Showing 63001 words to 66000 words out of 122554 words

Chapter 22 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt

26 Jan 2025

23749

Bellon ke kallonsa Tunda Suka Shigo Yake Tsiyayan Hawaye lokaci Daya Muktar ya Rumgumesa kawai ya saki Muryansa Cikin Kuka yana Fadin"Ka tashi don Allah..Bello kai kadai nake Dashi Dan"uwana Danake gani naji Dadi..Don Allah katashi Zuciyata tana Rawa in na kalleka acikin Wannan Halin Daada...Zoki gani Zokiga yadda Bellonki ya Dawo.."Yake Fada yana Sakin Shesshekan kuka.


Daada Dakyar ta saki hannun Aneensa ta karisa ga Bello da Muktar Hawaye na Zuba Cikin kwarmin idanuwanta Kallon Bello take bayan ta Hau kan gadon ta Karbi Dayan Hannunshi ta Jimke Cikin nata,Kallonta yake Cikin idanuwa,Hawayensa na Zuba Lokaci Daya Da Miyan bakinsa Hannu Daada ta saka tana Share mai gefen bakinsa Take Fadin"Innalillahi..Wa"inna illaihirraju"un..."Allah gareka muke Muka gareka zamu koma Allahuman Ajirni fi musubatihi..."Take Fada kafin itama ta kifa Hannun Bello kan Fuskarta tana kuka mai Taba Zuciya Bello kuka ya Muktar kuka Daada Kuka Aneesa ma Durkushewa Tayi tana Kuka Hakama Anty Rahila kukan Take,Sosai na Tsausauyin Bello da Makusantanshi.


Sai da Suka yi kuka mai Isarsu kana ya Muktar ya Dago ya saka Hannu yana Sharema Bello Hawaye da miyau lokaci Daya yace"Na maka alkawarin koda Zan Rasaka Duka Dukiyata zan Tashi na Nemarka lafiya Bello..Da Izinin lahi zaka warke zaka kara takawa da kafafunka Dat iz my promise.."Yafada kafin ya mike Lokaci Daya yana Share kwallah Dakin ya Fita yakoma Falo wayarsa ya Fiddo ya lalubi Dr Nura na Asibitin Murtala Aminu kano yaci Sa"a bugun Farkon ya Daga Ko gama gaisawa basuyi ba Muktar yake sanar da Dr.Nura zai kawomai Wani Emergency yanzu Cikin mamaki Dr.Nura ke Fadin"Bataliyan Sojan kasa Waye ba lafiya kuma..?


Cikin Share kwallah Muktar yace"Bello ne...Kanina ne Bello Muhammed Jikamshi.."Cikin Tashin Hankali Dr.Nura yace"Subhannallah meya sameshi..?.


ya muktar ya Hadiye Kukan Dake Cin Ranshi yace"Don"t know How to Explain Dr.Buh dai muna Tafe Dashi yanzu..? Yafada yana Jin kamar ya kara rushewa da kuka,Jin Haka yasa Dr.Nura ya amsamai asanyaye Suka yanke Kiran Dr.Nura da Muktar abokai ne Tun na yarinta Domin tare Sukayi primary sch dinsu har Zuwa matakin Secondry kuma Tare Suka Tafi kasar Chicago Hado Digree dinsa na Farko Shi Bayan sun gama ya Dawo yayi Joining din Amry,shikuma Dr.Nura yatafi kasar Malesia ya karancin Liktanci Bangaren kashi ammh.


Ya Mukrar bai koma Dakin ba sai da ya Zauna Bisa Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa ya Sharbi kuka son Ranshi Sai da yayi ya koshi kana ya Share Hawayensa ya Mike ya koma Daki Haryanzu kukan Suke Babu mai Rarrashin Wani Daada gwanin ban Tsausayi ga Tsufa da Jarabawan Allah eh mana Jarabawa ce mana Wanda bawa bai yi Tsammani ba,bai kuma bai isa ya tsallake ba


Dafa Kafadan Daada ya Muktar yayi wacce ke Faman Share ma Bello Hawaye da Miyan Dake Zuba Daga bakinsa,yace"Daada kibar kuka Hakanan Jarabawan Ubangiji ne Addu"a zamu tamai Allah ya bashi lafiya.."Daada na kallon Bello take Fadin"Dole nayi kuka Muntari Kaduba kaga Bello fa lafiyanshi kalau Aneesa Tace Jiya koma miye Cikin Dare ya sameshi Zuciyata na Bugawa ina Tunanin meya samu Bello Haka..? Ko kuma waye yama Bello Haka..? .


Tafada ta Tsiyayan Hawaye ya Muktar ya cije baki yana Fadin"Bamu sani ba Daada Wannan bayanin sai Bello ya samu lafiya,yanzu dai Asibiti zamu Wuce yanzu nagama mgana da Abokina Dr.Nura.."Gyada kai Daada Tayi kafin Tatashi Tana Share kwallah kai Tsaye Ya Muktar ya Sunkuya yana Fadin"Zan kai kai Asibiti Kaji Da yarda Allah zaka samu lafiya.."Da ido yabishi da kallo Lokaci Daya yana lumshe ido,Cak Ya Muktar ya Dago Bello ya kuma Sabashi kafadanshi Zuwa waje yana Fadin"Daada ku zauna anan Zan Tafi Asibitin dashi Abunda ke Ciki zan kira Wayar Rahila na Sanar daku.."


Kafin Daada Tayi mgana Aneesa Ta Mike tana Fadin"Don Allah Zani...Zan biku..",Take Fada Tana Hawaye Batare da Wani Tunani ba Ya Muktar ya Gyada mata kai kafin ya Fice Daga Falon ta Gudu ta bi bayanshi tana Fama da Hijabin Datayi Sallah Daada batayi gardama ba Domin Jiri take gani kartaje ta Fadi Har Waje Suka rakasu Shikanshi mallam Inuwa Daya Taimaka Suka saka Bello amota sai da ya Fitar da Kwallar,Ya muktar ya Shiga Gidan gaba Aneesa ta Zauna baya tare da Bello ta Cicccibi kansa ta Dora bisa Cinyarta Tana Shafa kanshi Hawayenta na Diga Bisa Fuskarsa,Suka Fice Daga Haraban gidan Motar tawagar Ya Muktar ta mara musu Baya.


11pm daidai Suka yi parking Afilin Asibitin Haraban Murtala Amunu kano,Kiran Dr Nura yayi Nan da nan Sai ga Nurses da Gadon marasa lafiya,Tare da Dr.Nura Tunda aka Fito da Bello Daga Motar aka Dorashi kan Gadon marasa lafiya Nurses suka Shiga gungungara sa da Gudu Aneesa na binsu Abaya Dr.Nura ke Sarke da Hannun ya Mukrar yana jin bayanin kan Ciwon bello Cikin karfin Gwiwa yace mai..


"insha Allahu i will Try my Best Naga Bello ya samu lafiya."Yafada Daidai Lokacin da Suka iso Kofar Emargency inda Aka Shiga da Bello gyada kai Muktar yayi kafin yace"Ina godiya Abokina..Allah yaasa.."Daganan Suka saki Hannun Juna Cikin Sauri da Sassarfa ya Shige Emergency Room din ya bar Ya Muktar tsaye yana Sauke Numafashi Aneesa ko Waje ta nema ta Zauna tana Share Kwallah.


Su Daada na gida Tun bayan Fitarsu Muktar suna Fama da Zullumi Ciki Zukatan su suna Fatan Allah yabama Bello lafiya.


*****


Sai wajen Karfe 4am na Asuba Dr.Nura ya Fito Daga Emergency Room,Lokaci Daya ya yafito Muktar Dake Tsaye awajen yana Safa da marwa barci ko kadan baizo idanuwansa ba gwarama Aneesa ta bingere nan Bisa Teburin Datake Zaune ammh barcin baiyi Nisa ba,Fitowar Dr.Nura yasa Ta Farka Tana ganin Ya muktar ya bi bayanshi itama ta Rufamusu Baya


Suna Shiga Office din,Aneesa Itama ta Shigo Cikin mamaki Dr.Nura ke kallon Aneesa Wacee kallo Daya zakamata ka Fahimci bata Cikin Hayyacinta,cikin mamaki yace"wannan fa tare kuke..? Gyada kai Ya Muktar yayi kafin yace"Matarsa ce.."Cikin Tsausayawa Dr.Nura yace"Ayyah...Srry Hv a sit naga kamar ma Jiri take gani.."Yafada adaidai domin Aneesa bata gani Sosai yunwace da Rashin barcin ke Dawainiya da Ita da Sauri Ta Nemi waje ta Zauna tana Sharbe kwallah Dr.Nura da Ya Muktar Suna mata kallon Tsausayi.


Shima ya Muktar kujeran ya nema ya Zauna yana Fadin"Dr ya ake ciki..? Kungane mtsalan Data Faru da Bello..? Kan Dr.Nura na Duke yana Cigaba da Rubuce Rubucensa sai Zuwa chan ya Dago yana Zare Siririn Glass din Dake idonsa yace"Agaskiyan mgana Muktar jikamshi..Mun iya bakin kokarinmu Wajen gwaje gwaje kan Bello ammh bamu gane menene mtsalan ba Duk Na"urorinmu Normal suke Nuna ma Sai dai zuwa gobe da Safe zamu Mai scaning din kugunsa da Bayansa Muga ko ta nan ne mtsalan take.."Dafe kai ya muktar yayi yana Fadin"Ya Allah..."Kawai yake fada cikin Dauke kananan Hawayensa Aneesa ma Danne kukanta take Tana kallon Ya Muktar yadda yake Dauke Hawayensa yana Cigaba da jin bayanin Dr.Nura


"Wannan Shine karon Farko da muka taba samun irin wannam Case din akawo mana patient Ba lafiya haka ammh kuma mu Dorashi kan Duka Na"u'orinmu Ammh Basu Nuna mana komai ba, Nuna mana Suke komai na Jikinshi Normal ne.."ya muktar ya Girgiza kai yana Fadin"Allah kadai ne masanin Abunda ya Faru.."Yafada Lokaci Daya yana mikewa hannu ya mikama Dr.Nura yana Fadin"Nagode Dr..Zuwa goben dai in baku gane komai ba zan mana Booking din Jirgi na Fita Dashi wani Babban Asibitin kashi Dake New Delhi India."


Mikewa Dr.Nura shima yayi yana Fadin"Insha Allahu...Ina bayanka Domin Sunfi kwararru akan Harkan abun ya shafi kashi.. Allah dai ya bashi lafiya so painfull.."


Ya muktar bai yi mgana ba illah Jinjina Hannu Da Sukayi Lokaci Daya yana cema Aneesa"Muje gida..'Dr Nura yace"Kafin ku Dawo zamu kaishi Daki na Musamman.."ok kadai yace Suka Fice Daga Office din yana gaba tana binshi abaya bai bita Zuwa gida ba,Ita kadai ya saka Inuwa Direba ya koma da Ita Shikuma ya Wuce masallacin Cikin Asibitin..


Haka Aneesa takoma gida ta iske Su Daada ba wanda ya Runtsa sunyi kuka har sun gaji ita tadaina kukan Sarari sai dai na Zucci nan ta zayyanemusu bayanin Likita sai kukan Daada ya karu,Anty Rahila na lallashinta Suna nan Zaune har Lokaci sallar Asuba tayi Aneesa batayi Wanka ba sai da Wanke kayan Bello wanda ya bata Ta Shanya Cikin bayi kana tayi Wanka da Dauro alwala ta Fito,Dukkansu bayan sun idar da sallar addu",an samun sauki ga Bello suketa jerawa,Karfe 7am na Safe Ya muktar ya kirasu awaya yana Sanar dasu an Shiga da Bellon yin Hoton kugunsa da Baya aga Abunda Sakamako ya Fita Ammh Bello dai yana nan yadda Suka kawoshi babu Abunda ya Chanza.


Kafin Rana tayi lbrin Abunda ya Faru da Bello ya karade Dangi Daada Har waya tayi Chan Adamawa ta sanar musu Hakama Anty Rahila ta kira Borno ta sanarmusu Halin da Ake Ciki Shima Ya Muktar Daga barayinsa kuma Shi ya kira Su Abba kabiru ya sanar dasu Abunda ke Faruwa,Kowa yaji sai Abun ya Dafashi Sosai Wani Abun Tsausayin ma basu sai Wanda Suka zo suka ganshi.


Kwana biyu Bello yana Asibitin Murtala Duka sakamakon Hoton da Akayimai Sun Fito ammh kuma Babu Abunda ya Nuna Wani mtsala ya Faru da Bello kugunsa lafiya lau haka bayanshi,Ammh kuma ya na nan yadda Suka kawoshi Nurses ke kula dashi Zuwan wannan Lokaci Daga Daadan Har Anty Rahila da Aneesa Sun fige sun gama ramewa Saboda Zullumi Tuni kuma lbrin Halin da Bello ke Ciki ta kai kunnen Hukumar Jami"ar Bayero Universty,Daga Dalibai har malamai Haka Suke Taruruwan Zuwa ganinsa Duk da ba"a bari a Shiga agansa sai dai ta glass jikin Kofar,duk wanda yazo haka yake Fita da Kuka in yaga Mr bello Cikin Wannan Halin Wai The young Teacher kwance yana Kashi da Fitsari duk Akwance baya iya Tsinanamai kanshi komai ,ko wanda baisanshi ba in ya samu lbrinsa sai ya Zubarmai da kwallah


Arana ta Uku ne Su Abba kabiru suka zo Asibitin Shida Abba garba da ya hashim Suma sun Tsausayama Halin dq Bello yake Ciki sosai kuma sun goyi bayan Fita Dashi kasar Waje,acikin ransu basu taba kawo a ransu suna Dansu na da alaqa da Cutar bello ba,Tun Asafiyar Ranar Muktar ya gama musu booking din jirgin da zai kwashesu zuwa Kasar india,Washegari kuma su ya Ali Suka zo suma Wayyo Sai da Suka Zubarma Bello kwallah,saboda Tsausayi Ga Muktar Shima Daya Zabge Lokaci Daya saboda Damuwa basu Tafi ba Sai Washe garin Ranar da su ya muktar Suka Lula Kasar India,ya muktar ya Sunusi Daada,Aneesa,Anty Rahila,Junior da Hibba sai Ya hashim Daya bisu Sai Fatan Allah yasa adace.


Ki biya ki karanta cikin Salama.


*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_




*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty�_


*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*


      *🅿�22*


*INDIA*
_New Delhi_


Suna Sauka Ababban Filin Saukan Jirage na Kasar India New Delhi,Motar Babban Asibitin kashi na kasar Wato *FORTIS HOSPITAL NEW DELHI* Asibitin da Aka kawo *CAPTAIN ALIYU ABDULNASEER TAMBARI BUZU* (Littafin ALIYU GADANGA).


 Already dama Tun Suna kano Dr.Nura ya Turamusu Dukkan Wasu Bayanan Gwaje gwajen da Suka ma Bello zuwa asibitin Bayan sunyi magana Da babban Likitan kashi na Asibitin Dr Khabirkhan ba Idiyan Likita ne wanda ya karanci Shashen kashi,Hatta Da hotel din da Zasu sauka Sai da Dr.Nura yayi musu booking.


Suna Zuwa cikin Asibitin Dr.Khabirkhan ya karbesu Hannu Bibbiyu nan da nan aka Shiga da Bello Zuwa Cikin Dakin Bincike Duk da bayanan da Dr Nura ya Turomishi ta Email dinsu dokar asibiti ne kuma da Tsarin aiki Daga Barayinsu sai sun Sake Dorashi Bisa Na'u'rorinsu domin gano Inda mtsalar take,Nan Suka Wuni a Asibitin basu samu wani bayani ba Tunda har Zuwa Lokacin basu Fito da Bello Daga Dakin Gwaji ba


*JW MARROTT HOTEL NEW DELHI..* Suka Sauka Aneesa da Daada Dakinsu Daya ya Muktar da Anty Rahila da ya"yansu Dakinsu Daya sai Ya Hashim Da ya sunusi suma Dakinsu Daya,kowa kagani cikin damuwa Sukuku,Kamar ma Aneesa Taji lbri Wacce Duk ta Zabge Atsaye Idanuwanta Sunyi Zuru zuru ga Rashin barci ga Damuwa kukan kam sai na Zucci ta daina yin na Sarari.


****
*KADUNA*


kasim tsaye Cikin Falonshi Wayace Akunnansa yana mgana Lokaci Daya yana Daga Lemon Maltinan Dake Hannunshi yana Kurba,Lokaci daya ya saki Wata Dariya mai cike da Nishadi kafin ya Dakata yana Fadin"Wato Haruna na yarda da Aikin wannan Bokan,Kai kaji lbrin kuwa Dazu Abba Kabiru ke gayamin Duk likitocin Dake Asibitin Murtala Aminu kano Sun kasa gano mtsalan komai yanzu Haka suna India Sun Kaishi inda kwarraru Suke...Hhhh..Lalle araina nace Haka zasu je kuma Haka zasu Dawo.."


Ya karishe Fada yana kara Kecewa Da dariya kafin ya Dakata yana Sauraran Haruna Dake Fadin"Bana gayamaka ba...? Ai ko Duka asibitocin Kasashen Duniyan nan zasu zagaya dashi Wlh Haka zasu Dawo Dashi domin babu likitan da Zai iya sanin mafarin komai sai wanda ya kullashi Shi kadai zai iya warware komai.."Dariya Kasim ya sake saki kafin yace"Tun bayan Faruwan lamarin bantaba jin kaina Cikin Farinciki ba Irin na Yau...Nagode Sosai Haruna kasa na Farajin kamshin Aneesa ta kusa Zama nawa.."




Haruna yayi wata Dariyan kasaita kafin yace"Karka damu Mutumina,Kawai ka jira lokaci suna gama yawan kasashen zasu Hakura su Dawo Dashi gida nasan Daga Lokacin ko ita Aneesa bata Fara tunanin komai ba iyayenta Zasu Fara Tunanin Rabata Dashi,Domin zama da Nakashasshe sai Dole ko nace Gawa mai Rai.."Yafada yana Dariya Lokaci daya Suke Dariyan muguntan da Haruna kafin Kasim ya tsaigata da Dariyan yana Fadin"Zan so na ganshi fa..? Zan so naga idanuwan izza da takamar nashi naga yanzu yana dasu kokuwa.."


Haruna yace"Ina ai sai dai kaga Tarin kashi da Fitsari Daga Zaune mallam.."Kara saka Dariya Sukayi kamar Wasu mahaukata,sai da sukayi ya ishesu kana Kasim yace"zan Tura maka duka kudin aikin kaje ka kai mai kamika sakon godiyata garesa,saboda office yasa bazan samu zuwa ba.."


Haruna yace"No wahala karka wani Damu.."Daga Haka suka yanke Kiran Bisa Kujera Kasim ya Fada yana Sakin Dariya Lokaci Daya yana Jefar da gwangwanin maltinan Dake hannunsa Wanda yagama Shanyewa Dariya yake Cike da Nishadi kafin ya Saki Mirmishi yana Shafa Sajensa yana Fadin"Aneesa kin kusa Dawo gareni Dama ke din Tawa ce Ni kadai..",yake fada yana kara sakin Wani mirmishi mai cike da Ma"anoni.....


****
_New Delhi_


Kwanansu uku kenan da zuwa kasar ammh haryanzu Dr khabir khan bai musu wani bayani ba Kuma Har Tsawon Wadanan kwanakin Bello na Cikin Dakin gwaje gwaje ba'a fito dashi ba saboda abunda ya matukar basu mamaki yadda duk sakamakon gwaje gwajen Dake Fitowa,Normal babu mtsalan Komai Shine Abunda yake basu mamaki ga Bello yana nan Jiya iyau abinci ma sai Cikin Ruwan Alluran dasuke Sakamai ne yake samun Karfin Jiki.


Akwana na Hudu ne Dr kabir khan ya kira ya Muktar Da ya Sunusi Da ya Hashim Zuwa Cikin Offce dinsu yana kora musu jawabin Sakamakon gwajen gwajen da Suka ma Duk wasu kasusuwan Bello Dake da alhakin Tashinshi ko Tsayuwarshi Haka bangaren Mganarsa ma Hatta Hotoon kansa da kwakwalawarsa sai da Sukayi ammh komai Normal yake Nuna musu.


Bayani yake musu Lokaci Daya yana Nuna musu gwajen gwajen Hotunan,ya muktar Daya Shiga wani yanayi Cikin Harshen Turanci yace"Dr bawani Taimako da zaku mana ne ,?nan ne kadai Hop dinmu.."Shuru Dr khabir khan yayi kafin yace"agaskiya bazai iya cewa komai ba yanzu Ammh mganar gaskiya Wannan ne Karo na Farko da Suka samu Irin wannan case din sai dai zasu jaraba sanyashi cikin Wasu Injina Na Tsawon Wata Daya Sukagani in Har Bai tashi ba zasu koma bangaren kashi toh gaskiya indai Duk Hakan bai sa ya tashi ba Toh basu da wani Abunda zasu ma Bello.."Hankalinsu Duk ya Tashi Sosai Da jin wannan bayani Cikin Daukewar Hawaye Muktar yace"ajaraba agani Insha Allahu inaji ajikinsa Bello zai Tashi.."Da wannan Shawaran Suka Rufe Tattaunawansu,sai kuma Ranar ne aka Fito da Bello Daga dakin gwaji zuwa dakin matakin Farko,Ba"a barsu sun Shiga ba ammh daga bakin kofar suna iya Hangensa ta Cikin galisan Wajen,Aneesa Ranar da kuka Wiwi Suka koma Masauki Saboda yadda aka sanya Bello Cikin Wani Inji mai Jijjigar da Jikin Mutum,Daada kuwa ta koka ta koka kamar Ranta Zai Fita Duk ta Zabge ta rame kamar ba Ita ba Wani Abun Tsausayin ma Mai Rai kwance ba mgana ba motsi sai dai Numfashi,rai mai alfarma kawai ammh kowani bawa yaga Halin da Bello ke Ciki sai ya Koka mai.


Kullum sai dai suzo su lekasa su koma Aneesa sai tafi awa Daya Tsaye tana kallonsa tana Share kwallah Ranar da Suka Cika Sati da Zuwa Ya Sunusi da ya Hashim suka barsu anan suka koma Nageria cike da Fatan samun lafiya ga Bello,Ya muktar kuwa da Anty Rahila sai da Sukayi Sati Uku kana Suka koma Shida Yara saboda mkranta da kuma Aiki aka bar Daada da Aneesa Wajen Bello wanda sai yayi Wata Daya Cikin Wannan Na"uran injin din kana Za"a Fito dashi asake sabon Gwaje gwaje.


Shikanshi Ya Muktar din yana Nageria ne ammh Zuciyarsa gabadaya suna india kafin Tahowarasu ya Siyama Aneesa Waya saboda jin Halin da Suke Ciki kullun dai Jiya iyau Kullum Ya Muktar Cikin Waya Suke da Dr Khan Amsa Daya ne,Sai wa"adi ya cika Kana za su sake Gwaji suga ko ansamu Cigaba,Kullum baya barcin kirki Salloli yake da addu"an Allah ya Tashi kafadun Bello,mutane Dadama sunzo har gidan Yimai jajen Abunda ya Faru Duka iyalan Abba kabiru da na Abba garba mama Sahura da Umma Zulfa da Zubaida wanda kowacce Dataj lbrin Abunda ya Faru da Bello sai da ta girgiza Cikin Zuciyar iyayensu kuwa Hamdala Suke Da ba wacce Ya Auri yarta da yanzu an sakasu Acikin Wahala Umma Harda cema Anty Rahila Aneesa ne Abun Tsausayi Da kuruciyarta Zata kare da Aikin gaton kwance Anty Rahila dai bata tanka mata ba Saboda Ta gane inda ta Dosa,Hatta Inna Rukayyah Daga kano tazo,ta kwana biyu ta koma,Shikanshi Kasim ya kira Ya Muktar awaya yana mai jaje harda Nuna Tsausayi Kamar na Allah Nan ko yana kashe Wayar yayi ta Dariya.


Mutanen Borno Kuwa Ya Ali yazo Shida Anty Nafee,sunyi kwana Daya Suka koma,bayan suma Anty Yagana tazo gwanin ban Tsausayi ba wacce suke Tsausayamawa Irin Aneesa Tana karamar yarinya ta Hadu da Jarabta Rayuwa.,Kawayen Aneesa Kuwa B.kaita ce Taji Aneesa Shuru sai ta kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login