi,Ran Anty Rahila ya baci Ta kalli Daada Tana Fadin"shikenan Karki Fasa Don Ubanki,Ya Ali zan kira na Sanarmawa Daga za"a Taimake ki zama Mai ilimi ko wa kika ga yana zama ba Ilimi.."Tafada tana Juyawa Da Sauri Daada Tace"A"a Rahila Karki Kirashi Kyaleta Zata Hakura.."Da Sauri Aneesa Tace"Wlh bazan Hakura ba..Ni bazan Koma Ba Sai dai ko In Ya Alin yazo ya Kasheni.."Tafada Tana kara sakin kuka yiyiiii..


Takaichi Ya kama Anty Rahila takalli Aneesa Tace"Toh Wlh bazan zauna Dake ba Tunda kika ki Makranta sai dai ki koma Borno Kuwa.."Tura Baki Aneesa Tayi kafin Tace"Ba inda zani Wlh Ina gidan nan.."Tsaki Anty Rahila Taja kafin tace"Baki isa ba...Tunda bakison karatu Toh Borno zaki koma Ya Ali ya samu Wani ya Aura miki Shi Tunda Kika ki Karatu Dole ki zauna zaman Aure..."


Kara Mikewa Zaune Aneesa Tayi Idanuwanta Duka Awaje Tace"Aure Kuma Anty Rahila..? Hararanta Tayi kafin tace"Eh Indai bazaki Koma Mkranta ba Toh Tabbas Aure Ya Ali zai miki kin manta mganarshi Ta karshe..."Shuru Aneesa Tayi Tana Kifkifta ido Daada na kallonta kamar Tayi Dariya sai ta kanne Cikin Hawaye Aneesa Tace"Ni bazan yi Aure ba.."Tafada Cikin Tsawa Zakuda Kafada Anty Rahila Tayi kafin tace"Toh ki zabi Daya ko karatu ko Aure.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Mike Tana Fadin"Ni dai Wlh An Cuceni Allah ya sakamin.."Tafada kafin ta Zura da Gudu Zuwa Cikin Bedroom dinta Tana Kuka Daga Daada Har Anty Rahila Dariya Suka Kwashe Dashi kafin Anty Rahila ta Fice Tana Fatan Allah ya kara Shirya Aneesa.


Anty Rahila na Komawa Dakinta Ta Iske Missed call din Anty Nafee,Nan take ta bi bayan Kiranta nan Suka gaisa Shine Take Tambayanta Ina ta Shigane Take ta Kiranta bata Daga ba..? Nan Anty Rahila ke bata lbrin Diramar Aneesa.


Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Kema Rahila kinso sakama kanki Damuwa ne,Ko Su Ya Ali Aneesa Ta gagaresu ballatana ke,Kawai ku Tarkato ta Tadawo Gida Tunda Taki karatu Su Ya Ali su samu wani Garaugarai Su Auramata taje chan Ta karata Tunda Bata da Mutumci.."Tafada Cike da Jin Haushin Aneesan Domin Tana Bakinciki yarda Rahilan Ta Dauki Aneesa Taso Ace Sanah Dinta Rahila ta Dauka Domin Duk Ciki batakai su Karfi ba Mijinta bai da Wani Hali Sosai.


Mirmishi Anty Rahila Tayi kafin tace"Kayya Anty Nafee,Kema kinsan Duk Wanda yama Anee Aure yanzu Wlh yajama kansa Domin karamar Bazawara zata zama,Bajin mgana take yi ba Yanzu dai Dole ta koma Makranta Bello ne Daidai da Ita.."Tafada Tana Dariya Tabe baki Anty Nafee Tayi kafin tace"Hmumm kamar Ta koma Sakara kawai ta samu gata bata sani ba,In Da ace Sanah ce kika Dauka Rahila ba Ruwanki da Damuwa kindai Santa yarinya ce mai Natsuwa kamar Uwarta Rahila.."Tafada Tana yar Dariya,Tsam Anty Rahila Tayi kafin tace"Ammh nake ga Da Aneesa da Sanah Duk Dayane Awajena Anty Nafee,Kuma karki Manta Aneesa Kanwarmu ce Auta take ga Baba kuma kafin mutuwarsa Ya bamu Amanarta ne,in muka barta tayi kukan Maraici Allah zai Tambayenmu. "


Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Toh..Toh Uwar Tsari da Mgana barni Haka,Muyi mganar dana Kiraki Saboda Ita bana Bukatar Jin Lbrin Aneesa.."Tafada kafin ta cigaba da Sanar da Ita Dalilin Kiran bata damu ba Ta saki Jiki Suka yi Mgana Sanin Halin Anty Nafee din Tun Farko bata so ta Dauki Aneesan Tama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login