Showing 81001 words to 84000 words out of 122554 words
Chapter 28 - MR. BELLO Complete Book Hausa Novels by Janafty .txt
hannun nashi Dayake mikomin cikin hawaye nace"Kalli fa..ka daga hannunka..."Nafada cikin mamaki yana Rike hannun Shima kallona yake yana kuma bin Hannun nashi da kallo,Gudu na kwasa zan Fita muka ci karo da modibbo yaji ihu na ya Fito cikin Tashin hankali yace"Matar baffale lafiya naji kamar ihunki.?
Ina Haki ga hawaye afuskata nake Fadin"Kalli modibbo ya yi motsi da hannunshi harma ya Daga,duba kagani.."take fada tana nunamai hannun Bello wanda haryanzu yake ta motsi dashi cikin Farinciki da Sauri ya karisa garesa yana Fadin"Allah mai iko..Wlh da gaske. Kuwa..! Yafada cikin murna da Dariya Bansan sanda na isa kusa dashi na Fada jikinsa na Rumgumeshi ina Murna kamar amafarki naji ya saka hannunsa guda dayan ya Rumgume bayana dashi,saboda Farinciki bansan Lokacin dana kai bakina saman bakinshi namai sumba mai tsawo ko modibbo banji kunya ba Shiko cikin Farinciki ya shiga turamu nida shi Saman Wheelchair din yana Dariya har zuwa falo.
Nida Modibbo akasa rasa wayafi wani rawan jiki wajen kiran Waya,ni Daada na fara kirana ina murna ina gayamata shi kuma Modibbo Ya muktar ya kira ya Fadamai gabadaya lbrinmu ya Sanyaya musu rai,haka Ya muktar ya kira modibbo Video call,bayan ya koma gida suka hadu dasu Daada suka gani suka Tabbatar,Farinciki ya cika zuciyar Daada Data ya muktar sai da sukayi kwallah lalle mai Rai kar ya cire hop,shi kuma Bello Ranar Wuni yayi Daga hannu yana Tunanin kamar in ya maida zai koma ya kwanta kamar baya,Allah Sarki....
Ki biya ki karanta cikin Salama...
*Anitha...*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_
*Wattpad:Janafnancy13*
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*
    *🅿�28*
Ashe haka kowacce mace takejin Farinciki in Wani Abun cigaba ya samu mijinta,Hakance ta faru dani domin nafi kowa murna nice lbri har Borno na kira su Mama yana ina sanar dasu suma sunyi murna Mama falmata ta sake bani Shawaran na Dage kar na Nuna gajiyawata da Kula da Bello Watarana zai mike ya taka da kafafunsa kamar bai taba irin wannan ciwon ba...
Hakama Daada cikin Farinciki tayi waya chan Adamawa tana Labartama Baffa Hardo cigaban da aka samu shima yana Nuna Tsantsan Murnan,kuma yace acigaba kar afasa,shima yana nan yana tayasu da addu'an Allah ya karya koma menene,saboda jin dadi Kwana uku da Faruwar Haka sai ga Ya muktar dasu Daada sunzo,Sunga ko Abun mamaki Domin Yana iya Rike abu mara da Nauyi da Hannun,Har Junior dake hannuna sai da ya rikemai hannu Muko gabadaya Farinciki yaki barin Zukatanmu nan suka kwana sai washegari suka koma Abuja Sunbar Hibba agida saboda Makranta wajen Jummai.
Ganin irin Cigaban da Aka samu ne ya sanyani na Dage da Karatun Qur"anin da nake mana Duk Dare kafin mu kwanta bayan Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko Daga Adamawa nima ina yin nawa na Tofe da Addu"o'i na bashi yasha kuma na Shafemai duka Jikinsa Safe da rana da yammah,Fatana kawai Watarana Naga Mijina ya mike da kafafunsa kamar kowani Namiji mai Cikar zati da Haiba.
Samuwar lafiyan Hannunsa Guda Daya sai yabashi wani karfi,ko Wucewa nazo yi ta gabanshi yanzu zai saka hannu ya jawoni na Fada kan cinyarsa ya saka hannu ya zagayo dashi Daga bayana yana Kallona domin na lura har karkacewar kan daya keyi yanzu ya Rage hakama Zubar da miyau sai mu Wuni kansa bai karkace ba,Ko wanka nake mai ina kokarin kauda kai bana so mu hada ido ammh sai ya Shammace ni ya Fizgoni na Fada Jikinsa,ya Kuramin ido yana kallona Ni kuma Duk kunya sai ta kamani na Dinga Hararansa ina Turamai baki.
Yana kokarin taimaka min in zan Rikosa,sai ya rikeni da hannu Daya wani lokacin in na Dafa bango mu iya tsayawa in ko ban Dafa ba sai mu tafi kasa,nafadamai ni dashi muna Haki,Duk lokacin da Na tsinci kaina bisa kirjin Bello sai na samu kaina cikin wani Farinciki mai girma wanda baya wuce misali,Yanzu salon daya koya da daddare in zamu kwanta bayan nagama shafemai jiki da ruwam zamzam sai yarike hannuna gam,yana kallona ya nace sai na saka idanuwana cikin nashi wanda suke kashemin jiki na Fada jikinsa bansani,Haka zan lafe bisa kirjinsa ina jin Bugun Numfashi,Zuciyata na bugawa,Haka zai sanya Hannun sa mai lafiya ya zagayo Kuguna Dashi,kawai shi dai yajini cikin Jikinsa yana sanyanshi Natsuwa sosai ni kuwa Bugawar Zuciya yake sani jikina ya mutu..Gabadaya na kasa katabuka komai kamar mara lafiya.
Tun bayan Hannunsa Guda Daya Fara samuwa,babu kuma inda Shima yamotsa bayan Hannu,muna dai cigaba da gayama Allah,jidda ta cika alkwari munyi waya da ita tazo kuma har gida tare da mijin da zata Aura basu dade ba suka Tafi bayan ta kawo mana kayan ciye,ciye dama Tun Ranar da mukayi fada da yan matanan na Shopprite ban kara marmarin komawa ba Ko Raihana da Modibbo sunce bazamu Fita bane,sai na Daure Fuska nace bazamu kara Fita ba in zasu ne su daawo lafiya Duk ko naga Bello na jin Dadi in muka Fita niko na Dakile Haka saboda basai mun Fitan bane balle har Wata mace ta ganshi ta yaba ko kuma tace mai baida Mamora ba Shidai sai dai ya kalleni kawai cikin Ransa yana Mirmishin komai na Aneesa bai chanza ba.
****
*KATSINA*
Tun last Week Kasim ke gida,Yana Hutun karshen Shekara wato Annual Leave kenan,har kuma Zuwa wannan Lokacin bawai kasim ya Daina Neman matanshi bane da Shaye shaye a"a sai ma Abunda yayi gaba Shiyasa bai cika zuwa katsina ba saboda baya samun yarda yake so..yafi jin dadin Rayuwarsa Abariki kaduna.
Neman matan nasa ma ya karu ne bayan ya rasa Aneesa wacce ko Da Rana daya Sonta bai ta Fita Daga Ranshi ba,yana jin Duk Duniya in bai Dandani Zumar Aneesa ba bakinciki da Sha"awarta zasu iya kasheshi,yan mata kuwa Da inda yaga Baka doguwa shikean kuma Zai tayaki dakin sallama Shikenan in kuma suna cikin Harkan ne sai ya fara kiran sunan Aneesa yana ihu kamar mahaukaci Yanmatan Shashancin nashi suna matukar mamaki wacece wannan Aneeesa da Kasim yake kiran sunanta in suna Tare,shi kuwa sai in ya gwada su da Aneesa ne ma yake samun jin Dadi ammh in ba Haka ba ko alama Zuciyarsa basu kawomasa jin dadi da kowacce mace sai Aneesa.
Cikin Lokacin ne ya Hadu da Wata Aisha Maiduguri,Saboda yanayinta da Aneesa gasu kuma yan gari Daya ya sanya Suka Dinke itama karatu tazo nan kasu,tabi Rudin Duniya ta lalace Duk Soyayyar kasim din ne ta Rinjayeta atakaice ma Shine ya Fara saninta amace bayan ya mata alkawarin zai aureta,Haduwarsa da Aisha yasanya take debemai kewar Aneesa Domin suna da yanayin Tsarin Halitta hatta bakinsu Kuma itama cikakkakiyar kanuri ce,Agidanshi ma take da zama suna Sheke ayarsu karatu kuma sai tayi sati bata shiga cikin makaranta ba Allah ne ya Doramata soyayyar Kasim Acikin Ranta mai zafi wanda takejin in babu shi bazata iya rayuwa ba,saboda ita baya son zuwa gida yan zuma hutu suka samu Dakyar ya lallaba ta tafi gida akan zai zo insha Allahu,shiyasa tatafi shi kuma yazo gida ammh cikin ranshi baya jin zai iya Auran Wata mace bayan Aneesa wanda duk kwakwan Aisha ta kasa gano wacece Aneesa Awajen kasim abunda ke bata mamaki ko giyanshi yasha ya bugu har ya Dawo hayyacinsa yana kallonta amatsayin Aneesa ne,in ko suna Masha'arsu Ya dinga Kiranta Aneesa kenan abun na damunta in kuma ta tambayeshi baya gayamata,alhalin kuma hatta Fuskar wayarsa Hoton Aneesa ne Ko Haruna Dayake abokinsa tayi tayi ya Sanar da ita yaki saboda Kasim bai bashi da damar Haka ba tasha yin Fushi da Bar gidan ta koma mkranta ammh kasim baya Damuwa da kanta take gajiya ta dawo kalmar Daya yake yagamata albarkacin Aneesa take ci in ba haka da yanzu ya Rabu da ita jin haka yasa ta Shiga Taitayinta domin bazata jure ganin Rabuwarta da kasim ba,Tunda ta lura ma kamar Aneesa bata kusa dashi sai take kokarin Danne kishinta akan Aneesa kodon ta samu cikar Burinta.
Wannan karon ne ya yi niyyar Zuwa gidan Ya muktar ya Duba Bello kuma yaga Aneesa bawai don Abba kabiru ya matsamai ba sai domin yana son ya kara Tozali da Aneesar bayan Kwashe Shekara bai saka ta cikin idanuwansa,Su Abba kabiru bama su san Bello ya koma kano sun koma kano ba Duk da shi Kasim yana da lbrin komai toh bazuwa sukeyi ba,Dama saboda Zullumin Bello ne toh yanzu basu da wani mtsala da hakan,Gabadaya ma Dukiyar da suka hamdama ta kare dama kanfani Daya ne ya Rage shima bashi ya saka sun saidashi batare da sunga ma wanda ya siya kamfanin ba.
*****
Da yammah ya Shirya cikin Riga da wando black and White na kamfanin DKNY,ya tafi gidan Ya Muktar koda yaje bai sameshi ba sai dai Anty Rahila duk da yasan Su Bello basu agidan,sai ya zauna suka gaisa da Anty Rahila cikin Hikima ya Hillaceta da cewa yazo gaida Bello ne sai tace ai suna kano ya nuna jimami sosai nan take yace ta bashi Addreess din gidan nasu dake kano bata kawo komai acikin Ranta ba ta bashi bai jima ba yatafi ko Shashen Daada bai shiga ba,yana Sauri harda bata 5k ta bama Junior ta karba tana ta godiya duk da tafi karfin Haka ammh alheri nada Dadi.
Yana cikin mota yana Dariya Shikadai cikin Muryan Tsausayi yake Fadin"Aneesa...Ban so nayi miki Haka ba,buh ammh ke kika Nuna Taurin kai kinki gane Cewa Nine mai sonki har Abada kika zabi ki Zauna da nakashasshe Saboda Taurin kanki..Zan Ji dadi Dake kuma agaban idanuwanshi ina Fatan Hakan yayi sanadiyar Bugawar Numfashi ya mutu...Ki zama tawa har Abada."Yafada Idanuwansa na kadawa Lokaci Daya kuma ya kece Da Dariya kamar mahaukaci yana Buga Sitiyarin Mota.
****
Yau Tunda na tashi najini bana jin Dadi ganinan ne dai ban gane kaina ba,Dakyar na iya mana Breafsat,Tun safe Modibbo baya nan ya fita Jugging ni na saka mayafi na kaima Salihu maigadi na Shi na Dawo cikin gida,Bello kadai nayi ma wanka na gyarashi ni kuwa kaina ne yamin Nauyi Sosai,Lokaci Bayan Lokaci kuma gabana sai ya Dinga faduwa
Muna cikin bedroom dinmu Ina Zaune Bisa gado shi kuma yana Gabana Bisa Wheelchair dinsa ina bashi Soyayyen Arish din dana mana da kwai ina Hadamai da Kofin Tea din dake hannuna,Tun da muka tashi ya lura bana walwala kamar bana jin Dadi yana ta nacin kallona ni kuma bana so ya Fahimci wani Abu yanzu nan duk zai Shiga damuwa.
Kofin tea din na Kai bakinshi da Sauri ya saka hannunshi mai lafiya ya Rike min hannu Lokaci Daya yana kallona ,Marairaicewa nayi kafin nace"Kasha mana..? Ko ka koshi ne..? Bai min wata alama ba illah ido kadai Daya sakarmin ganin Haka sai na zame hannuna na Dauki Kofin Tea din da Filet din Dankali na Fita Dashi Zuwa kichen na Dawo,Ina Shigowa jiki na rawa na Nufi gado jin Kaina kamar zai Zage gida biyu na Fada ina Sauke Numfashi cikin damuwa yake bina da kallo yana so ya tambaye ni meke damuna ammh kuma bashi da baki tasani kadai yayi yana ta kallona..
Ganin kwanciya bazai min bane ya sa na tashi ina Rangaji na Bude Side drower din gadon na Dauko Pracetamol na balla guda biyu na Sha da Ruwan zam-zam Din Bello Dake saman Side drower din gadon na koma na kwanta ina Runtse dafe da kaina Lokaci Daya naji ya Sauke Ajiyar Zuciya Dagowa nayi ina kallonsa Cikin Fitar hawaye nace"Kaina...ke ciwo B.love.." Dama Haka nake cemai,Ido ya sake kuramin yana kallona cikin Zuciyarsa yana Fatan Allah sa ba aljanun dana kwaso amkaratan bane suke neman taso min,ina nan kwance ina juye juye kaina kamar zai tsage gida biyu,Kuka nake ahankali lokaci Daya ina Salati Ya Shiga damuwa da Hannun Dayan ya ke Danna Abun kekensa ya Shiga Turashi Zuwa gaban gadon Danike sai dai ji nayi ya Dora hannunsa Bisa goshina da Sauri na Dago kaina Jajur ina kallonsa kamar wata mayya,shi kuwa cikin Zuciyarsa yake karantamin addu"a,Cikin ikon Allah sai naji ya Fara Sauka natsuwata na Dawo wa jikina Zufa na ketomin ko ta ko"ina Hannunsa na Rike ina kallonsa Hawaye na bin gefen Kumatuna nace"Nagode garkuwata..."Lokaci Daya kawai naga ya sakarmin mirmishi har Kumatunsa ya lotsa da Sauri na mike Zaune har ina Bige masa kafa na tallafi kumatunsa na Duka hannayena Guda biyu ina Fadin"Kaga mai kayi..?Mirmishi fa kamin.? Sau biyu kenan kataba min mirmishi Don Allah karamin nagani.."Tafada Lokaci Daya hawaye na Zubomin.
Kallona yayi kafin ya saka hannunsa yana gogemin kwallah Zuwa Saman goshina yana Sharemin Zufa,Kaina na lamgwabe ina kallonsa wani madaran kaunarsa na kara shiga Raina hannunsa na riko na Sumbata Lokaci Daya na matse Bisa Kirjina ina lumshe ido Zuru yayimin yana kallona niko cikin Raina Fadi nake I love u B.love..."
Ban bude ido ba na,kara Sulalewa na kwantar dakaina Bisa Filo ina Rumgume da Hannunsa,Shikuma bai cire ba illah ido Daya sakarmin Cikin kankanin Lokaci barci yayi Nasaran kwasheni,Yana zaune yana kallona kuma bai yi yunkuri cire hannunsa dana Nannade bisa Kirjina.
Barcin mai yi wani Nisa ba Na tashi sai lokacin naji kunya ganin yadda na matse mai Hannu,Tashi nayi ina Kauda ido kar mu hada ido Shiko ajiyar ya Sauke ganin namike garau na Fada Tiolet,wanka nayi na Fito,ganinshi Zaune yana kallona yasa na Isa gabanshi na Dauko karamin Qur"ani na Budemai Suratul Bakara na saka mai ahannunshi ina Fadin"Karanta kafin na Shirya kaji..? Bai min gaddaama ba ya karba aransa yana mamakin wai zan mai wayau kar ya kalleni,Ina Shafa mai ina kallonsa ta Wutsiyar ido shikuma sai ya maida kansa ya Jingina da Wheelchair dinsa kamar yana karatunsa Harda mai da kai gefe ganin Haka yasa na Dauko kayana na saka Riga da Sikat na Less mai kalan Blue da Pick,ina Tunanin hankalinsa na wajen karatu Ashe Duk Abun da nake yana kallona sai zan Dago kai sai ya sauke idanuwansa kasa kamar bani yake kallo ba.
Sai da na gama Shiryawa tsab nayi irin Daurin Zahra buhari na Daure gashina da Band,wanda Raihana ta matsamin mukaje aka Gyaramin Kaina,nayi kyau sosai Harda jan baki na Shafa da kwalli bayan na gama na juya ta gabanshi ina Fadin"ya kagani...?Nayi kyau..?kuri yayimin da ido Lokaci Daya naga idanuwansa sun chanza launi Kasa yayi da idanuwan nasa yana mikamin Qur"anin Hannunsa da Sauri na karba,Na maidashi mazauninshi ina Fadin"Ko ka nuna alamun nayi kyau kuma fa wa kai nayi mawa kaima kaji kanka amatsayin Namiji da matarka zata maka kwalliya kagani...."Ban gama mitana ba naji ya saka Hannu ya Fizgoni na Fado Kan Jikinsa,.
yarr."Naji lokacin Daya Rike kuguna da Dayan Hannunsa Dagowa nayi,Ina kallonsa Lokaci Daya hancinmu na haduwa waje Daya,cikin idanuwan nake kallo Shi kuma yana kallona cikin wani Shauki,Lumshe idanuwan yayi ya kara matsoni sosai ni kuma na lafe ina Sauke Jiyar Zuciya bayan na saka hannuna na Dafe kirjinsa Bansan Lokacin Dana Fara Shafa kirjinsa ba Cikin wani Salo,lokaci Daya ina kallonsa Idanuwansa ya lumshe yana maida Numfashi sama sama,bakinsa ya Karkato kaina,Hancinsa na Fitar da Hucin Numfashinsa cikin Wani Shauki da bansan ni Aneesa ina da Shi ba kawai naji lebena saman lebenshi na Dora Lokaci Daya ina kallon kyakyawan Fuskarsa.
Mun Dade Ahaka batare da Nayi yinkurin yimai wani Abu ba Shi kuwa Jira kawai yaji na Fara Sumbutar lebensa Tunda shi bazai iya Sarrafa bakina ba Ganin yadda naga Zuciyarsa na bugawa yasa nayi Saurin Kwace Jikina na Tashi Daga kan jikinsa Lokaci Daya kuma naji Muryan Raihana na kirana Daga Falo Ajiyar Zuciya na Sauke ina Kallonsa Lokaci Daya ina Tura baki,Zuwa nayi gabanshi ina Hararanshi ban Lura da jan baki Dana Shafamai saman kumatunsa ba,da kuma saman lebensa,na Shiga Turasa Zuwa Falo.
Muma Fitowa Naga Raihana Zaune Bisa Cafet suna karyawa Ita da Modibbo baki na Rike ina kallonsu cikin Dariya Suke gaisheni Harara na sakarma Raihana bayan na kai Bello gaban Kujera mai zaman mutum biyu na Koma na Zauna bayan na juyashi yana kallon Modibo.
Raihana ta Shagwabe tana Fadin"Ya modibbo wai me nayi ma Amaryan gidan ne take ta Harara ta Tun Dazu..? tafada tana Dariya yana Tura kwai cikin bakinsa yace"Ah ina zan sani Raiha..Kila Haushi Takeji Suna cikin Soyewarsu da Baffale kika katsesu.."Yafada yana kallon Bello yana Dariya kasa kasa.
Itama Sai Lokacin ta Lura da Jambakin Daya bata ma Bello Fuska Kallon Juna Sukayi suka kara saka Dariya na Harzuka na mike ina Hararan su cikin Bata Rai nace"Eh din,wai ku lafiyanku kuwa kuna ta dariya kamar wasu Shashashun madina.."Raihana ce tace"Gani mukayi Yau kwalliyar Ya Bello har da su jambaki ne."Sai da ta Fada na kallesa na gani sai kunya ta kamani na Rufe Fuska na Kwashi Sauri Zuwa Daki Gabana na Bugawa,Bisa gado na Fada ina Fadin"Karsu cemin wannan anyi zalamarmiya Mutum na Zaune ba lafiya ina kwakwaminsa.."Wata Zuciya tace"shifa ya kwakwumuke Aneesa.."Ido ta Runtse tana Tunanin Yanayin Lokaci daya ta saki Mirmishi ita kadai ..
Modibbo ko Da Raihana Dariya suka kara sakawa Shima Bello ido ya lumshe yana Dariya Cikin Zuciyarsa,Sai da nagama goge kunyata kana na Fito ina Hade rai kamar su karamin Wata mgana basu tankani ba sai Dariya kasa kasa,ban tankasu ba illah Littafin dana maida Hankalina ina karantawa Kwana Sittin na Sumaiyyah Abdulkadir,tun muna mkarata Nida su B.kaita muke taba karatu Dawowarmu kano da Haduwata da Raihana yasa na kara gwanancewa,ita ke siyo min in sun Fita da Modibbo,In ta karatu ina karantama Bello,Alhamdulillah ina karuwa sosai Musamman Littafan marubuta na kamar su Halima Abdullahi k/mashi da Zulaihat sani kagara,Rahma hassan Zaria,Sa"adatu waziri gombe,Sumaiyyah Abdulkadir Takori,gaskiya Yana jin dadin littafinsu su ka kara sakani na kara zama mace sosai na kara wayewa da sanin Duniya,nan ne nake kara koyon wasu girke girken,saboda karatun littafin ne nagane cewa na kamu da matsananciyar soyayyar Bello.
Tunda ni ba Whatsop nakeyi ba B.kaita tayi tayi na Bude mu dinga Haduwa Naki,Raihana,ma har Budemin tayi na goge gani nake Dana Fara Hankalina Zai Dauke Daga kula da mijina.
Raihana ta tattara komai ta kai kichen ta Wanke min Duka Abubuwan Dana bata ta gyaramin Kichen din,ta kuma Fito falo ta gyarashi tsaf ta yi mooping Ta goge Komai na Cikin gida Harda